Assalamu... moreShuwagabannin wannan gasa, Alƙalai, abokan Muhawara, manazarta, masu saurare.
Assalamu Alaikum.
Sunana Umar Dalha.
Wakilin ƙungiyar Golden Pen Writer's Association. A yau ga mu a gaban ku, tare da tarin hujjoji na kare muradin cewar; Laifi Matar ne da ke bin mazan banza a waje.
Ana zaton wuta a maƙera, sai ta tashi a masaƙa. Babu laifin miji a wajen bin maza da matar shi take. Kwaɗayi, mabuɗin wahala. Domin kuwa abun a bayyane yake, wasu matan son abin duniya ya rufe masu ido, har ya kai ga duk ƙoƙarin mijinta bata gani ko ince ta raina, ita burinta ace komai ta nema dole ta same shi a lokacin da take so, in har matar aure zata sa irin wannan a zuciyarta dole ne ya kaita ga halaka bi ma'ana zina da igiya aurenta.
Baki da gashin wance, ba kya yi kitson wance ba. Abu na biyu kuma hangen rayuwar wasu cikin ƙawayenta ko dangin ta, na cewa lallai duk abinda ta gani a wajen su sai ta ce ita ma sai ta... less
Autar YayahWannan haka yake, musamman a wannan zamanin da muke ciki wacce kusan kashi casa'in cikin d'ari harkar karya ne a ciki, musamman a social media, kece kullum idan kika hau online zaki ga wance tayi d'au wanka da kayanta masu tsada wankan yau daban na gobe... moreWannan haka yake, musamman a wannan zamanin da muke ciki wacce kusan kashi casa'in cikin d'ari harkar karya ne a ciki, musamman a social media, kece kullum idan kika hau online zaki ga wance tayi d'au wanka da kayanta masu tsada wankan yau daban na gobe daban, ga mata da karancin tunani, kin zo zuciyar ki ta kwad'aita maki, gashi baki da halin hakan, duk irin wannan yana sakawa mata ta fad'a wannan harkar, don haka babu laifin miji a bin mazan da mata take yi a waje.
Bushirat
Wannan gsky ne ya umarr wasu matan nafara samun matsalane tun bisa ga tarbiyya da aka basu shi a gidan su, Allah ubangiji ya karemu ya kuma shiryi masu aikata hakan.
Fatima Batulah Umar
Abunda yake jawo wa wasu halaka kenan kaɗayi da son abun duniya, wasu matan basu iya hkr da rashin mijinsu duk abunda kika ga wata tayi to ke ma sai kinyi idan mijin naki bashi da sai ki fara bin wasu domin su yi miki abunda kike so
Umar Dalha → MARUBUTA:
Sabo tushen wawa. Da kamar wuya, gurguwa da auren nesa. Wasu matan da ke da ɗabi'un bin mazan banza kuma, sun samo asalin hakan ne tun suna ƴan mata. Sun kasance suna bin mazan banza har Allah ya kawo masu mazajen aure. Mai... moreUmar Dalha → MARUBUTA:
Sabo tushen wawa. Da kamar wuya, gurguwa da auren nesa. Wasu matan da ke da ɗabi'un bin mazan banza kuma, sun samo asalin hakan ne tun suna ƴan mata. Sun kasance suna bin mazan banza har Allah ya kawo masu mazajen aure. Mai hali, baya barin halinsa.... moreSabo tushen wawa. Da kamar wuya, gurguwa da auren nesa. Wasu matan da ke da ɗabi'un bin mazan banza kuma, sun samo asalin hakan ne tun suna ƴan mata. Sun kasance suna bin mazan banza har Allah ya kawo masu mazajen aure. Mai hali, baya barin halinsa. Daga lokacin da ta yi auren bayan ƴan kwanaki kaɗan zata fara tunanin bin mazan banza, komai kyautatawar da mijin ke mata, ba bu ruwan ta sabo da ta saba da bin mazan. Sabo tushen wawa. Hmm lallai A yi sha'ani, ɗanbirni ya cuci na ƙauye.
Duk wanda ya daka rawar wani, zai rasa turmin daka tasa. Wasu matan kuma bokaye ke fara sa su bin mazan banza a waje ba tare da shi mijin ya san me ke faruwa ba. Boka shi ne zai yi silar fara bin mazan ta a waje, daga lokacin da son zuciya ya kaita... less
Umar Dalha
Kuma dama duk inda son zuciya yake, to tabbas sai anyi na dama. Mata masu bin maza waje, tabbas mafi yawa suna yin nadama abisa wautar da suka aikata.
Anup JanyauKwarai da gaske, tin anan duniya Allah ke nuna musu kuskuran su, saboda sun cika maciya amana, kinada mijinki na sunnah amma kije waje kina bin mazan banza, wallahi waennan matan idan har basu tuba sun dawo ga Allah ba sun roki gafararsa da ta mazajen su... moreKwarai da gaske, tin anan duniya Allah ke nuna musu kuskuran su, saboda sun cika maciya amana, kinada mijinki na sunnah amma kije waje kina bin mazan banza, wallahi waennan matan idan har basu tuba sun dawo ga Allah ba sun roki gafararsa da ta mazajen su bazasu taba gamawa da duniya lafiya ba.
Anup JanyauWasu matan tun daga wurin tallah lokacin suna yan mata suke b’ata tarbiyar su, ana basu kuɗin da basu taka kara suka karya ba ko da sunyi aure ba zasu iya barin wannan mugunyar rayuwar ba dole sai sun nemi maza a waje.
Misali a da chan kafin tayi... moreWasu matan tun daga wurin tallah lokacin suna yan mata suke b’ata tarbiyar su, ana basu kuɗin da basu taka kara suka karya ba ko da sunyi aure ba zasu iya barin wannan mugunyar rayuwar ba dole sai sun nemi maza a waje.
Misali a da chan kafin tayi aure tana samun makuddan kudade tana kashewa duk abinda take so tana yiwa kanta, amma ta zo tayi aure bata samun wasu makuddan kuɗi a wurin mijinta waƴanda zasu isheta jin dadin rayuwarta. To shikenan an samu matsala sai kawai taga ai tsayawa gareshi bata lokaci ne gwanda ta je inda ake take samun kuɗi masu tsoka tun da ta san yadda harkar take, shikenan sheɗan ya kaɗa mata gangar ta cigaba da kazamtacciyar rayuwar da ta baro a baya. . less
Umar Dalha → MARUBUTA:
Allah wadarai naka ya lalace, raƙumin dawa ya ga na gida. Wasu matan son zuciya ne ke damun su. Idan mace har ta kasance mai son zuciya koma yaya mijinta yake da arziƙi kuma ya wadata ta, ba zai iya hana ta bin mazan banza ba a... moreUmar Dalha → MARUBUTA:
Allah wadarai naka ya lalace, raƙumin dawa ya ga na gida. Wasu matan son zuciya ne ke damun su. Idan mace har ta kasance mai son zuciya koma yaya mijinta yake da arziƙi kuma ya wadata ta, ba zai iya hana ta bin mazan banza ba a waje, tunda duk inda son... moreAllah wadarai naka ya lalace, raƙumin dawa ya ga na gida. Wasu matan son zuciya ne ke damun su. Idan mace har ta kasance mai son zuciya koma yaya mijinta yake da arziƙi kuma ya wadata ta, ba zai iya hana ta bin mazan banza ba a waje, tunda duk inda son zuciya yake to tabbas sheɗan nan yake baje kolin sa.
Banza girman mahaukaci, ƙaramin mai wayo yafi shi. Abu na 4 kuma, wasu matan ba su da isasshen ilimi ne. Shiyasa addinin musulunci ya yi mana ko yi da cewar; "Ana auren mace ne sabo da abubuwa guda hudu, na farko dan dukiyarta, na biyu dangantakarta, na uku don kyawunta, na hudu saboda Addininta".
Sai Manzon Allah (S.A.W) yace amma ka zabi ma'abociyar Addini tafi.
Hakika idan ka auri mace mai Addini mai bin umarnin Allah, zata kasance mai biyayya ga... less
faika Abubakar ouum khaleel
Dama indai akwai ilimi to dole mace ta maida lamuranta ga Allah,inko har kana bin dokokin ubangiji to shiko zai kareka daga sab'a masa.
Mukhtar Musa Karami Abu Hisham →... moreMukhtar Musa Karami Abu Hisham → MARUBUTA:
5/1/2021
MUHAWARA.
GABATARWA TARE DA... more5/1/2021
MUHAWARA.
GABATARWA TARE DA MARABA
Assalamu alaikum
A madadin abokan aiki na wannan Muhawara Muna yiwa Alkalai
tare da wakilan kungiyoyi,gami da sauran masu bibiyar wannan muhawara muna yi muku maraba da kasancewa da mu,fatan za mu baiwa...
Assalamu alaikum. Barkanmu da yau barkanmu da sake saduwa wannan ranar da muke gabatar muku da baƙon mako.
Kamar kullum mu kan zaƙulo haziƙan Marubuta har ma da mawaƙa don tattauna abubuwan da suka shafi rubutunsu har ma da rayuwarsu,in Sha Allahu... moreAssalamu alaikum. Barkanmu da yau barkanmu da sake saduwa wannan ranar da muke gabatar muku da baƙon mako.
Kamar kullum mu kan zaƙulo haziƙan Marubuta har ma da mawaƙa don tattauna abubuwan da suka shafi rubutunsu har ma da rayuwarsu,in Sha Allahu yau ma mun zo muku da wani gogaggen marubucin don tattaunawa da shi. An ce "waƙa a bakin mai ita...