Bashir Adam
BAKANDAMIYA (1)
???? “IN KA ?I JI....” ????
GABATARWA:
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin ?ai, Tsira da Aminchi su Tabbata ga Shugabammu Annabi Muhammadu (S.A.W) Da Alaye Da Sahabbansa baki ?aya, Amin. Bayan haka:
“IN KA ?I JI...” Labari ne akan wani matashi mai suna Gagare, wanda ya gagari mahaifanshi, ya zama ri?a??en mashayi ?an bangar Siyasa.
Abubuwa marasa kyau na wa'azi sun same shi amma bai tuba ba, ya biye wa Shai?an har ya ?auracewa iyayensa. Dalilin hakan ne a ?arshe har ?waya ta sanya ya haukace ya zama wula?antacce a cikin al'umma. Ina fatan labarin zai nisha?antar, ya ilmantar kuma ya fa?akar. A sha karatu lafiya.
— Bashir Adam.
*** *** ***
A DANDALIN SHAYE-SHAYE
Zaune a dandalinsu na shaye-shaye suna fuskantar juna kamar yadda suka saba zama, matasa ne guda uku: Gagare, Goje da ?azaza, kowanne ya tuzgu?e dafe da hannu guda a ?asa, gudan hannun kuma rike da tsumma yana zu?ar Sholisho.
Hira suke yi irin tasu ta bugaggun mashaya wa?anda suka yi nisa cikin harkar chaskalewa.
Gagare ne ya fara magana cikin murya irin ta bugaggu, ya ce, “Kai! Wallahi băbă ba abinda ya fi rusu da?i! Don ni in har ina da ?waya ba ni da wata matsala! Wallahi ni fa da in rasa ?waya gwamma in rasa abinci!”
Goje shima cikin muryar makakku, yace: “?warai kuwa băbă, Wallahi gwamma rashin abinci da rashin ?waya! Ai ni shi yasa ma kuka ga kwata-kwata ba na bari ?waya tana yanke min!
Loading...