• Contrast
    • Font
    • A
  • Sign In
  • Sign Up
    Loading ...
View All Updates Mark All Read
Bakandamiya
  • Shafin Farko
  • Makalu
    • Browse Entries
  • Bidiyoyi
    • Browse Videos
  • Sautuka
    • Nemo Sautuka
  • Hotuna
    • Browse Albums
    • Browse Photos
  • Zauruka
    • Browse Groups
  • Tambayoyi
  • Sanarwa
    • Bukukuwa Masu Zuwa
    • Past Events
  • Ra'ayoyi
    • Browse Polls
  • Sana'o'i
    • Browse Listings
  • Updates
  • About
  • Abokai(100)
  • Hotuna(1)

Updates

The post was not added to the feed. Please check your privacy settings.
  • Mustapha musa abu Aisha
    Mustapha musa abu Aisha
    { Suratul- Fãtiha }
    ‏ﻗﺎﻝ الامام اﺑﻦ ﺍﻟﻘﻴـﻢ ﺭﺣﻤـﻪ ﺍﻟﻠﻪ تعالى:
    ‏ﻭﻟﻮ ﺃﺣﺴﻦ ﺍﻟﻌﺒﺪ ﺍﻟﺘﺪﺍﻭﻱ ﺑﺎﻟﻔﺎﺗﺤﺔ ،
    ‏ﻟﺮﺃﻯ ﻟﻬﺎ ﺗﺄﺛﻴﺮﺍً...  more
    { Suratul- Fãtiha }
    ‏ﻗﺎﻝ الامام اﺑﻦ ﺍﻟﻘﻴـﻢ ﺭﺣﻤـﻪ ﺍﻟﻠﻪ تعالى:
    ‏ﻭﻟﻮ ﺃﺣﺴﻦ ﺍﻟﻌﺒﺪ ﺍﻟﺘﺪﺍﻭﻱ ﺑﺎﻟﻔﺎﺗﺤﺔ ،
    ‏ﻟﺮﺃﻯ ﻟﻬﺎ ﺗﺄﺛﻴﺮﺍً ﻋﺠﻴﺒﺎً ﻓﻲ ﺍﻟﺸﻔﺎﺀ.
    [‏📚ﺍﻟﺪﺍﺀ ﻭﺍﻟﺪﻭﺍﺀ / ٨]
    ══════ ❁✿❁ ═════
    Ibnul Qayyim (Rht) ya ce:-
    da ace mutum zai kyautata yin Mãgani da (Suratul-fãtiha) To da yaga Wani Babban Ta'asirin ban Mamaki game da Samun Waraka.
    [📚ﺍﻟﺪﺍﺀ ﻭﺍﻟﺪﻭﺍﺀ / ٨]
    ══════ ❁✿❁ ═════
    Allah yasa mu dace
    اللهم فرج هم المهمومين من المسلمين، ونفس كرب المكروبين، وقض الدين عن المدينين، وشفي مرضانا ومرضى المسلمين،  less
    • Thu at 10:35 AM
    • Amrah Auwal and Rahmatu Lawan like this.
  • Mustapha musa abu Aisha
    Mustapha musa abu Aisha
    MANYAN AIYUKAN IBADA GUDA 10 A CIKIN RAMADHANA:


    Darasi na...  more
    MANYAN AIYUKAN IBADA GUDA 10 A CIKIN RAMADHANA:


    Darasi na biyu-(2)

    *2-RAYA DAREN RAMADHANA DA IBADA*

    Manzon Allah ﷺ yana cewa:
    *(Duk wanda ya raya daren Ramadhana da ibada,yana mai Imani kuma yana mai neman ladar Allah,an gafarta masa abinda ya gabatar na zunubansa)*
    @ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻭﻣﺴﻠﻢ.

    Allah yana baiyana masa bayinsa na musamman sai ya siffantasu da raya dare da yin sallah.

    Allah yana cewa:
    *(ﻭﻋﺒﺎﺩ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﻤﺸﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﺍﻷﺭﺽ ﻫﻮﻧﺎً ﻭﺇﺫﺍ ﺧﺎﻃﺒﻬﻢ ﺍﻟﺠﺎﻫﻠﻮﻥ ﻗﺎﻟﻮﺍ ﺳﻼﻣﺎً.ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﺒﻴﺘﻮﻥ ﻟﺮﺑﻬﻢ ﺳﺠﺪﺍً ﻭﻗﻴﺎﻣﺎ‏)*
    @ﺍﻟﻔﺮﻗﺎﻥ 63 ـ 64.

    Yin sallar dare ya kasance daga cikin manyan halayen Manzon Allah ﷺ .

    Daga A’isha R.A tana cewa:
    *”Kada ku daina yin sallar Qiyamul laili domin Manzon Allah ﷺ ya kasance baya barin yin sallar dare,idan baya da Lafiya ko yana cikin nauyin jiki sai yayi sallar Azaune”*

    Umar Bin Khaddab R.A ya kasance yana yin sallar cikin dare abinda Allah ya sauwake masa,idan rabin dare yayi sai ya tayar da Iyalinsa suyi sallah,sai ya riqa karanta wannan aya:-
    *(ﻭﺃﻣﺮ ﺃﻫﻠﻚ ﺑﺎﻟﺼﻼﺓ ﻭﺍﺻﻄﺒﺮ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﻻ ﻧﺴﺄﻟﻚ ﺭﺯﻗﺎ ﻧﺤﻦ ﻧﺮﺯﻗﻚ ﻭﺍﻟﻌﺎﻗﺒﺔ ﻟﻠﺘﻘﻮﻯ)*
    @ﻃﻪ ﺍﻵﻳﺔ 132.

    Ibn Umar R.A ya kasance yana karanta wannan aya:-
    *(ﺃﻣﻦ ﻫﻮ ﻗﺎﻧﺖ ﺁﻧﺎﺀ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﺳﺎﺟﺪﺍً ﻭﻗﺎﺋﻤﺎً ﻳﺤﺬﺭ ﺍﻵﺧﺮﺓ ﻭﻳﺮﺟﻮ ﺭﺣﻤﺔ ﺭﺑﻪ)*
    @ﺍﻟﺰﻣﺮ ﺍﻵﻳﺔ 9.
    Sai yace:
    *”Wannan aya tana maganane akan Usman Dan Affan R.A”*

    Ibn Hatim yana cewa:
    “Ibn Umar R.A yana fadin hakane saboda yawan yin sallar dare na sayyadina Usman R.A,ya kasane yakan sauke alqurani acikin raka’a daya”

    Daga Alqamah Bn Qais yana cewa;Na kwana tare da Abdillahi Dan Mas’ud R.A a wani dare,sai ya tashi yake sallah cikin farkon dare,ya kasance yana yin karatu daki daki irin karatun limami acikin masallaci,har sai da dare ya rage kadan sai ya tashi yayi wutiri”

    Yana da kyau kuma sunnane ga mai Azumi ya kiyaye sallar Tarawinsa gaba daya tun daga farkon azumi har zuwa karshe,kuma yayi tare da liman a masallaci shine yafi lada.

    Saboda fadin Manzon Allah ﷺ:-
    *(Dukkan wanda yayi sallar Tarawi ko qiyamul laili tare da liman kuma ya tsaya tare da liman har aka kammala sallar,za’a rubuta masa ladar yayi sallah dukan daren baki daya)*
    @ﺭﻭﺍﻩ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﻦ.

    Allah ne mafi sani.

    Mu hadu a Darasi na gaba insha Allah.

    *Allah ka sanya mu cikin yan aljanna sanadiyyar wannan azumi na Amin*  less
    • Thu at 7:56 AM
    • Adamou Bagna Mahamane and Bakandamiya like this.
  • Mustapha musa abu Aisha
    Mustapha musa abu Aisha
    SAKO ZUWA GA MATA

    *_NASIHOHI GUDA 40 GA...  more
    SAKO ZUWA GA MATA

    *_NASIHOHI GUDA 40 GA MATA_*

    Darasi na biyy-(2).

    *6-"An hana mata su baiyana kwalliyar su da adon su lokacin fita daga gida"*.

    Daga Fudhalata Bn Ubaida R.A daga Annabi s.a.w yace:
    (Mutane ukku kada ka tambayi halin da suke ciki:-
    *_Mutumin da ya rabu da jama'a yayi tawaye ga shuganansa,har ya mutu yana mai sabawa shugabansa_*
    *_Da bawa ko baiwa da ya gudu daga wajan Ubangidansa har ya mutu_*
    *_Da matar mijinta baya nan kuma ya barma kayan abinci dana rayuwa,amma sai ta fita a bayansa tana mai baina Kwalliyarta.kada ka tambayi halin da wadan nan mutane suke ciki a gobe alqiyama)_*.
    @ﺻﺤﻴﺢ, ﺃﺧﺮﺟﻬﺎ ﺃﺣﻤﺪ ﻭﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻓﻲ ﺍﻷﺩﺏ ﺍﻟﻤﻔﺮﺩﻭﺍﻟﺤﺎﻛﻢ
    ﺍﻟﺘﺒﺮﺝ
    _TABARRUJ_
    abinda ake nufi da kalmar:
    _"TABARRUJ"_ shine mace ta bayyana kwalliya ko adonta dan maza su gane wadan da harunne suga kwalliyarta ko adonta

    *7-"Kada mace tayi tafiya ko bulaguro sai da Muharraminta"*

    Daga Ibn Abbas R.A Manzon Allah s.a.w yace:
    *(Kada mace tayi tafiya face sai da muharraminta)* sai wani mutum yace ya Manzon Allah idan zatayi ni ina son na fita da runduna kaza da kaza wajan yaki, kuma matata tanason zuwa aikin hajji?? Sai Annabi s.a.w yace:
    *(Ka tafi ka fita tare da ita zuwa wajan aikin Hajjin)*.
    @ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ.

    *8-"kada mata suriqa shiga kofar masallaci ta kofar da maza suke shiga "*.

    Wato a kebewa mata kofarsu da ban ko su su kebe kofarsu da ban a masallaci.
    Daga Nafi'u daga Ibn Umar R.A yace: Manzon Allah s.a.w yace:
    *(Da dai mun barwa mata wannan kofar su kadai)*.

    Imam Nafi'u yake cewa:
    "Daga nan Abdullahi dan umar bai sake shiga daga wannan kofar ba har ya mutu".
    @ﺣﺴﻦ ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ.

    *9-"An hana mata suriƙa tafiya a tsakiyar hanya".*
    Su koma gefen Hanya Shine yafi alkhairi a akan su.

    Daga Abi Usaid Al'ansary R.A yane cewa"Lallai naji Annabi s.a.w yana cewa alokacin fita daga Masallaci sai Maza da Mata suka chakudu akan hanya sai yace ga mata
    *(Ku dai saurara ku dakata tsakiyar hanya bata dace daku ba,kuriqa bin gefan hanya)* daga nan sai mata suka riqa bin gefan hanya da gefan katagu har tufafunsu yana taba bango".
    @ﺣﺴﻦ ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ.

    Allah ne mafi sani.

    *Mu hadu a darasi na gaba insha Allah*.  less
    • Thu at 6:12 AM
    • Mustapha musa abu Aisha, Adamou Bagna Mahamane , and Mukhtar Musa Karami Abu Hisham like this.
  • Mustapha musa abu Aisha
    Mustapha musa abu Aisha
    DAGA CIKIN KUSA-KUREN MAI SALLAH

    #DARASI NA FARKO-(1)

    #KUSKURE NA DAYA
    *1-Wasu daga cikin...  more
    DAGA CIKIN KUSA-KUREN MAI SALLAH

    #DARASI NA FARKO-(1)

    #KUSKURE NA DAYA
    *1-Wasu daga cikin masu yin sallah suna yin karatun sallah a zuci ba tare da motsa Harshen su ba,kuma suna yin hakan wajen Azk na Ruku’u da Sujada*.

    #ABINDA YAKE DAIDAI
    *{A lokacin karanta Fatiha da Sura acikin sallah wajibi ne mutum ya motsa harshen sa dan mai yin sallah ya jiyar da kansa abin da yake karantawa,sannan haka zai aikata lokacin da yake Azkr da addu’a acikin ruku’u da sujada da zaman Tahiya da makamantan su}*

    KUSKURE NA BIYU
    *2-Wasu daga cikin masu bin Liman lokacin da suka shiga masallaci Liman yana RUKU’U KO SUJADA,sai su yi KABBARA daya kadai su shiga cikin ruku’u ko sujada*

    ABIN DA YAKE DAIDAI
    Idan mutum ya shiga masallaci a lokacin da Liman yake cikin *RUKU’U ko SUJADA* zai bi liman ne da yin *KABBARORI* guda biyu kabbara ta farko tare da Niyyar itace kabbarar Harama,ta biyu kuma ta shiga ruku’u ko sujada, amma idan babu wadatar lokacin da zai yi hakan,to sai yayi kabbara guda daya wato kabbarar harama sai ya shiga ruku’u ko sujada.

    KUSKURE NA UKU
    *Rashin bayyana fadar AMEEN bayan gama Suratul Fatiha ga Mamu da Liman*

    ABIN DA YAKE DAIDAI
    Shine Liman da Mamu zasu bayyana fadar *AMEEN* bayan gama *FATIHA* acikin sallar da ake bayyana karatu.
    @ﺳﻤﺎﺣﺔ ﺍﻟﺸﻴﺦ / ﻋﺒﺪﺍﻟﻌﺰﻳﺰ ﺑﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﺑﺎﺯ ‏] ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ
    ‏@ﻓﻀﻴﻠﺔ ﺍﻟﺸﻴﺦ / ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﺻﺎﻟﺢ ﺍﻟﻌﺜﻴﻤﻴﻦ ‏] ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ
    ‏@ﻓﻀﻴﻠﺔ ﺍﻟﺸﻴﺦ / ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺠﺒﺮﻳﻦ ‏] ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ
    ‏@ﻓﻀﻴﻠﺔ ﺍﻟﺸﻴﺦ / ﺻﺎﻟﺢ ﺑﻦ ﻓﻮﺯﺍﻥ ﺍﻟﻔﻮﺯﺍﻥ ‏] ﺣﻔﻈﻪ ﺍﻟﻠﻪ
    @ﻭﺍﻟﻠﺠﻨﺔ ﺍﻟﺪﺍﺋﻤﺔ ﻟﻺﻓﺘﺎﺀ
    ﺟﺰﺍﻫﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻦ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﻭﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﺧﻴﺮ ﺍﻟﺠﺰﺍ

    Allah ne mafi sani

    Allah ya bamu ikon gyarawa,mu haɗu a Darasi na gaba insha Allah  less
    • Tue at 7:43 PM
    • Bakandamiya likes this.
  • Mustapha musa abu Aisha
    Mustapha musa abu Aisha
    ABUBUWAN DA AKE SO A YAWAITA SU A RAMADAN

    *1-Yawaita karatun Alkur’an,da tafsirnsa da kokarin sanin...  more
    ABUBUWAN DA AKE SO A YAWAITA SU A RAMADAN

    *1-Yawaita karatun Alkur’an,da tafsirnsa da kokarin sanin ma’anoninsa*

    *2-Yawaita kyauta, musamman ga ‘yan uwa da abokai da masu karamin karfi*

    *3-Sadaka da ciyar da mai azumi lokacin bude baki da lokacin sahur*

    *4*Yin sallar nafila na rana dana dare.(Tarawihi ko Tahajjudi)*

    *5-Shiga i’tikafi da yawaita ibada ta musamman*

    *6-Yawaita yi wa Annabi salati*

    *7-Yawaita neman gafara (Istigifari) da tuba da komawa zuwa ga Allah*

    *8-Zuwa wajen wa’azi da sauran darussa kamar tafsir da sauransu*

    *9-Yawaita yin tuba ga Allah da mayar da hakkin ga masu shi da nisantar sabon Allah*

    *10-Ciyar da abinci dafaffe da danye*

    *11-Kiyaye salloli akan lokaci da taimakon mahaifa*

    Sheikh Muhammad Salih al-Munajid ya fada a cikin littafinsa (As-siyam) cewa: *“Daga cikin abubuwan da ke wargaza kyawawan ayukkan mutum kuma su haifar masa da zunubai musamman a lokacin azumi,akwai kallon finafinai,da wasanni, da sharholiya,da zuwa wajen taro mara anfani,da zama a kan kwalbati ko kan hanyar jama’a, da yawo a mota ko mashin a cikin gari ba tare da dalilin da shari’a ta yarda da ya gajiyar da kansa da rana ba, yadda da daddare ya kasa yin karatun al’qur’ani ko sallar tahajjud*

    Don haka ba a yarda mai azumi ya rinka ;

    *1-kallon fim din ‘yan Hausa, fitsararru masu yada fasadi da vata tarbiyya,da duk wani fim na batsa ko wanda ya ke nuna rashin kunya ko rashin kirki.

    *2-Zuwa kallon qwallo:Bai halarsta ga mai azumi ya je ya kalle su ba, domin kallon qwallo haramun ne,akwai nuna tsiraici kamar fitar da cinya wanda bai halasta ba ga namiji da mace. Manzon Allah ya ce cinya tana daga al’aura. Haka ya gaya wa wani mutumi da ya fitar da cinyarsa. Sai ya ce masa, ‘Rufe cinyarka domin cinya tana da ga ala’ura*
    [61]

    *3-Karta da caca Allah ya hana su a cikin suratul Ma’ida su ma haramun ne ga mai azumi da ma wanda ba ya azumi*

    *4-Hira da ‘yammata*

    *Ya Allah ka isar da rayuwar mu watan Ramadhana muna imani da kyakkyawar niyya*.  less
    • Tue at 7:20 PM
    • Rahmatu Lawan and Bakandamiya like this.
  • Mustapha musa abu Aisha
    Mustapha musa abu Aisha
    Sheikh Ibni-Uthaimeen (Rh) ya ce:
    أَعْظَمُ حُقُوق البَشَر هُوَ ⁧حَقُّ الوَالِديْنِ؛ لِأَنَّ اللهَ جَعَلهُ فِي المَرْتَبَةِ الثَّانِيَةِ بَعْدَ...  more
    Sheikh Ibni-Uthaimeen (Rh) ya ce:
    أَعْظَمُ حُقُوق البَشَر هُوَ ⁧حَقُّ الوَالِديْنِ؛ لِأَنَّ اللهَ جَعَلهُ فِي المَرْتَبَةِ الثَّانِيَةِ بَعْدَ حَقِّهِ".
    [📚تَفْسِيرُ سُورَة النِّسَاء ج١ ص ٩٠٣]
    ══════ ❁✿❁ ═════
    Mafi girman hakki akan mutum shi ne Hakkin Iyaye, domin Allah ya danfara shi da hakkinsa, Ma'ana daga hakkin Allah hakkin iyaye shi ne na biyu.
    [📚تَفْسِيرُ سُورَة النِّسَاء ج١ ص ٩٠٣]
    ══════ ❁✿❁ ═════
    ربنا اغغر لنا ولوالدينا ولجميع المسلمين والمسلمات، والمؤمنين والمؤمنات الأحياء منهم والأموات ياحي ياقيوم
    #Fatan_Alkairi  less
    • Mon at 6:05 PM
    • Adamou Bagna Mahamane and Rahmatu Lawan like this.
  • Mustapha musa abu Aisha
    Mustapha musa abu Aisha
    MANYAN AIYUKAN IBADA GUDA 10 A CIKIN RAMADHANA

    Darasi na...  more
    MANYAN AIYUKAN IBADA GUDA 10 A CIKIN RAMADHANA

    Darasi na Farko-(1)

    *1-AZUMI*
    Aiki na farko kuma mafi girman aiyuka acikin wannan wata mai albarka,shine azumi,dukkan wata ibada da akeyinta a wannan watan tana da alqane da Azumi kuma tana biyo bayana Azumi ne.

    Manzon Allah ﷺ yana cewa:
    *(Dukkan aiyukan dan Adam ana bashi ladar aiyuka goma ga kowane kyakkyawan aiki guda,har ya dari bakwai,Allah Mai girma da buwaya yana yana cewa:"Inbanda Azumi,domin Azumi nawane,ni zan bada ladarsa,mai Azumi yana barin sha'awarsa da abincinsa da abin shansa,saboda ni,mai Azumi yana da farin ciki guda biyu,lokacin bude baki da kuma lokacin haduwa da ubangijinsa ranar alqiyama,Warin bakin mai Azumi yafi kamshin turaren Miski awajan Allah)*
    @ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻭﻣﺴﻠﻢ.

    Manzon Allah ﷺ yana cewa:
    *(Wanda yayi Azumin watan Ramadhana yana mai imani yana mai kwadayin lada,an gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa)*
    @ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻭﻣﺴﻠﻢ.

    Hakika babu wanda yake samun wannan lada da rabo mai tsoka ta Azumi,sai wanda ya nisanci sabon Allah acikin azuminsa kamar yadda ya nisanci ci da sha da sha'awrsa.
    Saboda Fadin Manzon Allah ﷺ
    *(Dukkan wanda bai nisanci zancen zurbar "wato karya da maganr banza" da aiki da ita ba,to Allah bashi da wata buqata acikin azuminsa,ko yaci ko ya sha)*
    @ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ.

    Kuma Manzon Allah ﷺ yace:
    *(Azumi garkuwane, idan ya kasance ranar Azumin dayanku,kada yayi zancen batsa,kada yayi fasikanci,kada yayi wauta,idan wani ya zageshi ko ya dokeshi,sai yace ni mai Azumine)*
    @ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻭﻣﺴﻠﻢ.

    Idan kana Azumi ya bawan Allah,to kayi azumi da dukkan gabbanka,jinka ya kame daga jin haramun,ganinka ya kame daga kallon haramun,bakinka da harshenka ya kame daga maganganun haramun,wanda yayi irin wannan azumin shine yayi atsami mai kankare masu zunubai.

    Allah ne mafi sani


    Mu hadu a Darasi na gaba insha Allah.

    *Allah ka sanya mu cikin yan aljanna sanadiyyar wannan azumi na Amin*  less
    • Mon at 5:48 PM
    • Adamou Bagna Mahamane and Rahmatu Lawan like this.
  • Mustapha musa abu Aisha
    Mustapha musa abu Aisha
    Ibni-Uthaimeen (Rh) ya ce:
    على العاقل أن يكثر من النوافل ما دام في حال الصّحة لأن جميع النوافل التي يعملها في صحته إذا مرض وعجز عنها، كتبت له كاملة كأنه...  more
    Ibni-Uthaimeen (Rh) ya ce:
    على العاقل أن يكثر من النوافل ما دام في حال الصّحة لأن جميع النوافل التي يعملها في صحته إذا مرض وعجز عنها، كتبت له كاملة كأنه يفعلها.
    Yakamata ga duk wani mai hankali ya Yawaita yin Nafila Matukar yana Cikin yanayin koshin Lafiya, domin baki dayan Nafilolin da yake Aikatawa a halin sadda yake da Lafiya, idan yayi Rashin Lafiya ya gaza aikata ta, Za'a Rubuta Masa Lada Kwatankwacin abin da yake Aikatawa na Nafilar.
    [📚 الشرح الممتع - ٤ / ٨٠]  
    • Mon at 10:56 AM
    • Amrah Auwal likes this.
  • Mustapha musa abu Aisha
    Mustapha musa abu Aisha
    MU TUBA DAGA ZUNUBAI BAKI DAYA

    النووي -رحمه الله :
    Yana...  more
    MU TUBA DAGA ZUNUBAI BAKI DAYA

    النووي -رحمه الله :
    Yana cewa:
    *_Da mutum zai yi zunubai mai maimaita zunubai har sau 100 ko sau 1000 ko fiye da hakan, sannan ya tuba daga dukkan zubansa a lokaci daya, Allah ya gafarta masa kuma ya kankre dukkan zunubansa baki daya, ya koma kamar wanda bai taba yin su ba_*
    @شرح صحيح مسلم (75/17)


    Allah ne mafi sani


    Allah ka gafarta mana baki daya.  
    • Mon at 9:13 AM
    • Rahmatu Lawan and Bakandamiya like this.
  • Mustapha musa abu Aisha
    Mustapha musa abu Aisha
    # TANADI GUDA 10 DAN SHIGA WATAN RAMADHANA


    Darasi na...  more
    # TANADI GUDA 10 DAN SHIGA WATAN RAMADHANA


    Darasi na Ukku-(3)


    *6-YIN GAFARA DA YAFIYA GA JUNA KAFIN SHIGA WANNAN WATA TARE DA SHIRYAWA DA WANDA KUKA SAMI SABANI*.

    *"Yin yafiya da afuwa ga yan uwanka musulmai tare da neman gafara ga wanka ka sabawa kafin shiga watan Ramadhana"*

    Kada ka yarda ka shiga watan Ramadhana tare da hakkin wani akanka face ka nemi gafararsa kafin shiga wannan watan,kuma kada ka yarda ka shiga wannan watan kana mai jin hanshi da rike wani musulmai acikin zuciyarka,ka yafewa dukkan musulmai kafin shiga wannan watan mai albarka.
    Manzon Allah s.a.w yana cewa:
    *(Allah yana yin dubi zuwa ga dukkan halittunsa acikin daren rabin Sha'aban,sai yayi gafara ga dukkan halittunsa inbanda mushriki da wanda yake gaba da dan uwansa ko wanda baya shiri da dan uwansa)*
    @ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ﻭﺍﻟﺘﺮﻫﻴﺐ 1016

    Dan haka kowa yayi gafara ga dan uwansa kowa ya shirya da wanda suka bata kafin shiga wannan watan.
    Sahabban Manzon Allah s.a.w sun kasance basu shiga wannan watan da hakkin wani ko jin haushin wani.
    An tambayi Ibn Mas'ud ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ
    Ya ya ku Sahabai R.A kuke fuskantar watan Ramadhana yaya kuke shiga watan Ramadhana??
    Amsa
    Sai yace:
    *"Babu wani daya daga cikin mu,da zai fuskanci watan Ramadhana ko zai shiga watan Ramadhana,face babu daidai kwayar zarra na hakkin dan uwansa ko jin haushin dan uwansa a cikin zuciyarsa"*
    @ﺫﻛﺮﻩ ﺍﺑﻦ ﺭﺟﺐ ﻓﻲ ﻟﻄﺎﺋﻔﻪ.


    7-YIN MURNA DA ALBISHI GA JUNA DAN SHIGOWAR WATA RAMADHANA.
    *"Nuna murna da farin ciki da shigowa wannan watan mai albarka,tare da yin albishir ga yan uwa musulmai."*

    Ya tabbata daga Manzon Allah s.a.w yakasance yana albishir ga sahabban sa da shigowar wannan watan mai albarka.
    Manzon Allah s.a.w idan watan Ramadhana ya shigo yana yin albishir ga Sahabbansa sai yace:
    *(Watan Ramadhana yazo maku,watane mai albarka da Allah ya rubuta maku yin azuminsa,acikinsa aka bude kofofin aljanna,kuma a rufe kokofin wuta)*
    @ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺣﻤﺪ.

    Sahabban Manzon Allah s.a.w da Tabi'ai suma sun kasance suna murna da albishir ga junansu da shigowar wannan watan mai albarka.wani farinciki da albishir yafi na shigowar watan Ramadhana watan da Allah yake yanta bayinsa daga wuta zuwa aljanna.


    Allah ne mafi sani.


    _Mu hadu a darasi na gaba insh Allah_.


    *( ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺑﺎﺭﻙ ﻟﻨﺎ ﻓﻲ ﺭﺟﺐ ﻭﺷﻌﺒﺎﻥ ﻭﺑﻠﻐﻨﺎ ﺭﻣﻀﺎﻥ )*  less
    • Mon at 8:59 AM
    • Bakandamiya and Rahmatu Lawan like this.
  • Mustapha musa abu Aisha
    Mustapha musa abu Aisha
    *MU KOYI IBADA*

    *Darasi Akan...  more
    *MU KOYI IBADA*

    *Darasi Akan Azumi*

    FITOWA TA GOMA SHA DAYA-(11)

    *_ADADIN RAKA’O’IN SALLAR
    TAHAJJUD/TARAWIHI*
    Sallar tarawihi raka’a goma sha daya ce. An samo ruwaya daga Nana A’isha Allah ya qara mata yarda, wanda yake nuna cewa Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam na yin raka’a goma sha uku.
    @Bukhari

    ita ce ruwayar da mai Risala ya kawo a cikin littafinsa Risalah
    @Risalah ta Abi zadil al Qiyrawan, Amma in ka duba Bugyatul Mutadawi’i ya hada hadisan duka ya yi bayaninsu.
    Don haka idan mutum ya yi sallar tarawihi ba zai yi tuhajjidi ba sai dai in ya tashi ya karanta Al-Kur’ani.

    Wasu malaman kuma sun ce zai iya yi matuqar bai yi wuturi ba amma in ya yi wuturi ba zai yi ba domin Tahajjudi sai bayan an yi barci an farka ake yinta.

    Shi kuwa babban Malami Sheikul Islam Ibn Taimiyya ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bai qayyade yawan raka’o’i sanannu ba, sai dai shi ba
    ya wuce raka’a goma sha daya ko sha uku a Ramadan ko ba Ramadan ba.

    Sai dai ya kasance yana tsawaita raka’o’i, amma a qarshe ya nuna cewa idan ka qara har ta wuce raka’a goma sha daya ko sha uku ba komai,
    amma ya nuna cewa da za a tsaya a sha daya ko sha uku ya fi in dai za a iya dadewa cikin tsayuwar.
    @Majmu,ul fatawa mujalladi 22
    shafi 272-273

    Ibn AbdulBar a cikin littafinsa
    ‘Attamhid’ ya ce ba bu sabani
    tsakanin musulmai cewa sallar dare ba ta da adadi qayyadadde domin nafila ce, aiki ne na alheri, wanda ya so ya taqaita wanda ya so ya yawaita.
    @Attamhid

    Sheikh Mustaphal Adawi ya rubuta littafi mai suna ‘Risalatu Allatifa Fi Adadi Raka’ati Kiyamullaili’ A cikin littafin nasa yana da fahimtar cewa zaka iya wuce raka’a goma sha daya
    ko goma sha uku. Allah shi ne mafi sani.
    @Risalatu Allatifa Fi Adadi
    Raka’ati Kiyamullaili’
    Kamal Abu Malik ya ce wanda yake tunanin cewa sallar tarwihi iyakarta raka’a goma sha daya, ya ce to ya yi kuskure.
    @Sahih fqhu Sunnah 1-415
    Manzon Allah ya yi sallar tarawihi sau uku a cikin jam’i, daga baya ya bari saboda tsoron kar a wajabta ta a
    kan al-ummarsa.
    @Sahih fqhu Sunnah 1-415

    Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya ce wanda ya yi sallar tarawihi yana mai imani kuma yana mai neman lada, Allah ya gafarta masa zunubansa.

    Malamai sun tara dalilai waje daya suka ce wanda ya yi sallar tarawihi cikin jam’i ya fi lada don haka a yi a jam’i
    ya fi.
    @Bukhari da Musulim

    Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
    wata rana da daddare ya shigo
    masallaci sai yaga mutane a qarshen masallaci sai ya yi tambaya ya ce wadancan me su keyi sai mai magana ya ce mutane ne basu da hadda Qur’ani Ubay bn Ka’ab yake
    masu limanci sai Annabi sallallahu alaihi wa alihi wasallam ya ce ‘’sun dace kuma sun kyauta’’.
    @Salatut Tarawihi

    Wannan hadisin ya nuna mana a fili lalle sallar Tarawihi tana da asali, domin Annabi sallahu alaihi wa’alihi wasallam ya yi kuma ya tabbatar kamar yadda muka gani a hadisin da ke sama, don haka wanda ya ce sallar Tarawihi/Tahajjudi bidiace to yana qokarin danganta bida ga Annabi
    sallahu alaihi wa’alihi wasallam da Sahabbansa Allah ya kauta.
    Bayan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya rasu, Sayyadina Umar ya raya sunnar tarawihi cikin jam’i.

    Don haka ba bidi’a ba ce sallar tarawihi ko Tahajjud a cikin jam’i domin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a
    gare shi ya yi ta har sau uku.
    Kuma ya bar yi ne don tsoron kar a wajabta ta ga al-ummarsa. Don haka wanda
    ya ce sallar tarawihi bidi’a ce
    wannan mutumi yana nuna wa
    duniya cewa lalle shi jahili ne.

    Kuma yana qoqarin dangata bidi’a ga Manzo tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Sahabi mai daraja wanda yana da ga cikin wadanda Annabi ya ce a yi koyi da sunnarsu kuma ya razanar da mu kan bidi’a mu nisance ta yana da kyau mai karatu ya duba Majmoo’ al- Fataawa, 22/234, 235 na ibn Taimiyya
    zai ga magana gamsassa da take nuna cewa wanda ya ce Umar yana nufin Tarawihi /Tahajjudi bidi’a ce yayi
    kuskure babba domin sahabbai basa yin bidi’a yana da kyau mai karatu ya duba domin qarin ilimi.  less
    • Mon at 8:51 AM
    • Bakandamiya likes this.
  • Mustapha musa abu Aisha
    Mustapha musa abu Aisha
    #LOKUTA DA WURARE GUDA 8 DA AKE SO KA YIWA MANZON ALLAH SAW SALATI A.

    1-Bayan gama amsa kiran Allah.

    2-Acikin Tahiya ta farko da Tahiya ta...  more
    #LOKUTA DA WURARE GUDA 8 DA AKE SO KA YIWA MANZON ALLAH SAW SALATI A.

    1-Bayan gama amsa kiran Allah.

    2-Acikin Tahiya ta farko da Tahiya ta biyu kafin sallama.

    3-Acikin Hudubobi kamar ta juma'a da Idi da sallar rokon ruwa.

    4-Akarshen adduar Alqunutu

    5-Tsakanin kabbarorin sallar Idi.

    (ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺻَﻞِّ ﻋَﻠَﻰ ﻣُﺤَﻤَّﺪ ﻭﺳﻠﻢ)

    6-Lokacin sallar gawa bayan.kabbara ta biyu.

    7-Lokacin a addua acikin sallar dare.

    8-Lokacin da aka ambaci sunan Manzon Allah a alqurani a sallar nafila.

    Manzon Allah s.a.w yana cewa:
    (Allah ya tumurmusa hancin wanda aka ambaci Manzon Allah s.a.w awajasa,amma baiyi masa salatiba).
    @ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭی

    ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺻَﻞِّ ﻋَﻠَﻰ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ ﻭَﻋَﻠَﻰ ﺁﻝِ ﻣُﺤَﻤَّﺪ ، ﻛَﻤَﺎ ﺻَﻠَّﻴْﺖَ ﻋَﻠَﻰ ﺇِﺑْﺮَﺍﻫِﻴْﻢَ ﻭَﻋَﻠَﻰ ﺁﻝِ ﺇِﺑْﺮَﺍﻫِﻴﻢَ ﺇِﻧَّﻚَ ﺣَﻤِﻴﺪٌ ﻣَﺠِﻴﺪ ، ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺑَﺎﺭِﻙْ ﻋَﻠَﻰ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ ﻭَﻋَﻠَﻰ ﺁﻝِ ﻣُﺤَﻤَّﺪ ، ﻛَﻤَﺎ ﺑَﺎﺭَﻛْﺖَ ﻋَﻠَﻰ ﺇِﺑْﺮَﺍﻫِﻴْﻢَ ﻭَﻋَﻠَﻰ ﺁﻝِ ﺇِﺑْﺮَﺍﻫِﻴﻢَ ﺇِﻧَّﻚَ ﺣَﻤِﻴﺪٌ ﻣَﺠِﻴﺪ "  less
    • Mon at 7:09 AM
    • Bakandamiya and Lawan like this.
    • Mustapha musa abu Aisha
      Lawan Jazaakallahu khair
      • Mon at 8:11 AM
      • -
      • Report
  • Mustapha musa abu Aisha
    Mustapha musa abu Aisha
    KALMAR DA ZAKA FADA ALLAH YAYI MAKA GAFARA

    Dukkan wanda yake son samun gafarar Allah to ka yawaita ambaton Allah musamman karatun alqurani da kuma abinda ya tabbata na zikiran Annabi ﷺ, wannan itace hanya mafi girma ta samun gafarar Allah bayan...  more
    KALMAR DA ZAKA FADA ALLAH YAYI MAKA GAFARA

    Dukkan wanda yake son samun gafarar Allah to ka yawaita ambaton Allah musamman karatun alqurani da kuma abinda ya tabbata na zikiran Annabi ﷺ, wannan itace hanya mafi girma ta samun gafarar Allah bayan inganta tauheedi da Aqeedar bawa.

    *Ga wadan su kalmomi mu hardace su mu yawaita fadarsu dan samun gafarar Allah,sannan mu koyawa yan uwanmu mu yada su a tsakanin mu*

    Zababban masoyina da Manzon Allah ﷺ yana fadawa daya daga cikin Sahabbansw sai yace;-
    *(Shin bazan koya maka ba wadan su kalmomi ba,wanda idan ka fadesu Allah zai gafarta maka?)*
    idan kazon a gafarta maka sai kace;-

    ▩لا إله إلا الله العليّ العظيم▩
    *"LAA ILAHA ILLALLAHUL ALIYIL AZEEM"*.

    ▩ لا إله إلا الله الحكيم الكريم▩
    *"LAA ILAHA ILLALLAHUL HAKEEMUL KAREEM"*

    ▩لا إله إلاّ الله سبحان الله ربّ السموات السَّبع وربّ العرش العظيم▩
    *LAA ILAHA ILLALLAH SUBHANALLAH RABBIS SAMAWATIS SABA'I WARABBIL ARSHIL AZEEM*

    ▩ الحمد لله ربّ العالمين▩
    *ALHAMDULILLAHI RABBIL AALAMEEN*.
    @صحيح الجامع للألباني 2621.

    ALLAH NE MAFI SANI  less
    • Apr 4
    • Lawan, Amrah Auwal, and Adamou Bagna Mahamane like this.
  • Mustapha musa abu Aisha
    Mustapha musa abu Aisha
    SAƘO ZUWA GA MATA IYAYEN AL'UMMA

    *_NASIHOHI GUDA 40 GA MATA_*

    ...  more
    SAƘO ZUWA GA MATA IYAYEN AL'UMMA

    *_NASIHOHI GUDA 40 GA MATA_*

    Darasi na farko-(1)

    *1-Zaman mace a gidanta yafi alkhairi ga fitarta ko da zuwa masallacine*.

    Daga Ibn Umar Allah ya kara masa Yarda yace;Manzon Allah s.a.w yace:
    *(Kada ku hana mata bayin Allah zuwa masallaci idan sun nemi izinin zuwa, amma su zauna a dakunansu shine mafi alkhairi a garesu)*.
    @ﺻﺤﻴﺢ ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ﻭﺍﺑﻦ ﺧﺰﻳﻤﺔ .

    *2-Idan zaki fita ki nemi izinin mijinki,ku kuma maza ku basu izin fita idan wata buqata tasu idan ta kama*.

    Daga Nana Aisha R.A yana cewa:
    _"Nakancewa Annabi s.a.w kabani izini dan na fita naje wajan mahaifana"_.
    @ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( 4141 ‏) ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏( 2770 ‏) .

    Imam Iraqi yake cewa wanna Hadisin Hujjane da kuma dalili akan kada mace ta fita daga gidan mijinta koda zuwa gidan mahaifantane sai da izinin mijinta.
    @ﻃﺮﺡ ﺍﻟﺘﺜﺮﻳﺐ " ‏( 8/58 ‏)


    Daga Nana Aisha R.A daga Annabi s.a.w ya ce:
    (Hakika an bada izinin mata su fita idan wani buqata ta kama).
    @ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ .

    *3-Yawan fitar mata da yawan yawansu yana kawo fasadi*.

    Daga Abdullahi Bn Mas'ud R.A daga Annabi s.a.w yace:
    *(Lallai mace al'aurace idan tafita Shaidhan yana kara kawata halittarta mafi abinda yafi samun matsayinta a wajan fuskar Ubangijinta ta zauna agidanta)*.
    @ﺻﺤﻴﺢ ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ، ﻭﺍﺑﻦ ﺧﺰﻳﻤﺔ ﻭﺍﺑﻦ ﺣﺒﺎﻥ .
    Shaidhan yana kara kawata adonta da kwalliyarta da kyawunta da halittarta ga maza sai su riqa tallonta har suyi sha'awarta daga nan sai sabon Allah ya biyo baya.

    *4-Kada mace ta fita daga gidan mijinta sai da izininsa kuma idan bai bata iziniba to kada ta fita ta zauna agidanta shine mafi alkhairi*.

    Daga Ibn Abbas R.A yace"wata mata tazo wajan Annabi s.a. w sai tace;Yaa Manzon Allah s.a.w minene miji akan matarsa?? Sai yace;
    *(Kada tafita daga gidansa sai da izininsa,idan kuma ta fita tsinuwar mala'ikun sama da mala'ikun rahama tana tabbata agareta har sai ta dawo)*.
    @ﺍﻟﻤﻨﺬﺭﻱ ﻓﻲ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ﻭﺍﻟﺘﺮﻫﻴﺐ ﻭﻋﺰﺍﻩ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻄﺒﺮﺍﻧﻲ

    Daga Ibn Umar R.A yace:
    Wata mata ga Sayyadina Umar R.A ta kasance tana zuwa Sallar Assuba da Isha'i a masallaci, sai akace mata miyasa kike fita bayan umar baya son hakan saboda kishinsa?sai tace mi ya hanashi ya hanani? Sai akace mata saboda fadan Annabi s.a.w;
    *(Kada ku hana mata bayin Allah zuwa Masallatan Allah)*.
    @ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ .

    *5-Kata mace ta sanya turare ko kayan mashi lokacin fitarta daga gida koda zuwa masallacine*.

    Daga Abi Musa Al'ash'ary R.A yace: Manzon Allah s.a.w yace:
    *(Idan mace ta sanya Turare ta wuce wajan mutane dan suji kamshin wannan turare,tana da kaza da kaza)ya fadi maganganu masu nauyi sosai akanta.

    Awata riwayar yace:
    *(Ita mazinaciyace)*.
    @ﺣﺴﻦ ﺻﺤﻴﺢ ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ.

    *Turare kala biyune na mata*:
    _1-Akwai turare wanda kamshinsa yake tashi daga nesa wannan haramunne mace tasanya shi ta fita sai dai ta sanya agidanta da mijinta. Domin babu abinda yake saurin tunawa namiji son jima'i irin turaran mace da kamshenta_.

    _2-Marar tashin kashi sai a zo kusa da ita za'aji kamshinsa,to wannan shine ake so mace ta sanya lokacin fita domin sanya turare ibadane_.

    Allah ne mafi sani.

    Mu hadu a darasi na gaba insha Allah.  less
    • Apr 4
    • 6 person likes this
  • Mustapha musa abu Aisha
    Mustapha musa abu Aisha
    HAKKOKI GUDA 10 NA MAHAIFA BAYAN RASUWARSU

    Darasi na...  more
    HAKKOKI GUDA 10 NA MAHAIFA BAYAN RASUWARSU

    Darasi na farko-(1)

    Yana cikin biyayya da kyautatawa mahaifa da hakkinsu akan mu bayan Allah ya karbi rayuwarsu;

    *1-Nema masu gafara da yi masu Istighfari*

    Ya kai dan uwana wajibine mu yawaita nemawa mahaifanmu gafara a wajan Allah alokacin da suke raye sannan mu kara nema masu gafara da yi masu istighfari kowane lokaci mai yawa bayan mutuwarsu.
    Manzon Allah SAW yana cewa;
    *(Lallai Allah yana daukaka Daraja da matsayin mutum Salihi acikin aljanna,sai bawan yace;Ya Allah daga inane nake samun karin wannan daukaka,sai Allah yace masa;Saboda ISTIGHFARIN ya'yanka)*
    @ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ

    *2-Yi masu addu'a*

    Wajibine ga kowane Da na kwarai ya riqa yima mahaifansa addu'a duk lokacin da zai roki Allah,kuma ya kara dagewa da wannan addu'ar a garesu bayan rasuwars.

    Yana daga cikin alamar kai na kirkine a sameka kana yawaita addua ga mahaifanka.
    Manzon Allah SAW yana cewa;
    *(Idan Dan-Adam ya rasu,ladar aiyukansa sun yanke sai guda ukku kadai;Sadakar da yayi mai gudana,ko ilimin da ya koyar ake amfanuwa da shi,da Da nakwarai da zai riqa yi masa addu'a)*
    @ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ.

    *3-Biya masu dukkan basuka da yake kansu*

    Bashi kala biyune kamar yanda Manzon Allah SAW ya bayyana;
    -Bashin mafi girma bashin Allah

    -Bashi mai girma bashin dake tsakanin mutum da mutum.

    Dukkan wadan nan basukan hakkine na mahaifanmu akanmu da mu sauke masu bayan rasuwarsu.

    Manzon Allah SAW yana cewa;
    *(Ran mumini idan ta mutu ana kangeta daga isa zuwa ga rahama har sai an biya mata bashin da yake kanta)*
    @ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ.

    Manzon Allah SAW yana cewa;
    *(Wanda yayi mutuwar Shahada ana gafarta masa dukkan komai inbanda bashin da yake kansa)*
    @ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ

    Annabi SAW yace;
    *(.........Bashin Allah shine yafi chanchanta da abiya masa)*
    @ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ.

    *4-Cikisa bakancensu da alqawulansu na alkhairi*

    Wajibine a biya masu bakancensu da alkawulansu na alkhairi,kamar Azumi ko aikin hajji ko Umara ko wani daga cikin alkawula na alkhairi.

    *5-Biya masu hakkin kaffara da yake kansu*

    Kamar kaffarar kisan kai bisa kuskure ko kaffara ta rantsuwa ko wanin wannan to shima yana cikin hakkin mahaifa akan ya'yansu da su biya masu bayan rasuwarsu.

    Wata mata tayi bakancen zakayi azumi na wata guda,amma bata samu damar cikawa ba har ta rasu,sai yan uwanta sukazo wajan Manzon Allah SAW suka bashi labari,sai yace;
    *(Shin da abana binta bashi zaku biya mata??* sai sukace Eh ya Manzon Allah,sai yace;
    *(To bashin Allah shi yafi chanchanta da abiya)*
    @ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ.

    Da matar nan da ta tambaye Manzon Allah SAW cewa;-
    "Mahaifiyata ta rasu ana binta azumin wata guda,sai yace;
    *(Ki rama mata)*
    @ﺃﺑﻮ ﺩﻭﺩﺍ.

    Manzon Allah SAW yace;
    *(Dukkan wanda ya rasu ana binsa bashin azumi to yan uwansa su biya masa)*
    @ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ

    Allah ne mafi Sani.

    *Mu hadu a Darasi na gaba insha Allah*  less
    • Apr 4
    • 4 person likes this
  • Mustapha musa abu Aisha
    Mustapha musa abu Aisha
    *_FALALAR YIN SALLAR GAWA TA RAKA GAWA ZUWA MAQABARTA_*

    Yana daga cikin hakkin musulmi akan musulmi idan ya mutu yayi rakiyar gawarsa zuwa binneta,sabban babban gatan da zakayiwa dan uwanka idan ya mutu shine ka tsaya a kyautata gyarasa da yi masa...  more
    *_FALALAR YIN SALLAR GAWA TA RAKA GAWA ZUWA MAQABARTA_*

    Yana daga cikin hakkin musulmi akan musulmi idan ya mutu yayi rakiyar gawarsa zuwa binneta,sabban babban gatan da zakayiwa dan uwanka idan ya mutu shine ka tsaya a kyautata gyarasa da yi masa sittira kamar yadda Manzon Allah ﷺ ya koyar.
    Manzon Allah ﷺ :-yace:
    *(Wanda yayi rakiyar gawar Musulmi,yana mai imani kuma yana mai kwadayin lada,ya tsaya har aka gama sallah kuma aka gama binnesa,yana dawowa da ladar Qiradi guda biyu,kowane Qiradi yakai girman dutsen Uhudu,wanda yayi mata sallah kadai,sai yadowa bai halarci binnetaba,to yana da ladar girman Qiradi guda daya)*.
    @ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ

    Manzon Allah ﷺ :-yana cewa:
    *(Babu wani mamaci da za'a sami taron jama'a na musulmai,da suka kai mutum dari, suyi masa Sallah,dukkan su sune neman cetonsa a wajan Allah,face Allah ya basu cetonsa)*.
    @ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ - ﺭﻗﻢ : ‏( 947 ))

    Manzon Allah ﷺ :-Yace:
    *(Babu wani mutum musulmi da zai mutu,sannan a sami mutane arba'in wadanda basu shirka da Allah,su tsaya akan gawarsa,face Allah ya basu cetonsa)*.
    @ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ - ﺭﻗﻢ : ‏( 948 )

    SUNNAR Rakiyar gawa shine kana mai imani da ikhalsy da neman lada a wajan Allah shi kadai,yayi mata sallah,sannan ya rakata zuwa maqabarta har agama binneta yin hakan sunnace ta Manzon Allah ﷺ ga Maza kadai banda mata.

    Allah kasanya mucika da Imani.  less
    • Apr 3
    • 4 person likes this
  • Mustapha musa abu Aisha
    Mustapha musa abu Aisha
    *HANYOYI GUDA 25 NA SHIGA ALJANNA DAGA BAKIN MANZON ALLAH*


    Darasi na...  more
    *HANYOYI GUDA 25 NA SHIGA ALJANNA DAGA BAKIN MANZON ALLAH*


    Darasi na Biyu-(2)
    11-Wanda ya fadi wannan zikiri:-
    *"ﺭﺿﻴﺖ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﺭﺑﺎً، ﻭﺑﺎﻹﺳﻼﻡ ﺩﻳﻨﺎً،ﻭﺑﻤﺤﻤﺪ ﻧﺒﻴﺎً*
    _RADHITU BILLAHI RABBAN,WA BI ISLAMI DINAN,WA BI MUHAMMADIN NABIYAN_ *Aljanna ta waja agareshi*.
    @ﺃﺑﻮﺩﺍﻭﺩ.
    12-Wanda karshen maganarsa anan duniya itace:-
    * ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ*
    _LAA ILAHA ILLALLAH_
    *ya shiga aljanna*.
    @ﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ .

    13-Duk wanda ya fada:-
    * ﺳﺒﺤﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻩ*
    _SUBHALLAHIL AZEEMI WABI HAMDIHI_
    *An dasa masa itaciyar dabino agidan aljanna*.
    @ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ.

    14-Wanda ya mutu yana mai kubuta daga wannan abubuwa guda ukku:
    *Girman kai*
    *Da satar dukiyar ganima*
    *Da bashi,ya shiga aljanna*.
    @ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ.

    15-Wanda ya dauki nauyin kulawa da yan mata guda biyu,zai shiga aljanna tare da ni.
    @ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ.

    16-Wanda yayi ladanci na tsawon shekara goma sha biyu,aljanna ta wajaba agareshi.
    @ﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﺔ.

    17-Wanda ya roki Allah aljanna sau ukku yana mai cewa;
    *ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺃﺩﺧﻠﻪ ﺍﻟﺠﻨﺔ*
    _ALLAHUMMA ADKHILNAL JANNATA_
    *Allah zai sanya shi a aljanna*.
    @ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ.

    18-Wanda ya duba marar lafiya ko ya kai ziyara ga dan uwansa dan Allah,sai wani mai kira yayi kira yace:
    *Kaji dadi kasami babban rabo kuma ka sami masauki a gidan aljanna*
    @ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ

    19-Lallai yawan fadar gaskiya yana shiryarwa zuwa ga dha'a,ita kuma dha'a tana kai mutum zuwa aljanna.
    @ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ.

    20-Allah ya dorama kansa ga dukkan wanda ya fita jihadi dan daukaka kalmar Allah,babu abinda ya fitar da shi sai jihadin da kuma gaskata maganar Allah,Allah zai shigar da shi a aljanna.
    @ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ.

    21-Ya ku mutane,ku riqa yãda Sallama a tsakaninku,ku ciyar da abinci dan neman lada,kuyi sallah a lokacin da mutane suke barci a cikin dare,zaku shiga aljanna cikin aminci.
    @ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ.

    22-Daga aikin Umara zuwa wata Umarar, Allah yana kankare laifin da akayi a tsakaninsu,amma shi aikin hajji karbabbe,baya da wani sakamako sai gidan aljanna.
    @ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ.

    23-Allah yana da wadansu sunaye guda 99 dare babu guda daya,wanda ya kiyaye su zai shiga aljanna.
    @ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ.

    24-Hakika naga wani mutum yana kaikawo acikin aljanna,saboda wata itaciyace da ya cireta daga kan hanya tana cutar da mutane,sai Allah ya shigar da shi aljanna saboda ita.
    @ﻣﺴﻠﻢ.

    25-Wanda ya karanta Shugaban Istighfari da safe yana mai imani da shi mai yarda dashi da yakini,sai ya mutu kafin yamma,ya shiga aljanna,wanda ya karanta da yamma ma haka, shugaban Istighfari shine kace;-
    *ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺃﻧﺖ ﺭﺑﻲ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺧﻠﻘﺘﻨﻲ ﻭﺃﻧﺎ ﻋﺒﺪﻙ ﻭﺃﻧﺎ ﻋﻠﻰ ﻋﻬﺪﻙ ﻭﻭﻋﺪﻙ ﻣﺎ ﺍﺳﺘﻄﻌﺖ، ﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﺷﺮ ﻣﺎ ﺻﻨﻌﺖ، ﺃﺑﻮﺀ ﻟﻚ ﺑﻨﻌﻤﺘﻚ ﻋﻠﻲ ﻭﺃﺑﻮﺀ ﻟﻚ ﺑﺬﻧﺒﻲ، ﻓﺎﻏﻔﺮ ﻟﻲ، ﻓﺈﻧﻪ ﻻ ﻳﻐﻔﺮ ﺍﻟﺬﻧﻮﺏ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ *
    @ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ.

    *Allah ne mafi sani, ya Allah kasanya ni a aljanna ni da sauran dukkan musulmai baki daya*.  less
    • Apr 3
    • 5 person likes this
  • Mustapha musa abu Aisha
    Mustapha musa abu Aisha
    *MU KOYI IBADA*

    *Darasi Akan...  more
    *MU KOYI IBADA*

    *Darasi Akan Azumi*

    FITOWA TA GOMA-(10)

    *WADANSU ABUBUWAN DA YA KAMATA MAI AZUMI YA QARA NISANTARSU*

    1-Mayar da dare ya zama rana.(Dogon hira)

    2-Yin barci har lokacin salla ya wuce.

    3-Almubazzaranci wajen cin abinci.

    4-Tozartar da lokaci.

    5-Yin sahur da wuri, kuma a koma a yi barci har lokacin sallar asuba ya wuce.

    6-Qin yin sallar Tarawihi.

    *ALLAH YA KEBE WATAN RAMADANA DA*

    1-Mala’iku na roqa wa mai azumi gafara har ya yi buda baki.

    2-Warin bakin mai azumi ya fi qamshin turaren miski a wajen Allah.

    3-Ana Daure masu tsaurin kai daga cikin shedanu.

    4-Ana bubbude kofofin Aljanna a kuma rufe kofofin wuta.

    5-A cikin Ramadana ne daren Lailatul Qadri yake.

    6-Ana gafarta wa mai azumi a qarshen ramadana

    *UMRA A CIKIN WATAN RAMADANA*

    Haqiqa umra tana daga cikin manya-manyan ayukka da ke da katafariyar lada mai yawa a wajen Allah musamman a cikin Ramadan.An samo hadisi daga Ibn Abbas Allah ya kara masa yarda ya ce; Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
    *(yin Umura a cikin ramadana yana daidai da kamar ka yi aikin Hajji tare da ni ne)*.
    “wato tare da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi”
    @Bukhari da Muslim

    TAHAJJUD/TARAWIHI
    Tahajjud,Qiyamul-lail, Sallar Tarawihi dukkansu ma’anarsu daya,matukar dai a cikin watan Ramadan ne,Mutum ya yi sallar nafila a gida ya fi lada da ya yi ta a masallaci amma banda na watan Ramadan.
    Sallar tarawihi a cikin azumi ka yi ta a cikin jam’i yafi da ka yi kai kadai a gida.Sayid Sabiq ya ce junhuru sun tafi kan cewa sallar tarawihi/Tahajjudi cikin jam’i
    yafi lada da ka yi kai ka dai a gida.
    @fiqhuSunnah.

    Sheikh Zainudden Abdurrahaman ib Rajab al-Hambali ya ce:
    *Malamai sun dogara ne da hadisin da ya nuna cewa duk wanda ya yi sallar dare tare da limani har ya gama za a rubuta mai ladan ya sallaci daren ne baki aya.

    Shi kuwa Imam malik yana ganin ka yi a gida ya fi shi yasa ma yake yin nasa sallar Tarawihin/Tahajjudinsa a gida, dogaransa da maganar Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam da ya ke cewa; *(Mafificiyar sallar mutum wanda ya yi a gida sai dai in ta farilla ce)*wannan itace hujjarsa,su kuma Junhurun Malamai hujjar su ita
    ce hadisin da ya ce; *(wanda ya yi sallar dare tare da limami har yagama za a rubuta mai ladan ya sallaci daren ne baki daya)*duba Muguni na ibn Qudamah 607/2 da Qiyamu Ramadan 19-20.

    Imam Ahmad bn Hambal yana yin sallar Tarawihi ne a masallaci yana bin limami har sai angama sallah saboda ya sami ladan da Annabi sallallahu alaihi wa’alihi wasallam ya fada na ladan wanda yabi liman sallar dare har ya gama,Malamai dai sun rinjaya a kan yin sallar Tarawihi/Tahajjudi a masallaci ya fida lada da kayi kai kadai a gida, wallahu a’alam.

    Allah ne mafi sani

    *Ya Allah ka isar da rayuwar mu watan Ramadhana muna imani da kyakkyawar niyya*.

    Mu hadu a Fitowa ta gaba,insha Allah.  less
    • Apr 3
    • 5 person likes this
  • Mustapha musa abu Aisha
    Mustapha musa abu Aisha commented on Ummyter Abdallah's photo.
    اللَّهُمَّ اغْفِرلَي ابي وَارْحَمْهُ وَعَافِهِ وَاعْفُ عَنْهُ وَأَكْرِمْ نُزُلَهُ وَوَسِّعْ مُدْخَلَهُ وَاغْسِلْهُ بِالْمَاءِ وَالثَّلْجِ وَالْبَرَدِ وَنَقِّهِ مِنَ الْخَطَايَا كَمَا نَقَّيْتَ الثَّوْبَ الأَبْيَضَ.
    • Apr 3
    • 6 person likes this
    • View all 9 comments
    • Mustapha musa abu Aisha
      Hauwa'u Muhammad Ameen Ya Allah, Allah Ya gafarta masa
      • Apr 3
      • -
      • Report
    • Mustapha musa abu Aisha
      Hafsat Moh'd Arabi Allah yajikansa da rahama yasa yahuta Ameen
      • Apr 3
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Mustapha musa abu Aisha
      Ummyter Abdallah Amin ngd
      • Apr 3
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Mustapha musa abu Aisha
      Almustapha Adam Muhammad Allah ya jaddada Rahama gunsa
      • Apr 4
      • -
      • Report
    • Mustapha musa abu Aisha
      Ummu Asimii Ameen ya Allah, ubangiji Allah ya jiƙansa. Ya gafara ta mishi yasa aljannace makomarsa
      • Apr 4
      • -
      • Report
  • Mustapha musa abu Aisha
    Mustapha musa abu Aisha
    TASBIHI A BAYAN SALLAR FARILLAH KALA SHIDA NE

    Ibn Usaimeen Allah yayi masa Rahama yana cewa:
    *"Ga dukkan wanda yake so yabi sunnar Manzon Allah SAW kuma ya dace da ita yana da qa'idodi guda uku"*

    1-Qa'ida ta...  more
    TASBIHI A BAYAN SALLAR FARILLAH KALA SHIDA NE

    Ibn Usaimeen Allah yayi masa Rahama yana cewa:
    *"Ga dukkan wanda yake so yabi sunnar Manzon Allah SAW kuma ya dace da ita yana da qa'idodi guda uku"*

    1-Qa'ida ta farko
    *"Kayi kokarin aiki da wannan sunnar da kokarin kiyayeta batare da kariba ko ragi"*

    2-Qa'ida ta biyu
    *"Kiyaye sunnar kamar yadda tazo kada a mantata ko a ki aiki da ita"*

    3-Qa'ida ta ukku
    *"Aikata sunnar a matsayin koyi da Manzon Allah SAW ba al'adaba ko kaga mutane sunayin hakan,kaji kanayin koyine da Annabi s.a.w"*

    1-SIGA TA FARKO
    -Subhãnallah 33
    -Walhamdulillah 33
    -Wallahu Akbar 33
    Sai a cike na dari da
    -ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ . ﻟﻪ ﺍﻟﻤﻠﻚ ﻭﻟﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻭﻫﻮ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﻗﺪﻳﺮ .
    -Lã ilaha illallahu wahdahu lã sharika lahu lahul mulku walahul Hamdu wahuwa ala kulli shai'in Qadir.
    Manzon AllaH SAW yace:
    *(Wanda ya fadi wannan bayan kowace sallar farilla, an gafarta masa zunubansa ko da sun kai yawan kumfar teku)*
    @ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ

    2-SIGA TA BIYU
    -Subhãnallah 33
    -Walhamdulillah 33
    -Wallahu Akbar 34
    Manzon Allah s.a.w yana cewa:
    *(Wanzazzune mai fadarsu ko mai aikata su baya tabewa,Subhãnallah 33,Walhamdulillah 33,Wallahu Akbar 34 a bayan kowace sallar farilla)*
    @ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ

    3-SIGA TA UKKU
    -Subhãnallah 10
    -Walhamdulillah 10
    -Wallahu Akbar 10.
    Sukace ya Manzon Allah,ma'abuta dukiya sun tafi da daraja madaukakiya da ni'ima tabbatacciya,sai yace:
    *(Ta yaya hakan??)*
    Sai sukace;
    "Suna yin sallah kamar yanda muke yin sallah,suna jihadi kamar yanda muke jihadi,sannan suna ciyarwa da sauran dukiyarsu,mu kuma bamu da dukiya. Sai Manzon Allah s.a.w yace:
    *(Shin bazan baku labarin wani abu ba?? Wanda zaku kamo wanda ya wuceku,kuma ku tserewa wanda yake bayanku,kuma babu wanda zaizo da irin abinda kuka samu sai wanda ya aikata irin abinda kuka aikata,kuyi; Subhãnallah 10
    -Walhamdulillah 10
    -Wallahu Akbar 10, a bayan kowace sallah ta farillah)*
    @ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ

    4-SIGA TA HUDU
    -Subhãnallah 25
    -Walhamdulillah 25
    -Wallahu Akbar 25.
    @ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ.

    5-SIGA TA BIYAR
    -Subhãnallah 33
    -Walhamdulillah 33
    -Wallahu Akbar 33
    Talakkawan Madina sunzo wajan Manzon Allah SAW,sai Sukace ya Manzon Allah,ma'abuta dukiya sun tafi da daraja madaukakiya da ni'ima tabbatacciya,sai yace:
    *(Ta yaya hakan??)*
    Sai sukace;
    "Suna yin sallah kamar yanda muke yin sallah,suna yin azumi kamar yanda muke yin azumi jihadi kamar yanda muke jihadi,sannan suna ciyarwa da sauran dukiyarsu,mu kuma bamu da dukiya. Sai Manzon Allah s.a.w yace:
    *(Shin bazan baku labarin wani abu ba?? Wanda zaku kamo wanda ya wuceku,kuma ku tserewa wanda yake bayanku,kuma babu wanda zaizo da irin abinda kuka samu sai wanda ya aikata irin abinda kuka aikata,kuyi; -Subhãnallah 33
    -Walhamdulillah 33
    -Wallahu Akbar 33 bayan kowace sallar farillah)*
    @ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ.

    6-SIGA TA SHIDA
    -Subhãnallah 11
    -Walhamdulillah 11
    -Wallahu Akbar 11
    @ﺃﺧﺮﺟﺔ ﻣﺴﻠﻢ.

    Wadan nan sune sigogin Tasbihin da ya tabbata a sunnar Manzon Allah s.a.w ya kamata ga dukkan musulami ya riqa yin wadan nan Tasbihi yana chanchanzawa lokaci zuwa lokaci dan ya yi aiki da koyi da Manzon Allah gaba daya.

    Allah ne mafi sani.  less
    • Apr 3
    • Rahmatu Lawan, Bakandamiya, and Zaharadden Nasir like this.
View More
Loading ...

About

Personal Information

  • Cikakken Suna Mustapha musa abu Aisha
  • Jinsi ko Nau'i Na miji
  • Ranar Haihuwa March 31, 1985
  • Takaitaccen Bayani Mai son jama,'a da girmamawa

Contact Address

  • Sunan Gari Zangon Daura Katsina state
  • Kasa Nigeria

Abokai

  • Bakandamiya GORON JUMMA'A BA A YIN WUTRI BIYU A DARE DAYA Tambaya: Assalamu alaykum, Malam don Allah Malam amma naji wasu sunce wai idan mutum yayi wuturi a lokacin da ya yi sallan tarawi, toh wai idan zai yi nafila a cikin dare zai kara raka'a daya ya cika wuturin da ya yi da sallah tarawi. shine nake neman karin bayani plxx malam. Amsa: Wa alaikum assalam, Annabi S. A. W. yana cewa ba a wutiri biyu a dare daya, Na'am akwai malaman da suka faɗi siffar da ka ambata, saboda in ka yi hakan zai zamar da waccan ta farkon shafa'i, tun da wutiri daya ake yi a dare. Amma abin da yafi shi ne ko dai barin wutirin tare da liman ko kuma in ka san za ka sake wata sallar daren In liman ya yi sallama kai sai ka tashi ka karo wata raka'ar don ta zama shafa'i kai a wurinka kafin ka yi sallama ,, wannan zai sanya ya zama ba ka yi wutiri ba a lokacin Annabi S. A. W. yana cewa: "Ku sanya sallarku ta karshe da daddare wutiri". Allah ne mafi sani. Amsawa: Dr Jamilu Zarewa 07/06/2017
  • Rahmatu Lawan Barka da jumma’a ‘yan uwa. Allah Ya sada mu alkhairan da ke cikinta!
  • Abdurrahman Sani
  • Nasiru mohd
  • Lawan Hello
  • sulaiman labaran
  • WADA SHARIFAI NIG LTD Hello
  • ibrahim adam
  • Ali Ahamed Muhammed Ina mai yima kowa fatan Alheri💝
  • Ahmad ahmad
  • Abubakar Rabiu KanoGurus [Gargajiya] Wakar Dan Kwairo Mai Dubun Nasara Sardauna http://arewablog.com/gargajiya-wakar-dan-kwairo-mai-dubun-nasara-sardauna/ [Gargajiya] Wakar Ali Makaho Hakuri Masoyana http://arewablog.com/gargajiya-wakar-ali-makaho-hakuri-masoyana/ Share To
  • maharaz sulaiman
Previous
Next

Hotuna

  • Wall Photo­s 13 photos

Previous
Next
© 2021 Bakandamiya  -  About  -  Terms  -  Privacy  -  Talla  -  Support  -  Contact  -  Mobile Site
  • Facebook
  • Twitter
  • Linkedin
  • Youtube
  • Pinterest
  • Instagram