Yusuf lawal Yusuf
ADDU'A TAKOBIN MUMINI 05
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, ya kasance idan ya ga jinjirin wata yana cewa:
"الله أكبر، ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺃَﻫِﻠَّﻪُ ﻋﻠَﻴْﻨَﺎ ﺑِﺎﻷَﻣْﻦِ ﻭﺍﻹِﻳﻤَﺎﻥِ، ﻭَﺍﻟﺴَّﻼﻣَﺔِ ﻭﺍﻹِﺳْﻼﻡِ، لما تحب وترضى، ﺭَبنا ﻭﺭَﺑُّﻚَ ﺍﻟﻠَّﻪ".
📚ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ (٣/١٥٧)
"Allahu Akbar, Allahumma Ahillahu Alaina Bil-Amni Wal-Iman, Was-Salamati Wal-Islam, Lima Tuhibbu Rabbuna Wa Tarda, Rabbuna Wa Rabbukallah". 📚 Tirmizi (3/157)
Ma'ana: "Allah ne mafi Girma, Ya Allah! Ka sanya tsayuwarsa a garemu ta zamo kwanciyar hankali ce, da imani, da aminci, da musulunci, da kuma gamokatar da abin da ka ke so Ya Ubangijinmu, kuma ka ke yadda da shi, Ubangijinmu da Ubangijinka (ya kai wannan jinjirin wata!) shi ne Allah". Allah ya sa mu dace
1st Muharram, 1442H. (21/08/2020).
✍️ Yusuf Lawal Yusuf