Jinjina ta mussaman ga Mahukuntar Bakandamiya tare da Malam Danladi Haruna, da ya bamu horo na musamman kan Rubutun gajeren labari, tare da Abu Hisham daya kasance mai... morehttps://www.mujallaradabi.com/2020/09/an-sanar-da-sakamakon-karshe-na-gasar.html?m=1
Jinjina ta mussaman ga Mahukuntar Bakandamiya tare da Malam Danladi Haruna, da ya bamu horo na musamman kan Rubutun gajeren labari, tare da Abu Hisham daya kasance mai shiryawa tare da kula da shiri. Ina dada godiya, domin darasin dana dauka a nan shi ya bani damar shiga wannan gasar har na yi nasarar zuwa ta 2. Nagode! Nagode!! Nagode!!!
An sami karin mutane 189 da suka kamu cutar Coronavirus a Najeriya, jimilla... moreLabaran Safiyar Lahadi 20/09/2020CE - 02/02/1442AH. Cikakkun labaran
An sami karin mutane 189 da suka kamu cutar Coronavirus a Najeriya, jimilla... moreLabaran Safiyar Lahadi 20/09/2020CE - 02/02/1442AH. Cikakkun labaran
An sami karin mutane 189 da suka kamu cutar Coronavirus a Najeriya, jimilla 57,145.
An fara tattara sakamakon zaben Gwamnan jihar Edo a matakin unguwanni da aka yi jiya.
'Yansanda sun umurci Gwamna Wike na jihar Rivers ya bar jihar Edo.
Jami'an tsaro sun kama wasu mutane 4 da suka cusa sunayen ma'aikatan bogi a jihar Bauchi suna amsar albashinsu.
Gwamna Mai Mala na jihar Yobe ya ce suna kokarin gani jam'iyyar APC ta kawo canji mai ma'ana.
Gwamnatin jihar Filato ta kashe Naira miliyan 366 a yaki da cutar Coronavirus.
Gwamnatin jihar Katsina ta tallafa wa marayu 1,100 a kananan hukumomin yankin Funtuwa.
Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kashe 'yan Boko Haram 16 da kame 11 a yankin Arewa maso Gabas.
Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya karrama wanda ya ƙirƙiro wa kasar babban makami mai linzami.
An tuhumi fitattun 'yan siyasa a Habasha da hannu a aikata ta'addanci.
Mustapha musa abu Aisha
MADALLA DA WANDA YA SAMI ISTIGHFARI MAI YAWA A LITTAFINSA GOBE ALQIYAMA
Wannan wani bangane na Hadisin da ya tabbata daga Nana Aisha R.A awata riwayar Annabi s.a.w yana... moreMustapha musa abu Aisha
MADALLA DA WANDA YA SAMI ISTIGHFARI MAI YAWA A LITTAFINSA GOBE ALQIYAMA
Wannan wani bangane na Hadisin da ya tabbata daga Nana Aisha R.A awata riwayar Annabi s.a.w yana cewa:
(Madalla da Wanda ya sami istighfari mai yawa a cikin littafinsa agobe... moreMADALLA DA WANDA YA SAMI ISTIGHFARI MAI YAWA A LITTAFINSA GOBE ALQIYAMA
Wannan wani bangane na Hadisin da ya tabbata daga Nana Aisha R.A awata riwayar Annabi s.a.w yana cewa:
(Madalla da Wanda ya sami istighfari mai yawa a cikin littafinsa agobe alqiyama).
@أخرجه أبو نعيم في «الحلية» وصححه الألباني مرفوعا في «صحيح الجامع» (3930).
فضيلة الشيخ محمد بوسنة حفظه الله:
Yana cewa:
"Istighfari yana da fa'ida mai yawa,ya kai bawan Allah kasani,lallai istighfari yana da fa'idodi masu yawa da falala da lada mai girma anan duniya da gobe alqiyama,dan haka ka kwadaitu wajan samun wannan lada mai girma da fa'idodi masu yawa, kada ka yarda Shaidhan ya rudeshi yayi asarar wannan falala mai girma.
DAGA CIKIN FA'IDAR ISTIGHFARI
*1-ISTIGFARI YANA HANA SAUKAR AZABA*
Abu Musa Al'ash'ary R.A yana cewa:
"Hakika Allah yayi maku kyautar aminci guda biyu daga azaba"
Amincin farko shine:
Rayuwar Annabi s.aw a tare da ku.
sai ya ambata fadin Allah Madaukakin sarki:
﴿وَمَا كَانَ الله لِيُعَذِّبَهُمْ وَأَنتَ فِيهِمْ وَمَا كَانَ الله مُعَذِّبَهُمْ وَهُمْ يَسْتَغْفِرُون﴾
(Kuma Allah bai kasance Yanã yi musu azãba ba alhãli kuwa kai kanã cikinsu, kuma Allah bai kasance Mai yi musu azãba ba alhãli kuwa sunã yin istigfãri).
@[الأنفال😸3]
Aminci na biyu bayan rasuwar Annabi s.a.w wanda ya rage har zuwa ranar alqiyama shine:
"Yawaita Istighfari"
*2-ISTIGHFARI SABABINE NA SAUKAR ALBARKAR RUWAN SAMA DA SAMU YA'YA MASU ALBARKA*
(Shi na ce, 'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku , lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne,Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga, "Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya, Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna).
@[نوح:10-12]
Kuma Allah yana fada game da fadin Annabi Hudu ga Al'ummarsa sai yace:
﴿وَيَا قَوْمِ اسْتَغْفِرُواْ ر less less
Sunnace mai karfi daga cikin sunnonin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama baya barin sallar wutiri hatta lokacin bulaguro,kuma yayi wasiyyar kiyaye Wutiri ga... moreMustapha musa abu Aisha
#SALLAR WUTIRI
Sunnace mai karfi daga cikin sunnonin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama baya barin sallar wutiri hatta lokacin bulaguro,kuma yayi wasiyyar kiyaye Wutiri ga Sahabbansa da sauran... more#SALLAR WUTIRI
Sunnace mai karfi daga cikin sunnonin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama baya barin sallar wutiri hatta lokacin bulaguro,kuma yayi wasiyyar kiyaye Wutiri ga Sahabbansa da sauran al'ummar sa baki daya,wutiri yana farawa daga raka'a daya ko uku ko biyar ko sama da haka amma mara.
#Da Wutiri ne aka rufe sallar dare, wanda zai iya tashi cikin dare yayi Sallah an so ya jinkirta wutirinsa zuwa karshen dare, domin yinsa a karshen... less
Hukumar INEC ta bayyana Gwamna Obaseki na jihar Edo a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan da aka gudanar... moreLabaran Yammacin Lahadi 20/09/2020CE -... moreSANUSI IBRAHIM BISCO
Labaran Yammacin Lahadi 20/09/2020CE - 02/02/1442AH. Cikakkun labaran
Hukumar INEC ta bayyana Gwamna Obaseki na jihar Edo a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan da aka gudanar... moreLabaran Yammacin Lahadi 20/09/2020CE - 02/02/1442AH. Cikakkun labaran
Hukumar INEC ta bayyana Gwamna Obaseki na jihar Edo a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan da aka gudanar jiya.
Gwamnatin jihar Lagos ta bayar da umurnin sake bude Masallatai da Coci-coci a jihar.
Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III ya naɗa sabbin hakimai 15 a jihar Sokoto.
Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya ce sun gamsu da sakamakon zaben jihar Edo.
Wasu 'yan bindiga sun sace sama da mutum 40 a jihar Zamfara.
Gwamantin jihar Neja za ta yanke ruwan barikin sojoji saboda kin biyan kudin ruwan.
Gwamantin jihar Katsina ta gina azuzuwa 1,026 a cikin tsawon shekaru 3.
Hukumar ICPC ta ce ta fara gangamin wayar da kan al'ummomin jihohin Sokoto da Kebbi da Zamfara illolin rashawa.
Mukhtar Musa Karami Abu Hisham → MARUBUTA:
Wasa kwakwalwa
1- a. Muhammadu bawa (dan Anace). Dan Anace ya tashi ne a hannun kanin mahaifiyarsa Anace Shahararen mawaki wanda a wurinsa ne ya koyi kida da waka, shiyasa ake masa lakaci da dan anace✔️
... moreMukhtar Musa Karami Abu Hisham → MARUBUTA:
Wasa kwakwalwa
1- a. Muhammadu bawa (dan Anace). Dan Anace ya tashi ne a hannun kanin mahaifiyarsa Anace Shahararen mawaki wanda a wurinsa ne ya koyi kida da waka, shiyasa ake masa lakaci da dan anace✔️
b. Musa (dan kwairo). Sunan yaron... moreWasa kwakwalwa
1- a. Muhammadu bawa (dan Anace). Dan Anace ya tashi ne a hannun kanin mahaifiyarsa Anace Shahararen mawaki wanda a wurinsa ne ya koyi kida da waka, shiyasa ake masa lakaci da dan anace✔️
b. Musa (dan kwairo). Sunan yaron mahaifinsa ne da ake kira dankwairo, saboda yaron yana da zakin murya da kuma kwarewa wajen anshin, sai musa ya rika kwaikwayonsa tare da kwaikwayon muryarsa, da aka ga musa ya kware kamar shi dankwairon na asali, sai shima ake kiransa da wannan lakabi na dan kwairo✔️
c.Haruna (uji). Yaci sunansa na yanka ne a wurin wan mahaifinsa Haruna, Malam haruna uji yana da mata mai suna iya kura, lokacin Uji yana karami matan kanin babansa suna masa wasa suna ce masa mijin iya kura, a wannan lokacin yara kannensa basu da baki sai suke ce masa ujin iya kura maimakon mijin iya kura. Tun ana danganta sunan da ujin iya kura har aka daina akw cewa Uji.✔️
d. Adamu (dan maraya) jos. Ya samu lakanin dan maraya ne bayan mutuwar mahaifansa yana karami, sunan da dama al’adace a kasar hausa ta kiran duk wanda ya rasa mahaifansa biyu yana karami✔️
e. Ibrahim (Narambada). Ya samu sunan Narambada ne dalilin wata karyarsa da ake cewa rambada, sai ake yi masa lakabi da Narambada✔️
(Maki 20)
2. Alhaji Abubakar kassu zurmi✅
(Maki 10)
3. Ibrahim ❌
4. Garara- fatar buhu wadda akeyi da rama✔️
Masaki- katuwar kwarya
Gyartai- mai dinkin kwarya da ludduna
Kaba- tsiro ne da ake yin tabarma da faifai da igiya✔️
Na-gani-ina-so- kayan kari ne da saurayi ke kaima budurwa ya nuna dai yana son ta✔️
Sahani- buta/gora
Karanga- takaddar sumunti ana nade nama da ita/ kashi wanda aka kwalkwale tas shima ana kiransa karanga✔️
Akushi- kwanan cin tuwo wanda ake sassakawa da icce✔️
(Maki 20)
5a- 1, Ana amfani da karan dauri wajen nuna zancen wani, 2, Ana kuma amfani dashi wajen rubuta tagwayen kalma✔️
B- Ana amfani da alamar motsin rai wajen sanar da mai karatu wani abu ya faru, na takaici, tsoro, mamaki ko kuma kaduwa.✔️
(Maki 10)
6- Wadansu Abokai guda uku, suna zaune ana fira kowa yana fadar abin da ya gani a yawon dunarya. Na karshen bada labari ya ce,
‘a kamaru akwai dutsin da ya gani, sai da ya yi... less
Mukhtar Musa Karami Abu Hisham → MARUBUTA:
Kamal... moreKamal bala
Q5
1... moreMukhtar Musa Karami Abu Hisham → MARUBUTA:
Kamal... moreKamal bala
Q5
1 Karan ɗori: ana anfani da shi ne wajen raba tagwayen kalmomi✔️
2 Sannam ana anfani da ƙaran-dori wajen haɗa kalma da kalma.✔️
Alamar matsin rai (!): alamar motsin rai ana anfani da wajen da mai karatu wani abu na ta kaici, tsoro, kaɗuwa, mamaki da dai sauran su.
Misali: wayyo Allah na!
(Maki 10)
Q6
Waɗansu abokai guda uku suna zaune a na fira ko wa ya na faɗar abin da ya ga ni a yawon duniyarsa, na ƙarshen bada labari yace a "kamaru akwai dutsin da ya gani sai da yayi shekaru biyu cur wuta na ci a kansa ba tare da ta mutu ba. anan ta ke guda daga cikin abokan ya kada baki yace to damina da tazo kuma sai meya faru? mai bada labari yayi jim sannan yace ƙuta da cewa nan fa ake yinta.✅⁉️
(Maki 10)
Q3 Yusuf ali✔️
(Maki 15)
Q1
Alhaji musa (ɗan ƙwairo): Ya samu wannan lakabi na Dankwairo tun lokacin da Mahaifinsa na da Rai.Mahaifinsa ya na da wani Yaro da ake kira Dankwairo, saboda yaron zakin murya gare shi da kuma kwarewa wajen karbin waka, to sai Musa ya rinka kwaikwayonsa tare da kwaikwayon muryarsa , to da aka ga musan ya kware kamar shi Dankwairon na asali, sai shima ake kiransa da wannan lakabi na Dankwairo.✔️
Alhaji mamman shata: yasa mu wannam sunam ne a wajen Magaji Salamu, shine ya sa mishi suna Shata Mijin mai daki, ita mai dakin kaka ta ce, ita ce ta haifi wanda ya haife ni„⁉️
Haruna (uji): asalin inkiyar haruna uji, sunan sa na yanka haruna, ya ci sunan wan mahaifinsa, wato malam haruna. malam haruna mai suna uji yanada mata mai suna iya kura, lokacin uji yana ƙarami matan ƙanin baban sa suna masa wasa suna cewa mijin iya kura, mijin iya kura' awannam lokacin yara ƙanensa ba su da baki, sai suke ce masa, ujin iya kura, mai makon mijin iya. wannam shine asalin inda haruna ya samo inkiyar haruna (uji).✔️
Ibirahim (narambaɗa): asali Ya samu sunan Narambada ne dalilin wata karyarsa da ake ce wa Rambada, don haka sai aka yi masa lakabi da Narambada.✔️
Adamu (ɗan maraya): laƙabin sunam ɗan maraya ya samo asali ne a lokacim da mahafinsa ya rasu, inda kuma mahaifiyarsa ta rasu tun bai yi wayo ba, hakan ya sanya ake kiransa dan maraya.✔️
(Maki 20)
Q4
Masaki_karamar ƙwarya.✔️
Gyartai_me gyara tukunya, ɗinke takalmi, da sauran su.✔️
Kaba_ciyawa ce da ake yin tabarma da ita.✔️
Na gani ina so_Kayan da saurayi yake aika ma da budurwa gidan su, dan a san da zaman shi.✔️
Akushi_kwano ne me murfi amma sassaƙa shi a keyi da katako, har yanzu kuma gidajen sarauta suna amfani da shi.✔️
Sahani: yana nufin sunan mahaifi.❌
Karanga: ana nufin gyaɗa.❌
Gagara: kalmar gagara tana nufin ƙiriniya ko kuma rashin ji.❌
Mukhtar Musa Karami Abu Hisham → MARUBUTA:
MARYAM... moreMukhtar Musa Karami Abu Hisham → MARUBUTA:
MARYAM HARUNA
*Amsoshin wasa... moreMARYAM HARUNA
*Amsoshin wasa ƙwaƙwalwa*
1.
A. Dan'anace: Anace kanen mahaifiyar Muhammad Bawa Dan'anace ne. To Anacen ne ya yaye Muhammadu Bawa kuma a wurinsa ya fara tasowa har ya samu tarbiyar farko. Wannan dalili ne yasa ake ce mishi Dan'anace.✔️
B. Dankwairo: Ya samu Dankwairo ne daga sunan kanen mahaifinsa Kwairo. Ance Kwairo ya kasance mai zakin murya don haka shi ma Dankwairo da ya taso da irin muryar Kwairo, sai ake ce mishi Dankwairo.✔️
C. Haruna Uji: Haruna sunan wani yayan mahaifin Haruna Uji ne, to shine sai ake zolayarsa da sunan matar yayan mahaifin nashi mai suna, Iya Kura, ake ce mishi Mijin Iya Kura. Yara kanana ba su iya cewa "Mijin" sai dai "Ujin." Don haka sai sukan kira shi da Ujin Iya Kura. Daga baya sai aka takaita sunan zuwa Uji kawai.✔️
D. Danmaraya: Ya rasa mahaifinsa tun yana da kwanaki saba'in kacal a duniya, daga baya kuma mahaifiyarsa ta rasu tun kafin ya isa munzalin yaye. A bisa wannan tasowar da ya yi ba mahaifa masu kula ta hakika gare shi ne sai mutane ke yi mishi lakabi da Danmaraya.✔️
E. Narambada: Rambada sunan karya (dabba) ne. Wannan karya kuwa ta Makada Ibrahim ce tun zamanin yana da kuruciya. Yana jin son karyar nan kwarai, don haka mutane tun a wancan lokacin sai suke yi masa lakabi da Narambada, wato na ita wannan karya ke nan.✔️
(Maki 20)
4.
1. Sahani: Butar Ƙarfe.✔️
.
2. Na-gani-ina-so: Kayan da iyayen yaro ke kai wa gidan mahaifan yarinya wanda ke nuna ɗansu ya ga ɗiyarsu yana so. Kayan na-gani-ina-so sun danganci abubuwa kamar sandar sabulu da hoda da turare dss.✔️
.
3. Garara: Ana yin buhu na zuba tsaɓa kamar gero ko dawa. An fi ganin garara a wurin yan mata masu tallar goro, wato wannan abin baki da suke rufe goronsu da shi domin kar ya bushe.✔️
.
4. Masaki: Katuwar kwarya.✔️
.
(5. Kambu: Ɗamarar da akan ɗaura a dantsen hannu domin kariya.)
.
6. Kaba: Tsiro ne da akan yi amfani da shi wajen yin igiya da soson wanka da malfa (tabarmar kaba) da mafici da wundi da gurunfa da sauran su.✔️
.
7. Akushi: Mazubin abinci ne na gargajiya wanda masassaƙa ke yi. Yana da sulɓi daga ciki, akan yi mishi zane-zane masu kyau a bayansa. Ana yin sa da murfi yadda za a rufe shi rikif.✔️
.
8. Gyartai: Shi ne mutum mai sana'ar ɗinkin ƙwarya. ✔️
9. Karanga: Wata kalar leda ce wadda ake koya wa mata dinki da ita a da, yanzu kuma ana yin amfani da ita kamar wajen rufe bakin kwandon tumatir.✔️
(Maki 20)
Nana Aicha Hamissou → MARUBUTA:
Assalamu alaikum jama'a Barkarmu da warhaka barkarmu da sake kasancewa da ku a cikin wannan shirin namu. Fatan na same ku lafiya? Ya gida ya haƙuri? Allah Ya ƙara mana shi. Fatan alkairi a gare ku gaba daya ahalin... moreNana Aicha Hamissou → MARUBUTA:
Assalamu alaikum jama'a Barkarmu da warhaka barkarmu da sake kasancewa da ku a cikin wannan shirin namu. Fatan na same ku lafiya? Ya gida ya haƙuri? Allah Ya ƙara mana shi. Fatan alkairi a gare ku gaba daya ahalin Bakandamiya na gaishe ku kyauta Admin... moreAssalamu alaikum jama'a Barkarmu da warhaka barkarmu da sake kasancewa da ku a cikin wannan shirin namu. Fatan na same ku lafiya? Ya gida ya haƙuri? Allah Ya ƙara mana shi. Fatan alkairi a gare ku gaba daya ahalin Bakandamiya na gaishe ku kyauta Admin da member na gidan MARUBUTA.
In ba ku manta ba a shirin da ya gabata mun tsaya a daidai inda na ce maku ana yi taro tsakanin ƴan'matan amarya da abokan ango, suna yi meeting wa junansu. Yadda meeting ɗin yake shi ne kafin zuwan ranar ango zai kira amarya ya faɗa mata rana kaza akwai meeting, ita kuma sai ta fara kiran kawayenta tana faɗa masu rana kaza akwai meeting tare da abokan ango(yawanci bayan sallar la'asar ake yi).
In ranar ta zo sai ƴan'matan amarya su taru gidan su amarya zuwa la'asar , in sun iso sai su yi shawara wa junansu abubuwan da za su rubuta wanda angaye za su ba su in sun je wajen su. Bayan sun gama tsarsawa sai guda cikinsu ta rubuta saman takarda. Sai a kira angaye a ce masu su zo su ɗauki ƴan'matan amarya , in kuma sun zo to sai su kwashi ƴan'matan amarya cikin mota su kai su inda za a gudanar da taron. Bayan an je an gaisa sai ɗaya daga cikin ƴan'matana amarya ta karanta takardar da suka yi rubutu a kai angaye suna saurare bayan ta gama su ma sai su ce ga abubuwan da su bayar sai ayi tattaunawa kowa yana magana wa junansu.
Ga abubuwan da ƴan'matan amarya suke cewa a ba su kamar haka:
Kuɗin kunshi
Kuɗin kari (breakfast)
Kudin kujeru da runfa
Kuɗin abincin ƴan'matan amarya ranar aure
Kuɗin damu
Katon Chewing-gum
Juice
Da sauran su.
In angayen ba su da mako🤣🤣🤭🤭🤭🤭 nan da nan ake gamawa in Kuma masu mako ne sai ayi ta fafatawa.
Bayan an gama sai su faɗi ranar da za su kai masu kuɗin da suka yi masu alkawari, wasu kuma tun ranar suke bayarwa kun san kowa da kalar halinsa. Daga nan sai su ba ƴan'matan amarya lemon su zo tafi da shi, wasu kuma tun can suke raba shi. Da suka gani yawanci wasu ba su sha a can suna jin nauyi sai suke bada shi ana tahowa da shi gidan amarya sai sun je can su raba. Sai su mayar da ƴan'matan amaryar gidansu amarya wasu kuma a kai su har gida in suna buƙatar hakan.
Mukhtar Musa Karami Abu Hisham → MARUBUTA:
AMSOSHIN WASA KWAKWALWA DAGA ALKALAI.
1.
1.... moreMukhtar Musa Karami Abu Hisham → MARUBUTA:
AMSOSHIN WASA KWAKWALWA DAGA ALKALAI.
1.
1. Dan'anace: Shi Anace kanen mahaifiyar Muhammad Bawa ne (Dan'anace). Anacen shi ne ya yaye Muhammadu Bawa kuma a wurinsa ya fara tasowa, inda ya samu tarbiyar farko ta yarinta daga wurinsa. Wannan dalili ne ya... moreAMSOSHIN WASA KWAKWALWA DAGA ALKALAI.
1.
1. Dan'anace: Shi Anace kanen mahaifiyar Muhammad Bawa ne (Dan'anace). Anacen shi ne ya yaye Muhammadu Bawa kuma a wurinsa ya fara tasowa, inda ya samu tarbiyar farko ta yarinta daga wurinsa. Wannan dalili ne ya sa ake yi wa Muhammadu Bawa lakani da Dan'anace, wato shi d'a yake ga Anace.
2. Dankwairo: Alhaji Musa ya samu lakanin Dankwairo ne daga sunan kanen mahaifinsa mai suna Kwairo.An ce Kwairo, wato kanen mahaifin Alhaji Musa ya kasance mai zakin murya kwarai, don haka da shi Alhaji Musan ya taso da irin muryar Kwairo, sai ake ce mishi Dankwairo.
3. Haruna Ujin Iya Kura. Yadda abun yake shi ne, Haruna sunan wan mahaifin Haruna Uji ne, don haka sai ake zolayarsa da sunan matar wan mahaifin nashi mai suna Iya Kura, ake ce mishi Mijin Iya Kura. Yara kanana kuwa ba su iya cewa _"Mijin"_ sai dai "Ujin." Don haka sai sukan kira shi da Ujin Iya Kura. Daga baya sai aka takaita sunan zuwa Uji kawai.
4. Danmaraya: Allah Sarki, rayuwa! Alhaji Adamu ya rasa mahaifinsa tun yana da kwanaki saba'in kacal a duniya, daga baya kuma mahaifiyarsa ta rasu tun kafin ya isa munzalin yaye. A bisa wannan tasowar da ya yi ba mahaifa masu kula ta hakika gare shi ne sai mutane ke yi mishi lakabi da Danmaraya.
5. Narambada: Rambada sunan karya (dabba) ne. Wannan karya kuwa ta Makada Ibrahim ce tun zamanin yana da kuruciya. Yana jin son karyar nan kwarai, don haka mutane tun a wancan lokacin sai suke yi masa lakabi da Narambada, wato na ita wannan karya ke nan.
2
¹. Alhaji Abubakar Kassu Zurmi. Yana fadi da kansa cewar,
_" Kai Ubangidan Shanu da Gambu,_
_Na Dela albarkacinka nis sabu da Shata,_
_Hay yay yi man kujerah haji niz zo."_
². Alhaji Sale Gambara.
3.
Sheikh Dr. Yusuf Ali Galadanci.
4.
Sahani:> Butar Ƙarfe ke nan, wato _kettle_ da Ingilishi. A katsina ana ce mata _Kullu_ a Sakkwato kuwa sukan kira ta da _Kullumi._
.
Na-gani-ina-so:> Kayan da iyayen yaro ke kai wa gidan mahaifan yarinya wanda ke nuna ɗansu ya ga ɗiyarsu yana so, kamar dai a ce ɗaurin kaba ne. Sai dai kayan na-gani-ina-so sun danganci abubuwa ne kamar sandar sabulu da hoda da turare da makamantansu, ɗaurin kaba kuwa yan kuɗaɗe ne da manemi ke ba wadda yake so tun gabanin manya su shiga zancen.
.
Garara:> Algarara _(hessian da Ingilishi.)_ Ana yin buhu na zuba tsaɓa kamar gero ko dawa da ire-irensu. An fi ganin garara a wurin ƴan mata masu tallar goro, wato wannan abin baƙi da suke rufe goronsu da shi domin kar ya bushe.
.
Masaki:> Ƙatuwar ƙwarya ce da ƴan koda (masu sana'ar sussuka) ke amfani da ita wajen shiƙar hatsi, (a raba shi da ƙaiƙayi) idan an sussuka.
Kaba:> Tsiro ne da akan yi amfani da shi wajen yin igiya da soson wanka da malfa (tabarmar kaba) da mafici da wundi da gurunfa da sauran su. (A fronds of a young dum-palm).
.
Akushi:> Mazubin abinci ne na gargajiya wanda masassaƙa ke yi. Yana da sulɓi daga ciki, akan yi mishi zane-zane masu kyau a bayansa. Ana yin sa da murfi yadda za a rufe shi rikif. An ce idan an zuba abinci a cikin akushi aka rufe, to yana daɗewa bai huce ba, tamkar dai kula da zamani ya kawo.
.
Gyartai: > Shi ne mutum mai sana'ar ɗinkin ƙwarya. Calabash-mender da Ingilishi.
Karanga:> Wata kalar leda ce wadda ake koya wa mata dinki da ita a da, yanzu kuma ana yin amfani da ita kamar wajen rufe bakin kwandon tumatir.
5
6
Wadansu abokai guda uku suna zaune ana fira, kowa yana fadar abinda ya gani a yawon duniyarsa. Na karshen ba da labari ya ce a Kamaru akwai dutsin da ya gani sai da ya yi shekaru biyu cur wuta na ci a... less
*GODIYA* Ina ƙara miƙa godiya ta ga Allah madaukakin sarki wanda ya bani da ma da ikon sake zo maku da wannan ƙayataccen labarin, cikin hikimarsa da iyawarsa ya aramn damar dasa alkamina domin na yi nuni tare da ishara ga wani abun da ba dai-dai ba.
Tsira da aminci su ƙara tabbata ga Annabi Muhammadu (s.a.w) haka ga sahabbansa da iyalan gidansa.
*GARGAƊI* Wannan labarin gaba ɗayansa ƙirƙira ne, na kuma samar dashi ne don yin nuni tare da faɗakarwa akan wasu mutane masu irin halayyar da zata zo a labarin, idan hakan ya yi dai-dai da rayuwarka/rayuwarki, to hasashe ne kawai.
DEDICATED TO: ALL MEMBERS OF AREWA WRITERS ASSOCIATION
Ina fatan Allah ya ƙara haɗe kanmu, much love🥰🥰
Da misalin karfe 7 na safiyar ranar talata wata daleliyar mota ce ke sharara gudu akan titi, yayin da wata motar 'yan daba ke binsu a baya da alama hari suka kawo masu.
Tuƙi yake hankalinsa a tashe yayin da yake hangensu ta jikin madubin gefen motar, sai gudu yake shararawa kamar ba gobe, fatarsa shine ya isa makarantarsu yaron ya sauke shi lafiya, idan ya so ko miye shi ya faru akansa, amma ya na so ya kare rayuwar ɗan talikin yaron nan.
Gudun kawai yake yayin da hankalin ƙaramin yaron da ke zaune bayan motar [wanda ba zai wuce 11 – 12 years ba ] yay matukar tashi.
Abdul ya ja nakasasshiyar ƙafarsa tare da juyawa baya ya na hangensu ta cikin glass da idonsa wanda ya kasance kwaya ɗaya jal.
Ganin baƙar motar na cigaba da biyo su ya sanya ya juyo cike da firgici; ya buɗi bakinsa da ya kasance rabi, ya ce ‘’Dan Allah baba direba ka ƙara sauri, in sunka kama mu kashe mu za su yi.’’
Ya faɗa cikin muryarsa da bata fita dai-dai, saboda tawayar dake ga halittar bakinsa.
Idonsa kuwa sai tsiyayar da hawaye yake.
Nan fa hankalin baba direba ya kai ƙololuwa gun tashi.
A dai-dai lokacin ne kuma suka iso Abuja Road,titin da ya kasance tsit,saboda rashin hayaniyarsa.
Anan suka yi yunƙurin shiga gabansa da motarsu, har ma motarsu tana zozar tasa.
Cikin zafin nama Baba Direba ya ture motarsu tare da shammatarsu ya zubawa motarsa speed, kafin su ankara ya kai ƙarshen titin.
Ganin hakan yasa suka karo gudu, ba su kuma haɗuwa ba sai a round ɗin da zai sadaka da (Government house) gidan gwamnati na jihar Sokoto.
Saboda haka sai suka daina gudun, suna dai bin shi baya a hankali, kasancewar gun babbar hanya ce suna gudun jama'a su ankara da nufinsu.
Shi kuwa Baba Direba ya na ganin ya samu dama, sai ya miƙe hanya samɓal ta kan babban titi, su kuwa sai suka kewaya ta ɗaya hanyar, da zimmar su haɗu da shi ta hanyar da bata da hayaniya sosai don su samu damar sace yaron cikin sauƙi.
Da wannan damar Baba Direba ya yi amfani ya ci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali har ya isa *Abdulrashid Adisa Raji special school sokoto* ya sauke yaron.
¥¥¥¥¥¥¥¥
'yan daban kuwa, da suka tabbatar sun rasa shi, sai suka nemi guri suka faka motarsu.
Ogansu ne ya fito ya na neman wani layi a wayarsa, ringing biyu ana uku aka ɗaga kiran.
A can bangaren Kulu mai adashen sharri ce ta ɗaga wayar ta na masa kirari da cewa "An gaida Gumush, sannu sikelatu mai magana ƙahwahu masu tahiya da kansu, ka ga hitilar sheri, koy-yada ka ya yadama kai nai hitina, ga ka ranke-ranke amma sherinka ya hika yawa, yaya aiki ya yi kyau dai koh." Ta ƙarashe zancen da tambaya.
Shi kuwa Gumush tunda ta fara masa kirari, yake hura hanci, sai da ta dasa aya, sannan ya ce "Hajjiya an samu matsala, wallahi Direban nan shegen gudu ga rai, amma kat ki damu na rantse da takobina *Zarta* nan gaba bai isa ya hana mu ɗaukar yaron nan ba."
Wani uban tsaki mai adashen sharri ta ja, sannan ta ce "Amma wallahi ka ba ni kunya Gumush, ganin ƙwarewarka da can-cantarka yassa nit baka wanga aiki, amma shina kaka hwaɗamin wai an samu matsala?"
Cikin rangaji irin na 'yan maye ya ce "Ya isheki hwa to, ni dai yanzu ki hwaɗamin inda zan cimmiki in kai miki motakki, ki bamu 'yan canjinmu mu ware."
Wata uwar ashar ta lailayo ta ce "Kutuma! Kama raina ma kanka hankali wallahi, har ma wasu kuɗɗi kaka magana bayan ka ɓata muna plan?"
"Haba dai Hajjiya! Ke san dai dole ki bada na chaji, saboda wagga wahala da mun ka sha ni da yarana bai yiwuwa ta tashi ga banza."
Ya faɗa cikin Muryar 'yan ƙwaya da alama ya yi mankas ne, duk suma sauran yaransa a make suke.
Akan haushi bata samu damar sake cewa komai ba, kwatance kawai ta musu ta kashe wayarta ta na tunanin yanzu me zata gayawa Hajiya?
Cikin motar suka koma ɗaya daga cikin yaran ya ja motar suka nufi gun da ta kwatanta masu.
Ƙarfe ɗaya da rabi na rana aka tashi yara daga makaranta dama can Baba direba tun ƙarfe ɗaya ya nufi makarantar, don haka koda yara suka turo Abdul akan keken guragunsa sun tarar da Baba Direba a gate ya na jira, buɗe motar yayi ya sunkuci yaron ya saka shi a ciki, sannan ya juya ya ɗauke keken ya saka a Boot ɗin motar, ya kewaya ya shiga ya ja sai Sama-road unguwarsu Abdul ɗin kenan.
%%¥¥¥¥¥¥
Wata mata ce wacce ba za ta haura shekaru talatin da bakwai zuwa da takwas ba, zaune take akan kujerar falo ta miƙe ƙafarta akan table dake gabanta, sai kallon makekiyar screen tvn dake manne a bangon ɗakin take, gefe ɗaya kuma ga juice a gabanta tana kurɓa, hankalinta kwance, kallo ɗaya zaka mata ka fahimci tana cikin nishaɗi, don kuwa murmushi ne kwance akan fuskarta.
Turo ƙofar falon da aka yi ne ya dawo da ita daga duniyar nishaɗin da ta afka.
Zumɓur ta miƙe ganin Baba Direba ne ya turowa Abdul kekensa suka shigo falon, nan da nan fuskarta ta bayyanar da mamaki ƙarara ga kuma tsabar ɓacin rai kwance akan fuskarta, me hakan ke nufi? Ya ta ga Abdul anan ita dake zaman jiran gawarsa?
Baba direba ne ya tsinke mata tunani da cewa "Hajiya Barka da rana, ya gida?"
A hargitse ta juyo cikin murmushin yaƙe ta ce "Alhamdulillah! hak-kun dawo?"
"Eh, Hajiya." Ya bata amsa.
Murmushin yaƙe ta yi a karo na biyu ta ce "Sannunku da zuwa kun sha hanya, in ce dai babu wani abu da yas-same ku a hanyar tafiyarku da dawowarku?"
Ta ƙarashe zancen a lokacin da ta isa gaban Abdul ta tura kekensa zuwa tsakiyar falon.
Baba Direba ya ce "Babu komi Hajjiya, ƙila wani mummunan abu ya tashi hwaruwa, amma da yake Allah ya na kare salihan bayinsa waɗanda basu da haƙƙi a kansu, sai gashi mun dawo lahiya."
A firgice ta juyo ta kalle shi domin a zatonta ko ya gano shirinta ne, kun san an ce mara gaskiya ko cikin ruwa ya yi jiɓi.
Murmushi kawai Baba direba ya yi ya juya ya koma bakin aikinsa, zuciyarsa na masa saƙe-saƙe akan uwar ɗakinsa Hajiya Haseena.
Ita kuwa tura keken da yaron ke kai ta yi zuwa ɗakinsa, ta na buɗe ƙofa ta wawwaiga ta ga ba kowa, kawai sai ta ta tura keken da ƙarfi, ta juya abinta cike da jin zafi da raɗaɗin abinda ƙawarta Kulu ta mata.
Keken kuwa sai da ta haɗu da jikin gadonsa sannan ta tsaya sakamakon to kare tan da gadon ya yi, bawan Allah Abdul kuwa tuni ya faɗo ƙasa ji kake tim! Kansa ya ƙumu a ƙasa.
Ba ya da wani ƙarfi ko kuzarin da zai iya miƙewa da kansa, kasancewarsa gurgu wanda ƙafarsa take a lanƙwashe, gashi tun asali shi ba lafiyayye ba ne, hakan ta saka ya kasa tashi daga gun, ya na nan kwance sai kuka yake shi kaɗai, gashi kuma Mamma ta rufe ƙofar ɗakin bare wani ya hango shi ya zo ya taimake shi.
Ko da yake ba mai shigowa cikin falon nasu kai tsaye sai Abbunsa kuma yanzu ya tabbatar ya na kasuwa, saboda haka ya ci gaba da kukansa tare da yunƙurin taimakon kansa da kansa.
¥¥¥¥¥¥¥
Hajiya Haseena kuwa ta na shiga ɗakinta kai tsaye gun da wayarta take ta nufa, cikin fushi ta kira layin ƙawarta Kulu mai adashen sharri, sai dai har kiran ya tsinke bata ɗaga ba, kira biyar ta jera mata amma ba'a ɗaga ko ɗaya bs, a zuciye ta ajiye wayar ta koma kan gadonta ta kwanta ta na famar jijjiga ƙafa tare da ƙissima irin rashin mutuncin da za ta yiwa ƙawar tata, a ranta ta ce "Lallai Kulu ke raina ni, ni zaki yiwa haka?"
A bangaren mai adashen sharri kuwa, ba komai ne ya hana ta ɗaga wayar ba, sai tsoro da fargaba da suka gama mamaye ta, tasan yanda Hajiya ta ɗau zafi a maganar nan, ga shi ta yiwa hajiyar alƙawarin yau za'a gama da wannan matsalar, amma sai ga shi wancan banzan ya rosa masu plan, tun bayan da ya kawo mata motar ya juya take son ta kira Hajiya Haseena a waya amma ta kasa, sai ga shi yanzu ta kira, tabbas kuwa yaron ya koma gida shiyasa take nemanta, ta na ɗaga wayar kuwa tasan kan zancen shiyasa ta ƙi ɗagawa a nufinta bari zata yi sai hajiyar ta huce sannan ta kira ta ta lallashe ta.....
Tofah! Readers ku dagajin wannan labarin kunsan akwai sarƙaƙiya acikinsa.
Shin ya matsayin Hajiya Haseena ya ke agun Abdul?
Ina mahaifinsa?
Wace rayuwa yake fuskanta a cikin gidansu?
Shin wace iriyar halitta ce wannan ga Abdul?
Don cin cigaban wannan labarin ku biyo alƙalamin Ruky don jin ya za'a ƙare.
Adadin Comment naku shi zai bani damar ci gaba ko akasin haka.
Barkanmu da yau barkanmu da sake haɗuwa a sabon shirin na mu na baƙon mako,wanda yake zuwa muku duk ranar talata.
A yau shirin na mu ya yi tattaki wajen zaƙulo muku wani fitaccen, shahararren sannan kuma... moreAssalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu
Barkanmu da yau barkanmu da sake haɗuwa a sabon shirin na mu na baƙon mako,wanda yake zuwa muku duk ranar talata.
A yau shirin na mu ya yi tattaki wajen zaƙulo muku wani fitaccen, shahararren sannan kuma sanannen marubuci wato Malam Bukar Mada wanda yana ɗaya daga cikin waɗan da suka sabunta littafin nan mai suna Dare Dubu Da Ɗaya. Don jin wane ne shi da kuma nasarorin da ya samu a kan rubutu sai ku kasance da mu masu gabatarwa Maryam Haruna da Hauwa'u Muhammad, Muna yiwa babban bako Barka da zuwa. less
Tabbas kuwa ni ma ina daya daga cikin daliban MAKARANTAR MALAM BAMBADIYYA kuma babu laifi Farfesa ya taimaka mun fahimci abubuwa da yawa na dabarun rubutu
Rahmatu LawanAllah Ya saka wa masu shiryawa da gabatar da wannan shiri da alheri. Sannan ina yiwa bako, Mal. Bukar jinjina, Allah Ya kara basira da hazaka, amin.\n\nA min afuwa da jinkirin da na yi na mika tambayata.\n\nGame da rubuce-rubucen batsa da yanzu suka zama... moreAllah Ya saka wa masu shiryawa da gabatar da wannan shiri da alheri. Sannan ina yiwa bako, Mal. Bukar jinjina, Allah Ya kara basira da hazaka, amin.\n\nA min afuwa da jinkirin da na yi na mika tambayata.\n\nGame da rubuce-rubucen batsa da yanzu suka zama ruwan dare musamman a online writers, wani mataki ku ke dauka, a matsayinku na manya, akan su wadannan marubuta misali ko a kungiyance? Wato baicin wa'azi da ake musu na su ji tsoron Allah.\n\nSannan akwai wani hubbasa da ku ke yi domin hada kai da mahukunta don ganin an karya lagon irin waddannan bata garin marubuta? less
SANUSI IBRAHIM BISCO
...... moreSANUSI IBRAHIM BISCO
... more
Home
News
Politics
Culture & Arts
Policy
Science & Tech
Business
Exclusive
Hausa
SIGN IN
Welcome!Log into your account
your username
your password
Forgot your password?
PASSWORD RECOVERY
Recover your password
your email


Home Hausa
Hausa
Tarihi ya nuna Sarki Muhammad Sanusi 11 na iya zama Sarkin Zazzau
By
Fahad Galadanci
-
September 22, 2020
2
0

Wani marubuci Kuma masanin Tarihi Mai suna Malam Aldaurawiyah, Yace “Fadar masarautar Zazzau da ilahirin mutanen kasar Zazzau yanzu haka sun zura ido su ga wanda za a nada a matsayin sabon Sarkin Zazzau na gaba, bayan rasuwar Mai martaba Alhaji Shehu Idris”.
A nan a cikin wannan labarin, zan fada maku wani kyakkyawan dalilin da zai iya sa Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ll, ya zama sarki na gaba a masarautar Zazzau.
“Da farko, dalilan da ke yawo kan dalilin da yasa za a nada shi a matsayin Sarkin Zazzau saboda; Sanusi ya taba zama Sarki kuma ya fito daga gidan sarauta, ya yi karatun addini da na Zamani kuma na uku, Sanusi aboki ne ga gwamnan jihar kaduna dalilin da yasa Sanusi zai iya zama sarkin Zazzau shine saboda alaƙar kakannin da ke tsakanin masarautun Kano da Zazzau. Idan za ku iya tunawa daga tarihin masarautar Hausa, Bawo, ɗan Bayajidda ya haifi ‘ya’ya bakwai, waɗannan 7 bi da bi sun mulki Daura, Kano, Katsina, Zazzau, Gobir, Rano da Garin Gabas. Ana iya ganin Bawo akan lambar motar Sarkin Daura. Wannan ita ce fadar mai martaba sarkin Daura,wacce aka yi amannar ita ce hedkwatar asalin jihohin Hausa”.
Don haka, Kamar yadda tarihi ya nuna, manyan masarautun Zazzau da Masarautar Kano ‘yan uwan jini ne,’ ya’yan sarkin Daura, Bawo. “ “Allah Ya gafarta kurakuran Mai Martaba, Marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Dr. Shehu Idris kuma Ya ba shi masauki a Aljannatul Firdaus. Kuma Allah Madaukakin Sarki Ya zaba mana mafi alheri a matsayin magajinsa”
TAGS
Jihar Kaduna
Masarautar Zazzau
Muhammad Sanuni 11
Nasir Elrufai
Sarkin Zazzau
Tarihi
Previous article
HOW I BECAME THE ENEMY FOR REFUSING TO COMPROMISE 2007 SOKOTO ELECTION — DAHIRU YABO

Fahad Galadanci
RELATED ARTICLESMORE FROM AUTHOR

Hausa
ABIN AL’AJABI: MOTAR JIGILA TA NUTSE CIKIN GULBI DA FASINJOJI A JIHAR SAKKWATO

Hausa
DA DUMI-DUMI: KOTU A JIHAR KANO TA ZARTAR DA HUKUNCIN GIDAN YARI NA SHEKARU 10 GA YARO DAN SHEKARU 13

Hausa
’YAN BINDIGA SUN HALLAKA DPO, YARANSA A TANGAZA
LEAVE A REPLY
Save my name, email, and website in this browser for the next time I comment.
Follow us
8,915FansLIKE
11,220FollowersFOLLOW
Latest news

Tarihi ya nuna Sarki Muhammad Sanusi 11 na iya zama Sarkin...
September 22, 2020

How I Became The Enemy For Refusing To Compromise 2007 Sokoto...
September 22, 2020

Green Belts in Place to Forestall Climate Change, Says Tambuwal
September 21, 2020

Wolverhampton Wanderers vs Manchester: Previews and Team News
September 21, 2020
EDITOR PICKS

Tarihi ya nuna Sarki Muhammad Sanusi 11 na iya zama Sarkin...
September 22, 2020

How I Became The Enemy For Refusing To Compromise 2007 Sokoto...
September 22, 2020

Green Belts in Place to Forestall Climate Change, Says Tambuwal
September 21, 2020
POPULAR POSTS

FOOTBALL TRANSFER NEWS!
August 12, 2020

Sokoto Veterinary Doctors Rescue 75 Years Old Tortoise from Death
September 9, 2020

IPPIS Alternative: ASUU Unveils UTAS to FG, Now Ready for Integrity...
August 19, 2020
POPULAR CATEGORY
NEWS193
LOCAL84
NATIONAL81
ENTERTAINMENT39
INTERNATIONAL34
HAUSA20
OPINION19
POLITICS15
ECONOMY12

ABOUT US
Proudly covering Sokoto, its people, culture as well as what matters from within and around the nation,