_______๐ Biri da wando ta saka me santsi Light orange, ฦasan wandon me fela ne sosai, sai ta saka top fari iya gwiwar ta, me kwalliyan stones, sannan sai ta naษa blue ษin ษankwali a kanta, wanda ya fito mata da gashin ta ta ฦasan ฦeya, Light makeup tayi da ya fito da tsantsan kyawun ta, kai Masha Allah duk wanda ya ga RAUDHA wannan lokacin bazai so ya ษauke idanun sa ba, ta haษu iya haษuwa sai wanda ya gani, takalmin da ta saka me tsinin gaske ne cover me igiya, kalan Light blue da farin Socks a ciki, sai tashin ฦamshi take yi irin turaren nan na Arabian
Ramcy dake zaune saman sofan ษakin ta, sakin baki tayi tana kallon ta
Sai da RAUDHA ta matso kusa da ita, ta sanya hannun ta ta shafa fuskar ta tana murmusawa. Sannan a time ษin Ramcy ta rufe bakin ta bayan ta dawo da tunanin ta jikin ta
"What happened Besty?"
Gwauron numfashi Ramcy ta sauke kafin tace, "ban san me zan ce bane wlh Besty, haษuwar ki yayi yawa. Masha Allah gaskiya ki gode Allah".
Murmushin ta me kyau ta saki kafin ta lumshe ido ahankali ta furta, "Shukran Lak, linazhab".
Da ido Ramcy tayi mata magana, "wai what?"
"Let's go".
Miฦe wa Ramcy tayi tana gyara zaman gyalen ta, itama tayi shiga ne cikin baฦin yadi me santsi, ษinkin doguwar riga, duk da kasancewar ta baฦa but sosai tayi kyau matuฦa, kasancewar an yi wa rigan ado da jan zare sai Stones, kuma tayi amfani da jan ษankwali ne sai farin gyale.
Fita suka yi, inda tuni an gama taruwa su kaษai ake jira a wajen. A hanya suka haษu da Farida ta zo kiran su, sai suka tafi tare, itama kanta sai ya ba kwalliyan RAUDHAN take yi
Ita kuwa sai murmushi take saki me fid da sihirtaccen kyawun ta, tana takun nan nata ษai-ษai me ban sha'awa, kasancewar bata yafa gyale ba, shiyasa duk inda jikin ta ya juya ana ganin komi ta yanda take sarrafa jikin ta.
Tun doso wan su wajen sai idanun mutane kawai ya koma kanta, hakan yasa wasu da hankalin su be kai kanta ba, sai duk suka kallo wajen
Tana tsakiyar Farida da Ramcy ne, suna taho wa wajen
Nan da nan aka soma tafi sabida sanar wan da MC ke yi na zuwan ta, nan ya soma koษa ta yana kambama ta
Ita kuwa idanuwan ta na kan su Daddy da ta hange su, su ma suna mata murmushi, Suhaib har da ษaga mata babban yatsan sa alamun tayi zam-zam. ita kuwa ta saki murmushin nan da ke ฦara wa fuskar ta kyawu.
"Kai man juyo ka ga wata halitta don Allah". Cewar Sharif da yayi maganar a hankali kusa da kunnen Zulain dake waya ya karkace kai
Juyo wa yayi kuwa, yana shirin hararan sa sai idon sa suka sauka kan RAUDHA dake tafiya zuwa wajen zaman ta, take anan komi nasa ya tsaya illa idanun sa da ya lumshe ya sake buษe wa akanta, yana son tabbatar wa kansa itan ce ko kuwa?. Maganar Sharif ya sake dawo da shi hayyacin sa
"Ni wlh da na san S. Makamashi yana da ฦanwa irin wannan, ai da tuni ita na nema, me zai kai Ni zuwa waje gida be ฦoshi ba".
Shiru Zulain yayi don hankalin sa be gama dawo wa kan Sharif ba, bare ya tantance me yake faษa, idanun sa ฦyam akan RAUDHA har ta zauna ta yanda yanzu yake ganin fuskar ta sosai. A take ya saki wani irin ajiyan zuciya yana sake lumshe ido
A tare Sharif da Mom ษin sa da suke waya, suka je ho masa tambaya the same
Buษe idanun sa yayi yana kallon Sharif da ya tsaya kallon sa shima, sai kuma yayi saurin kara wayan a kunnen sa sosai yana faษin, "Mom zan kira ki letter please". Ya Yi saurin katse wayan be jira cewar ta ba, nan ya sake mayar da idanun sa kan RAUDHA gaba ษaya ya mayar da hankalin sa gare ta, sosai yaji daษin ganin ta da baki ma bazai iya furta wa ba, har wani sakin murmushi yake yi batare da ya sani ba
Sharif dake faman kallon sa baki sake, ya jinjina kansa ya ce, "cab ษijam.. Kar dai har ta sace maka zuciya daga kallon farko?"
Zulain be kalle sa ba don ba ya son abunda zai gilma ga kallon kyakykyawar nan, amma kuma sai ya ษata fuska yana kumbura shi irin maganar Sharif ษin fa ya fara isar sa
Murmushi kawai Sharif yayi be ce komi ba, ya mayar da hankalin sa shima ga abinda ake yi.
A lokacin RAUDHA ta miฦe ne tana speech da muryan ta me daษi da ya karaษe wajen. Sosai duk mahalukin dake wajen ya mayar da hankalin sa gare ta cike da sha'awa. Har ta gama aka soma mata tafi Raf.. Raf... Raf
Sannan sai Suhaib ya amsa ya sake ma kowa godiya tare da yaba wa ฦanwar sa, da nuna irin tsantsan ฦaunar da yake mata. daga nan kuma Daddy ne ya amsa shima ya soma yabon ta sosai, da abun mamakin da ta ba su, tare da nuna wa mutane tsantsan alfaharin da yake yi da ษiyar sa
Haka ake ta tafa wa cike da tsananin burge su da suka yi, don sosai iyalan suka burge kowa. Haka dai aka ci gaba da gudanar da partyn cike da sha'awa, inda daga baya MC ya kira RAUDHA domin ta taka
Murmushi kawai ta soma zuba wa, domin har yanzu ฦaunar ta da rawa yana nan, sai dai yanzu ba kamar da ba, duk da a yanzu ta koyo irin rawan larabawa ne, ko tana yi zaka ka bata cika yin irin na nan ba saboda ya zame mata jiki na larabawan. Tashi tayi ta fita ta soma taka wa a hankali tana dariya bakin ta ya ฦi rufuwa
Nan Suhaib ya taso ya soma taya ta
Yanda yake rawan ne sai da ya ba kowa dariya, sai tafi ake musu
Ita RAUDHA ta saka a sauya musu, don ta kasa yi sosai sabida waฦar Hausa ce, sai ta ce a saka mata na Laraba wa, ai nan ta soma taka wa irin nasu sosai, sai shima Suhaib ya biye mata suna yi tare, har da riฦe hannu irin na laraba wa yanda suke yi
Sosai yanzu ษin Suhaib yafi ba wa kowa dariya, kowa ka gani wajen nishaษi yake yi.
Lumshe idanu Zulain yayi saboda tsantsan wani farin ciki da yake ziyartan sa, sosai yarinyan ta matuฦar burge sa fiye da tunanin mutum, nan da nan ya ji soyayyar ta me tsananin ฦarfi ya kama sa. Har wani buga tagumi yayi da hannu biyu yana bin ta da kallo.
While sauran samarin, abokan Suhaib duk haka ne a wajen su, kowa fatan sa ya dace da mallakan kyakykyawar balarabiyyan nan.
๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐
Wata farar mota ce ta shigo cikin gidan a wannan lokacin, ahankali motan take tafiya har zuwa inda akayi parcking motoci, kamar mintuna biyu da tsayuwar motan aka buษe ฦofan, sai dai wanda ke ciki be fito ba, illa ziro fararen ฦafafuwan sa dake cikin baฦin sandal Shoes da yayi waje
Daga inda yake duk da akwai tazara sosai da inda ake partyn, amma kuma hakan be sa tattausan waฦar larabawan dake tashi a wajen kasa ratsa masa kunnuwa ba, take anan ya lumshe idanun sa cike da jin daษin waฦan, kamar shuษewar mintuna biyar ya buษe su yana aza idanun sa kan wayan sa dake saman cinyan sa, ษauka yayi ya soma dubo Numban Suhaib da yayi masa serving da Dude yayi kira
While Suhaib na filin rawa yana tiฦan rawa tare da RAUDHA, sai yaji wayan sa na ruri, dasauri ya saki hannun ta yana zira wa cikin aljihu ya ciro wayan, ganin sunan Dude a screen ษin wayan na yawo, sai nan da nan fara'an sa ya ฦaru, matsawa yayi gefe yana answer call ษin ya kara a kunne, "Dude".
"Surprise! Gani a cikin gidan ku".
Waro ido Suhaib yayi, "haba don Allah".
Murmushi yayi shi kuma yace, "ka zo ka gani, ina nan wajen parcking space". Daga haka ya katse wayan
Da sauri Suhaib yayi hanyar barin wajen
Inda RAUDHA ta kira sunan sa
Juyo wa yayi yana kallon ta. Ta ษage masa gira akan "ina zai je?"
Nuna mata yayi da hannu wai "yanzu zai dawo".
Ta marairaice fuska kafin ta juya ta nufi wajen zaman ta. A lokacin ne aka soma bata kyaututtuka.
๐๐๐
Suhaib na isa wajen parcking space, Rayyan dake mota ya fito yana rufe wa. Rungume juna suka yi cike da tsananin murna, kafin kuma su saki juna suna cafe hannayen su ko wanne baki a washe
"Dude wlh ka shammace Ni, nayi tunanin ba yanzu zaka dawo ba".
Murmushi Rayyan yayi yace, "dama wannan week ษin zan shigo, but sai naga dacewar shigowa yau ษin tunda naga yau ce ranan ฦanwar ta mu, sai in Taya ta murna".
Dariya Suhaib ya saki yana ฦara ba shi hannu suka cafe yace, "gaskiya ka kyauta, Daddy zai yi farin ciki da zuwan ka, to ya Uncle da Ammee, da su Faruk?"
"Alhmadulillah duk suna gaishe ku, akwai babban surprise ma, but bazan sanar maka ba sai muna gaban Daddy".
Murmushi Suhaib yayi yace, "ok mu je to, mun tsaya a nan".
Jan hannun sa yayi suka nufi cikin gidan. Har sun kusa ฦarisa wa wajen taron sai wayan Rayyan tayi ฦara, ogan sa ke kiran sa don haka yace ma Suhaib "yayi gaba zai zo". Wayan ya ษauka suka soma magana. Daga inda yake yana hango taron mutanen, inda fitilu masu haske suka haske wajen, kasancewar duhun magriba ta gabato, a time ษin ma shirin tashi suke yi.
Yana gama wayan sai ya nufi wajen, a time ษin har wasu sun soma barin wajen sabida an gama.
Tuni itama RAUDHA taja hannun Ramcy sun shige gida.
While su Daddy sun tsaya suna sallama da mutane.
ฦarisawa Rayyan yayi wajen Suhaib.
๐๐๐
Kai tsaye ษakin RAUDHA dake sama suka wuce, anan suka zube kan kujera kowa na faษan gajiyan da ya sha, sai kuma Ramcy ta tashi tana faษin, "oh na bar su Aunty Nafeesa a waje, kuma sun ce min tafiya za su yi, ina zuwa bari inje".
RAUDHA tace, "miฦo min wayan ki, but kar su tafi yanzu zan sauko sai mu gaisa, in yaso drever ya mayar da su, but ke nan zaki kwana ko?"
Dariya Ramcy tayi tana zaro ido, "No ai nima tafiya zan yi zuwa anjima kaษan, sabida Baba na gari kuma sai da yayi min gargaษin in dawo, ina tunanin ma zamu tafi tare kawai da su ne".
"Ok mu je to sai mu yi sallama". cewar RAUDHA tana miฦe wa tare da wayan ta dana Ramcy dake hannun ta
Ramcy kuma ษaukar jakan ta tayi suka fice.
RAUDHA tafiya take yi tana latsa wayoyin, kasancewar tana son tura pictures and videos ษin da Ramcy tayi mata ne a wayan ta, kuma tana son tura wa *ฦalby* a yanzu ษin.
Sai da suka fita waje, kafin suka haษu da su Amarya da Aunty Nafeesa suna shirin shigowa
Anan RAUDHA tayi musu godiya sosai, inda tasaka masu aiki suka kwaso musu kayan party ษin. har wajen motan da za'a tafi da su ta raka su, kasancewar gaba ษaya an gama watse wa, wasu sun wuce masallaci.
Su sun shiga mota, ita kuma ta tsaya da Ramcy suna ษan Surutu, har sanda ta gama tura wa kafin ta miฦa mata wayan. Sai da ta jira suka tafi tana ษaga musu hannu kafin ta juyo cikin gidan. Da ษan tazara tafiyan, ahankali take taka wa tana latsa wayan ta, inda take karanta text ษin da ฦalbyn ta ya turo mata, tana sakin murmushi cike da nishaษi, har sanda ta iso cikin gidan, ta hau Lifter ya wuce da ita sama. ษakin ta takoma ta shiga Toilet tayi wanka kafin ta ษauro alwala, kayan ta ta saka farar less mara nauyi tamkar yadi, doguwar riga akayi mata fitet amma me guntun hannu, sai ta tufke gashin ta ta saka hula Robber ja, ta ษaura Hijab tayi Sallah, sai da ta gama ta cire ta ษauki wayan ta tafito parlour'n sama, anan ta haษu da Farida da yaran ta tana buษe musu Chocolates suna sha
"My guys how far?" RAUDHA tayi maganar tana murmushi bayan da ta ฦariso wajen su
Nan suka tashi suka nufo ta, sai ta soma ba ma Abdul hannu suka cafe, sai kuma ta miฦa wa Haneep da ya miฦo mata nasa yana dariya da zilalar da yawu
Murmushi tayi ta saka nata hannun cikin nasa, sannan ta sumbaci goshin sa ta ce, "My Daddy , I love you so much".
Washe baki yayi cike da murna, cikin muryan sa da ba ya fita maganar sosai ya ce, "I lobi u Baby".
Shima wai yayi irin na Suhaib da yake kiran ta Baby
Sai suka saka mishi dariya daga ita har Farida dake kallon su
"Wow My Daddy wa ya koya maka faษan suna na?"
Abdul yayi saurin cewa, "Aunty ai yaji Daddy na faษa miki ne, kuma yanzu yace mu kira ki, sai ya ce miki i love You Baby, shi ne shima ya faษa, but be iya sanar da ke sauran ba".
Murmushi RAUDHA tayi ta shafa kan Abdul tana faษin, "kai kuma me wayau ga shi ka faษa".
Ya washe baki yana tsalle
Still murmushin tayi; tayi musu peck a kumatu, sanan ta shafa kansu, ta miฦe tana kallon Farida tace, "Aunty bari in zo".
Tashi za su yi su bi ta, sai Farida ta riฦe su tana ce musu "su zo ta gama ษare musu biscuits and Chocolates ษin".
RAUDHA tuni ta bar wurin, ta Steps ta nufi ฦasa, a hawa na biyu ta tsaya ta shiga parlour'n don duba Daddy, don tasan baza su wuce suna nan ba dukan su. Tana shiga wani ฦamshi ya doki hancin ta, lumshe ido tayi tana buษe wa, tabbas kamar ta taษa sanin me turaren nan, kamar ta taษa jin sa a wani waje, amma aina? Wurga idanu ta soma yi cikin parlour'n. Can ta hangi mutum saman kujera, sai dai bayan sa take hanga tunda kujeran da ya zauna a kai ya juya wa ฦofa baya ne
Kamar ta wuce sai kuma wani zuciyan nata ya bata umarnin zuwa ta ga ko waye, domin dai tana ji a ranta ta san koma waye ne, kuma farin sani tunda turaren sa ya tabbatar mata da hakan, amma kuma ta kasa tuna inda ta sani. Takowa tayi ta nufo wajen
Kasancewar bata da takalmi a ฦafafuwan ta sai Socks, shiyasa Rayyan be San da zuwan ta ba, ya ฦuฦe sai kallon zafafan hotunan ta da ta turo masa yake yi, yana zuba murmushi
Gab ta kusa isa wajen, inda ฦiris ya rage ta hangi abinda yake yi a wayan, sai ya juyo da sauri, sabida ajikin sa sai da yaji kamar da mutum a wajen, kuma take yaji ฦamshin turaren ta ya bugi hancin sa.
Haษa idon da suka yi, sai ta tsaya cakkk tana bin sa da kallo, ฦure sa da idanu kawai tayi ta kasa tunanin komi
Haka zalika shima idanun ya zuba mata, yana kallon ta cike da tsantsan ฦauna a idanun nasa, tare da tsatsan kewar ta gami da muradin ta cikin ransa. Komi nata ya sauya fiye da Da, ta sake girma da tsananin kyau. less less
Mustapha musa abu Aisha
FALALAR ZIKIRI DA AMFANIN SA.
1. Yawan zikri yana korar... moreMustapha musa abu Aisha
FALALAR ZIKIRI DA AMFANIN SA.
1. Yawan zikri yana korar sheษan
2. Yawan zikri yana jawo samun yardar... moreFALALAR ZIKIRI DA AMFANIN SA.
1. Yawan zikri yana korar sheษan
2. Yawan zikri yana jawo samun yardar Allah
3. Yawan zikri yana gusar da damuwa da baฦin ciki daga zuciya
4. Yawan zikiri yana jawo farin ciki da annushuwa da nasaษi a zuciya
5. Yawan zikiri yana ฦarfafa zuciya da jiki.
5. Yawan zikiri yana haskaka fuska da zuciya
7. Yawan zikri yana jawo arziki
8. Yawan zikri yana jawo samun kwarjini da jin dadi da farin jini
9. Yawan yana jawo samun ฦaunar Allah ta'ala, samun ฦaunar Allah shine babban buri.
10. Yawan zikri yana jawo kusanci da Allah, har a wayi gari mutum ya samu matsayin ihsani.
11. Yawan zikri yana jawo komawa zuwa ga Allah ta'ala, cikin farin ciki
12. Yawan zikri yana buษewa mutum kofa ta samun yarda, da kusanci (Alฦurbiyya) tsakanin sa da Allah ta'ala.
13.. Yawan zikri yana buษewa mai yinsa babun ilmi, duk sanda ya yawaita ambaton Allah, zai ฦara sanin Allah ta'ala.
14. Yawan zikri yana buษewa mutum matsayin ganin buwayar Allah ta'ala, da isar sa.
15. Yawan zikri zai sa Allah ya ambaci mai yawan yi, duk sanda ya Ambani Allah, shima zai ambace shi.
16. Yawan zikri yana raya zuciya domin zikri ga zuciya kamar kifi ne a cikin ruwa, yaya kifi yake kasancewa idan aka raba shi da ruwa? Haka mutum zai kasance idan baya ambaton Allah ta'ala.
17. Yawan ambaton Allah yana zama kamar abinci ga zuciya da rai.
18. Yawan zikri yana washe zuciya ya goge tsatsa daga cikin zuciya.
19. Yawan zikri yana kankare zunubi
20. Yawan zikri yana kare mutum daga ษimuwa da gafala.
21. Yawan zikri idan yana tuna Allah a cikin yalwa da wadata , Allah zai fidda shi daga cikin halin tsanani.
22. Yawan zikri yana tsaratarwa daga saukar azaba.
23. Yawan zikri yana jawo saukar nutsuwa da saukar rahma, da lulluษewar Mala'iku,
24. Yawan zikri yana shagaltar da harshe ga barin giba da gulma da ฦarya Annamimanci, da ashariya.
25. Majalisin da ake zikri, sheษan baya zama a wajan
Albarka tana sauka a Majalisin da ake zikiri.
26. Yin zikri yana kare mutum daga hasarar lokaci, da tashi da warin mushen jaki daga majalisi.
27. Duk wanda ya ambaci Allah a ษoye, har ya yi hawaye don ganin girman Allah, zai shiga inuwar al'arshi ranar Alฦiyama.
28. Idan yawan zikri ya ษaukewa mutum hankali, har ya zama baya rokon wata bukata, Allah zai bashi fiye da dukkan masu roฦo suka roฦa.
29. Zikri shine mafi saukin ibada mara wahala kuma ga yawan lada.
30. Daga cikin falalar zikiri, yana jawo a dasawa mutum bishiya a gidan Aljanna, kamar yadda yazo a hadisi, Duk wanda ya ce Subhanallahil azeem wa bihamdihi.
31. Daga cikin falalar zikri, Kalmomi guda biyu masu saukin faษa akan harshe masu nauyi akan sikeli, abin ฦauna a wajan Allah, Subhanallahi wa bi hamdihi subhanallahil azeem.
32. Dawwama a cikin zikiri yana ฦare mutum daga taษewa.
33. Zikri yana zama a kowane hali, babu sharaษin sai da Alwala ko tsarki.
34. Yawan zikri haske ne, a duniya da ฦabari da makoma da siraษi.
35. Yawan ambaton Allah shine tushen komai, idan ka sami arziฦin yawan sa ka gama sumun dukkan komai daga Allah.
36. Zikri yana kusanta abinda yake nesa, na buฦatu kuma yana nisanta abinda yake kusa, na damuwa da baฦin ciki.
37. Zikri yana tashin zuciya daga baccin gafala.
38. Yawan zikri yana jawo samun ษanษano mai faranta rai.
39. Mai yawan ambaton Allah, kada ka damu domin Allah yana tare da kai.
40. Yawan zikri yayi daidai da fita yaฦi da ciwar da dukiya mai yawa.
41.. Ambaton Allah shine tushen nuna godiya ga Allah, domin duk wanda baya zikri baya godiya.
42. Zikri yana jawo samun ni'ima daga Allah kuma yana tunkuษe Sakar fushin Allah. Mafi darajar mutane a wajan Allah shine wanda harshen sa ya zamo ษanye a wajan ambaton Allah ta'ala.
43. Allah ta'ala da Mala'ikun sa suna yin salati ga mai yawan ambaton Allah.
44. Yin zikri shine Asalin samun soyayyar Allah da tsira daga faษawa cikin maฦiya Allah ta'ala.
45. Yawan zikri yana jawo a sami katon dausayi a cikin aljanna.
46. Majalisin zikri wajan zaman Mala'ikun Allah ne.
47. Dukkan ibadu da Allah ya yi umarni a yi babbar Manufar su shine yawan ambaton Allah.
48. Dukkan ibadar da ake ambaton Allah da yawa a ciknsa tafi dukkan sauran ibadu kamar sallah bayan Tauhidi.
49. Yin zikri yana tsayawa a matsayin Sadaฦa da Aiyukan lada da ake yi da dukiya.
50. Ambaton Allah yana ฦara ฦarfin imani.
51. Yawan zikri yana sauฦaฦewa mutum duk wani abu mai wahala.
52. Yawan zikri yana jawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.
53. Zirki yana zama kariya daga sharrin magauta da maฦiya, musamman zikirin safe da yamma, da lokacin bacci.
54. Yawan zikri yana ฦare mutun daga munafunci domin munafukai basa ambaton Allah da yawa.
Misalin zikri,ูุงุงูู ุงูุงุงููู ูุญุฏู ูุง ุดุฑูู ูู ูู ุงูู ูู ููู ุงูุญู ุฏ ููู ุนูู ูู ุดูุก ูุฏูุฑ
duk wanda ya karanta wannan zikri ฦafa 100, da safe zai sami abubuwa guda biyar:
Kamar ya ฦดanta bayi goma, sai lada 100, za a kankare masa zunubi 100, zai zame masa tsari daga sheษan a wannan rana har zuwa yamma,... less
Maishaq Muhammad Wai Mai Yasa Al’ummah Duk Da Irin Kiranye Kiranyen Da Malamai Keyi Akan Gyaran Zuciya Basaji Ba Sa Kuma Yi Sai Watan Ramadhana Yazo, Anan Ne Zakaga Jin Tsoron Ubangiji Amma Da Zarar Watan Ya Gabata Sai Kuma Akoma Tamtar Ba’ataba Jin Tsoron Ubangiji Ba?!
Mustapha musa abu Aisha
KARANTA SURATUL BAQARA A... moreMustapha musa abu Aisha
KARANTA SURATUL BAQARA A GIDA
Manzon Allah ๏ทบ ya kwadaitar da mu akan yawaita karanta Suratul Baqara a gida, domin karanta musamman a gida akwai albarka ta musamman.... moreKARANTA SURATUL BAQARA A GIDA
Manzon Allah ๏ทบ ya kwadaitar da mu akan yawaita karanta Suratul Baqara a gida, domin karanta musamman a gida akwai albarka ta musamman.
Manzon Allah ๏ทบ yana cewa:-
*(Ku riqa karanta Suratul Baqara, domin roฦon karanta albarka ne, rashin...
*Darasi Akan... more*MU KOYI... moreMustapha musa abu Aisha
*MU KOYI IBADA*
*Darasi Akan... more*MU KOYI IBADA*
*Darasi Akan Azumi*
FITOWA TA BAKWAI-๐ต
ABUBUWAN DA KE KARYA AZUMI
*1-Jima’i:Akwai kaffara amma banda matar.Namiji ne kawai zai yi kaffarar* @Majmu’ul fatawa
*2-Zuwan Jinin Haila*
*3-Cin abinci da gangan*
*4-Yin amai da gangan*
*5-Zuwan jinin haihuwa*
*6-Shan taba ko wiwi da rana dama ita taba haramun ce shanta ko ba da Azumi ba*
*7-Allura a matsayin abinci ko qarin ruwa*
*8-Yin qarya tana vata Azumi ba karyawa ba*
*9-Cin duk wani abu mai Daukar sunan abinci da gangan*
ABUBUWAN DA BA SA KARYA AZUMI
*1-Kwana da janaba a jiki.Annabi ya kan wayi gari da janaba kuma yana mai azumi*
*2-Kurkure ‘baki da shaqa ruwa da yin aswaki*
*3-Sanya tozali da rana*
@Fathul Bari
*4-Sanya maganin ciwon ido*
*5-Sanya maganin ciwon kunne*
*6-Fitar maniyyi ta mafarki da rana*
@Subulussalam
*7-Yin qaho*
@Bukhari
*8-Rungumar mace da sumbatarta in ba ka da kaifin sha’awa*
*9-Zuba ruwa mai sanyi a fuska ko a kai*
*10-Dandana abinci amma a tofar bayan dandanawar*
*11-Amai ba da gangan ba.*
*12-Maganin da masu cutar ‘ASMA’ ke anfani da shi wato ( Inhaler ) lokacin azumi ba ya karya azumi*
*13*Shaqa maganin mura*
*14-Dibar jini a jikin mai azumi ba ya karya azumi*
@Fatawas-siyam, Uthaymin
*15-Cin abinci da mantuwa.[Allah ne ya ciyar da kai babu komi azuminka na nan]*
*16-Yin asuwaki ko makilin da burushi*
@Siyamu Ramadana na Jamil Zainu
*17-Yin wanka a rafi*
*18-Zuba ruwa a kai domin jin sanyi*
*19-Yin allura a jiki da sunan Magani bata karya azumi*
*20-Cire haqori ko cikesa ba ya karya azumi*
@Munajjid 70 Questions on Fasting
Idan mace tana da ciki sai ta ga jini ya zubo mata a gabanta,babu komai domin wannan ba jinin haila ba ne, azuminta yana nan bai lalace ba, ciwo ne ta nemi magani.
Amma da a ce tana haila sai ta ga hailarta ta dauke bayan alfijir ya fito ba zata yi azumi ba.
@Fatawas-siyam, Uthaymin
SHAN MAGANIN DAUKEWAN JININ HAILA DOMIN MACE TA YI AZUMI
Musulinci addini ne mai sauki baya kallafa ma mutum abin da bai iya wa, akwai hikimar Allah wajen yin hailar mace,Allah bai daura wa mace cewa ta sha wani magani domin jinin hailarta ya tsaya ba,amma da za ta sha wani magani domin hailarta ta tsaya babu komai kuma azuminta ya yi
matuqar dai wannan jinin ya tsaya,da sharadin cewa wannan maganin da ta sha baya cutarwa.
*Babban Malamin Hadisi Sheikh Muhammad Nasiruddeenil Albani ya ce babu laifi don mace ta sha magani don hailarta ta tsaya don ta yi azumi ko Hajji ba bu kome a gareta kuma azuminta ya yi*
@Fatawas-siyam, Uthaymin
*Shima Sheikh Mustafal Adawi ya ce babu komai azuminta ya yi indai wannan maganin ba zai cutar da ita ba kuma jinin zai dauke baki daya, amma da jinin zai dawo azuminta ya vace kuma sai ta rama wannan azumin*
@Fatawa Sheikh Albani 232
*Ya Allah ka isar da rayuwar mu watan Ramadhana muna imani da kyakkyawar... less
Mustapha musa abu Aisha
*_MA'ABUTA TAUHEEDI ALLAH YA HARAMTA MASU SHIGA WUTA_*
Suwane ne ma'abuta Tauheedi??
Ma'abuta... moreMustapha musa abu Aisha
*_MA'ABUTA TAUHEEDI ALLAH YA HARAMTA MASU SHIGA WUTA_*
Suwane ne ma'abuta Tauheedi??
Ma'abuta Tauheedi sune:-
"Masu bautar... more*_MA'ABUTA TAUHEEDI ALLAH YA HARAMTA MASU SHIGA WUTA_*
Suwane ne ma'abuta Tauheedi??
Ma'abuta Tauheedi sune:-
"Masu bautar Allah shi kadai tare da Ikhlasy tare riko da tafarkin Manzon Allah SAW,Sannan basu Shirka da Allah ko kadan,sannan sun nisanci dukkan Bidi'a da Son Zuciya,sune wadan sukayi imani da Allah shi kadai a matsayinsa na ABIN BAUTA NA GASKIYA kuma sukayi Imani da SUNAYEN ALLAH DA SIFFONSA MADAUKA,sannan basu wuce gona da Iri acikin sunayen Allah da siffofinsa,sannan sune sukayi Imani da Allah A matsayinsa na RABBU,wato shi kadan yake da Hallita kuma ya mallaketa kuma yake gudanar da al'amarinta baki daya..............".
Manzon Allah ๏ทบ yanà cewa:-
*(Babu wani daga cikin mutane da zai Shaida babu abin bautawa na gaskiya sai Allah shi kadai,kuma Annabi Muhammad ๏ทบ Manzon Allah ne,yana mai gaskata hakan acikin zuciyarsa,face Allah ya haramta masa shiga wuta)*
@ุตุญูุญ ุงูุจุฎุงุฑู - ุฑูู ุ (128)
Mi ake nufi da Shaidawa babu abin Bautawa da gaskiya sai Allah;-
*Yana nufi zuciyarka ta yarda hakan ta amince kuma ta gaskata hakan,sannan ka furta hakan da baki sannan ka bayyyana haka ta hanya yadawa tare da Ilimi hakan*.
Daga Ubbata bn Samit ุฑุถู ุงููู ุนูู Yace,naji Manzon Allah ๏ทบ yana cewa:-
*(Duk wanda ya Shaida babu abin bautawa na gaskiya sai Allah shi kadai,kuma Annabi Muhammad ๏ทบ Manzon Allah ne,Allah ya haramta masa wuta)*
@ุตุญูุญ ู ุณูู - ุฑูู : (29)
Manzon Allah ๏ทบ yanà cewa:-
*(Lallai Allah ya haramtawa Wuta cin naman wanda yace LAA ILAHA ILLALLAHU kuma yana nufin fuskar Allah da fadar hakan)*
@ู ุชูู ุนููู : (425-33)
yana cewa;-
Allah ya haramtawa wuta cin Naman ma'abuta TAUHEEDI,daga cikinsu àkwai wanda Allah ya haramta masa wuta gaba daya bazai taba shiga wutaba,sune masu imanin cikakke kuma masu ingantaccen tauheedi,wadan nan Allah ya haramta masu shiga wuta har abada,amma ma'abuta aikata manyan zunubai daga cikin ma'abuta TAUHEEDI kuma suka mutu basu tubaba,su wadan nan suna karkashin ganin dama ta Allah idan yaga dama ya gafarta masu ya shigar da su aljanna ba tare da wuta azaba ba,idan kuma yaga dama ya kama su da azaba daga baya ya shigar da su aljanna domin matsayinsu TAUHEEDIN da yake tare da... less
Maishaq Muhammad Assalamu Alaikum...
Barkanmu Da Wannan Lokaci Tare Fatan Alkhairi Ga Daukacin Ma’abota Wannan Manhaja Ta Bakandamiya, Allah Yasa Mu Karashe Yunin Wannan Lokaci Cikin Aminchi!
A ci gaba da kawo muku karon battar fasahar da marubuta ke yi a muhawarar da Bakandamiya ta shirya ta kuma ษauki nauyin aiwatarwa, a yau za ku ga yadda Hazaฦa Writers Association da Yobe Authors Forum suka ษarje guminsu tare da ruwan hujjoji a maudu&rsquo...
Mustapha musa abu Aisha
#MUTANE SUN KASU KASO BIYAR 5 GAME DA LADAR SALLAR SU
ุงูุนูููุงู ุฉ ุงูุฅูู ูุงู ู ุงุจููู ุงูููููููููููู ู ุฑูุญูู ููููููู ุงููู... moreMustapha musa abu Aisha
#MUTANE SUN KASU KASO BIYAR 5 GAME DA LADAR SALLAR SU
ุงูุนูููุงู ุฉ ุงูุฅูู ูุงู ู ุงุจููู ุงูููููููููููู ู ุฑูุญูู ููููููู ุงููู ุชุนุงูููฐ-:
Yana... more#MUTANE SUN KASU KASO BIYAR 5 GAME DA LADAR SALLAR SU
ุงูุนูููุงู ุฉ ุงูุฅูู ูุงู ู ุงุจููู ุงูููููููููููู ู ุฑูุญูู ููููููู ุงููู ุชุนุงูููฐ-:
Yana cewa:
"Mutane sun kasu kaso biyar 5 game da sallarsu da kuma matsayin sallarsu a wajan Allah:-
1-Mai laifi wanda Allah zaiyi masa Uquba saboda sallarsa.
Shine wanda baya cika sallarsa baya alwalar sallar ciakkiya kuma baya cika rukunan sallah baya cika wajiban sallar baya cika sharuddanta,yana yin sallar ne yanda yaga dama,sallarsa ta sabama irin Sallar Manzon Allah s.a.w, to mai irin wannan sallah Allah zaiyi masa uquba saboda sallarsa.
2-Wanda Allah zaiyi masa Hisabi akan sallarsa.
Shine wanda zaiyi sallah yazo da ita da rukunnanta da wajibanta da Sharuddanta,sai dai tun daga lokacin da aka kabbara sallar bai san ake cikiba har zuwa sallama,saboda zuciyarsa ta shiga tunani da shagala da tuniya ya manta ma sallah yake,da zaka tambayesa wani sura aka karanta bazai iya tunawa ba saboda zuciyarsa da tunaninsa basu cikin sallah,mai irin wannan sallah shine Allah zaiyi masa Hisabi akan sallarsa.
3-Akwai wanda Sallarsa take kankare masa laifukansa.
Shine wanda zai zo da sallarsa cikakkiya da rukunnanta da wajibanta da Sharuddanta cikakku,amma tun daga lokacin da ya shiga cikin sallar to yana cikin sauri da gaggawar yaga angama sallar,shaidhaninsa yana so ya karkatar da zuciyarsa amma yana kokarin yaki da zuciyarsa da shaidhan yaga ya maidao da hankalinsa gaba da akan sallarsa,mai irin wannan sallah shine Allah yake kankare masa laifunsa na tunanin da yake da saurin da yake acikin sallarsa,saboda jihadin da yayi na kokarin maido da zuciyarsa da tunaninsa cikin sallar.
4-Wanda yake dacewa da samun ladar sallarsa mai girma.
Shine wanda ya zo da sallarsa cikakkiya ta wajan rukunnanta da sharuddanta da wajibanta,da mustahabbanta tare da khushu'i da na zuciya dana gabbai ba tare da wani tunanin duniya ba acikin sallarsaba,to mai irin wannan sallah shine wanda Allah yake bashi ladar cikakkiyar sallarsa.
5-Wanda sallarsa take sanya ya sami kusanci da ita awajan Allah.
Wannan shine matsayin mai sallah mafi daukaka,shine wanda zaizo da sallarsa,cikakkiya ta wajan rukunnanta da sharuddanta da wajibanta,da mustahabbanta tare da khushu'i da na zuciya dana gabbai ba tare da wani tunanin duniya ba acikin sallarsaba tare da halarto Allah a zuciyarsa wato yana ganine na musamman da Allah zuciyarsa tana mai cike da tuna Allah da halartosa acikin sallarsa.
Dukkan wanda yazo da sallah wadda take dauke da sharudda da rukunnnai da wajibai da mustahabbai da khushu'i da cikakku tare da halarto Allah da tuna Allah da gani dashi kadai acikin sallarsa,kuma Allah yana kallonsa to hakika ya sami matsayi mafi daukaka daga cikin matsayin masu sallah,shine ya sami kusancin Allah ta dalilin wannan sallah... less
Takaitaccen Bayani
Ma'aboci karance karance ne domin karin ilmi da kaifin basira, Ma'abicin tafiye tafiye ne domin kara bude idabuwa cikin zamantakewa, Ma'abocin gudun cutarwa ne kuma Mai Rajin kare hakkin marayu, Mata da Yara duka. Bakomai bane kazama daidai haka ma bakomai bane na rashin daidai ka'iya zama daidai.