Amrah Auwal
*KU DUBE MU!*
Amrah Mashi
Nagarta Writers Association
*'KU DUBE MU'* Wannan kalma ce da ta zama nanatau ga dan Nigeria a yau, ta zama mafarkansa da yake fatan cikarsu a duniyarsu.
Rayuwarmu a dunkule take wajen hasko mana ababen da suke zama barazana ga shakar iskan da muke kyauta. Fargaba ta zama zananniyar shimfidar da ke kewaye da zukatanmu.
Yaushe ne *ZA A DUBE MU?* Yaushe ne wannan tsoron zai tsere daga gare mu? Adadin hargitsattsun layukan da ke kara rikicewa su ne ke sare mana gwuiwa a kan sa ran da muke da shi.
*KU DUBE MU!*
Jinin bil Adama a Nigeria, ya zama tamkar jinin kaza ko zakara da ke fita a kowanne lokaci, ba tare da nadama ko da na sani ba, sai ma farin ciki ga masu ita, domin kuwa idan ba su ci ba a bakinsu, za su siyar su samu kudi!
*KU DUBE MU!*
Anya kuwa yadda ake haike wa matayenmu ba zai nemi rinjayar adadin ma'auratan da suke raya sunna ba? Ba fata nake ba.
*KU DUBE MU!*
Abincin cinmu tsada!
Ruwan shanmu tsada!
Suturar da za mu suturta jikinmu tsada!
*KU DUBE MU!*
Tafiya a mota ta zame mana dole, sai dai a kasarmu ta Nigeria tana neman gagararmu. Komai girman uzurin mutum a wasu lokutan dole ya jingine su domin ci gaban numfashinshi.
*KU DUBE MU!*
Mutum zaune a cikin gidanshi, yana tsaka da walwala da iyalinshi masu garkuwa da mutane za su shiga, su ruguza nishadinshi, su rusa walwala da annashuwarshi.
*KU DUBE MU!*
Ilmi yana neman gagararmu. Muna ji muna gani 'yan ta'adda suna neman nakasta mana zukata. Suna neman kawo tsaiko ga wannan ilmin da ya zama fitilarmu
*KU DUBE MU!*
Cin hanci da rashawa na dad'a samun muhallin zama a tsakanin 'ya'yan Nigeria. Inda mai kakkarfan laifi zai cika aljihun mahukunta da wasu 'yan silalla, su sake shi, ya koma ya ci gaba da aikata wancan laifin ba tare da nadama ba.
*KU DUBE MU!*
Muhalli na neman gagararmu. Mutum da gidanshi amma 'yan ta'adda za su hana su kwanciyar hankali, dole su bar wurin su koma inda yake da kwanciyar hankali. Su zauna a ina? Babu! A karshe kila sai dai bara. Rayuwa ta gurbata.
*KU DUBE MU!*
Nomar da muka gada tun iyaye da kakanni muna ji muna gani ta fi karfinmu. An tada mu daga gonakinmu. Idan mun fito a karkashe mu. Mun hakura mun rungumi kaddararmu. Ba dole abinci ya tsadance ba?
*KU DUBE MU!*
Shugabanni;
Sarakunanmu,
Attajiranmu,
'Yan kasuwanmu,
'Yan siyasarmu,
Da duk wani mai fad'a a ji a fadin kasarmu ta NIGERIA, ina mai rokonku da ku dubi girman Allah KU DUBE MU.
KU DUBE MU!
KU DUBE MU!
KU DUBE MU!
©️Princess Amrah