• Contrast
    • Font
    • A
  • Sign In
  • Sign Up
    Loading ...
View All Updates Mark All Read
Bakandamiya
  • Shafin Farko
  • Mambobi
  • Zauruka
    • Browse Groups
  • Tambayoyi
  • Ra'ayoyi
    • Browse Polls
  • Makalu
    • Browse Entries
  • Bidiyoyi
    • Browse Videos
  • Sautuka
    • Nemo Sautuka
  • Hotuna
    • Browse Albums
    • Browse Photos
  • More
    • Kasuwa
      • Stores Home
      • Browse Stores
      • Browse Locations
      • Products Home
      • Browse Products
      • Products Pinboard
      • Categories
      • Browse Reviews
      • Wishlists
    • Sana'o'i
      • Browse Listings
    • Sanarwa
      • Bukukuwa Masu Zuwa
      • Past Events
  • Updates
  • About
  • Abokai(69)
  • Bidiyoyi(1)
  • Hotuna(1)

Updates

About

Personal Information

  • Suna Abbah
  • Sunan Mahaifi Abbas
  • Jinsi Na miji
  • Ranar Haihuwa August 10, 2000
  • Takaitaccen Bayani My is Abbah from Zaria

Contact Address

  • Sunan Gari Kaduna
  • Karamar Hukuma Zaria
  • Jaha Zazzau
  • Kasa Nigeria

Abokai

  • Bakandamiya GORON JUMMA'A Assalamu alaikum Malam, Mutum ya rasu sai ya bar yayye biyu maza, da yayye mata wadanda suke uba daya, da kuma mahaifiyar sa, ya za a raba musu gadon? Amsa: Wa alaikum assalam, Za’a raba dukiyar kashi shida, a bawa uwa kashi daya, ragowar kashi biyar din a bawa yan'uwa su raba, namiji ya dauki rabon mata biyu. Amsawa: Dr. Jamilu Yusuf Zarewa Daga zauren Fatawowin Rabon Gado Guda 212
  • Rahmatu Lawan GORON JUMMA'A INA YAWAN FITAR DA MANIYYI SABODA MIJINA BA LAFIYA Tambaya: Assalamu Alaikum , Dr macece mijinta ba yada lafiyan aure tsawon lokachi, sai ya zamana tana yawan releasing ba sai tayi wani dogon tunani na sha'awaba, ya matsayin ibadarta yake? Amsa: Wa alaikumus salam To gaskiya abin da yake daidai shi ne: ya nemi magani, in kuma bai samu ba, ana iya raba auran, tun da yana daga cikin manufofin aure, katange ma'aurata daga fadawa haramun, kamar yadda shararren hadisinnan ya tabbatar. Yawan fitar maniyyi zai iya zama lalurar da za ta iya haifar da saukin sharia, saidai na ki ba zai zama lalura ba, saboda iyayenki za su iya wajabtawa mijin neman magani, in kuma bai samu ba, za ku iya rabuwa, Allah ya azurta kowa dağa falalarsa. Cigaba da zamanku a wannan halin yana iya jefa ki cikin hadari, mata nawa ne suka zama mazinata ta hanyar wannan sababin? Ya wajaba ki yi wanka duk sanda maniyyin ya fita, tun da ya fita ne ta hanyar jin dadi. ALLAH NE MAFI SANI Daga zauren Filin Fatawa na Dr. Jamilu Zarewa 12/6/1437
  • Lawan Dalha Ya Allah Ka sada mu da alkhairan da ke cikin wannan rana; ka tsare mu daga sharri duniya da lahira. #JummaaMubarak
  • Adamou Bagna Mahamane Welcome Ramadan!
  • Ali Ahamed Muhammed Ina mai yima kowa fatan Alheri💝
  • Jamilu Abdulrahman KUKAN KURCIYA Da sunan sarkina zan fara Wannan da shi ne ya yiwo fara Ya yi kare kana ya yo kura Ya yi ruwa kuma kana ya yo ƙura Hikimar Allah sam ba ta da iyaka. Tsira da aminci gun baban Zahra Wannan da cikin annabawa ya yo zarra Wanda duk wata daraja tuni ya tara Sahabbai da alaihi duka na tara Salati gare sa na ke furtawa babu iyaka. Wai mu yaushe ne za ko mu hankalta Mu zam nutsuwa da neman mafita A wayi gari junanmu za mu fifita Ai ya fi ace kawunanmu muka fifita Ko ba komai hakan ai zai fishe ka. Mu kawunanmu kawai muke hange Ba mu duban wanda yake a jikin shinge Na ƙoluwa kawai muke hange Taddo shi kawai muka daddage Kai mai dogon buri kam kaiconka. Ƙaddara dai kowa da akwai ta sa Riga ce da babu mai cire ta sa Da zamu gane mu daina sa-in-sa Akan abin da zai zo ne komai nisa In kuma munƙi za mu wahalta kamar wanda ya sha molanka. Allah ka tsare mu da na shina Ka sa mu zamo masu yin murna Da Duk abin da ka tsara mana Alfarmar annabinka mijin Nana Ka sa kar mu zamu cikin masu yin shirka. Jamilu ne ke waƙar daga nan gefen Domin isar da saƙo ga 'yan can gefen Fatana kowa ko ya amfana Da ɗan abinda na samu a karatuna Wannan ita ce riba da ba ta da iyaka. ©️✍🏻 Jamilu Abdulrahaman (Mr. Writer) 08185819176 Haimanraees@gmail.com
  • Maryamerh Abdul Wasa-wasa, karatun boko na neman fin karfin talaka a najeriya. Allah mun tuba
  • Rabiatu SK Mashi
  • Aisha Sa'eed Abubakar (Aishan Umma) *AHALINA* *Na* *Aishan Umma* *???????? ZAMAN AMANA WRITER'S (Z.A.W)* https://www.facebook.com/ZAMAN-AMANA-Writers-FANS-311893699485963/ 2019 1 Cike da zumud'in yau zasu zauna da mahaifansu ababen alfaharinsu suka tashi daga bacci, sakamakon yau babu makaranta. A gaggauce Fahat yayi wanka yasa Aida ma taje tayi sannan yayiwa sauran k'annensa guda biyu, duk suka shirya sannan suka fito. Fahat ne yayi saurin shiga kitchen dan anan ya jiyo motsin Amminsu, har k'asa ya tsuguna ya gaisheta, suma sauran k'annensa da suka shigo kitchen d'in yadda suka ga d'an uwansu yayi hakan sukayi, ta amsa cike da fara'a had'i da kulawa, duk seda ta shafa kawunansu tana mai karanta musu addu'ar da Annabi Sallalahu alaihi wa sallam yake karantawa Hassan da Hussaini (u'izukuma bi kalimatillahi tammat min kulli shaid'anin wa hamma, wa min kullu ainin lamma). Tana matuk'ar son yaranta, sosai take k'aunarsu, har wani lokacin takanyi tunanin Kodai mutuwa zatayi ta barsu ne?. Fahat ne ya katse mata tunaninta ta hanyar cewa "Ammi bari naje na gaida Abbu na dawo na tayaki da wani abin mana se mufi yin sauri". "A'a d'an albarka jeka ku gaisa d'in daga nan kuje ku gyara d'akunanku tukunna ni na k'arasa wannan" cewar Ammi Kafewa yayi yace "ai tunda babu school yau to zan tayaki aiki insha Allah, Habibtyna ina k'aunarki, bana son naga kina gajiya da yawa. Mene amfanin Allah ya baki ni amma na gagara taimaka miki, gaskiya inde kina so na samu lada ki bari na tayaki kinji Ammi na?" Tayi murmushi had'e da shafa kanshi tace "na amince to yaron kirki, kaida kake namiji kaine me son shiga kitchen ita kam Aida ko a jikinta, yanzu ko nace tazo muyinma se raina ya kusan b'aci, ban san inda ta koyi k'uiya ba. Allah ya raya mana ku, ya tsareku ya kare ku, Allah yayi muku albarka ya kareku dukkan sharri, ina alfahari da samunku masoya na sanyin idaniyata." Daga haka ya je ya gaida mahaifinsu, se gashi ya dawo tare da Aida suka ci gaba da aikinsu suna hirarsu ta tsakanin uwa da yaranta. A haka ta dad'a samu tayi ta yi musu nasiha akan halin rayuwa. Su ko su Sa'eed da Alim suna can wajen mahaifinnasu suna tayashi hira sakamakon weekend baya zuwa ko ina. A haka suma suka kammala aikinsu suka fito da komai suka jere a dinning area, kowa kuma ya hallara akayi bismillah aka fara cin abinci cikin ladabi. Haka rayuwar gidan take tafiya cikin aminci gashi dai ba wani me kud'i bane me gidan sedai rufin asirin Allah da kuma wadatar zuci, amma zuciyar mutanen gidan tana cike da k'aunar juna da kuma tausayawa. Iyayen suna k'ok'arin ganin sun bawa yaransu tarbiyya daidai gwargwardo, haka ma yaran suna biyayya ga iyayen nasu, duk kuwa da irin soyayyar da suke nuna musu hakan besa raini ya shiga tsakaninsu ba. Rayuwar gidan abar sha'awa ce ga duk wanda ya gani sedai san barka. Alhaji Nasir Aliyu (Abbu) shine mahaifinsu Fahat, se mahaifiyarsu Maryam, sunyi aure tsawon shekara goma sha bakwai kenan a yanzu. Allah ya azurtasu da yara hud'u Fahat shine babba wanda yake da shekara goma sha shida, se Aida take bi masa ita kuma tana da shekara goma sha d'aya, se Sa'eed me shekara bakwai, sannan auta Alim me shekara hud'u a duniya. A yanzu haka Fahat yana SS 2 a makaranta sannan yayi saukar Al Qur'an tun yana shekara sha hud'u yanzu hadda yake, ita kuma Aida tana Pri. 6 itama takai kusan izifi 30 a Al Qur'an, Sa'eed yana Pri. 2 yana uzifi 10 a Al Qur'an, se auta Alim yana Nur. 2 shi kuma izifi biyu a Al Qur'an Kwatsam wata ranar Juma'a bayan su Fahat sun tafi makaranta wani irin ciwon ciki ya taso Ammi a gaba, da k'yar ta iya lalubar wayarta ta kira Abbu ta sanar masa, cikin tashin hankali shima ya baro office domin yaga meke damunta har haka?, dan tabbas duk ciwon da Maryam zata bud'e baki ta fad'a harta kira a waya ba k'aramin ciwo bane. Da hanzari ya shiga d'akin ganin halin da take cikine ya sashi fita nemo mota dan baze iya d'aukarta a babur ba cikin wannan halin. Allah sarki Ammi! Allah ya baki lafiya ???? *Aishan Umma* ??????????????
  • Abdull Hamza Marwat
Previous
Next

Bidiyoyi

  • video
    By Abbah Abbas
    23 views
Previous
Next

Hotuna

  • Wall Photo­s 7 photos

Previous
Next
© 2021 Bakandamiya  -  About Us  -  Terms  -  Privacy  -  Advertise  -  Support Center  -  Mobile Apps  -  Contact Us
  • Facebook
  • Twitter
  • Linkedin
  • Youtube
  • Pinterest
  • Instagram