'Ina ma ni ce a wannan yanayi da lokacin? Ina ma duniyata zai canza zuwa ga mafarkina? Duhun da yake kewaye ya gushe ya zamto haske. Koyaushe zan samu ...
Mubeena ɗakinta ta wuce cike da tunani barkatai, ta shiga kai komo tare da dunƙule hannun hagunta tana naushin damanta.
"Anya Mansoor ɗan ƙauye ne kuwa? meyasa zai kasance da yin wasu ɗabi'u irin haka, duk na nasan akwai taɓararru a ƙauye amma salonsa ya bambanta da nasu, ko meye abin sha'awa a shan sigari?"
Tambayoyi ta jerowa kanta da ba tada amsarsu, hakanan ta ji sai ta raba shi da wannan halin, sabo da shan sigari tana da matuƙar cutar da lafiyar dan Adam, ta saki ajiyar zuciya ta koma bisa gado ta zauna, nan take zuciyarta ta hasko mata surar jikin Mansoor, gabanta ya faɗi ras sai ta ji wani abu ya tsirgo mata tun daga kanta har zuwa babban yatsarta, jikinta ya ɗauki ɗumi ta runtse ido tana sauraren baƙon yanayin data tsinci kanta a ciki.
A Daren ranar Mubeena da tunanin Mansoor ta kwana, har sai da hakan ya haifar mata da yin wani irin mafarki mai wuyar fassarawa. Tana kwance bisa gado tana sauraren kiran sallar asubahi, ta buɗe ido tare da busar da iskar bakinta, mamaki take akan mafarkin da ta yi na Mansoor.
"Me yake shirin faruwa dani? Ta yaya Mansoor zai zama mijina matsayinsa na direban gidanmu, na shiga ukuna wani irin azal ke shirin auko min?"
Ta yi maganar a fili tana matsa kwallar dake shirin fitowa daga idonta. Miƙewa ta yi jiki a saɓule ta nufi ban ɗaki zuciyarta tana ƙara haska mata makarfin da ta yi, wani ɓangare na zuciyarta tana son ta kawar mata da wannan tunanin amma ta kasa, a haka ta yi alwala ta fito ta tayar da sallar Asubahi, tana idarwa ta faɗa gado dan komawa barci. Makarkin ya kuma faɗo mata a rai sai ta lumshe ido ta yi murmushi tana jan guntun tsaki, a haka barci ya ɗauketa cike da tunanin Mansoor.
Ɓangaren Mansoor shi kuma ya kwana cikin damuwa da tunanin hanyar da zai samu mafita akan abin da ya kawo shi gidan. Wannan shi ne karonsa na farko da zai fara aiki irin haka, yadda zuciyarsa take tunatar da shi irin karamcin da Baba ya yi masa, hakan sai ya sanya masa shiga mugun ruɗani, rauni da tsoron abin da zai yi, a haka barci ɓarawo ya sace shi cike da damuwa. Zuwa asabahi ya farka ya yi alwala ya nufi masallaci.
***** *****
Da misalin ƙarfe huɗu da rabi na yamma Mubeena ta turawa Mansoor saƙo a waya, akan yazo ya ɗauketa a wurin aiki zuwa gida, yana ganin saƙon ya isa office ɗin Baba ya bama Massinger key motarsa da bayani ya sanar masa sai ya fito, ya samu napep ya hau ya nufi wurin aikin Mubeena. Yana isa ya kutsa kai cikin gidan tv, ya hangota can tsaye jikin mota ita da Fanna suna hira. Ita ma Mubeena ta hangi shigiwarsa.
"Wow, wannan haɗaɗɗen gayen shi ne driver? gaskiya ya yi fa. Kinsan Allah ƙawata da kin wanke shi daga cutar talauci zai dawo Namiji mai aji"
"Malama ya ishe ki haka, daga ganinsa har kin fara zuzuta shi"
"Aaaa su Beena daga faɗar gaskiya, ko dai...?"
"Ko dai me?"
"Uhum ko dai kin faɗa tarko? kin san *SO SARTSE* baya sallama ko jiran lokaci yake damƙe mutum. Yadda naga kina wani kare shi da magana"
"Ke dai kika sani ƴar soyayya, amma ni kin san bana yinta balle ta dameni"
"Ina tausayinki Beena duk lokacin da so ya yi miki sartse, irin ku makancewa kuke yi ba ji ba gani"
"Kin ga Malama sai da safe na yi nan"
Sun ƙare maganar dai-dai Mansoor ya ƙaraso, ya gaishesu Fanna ta amsa tana ƙare masa kallo, har cikin ranta tana yaba kyawunsa.
'Matsalarsa guda ɗaya, talauci' ta ce a ranta.
Haka suka yi sallama Mebeena ta buɗe bayan seat ta zauna memakon gaba, Mansoor ya tada mota suka wuce. Yau ma kamar kullun wannan baƙar motar mai tinted tana biye da su a baya, ganin ba ita kaɗai bace yasa suka cikawa motarsu iska suka wuce, ajiyar zuciya ta saki tana son sanin su waye haka da suke bibiyarta, ta ɗaure fuskarta tamau taƙi kula Mansoor balle suyi hira, hakan da ta yi masa sai ya ji ba daɗi, ya shiga tunanin sigarin da jiya ta gani yana sha shi ne silar da ta sauya masa fuska. A haka suka isa gida ya yi parking ta fito ko ƙala bata ce masa ba ta soma tafiya.
"Mubee..."
Ya ce a tsorace ya kasa ƙarasawa, Beena ta tsaya ba tare data juyo ba. Ya fito daga motar ya isa har inda ta tsaya, yau ne karonsu farko da suka fara irin wannan tsayuwar suna fuskantar juna, Beena taƙi ɗago kai ta kalle shi fuska ɗaure, shi kuma ya ƙura mata ido tsananin tausayinta yana bin ko wani sassan jikinsa, cikin sanyin murya ya soma magana.
"Ga key motar, kuma dan Allah ki yi haƙuri akan..."
Ɗaga masa hannu ta yi ta ɗago kai suka haɗa ido, yarrr jikinta ya soma yi sai ta yi saurin kauda hakan a ranta, ta shiga natsuwarta cikin dakiya.
"Babu laifin da ka yi min, ka mance zancen jiya kwai, duk abin da ka yi rayuwarka ce ba tawa ba, key mota ka riƙe zan amsa da safe"
Ta ce tare da wuce shi tana sauraren irin harbawan da zuciyarta ke yi mata kamar zai faɗo ƙasa, ta cije leɓenta tana ambaton sunan Allah.
Runtse ido Mansoor ya yi ya buɗe ya naushi iska, zuciyarsa ta gama karaya da tausayin Beena, ya ɗaga kafaɗa ya wuce ɗakinsa yana nazari kansa ya ɗauki zafi, sigari kawai yake buƙata ya zuƙa ko zai samu natsuwa.
Mubeena tana shiga falo ta yi arba da Yaya Hafiz ya dawo daga tafiya, da gudu taje ta faɗa jikinsa tana murna, damuwar data shigo da shi nan take ta ji ya yaye a zuciyarta.
"Oyoyo Yaya Hafiz shi ne ba zaka faɗa mana zuwanka ba sai kawai mu ganka"
"My Beena nafi son na baku mamaki, ya aiki da fatan kina kula da kanki"
"Lafiya lau Babban Yaya magajin Baba, ya hanya"
Ta ce tana dariyar murna.
"Lafiya lau Beenan Mami, ya Hafsat da fatan kina haƙuri da ita dan kin san ba tada hankali"
"Ina ƙara haƙuri da ita kamar yadda ka sani"
"Ai dole ki yi haƙuri dani dan na zame miki ciwon ido, kuma wallahi ni ina da hankalina, haka kawai kai da Baba ku yi ta fifita Beena a kaina, me na yi muku ne?"
Hafsat ta ce tana zumɓuro baki cike da jin haushi.
"An fifita ɗin, ke da sam baki da natsuwa, ki sauya halinki ki ga yadda zamu riƙa ji da ke"
Cewar Yaya Hafiz yana hararanta.
"Kaga Yaya Hafiz tun tafiyarka nake fama da ita bata son dawowa gida da wuri in ta tafi makaranta, in na yi magana ta balbale ni da faɗa" cewar Mubeena.
"Kai bana son haka, ya zaku takurawa Autata, ai wani abin kune kuke tsokanota. Hafsatun Kiram rabu dasu kin ji"
Cewar Mami tana kallonta, sai Hafsat ta fashe da kuka.
"Ai kema wata rana faɗa kike min akan Anty Beena, munafuka kawai mai shiga tsakanina dasu Baba"
"What? Mubeena ce munafukar?"
Cewar Yaya Hafiz ya miƙe a zabure, Hafsat ta isa wurin Mami da gudu tana ɓoyewa a jikinta.
"Karka soma dukar min ɗiya daga dawowar ka, ai kune kuka fara tsokanar ta"
"Mami munafuka ta kirani fa" Cewar Beena ido cike da kwalla.
"Ko me ta ce kune kuka ja bana son mugunta, ke kuma karna sake jin kin kira min ɗiya munafuka, Hafsat ki natsu fa bana son shashanci"
Mami ta ƙare maganar kan Hafsat.
"Ai dama kunfi sonta ba kwa sona, ga shi goyon bayanta kuke yi"
Ta ce tare da miƙewa da sauri ta haye sama tana kuka wiwi, da tsaki Yaya Hafiz ya bi ta.
"Wawuya kina da shekaru ashirin da uku baki yi hankali ba"
Jikin Mubeena a sanyaye ta miƙe ta bi bayanta, sam bata son ganin kukanta da irin zancen da take faɗa.
"Bana son haka Hafiz, kai da Babanku kuna nuna bambanci akansu wannan yasa Hafsat ke ganin baƙin Mubeena, kuma nima bana jin daɗin haka, ku riƙa lallashinta kuna faɗa mata gaskiya, baku riƙa nuna cewa Mubeena ta fita ba, ku ke ƙara kunna wutar ƙiyayya a tsakaninsu, tunda Hafsat Yarinya ba tada hankali"
"Shi ke nan insha Allah zan kula"
Daga nan suka shiga ba da hira, yana bata labarin nasarorin daya samu a tafiyarsa.
Mubeena ta isa ɗakin Hafsat ta samu ƙofar a rufe, girgiza kai ta yi ta wuce ɗakinta, wanka ta yi ta sanya doguwar rigan material, mai kawai ta shafa ta ɗaura ɗan kwali ta ɗauki system ɗinta da waya ta fita zuwa garden, ta samu kujera ta zauna ta kunna system ɗinta ta shiga ciki ta kunna wani series film na ƴan Korea. Ta shagala a kallonta cike da nishaɗi a haka Mansoor ya fito daga ɗakinsa ya sameta a gurin, zama ya yi kan kujerar da take kusa da nata ya soma magana.
"Sannu da hutawa, ina so ki sani na koyi shan sigari a gurin abokaina tun ina makaranta, na yi rashin ji sosai amma duk da haka bai hana na yi karatu ba, na ta shi a rayuwa babu mai kwaɓa min sai Mahaifyata. Ina son na daina sha amma na kasa dainawa, ki yi haƙuri dan Allah kar ki sa Baba ya kore ni a gidan nan, dan na fara sabawa daku"
Ya ƙare maganar cikin salon yaudara yadda zai karya mata zuciya har ta ji tausayinsa, burinsa bai wuce ta amince da shi, yadda zai ƙarasa aikinsa ya wuce ba tare da wata matsala ba. Mubeena ta nisa sai ta tsaida film ɗin da take kallo ta ɗago ta kalle shi.
"Ni ba zan maka silar aikinka ba domin wannan taimako ne da Babana ya yi maka saboda Allah, nima kuma na buƙaci da in taya shi, maganar shan sigari na gaya maka wannan rayuwarka ce, shawara dai in zaka ɗauka shi ne ka bar sha domin kiwata lafiyarka, sannan ya kamata ka koyi riƙe amanar kanka wajen kula da duk abin da zai cutar da jikinka, in ka yi haka ka taimaki kanka da ƴaƴan da zaka haifa, domin yara sukan yi gado daga dabi'un iyayensu mai kyau ko akasin haka"
Tana kaiwa nan sai ta yi shuru tana sauraren abin da zai ce.
"Mubeenaa na yi miki Alkawari insha Allah zan bari amma ki ta yi ni da Addu'a, sannan ina buƙatar shawara akan haka"
Murmushi ta yi domin yadda ta ji ya ambaci sunanta, sai ta tsinci kanta a wani irin nishaɗi.
"Karka damu ina maka kallo a matsayin Yayanmu Hafiz, yanzu dai in kana shan kara uku a rana ka rage ka dawo biyu, in biyu ne ka dawo ɗaya, in ɗaya ne ka dawo rabi, ta hakane zaka fara himmar bari, sabo da ba zai yuwy kai tsaye ka iya bari ba sai a hankali, kawai ka sanyawa ranka iklasin cewa zaka bari, kar kuma ka yi danni ka bari sabo da Allah"
"Insha Allah, nagode sis Beee"
"Uhum Mubeena dai nafi so ka kira ni"
Ta ce da murmushi sosai a fuskarta, Mansoor yana kallonta cike da burgewa zuciyarsa tana fidda kwalla.
'Rashin kuɗi masifa ce, Mubeena ki yafe min ba da gangan zan cutar dake ba, sai dan in fita daga halin ƙuncin talauci da nake ciki'
ya yi maganar a ransa idonsa yana kawo kwalla, da sauri ya miƙe daga gurin ya koma can gefe, Mubeena ta bi shi da kallo cike da tsantar sonsa yana fusgar zuciyarta, sai dai wani ɓangare na zuciyata tana gargaɗinta kar ta faɗa a cikin hatsarin soyayya, dan *SO SARTSE* ne shigansa abu ne mai sauƙi amma fitansa abu ne mai matuƙar wahala.
Yaya Hafiz yazo ya sameta a gurin tana kallo, zama ya yi yana kallon ɓangaren da Mansoor yake zaune.
"Wancen kuma waye?"
"Sabon driver ne"
"Ok, shi ne na hango ɗazu kuna magana da shi, ya kama Beena kisan cewa ke Mace ce mai daraja, ki riƙa nisanta kanki da irin mutanan nan"
"Uhum Yaya Hafiz shima mutum ne kamar kowa, babu wanda yafi wani a gurin Allah sai wanda yafi imani, ni dai ba zan iya kyamatarsu ba dan suna talaka, yanzu ma magana muka yi ba wani abu ba ne"
"Ni dai na gaya miki ki riƙa kulawa, ajinki ya wuce nasu"
"To Yaya Hafiz zan kula"
"Yauwa ƙanwata ta shi muje na baki tsarabar ki"
Sai ya amsa system ɗin ya miƙe, ita ma ta miƙe suka wuce suna hira cike da natsuwa, Mansoor yabi bayan su da kallo.
'Wannan shi ne Yayan nasu? Da gani bai da kirki halinsa ɗaya da Hafsat, Beena da Baba da Mami sunfi kirki' ya ce a ransa.
*****
Cikin tsakiyar dare Mansoor ya kira Yallaɓai, bugu uku ya ɗauka cikin muryan barci.
"M.K ya aka yi ne?"
"Oga gaskiya bazan iya aiwatar da abin da ka sani ba, wallahi na karaya sabo da mutanan suna da matuƙar kirki da karamci, ka sauya min wani aiki"
"Kai bana son iskanci, in har kana son kuɗi to dole ka yi abin da na sanyaka, kuma wallahi in har ka yi kuskure ba zan kyaleka ba"
"Yallaɓai Allah ba zan iya raba Mubeena da rayuwarta ba, don Allah ka sauya kisan zuwa kan ƙanwarta Hafsat"
"Hahaha lallai na yarda kai baƙone a wannan harka, to ka sani Mubeena ita ce target ɗinmu, sabo da Alhaji Zanna yafi sonta fiye da kowa a cikin gidan nan, don haka ita zaka sheƙe"
"Gaskiya ba zan iya ba, sai dai na yarda ka rage kuɗin da zaka bani in ɗauko muku ita, kai sai ka sheƙeta da hannunka"
"To shi kenan na baka nan da wani lokaci ka yi ƙoƙari ka ɗauko min ita, da safe ka sameni a gida zan kai ka gidan da zaka kaita, in dai ka yi min haka dubu ɗari biyar ɗin dana yi alƙawarin baka suna nan suna jiranka"
Yana kaiwa nan ya kashe kiran, Mansoor ya miƙe ya shiga zagaye ɗakin yana tunanin ta ina zai fara.
Amincin Allah Ya tabbata a gare ku masu biye da mu a wannan shiri na dabarun rubutu. Idan ba mu manta ba wancan satin mun tsaya ne a rauni na biyu na labari, wato Iya hasaso abin da zai faru. Yau insha Allahu za mu tattauna a kan rauni na uku cikin jerin gwanon rauni ko nakasar da labari ke iya samu ya rasa nauyi a sikeli irin na Adabi. Wannan rauni shi ne RARRAUNAN SALO.
Salo ya ƙunshi irin yadda za ka riƙa saƙa maganganu da ayyukanka a cikin labari, don haka ana son salo ya zama ƙaƙƙarfa ko nagartacce, wato ya zamana ana karanta rubutu yanayin salon da aka yi amfani da shi ya riƙa tafiya da hankalin mai karatu. Ba wai salo ya zama rarrauna ko miƙaƙƙe ba irin wanda babu wani abu na armashi a cikinsa.
Misalin yadda za a fahimci muhimmancin salo a cikin labari shi ne, irin misalin mutane biyu da suka sayi atamfa ko shadda iri ɗaya masu tsada ɗaya. Ɗaya a cikin su ya kai wa tela wanda ya iya ɗinki sosai, ɗayan kuma ya kai wa tela wanda bai iya ɗinki ba. Duk tsadar shaddar ko atamfar da telan da bai iya ɗinki ba ya ɗinka, ba za ta burge mutane ba har ta ja hankalinsu idan an saka a jiki kamar ta telan da ya iya ɗinki. Za ku yarda da ni cewa atamfa ko shadda mafi araha za ta iya fin ita mai tsadar jan hankali idan ta samu tela mai kyau, to haka shi ma rubutun labari yake. Shi ya sa wani lokacin sai ka ga wani wanda labarin shi bai kai naka samun jigo mai kyau ba amma ya zo na ɗaya a gasa kai ba ka zo ba.
Marubucin da ya iya salo da ƙirƙira tamkar telan da ya iya ɗinki ne, hakanan marubucin da bai iya fitar da salo da alƙalaminsa ba tamkar tela ne da bai iya ɗinki ba. Shi ya sa mabanbantan marubuta za su iya ɗaukan jigon labari ɗaya amma ka tarar banbancin daɗin labaransu tamkar banbancin garɗin koko da madara. Mu nazarci waɗannan misalan:
RARRAUNAN SALO.
Na je wajenta jin hirarta mai daɗi ta barni a tsaye ta ƙi fitowa har na fara gyangyaɗi na gaji na tafi.
NAGARTACCEN SALO.
Na je ba wa ruhina abincin da yake muradi na daɗaɗan kalamanta masu yi min daɗi kamar ana sosa min kunne, ta bar ni a tsaye kamar kwatar raken da aka dasa har idanuwana suka fara nauyi, na fara gani dishi-dishi na yi gaba kafin bacci ya yi gaba da ni.
Abin lura, duk waɗannan misalan abu ɗaya ake so a ce a cikin su, abin tambaya a nan shi ne wanne daga cikin biyun ne zai fi jan hankalin mai karatu? Ga wasu misalan:
RARRAUNAN SALO.
Rantsattsiyar motar ta shige cikin asibitin da mai gadi ya buɗe ƙofar. Kallon ƙofar asibitin kaɗai ya isa ka fahimci asibitin masu kuɗi ne.
NAGARTACCEN SALO.
Rantsattsiyar motar ta sulala cikin asibitin da mai gadi ya buɗe wawakeken ƙyaurensa sululuf irin yadda maciji yake sulalawa raminsa, ba ka jin ko kukanta. Ƙofar da kallon ta kaɗai ya wadatar ka fahimci asibitin na masu yatsu da yawa ne.
A kawo mana wasu misalan na RARRAUNAN SALO da NAGARTACCE domin sake fahimta. Mu kwana lafiya.
Rahmatu Lawan
Masha Allah Tabarakallah! Lallai kuma zahiri ga banbanci sosoi tsakanin rauraunan da kuma nagartaccen salon cikin misalanka. Allah Ya kara basira!
*Bismillahir rahmanir rahim!*
_Free book ne daga farko har ƙarshe kamar yadda na ɗaukar wa readers alƙawari Insha Allah._
_Ƙagaggen labari ne banyi shi dan wata ko wani ba, sai dan ya faɗakar da al'umma ya kuma nishaɗantar dasu. Allah yasa zamu amfana da abin da ke cikinsa. Ameen_
_*Page 1.*_
*MAIDUGURI*
Garin Allah ya waye duk kan al'umma sukan ta shi domin fara gudanar da al'amuran yau da kullun, musamman Mata da suke cikin kitchen dan haɗa karin kumallon safe, Ma'aikata na ƙoƙarin shirin fita aiki, Yara suna ƙoƙarin shirin tafiya makaranta. Da misalin ƙarfe takwas na safe Mubeena ce ke saukowa daga matakalar bene cikin natsuwa, sanye take cikin riga da siket na atamfa, ta sanya dogan hijab mai hannu brown color, tana sanye da takalmi flat shoe rataye da handbag a kafaɗarta, fuskarta shafe da powder sai kwalli data sanya a dara-daran idonta wanda ya ƙara fidda kyawunsu, ta shafa lips stick kaɗan a bakinta yana sheƙi, ƙamshin turarenta ya gauraye falonsu yayin data kai ga saukowa, ta samu Mami da Baba zaune bisa Cushing mai mazaunin mutum biyu, tunda ta sauko suke binta da kallo fuskarsu ɗauke da murmushi.
"Mubeena har kin shirya kin fito? Kin karya kuwa? ina kika baro Hafsa? fatan ta tashi daga barcin asarar data saba kar tasa kiyi latti"
Cewar Mami cike da murmushi a fuskarta tana duban Mubeena.
"Mami zan karya a office, na tada Hafsat da kyar ta tashi, na dai baro ta tana sanya kaya, ina gudun kar na yi latti dan yau ina da shirin da zan gabatar da ƙarfe tara na safen nan"
"Kinga yi tafiyarki karta ɓata miki lokaci, in ta fito sai ta hau napep" cewar Mami.
"A'a Hajiya ki bari su tafi tare, kinsan Hafsat sai ana haƙuri da halinta, Mubeena yi haƙuri ki jirata Insha Allah ba zaki yi latti ba" cewar Baba yana ƴar dariya.
"Tom Baba bari na jirata, yanzu ma takwas da kwata da ɗan sauran lokaci. Ina tausaya mata ne dan samun abun hawa da safen nan akwai wuya kuma..."
"To ki tafi mana ɗin sai me, Baba nima ya kamata a siya min mota na huta da ƙorafin Anty Beena"
Cewar Hafsat lokacin da ta sauko daga matakala, ta katse maganar Mubeena.
"Kin ci gidanku na ce, daga saukowarki zaki fara da rashin kunya ko? maza zo ki wuce kan in ɓata miki rai"
Baba ya ce da faɗa cikin harshen kanuri.
Turo baki Hafsat ta yi tana gunguni rai a ɓace, ta rasa me yasa su Baba ke nuna banbanci tsakaninta da Mubeena, cikin ɗaure fuska ta gaishe su, suka amsa ba yabo ba fallasa. Baba ya ciro kuɗi a aljihunsa na gaba ya ƙirga dubu biyar ya miƙawa Mubeena.
"Mubeena ga shi, dubu uku kisa mai a mota dubu biyu ki riƙe na abinci, dan nasan zaki iya kaiwa yamma baki dawo ba"
"Ke kuma Hafsat ga dubu biyu nan ki riƙe"
Mubeena ta amsa tana godiya sai ta yiwa musu sallama ta wuce, Hafsat kuma ta tsaya akan sai Baba ya ƙara mata kuɗi zata siya handout.
"Hafast bana son wannan baƙin halin da ki ka hudo da shi Mubeena ƴar uwarki ce fa, amma ki rasa wacce zaki kishi sai da ita, tun wuri ki sauya hali kafin na sanya ƙafar wando ɗaya dake. Maza ki bace min da gani kanna saɓa miki... less
Rabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Rufewa:
Tun daga 1933 har zuwa yau ina kalubalantar duk wani mai bayyananniyar hujja wadda za ta fifita wata kafar isar da sakon gwamnati wacce ta shallake radiyo, ko ma wacce kafa ce mu zube ta a faifai mu gani idan... moreRabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Rufewa:
Tun daga 1933 har zuwa yau ina kalubalantar duk wani mai bayyananniyar hujja wadda za ta fifita wata kafar isar da sakon gwamnati wacce ta shallake radiyo, ko ma wacce kafa ce mu zube ta a faifai mu gani idan akwai riba. Ba domin hujjojina sun... moreRufewa:
Tun daga 1933 har zuwa yau ina kalubalantar duk wani mai bayyananniyar hujja wadda za ta fifita wata...
Jibrin Adamu Rano
Abu na gaba da nake so ku kai hankalinku kai. A cikin ku ai akwai wacce ta samu nasarar zama zakarar BBC Hikayata ta bana. Shin ta murya Maryam ta zagaya duniya kowa ya gan ta ko kuwa ta bidiyo na talabijin da wayoyi?
Maryamerh AbdulArewa dai arewa dai, arewa kuma me alaqanta da sakon Gwamnati? Duk kallonka da arewa, yaushe ka ga sun sako sakon Gwamnati? Tambaya ta Allah da annabi kenan. Da kake maganar cancer, kafin cancer ta kama mutum biyu, ciwon ido ta kama mutum goma. Me zaka... moreArewa dai arewa dai, arewa kuma me alaqanta da sakon Gwamnati? Duk kallonka da arewa, yaushe ka ga sun sako sakon Gwamnati? Tambaya ta Allah da annabi kenan. Da kake maganar cancer, kafin cancer ta kama mutum biyu, ciwon ido ta kama mutum goma. Me zaka ce da wannan? Ko kwana zamu yi a nan, ina tabbatar maka bazan gaji da baka hujja kan hujja akan rediyo ta fi talbijin tura sakon Gwamnati ba, sannan ba zan...
Rabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Uku:
A shekarar 2004 zuwa 2005 al'ummar garuruwan Agbowo da Orogun da ke jihar Oyo sun fuskanci matsaloli na mummunar ambaliyar ruwa. Gwamnati ta yi ta kokarin shawo kan matsalar, ta kuma zage dantse wajen... moreRabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Uku:
A shekarar 2004 zuwa 2005 al'ummar garuruwan Agbowo da Orogun da ke jihar Oyo sun fuskanci matsaloli na mummunar ambaliyar ruwa. Gwamnati ta yi ta kokarin shawo kan matsalar, ta kuma zage dantse wajen yin shirye-shirye na fadakarwa da... moreHujja Ta Uku:
A shekarar 2004 zuwa 2005 al'ummar garuruwan Agbowo da Orogun da ke jihar Oyo sun fuskanci matsaloli na mummunar ambaliyar ruwa. Gwamnati ta yi ta kokarin shawo kan matsalar, ta kuma zage dantse wajen yin shirye-shirye na fadakarwa da wayar da kai ga al'umma domin su fahimci illar da ke cikin toshe magudanan ruwa. A duba fa, gwamnati ba ta yi amfani da sojoji ko 'yan sanda ko wata hotiho wai ita talbijin ba, amma... less
Jibrin Adamu RanoKun bar bugun jaki, kun ɓige da bugun taiki. Ni fa abu ɗaya na ce, in da a ce gwamnati bata yi amfani da talabijin wajen nuna ainahin abin da ya faru ba, da babu wanda iya jin maganganun da kunne zai saka ya yarda kai tsaye.
Bayan na ga sanarwar a... moreKun bar bugun jaki, kun ɓige da bugun taiki. Ni fa abu ɗaya na ce, in da a ce gwamnati bata yi amfani da talabijin wajen nuna ainahin abin da ya faru ba, da babu wanda iya jin maganganun da kunne zai saka ya yarda kai tsaye.
Bayan na ga sanarwar a talabijin na ji babu daɗi sosai, har da safe nake ba wa abokaina labarin abin da na gani gwanin ban tausayi. To kamar yadda na faɗa wa abokaina, haka duk masu talabijin za su faɗa wa abokanan su na karkara da kuke da'awar cewa ba su da talabijin ko lantarkin da za su gani. less
Jibrin Adamu RanoNi fa magana ɗaya na yi, na ce muku na san lokacin da wannan matsalar ta faru.
Ban manta ba ina gida a zaune ina kallon talabijin na ga ana ta nuna irin ta'adin da ruwa ya yi musu.
Idan a rediyo za a faɗa, wa ye ma zai gane ainahin buƙatar taimakon da... moreNi fa magana ɗaya na yi, na ce muku na san lokacin da wannan matsalar ta faru.
Ban manta ba ina gida a zaune ina kallon talabijin na ga ana ta nuna irin ta'adin da ruwa ya yi musu.
Idan a rediyo za a faɗa, wa ye ma zai gane ainahin buƙatar taimakon da suke yi? Ai gani a talabijin ne ya jawo aka tausaya musu sosai suka samu wannan gudummawar.
Washegari da safe kuwa cikin alhini nake labarta wa abokaina irin asarar da waɗanda ambaliyar ta shaf. To idan ba ku sani ba ku sani, kamar yadda na ba wa abokaina labari, haka duk mai talabijin ɗin da ya kalla ya gamsu da gaske ne zai faɗa wa wanda bai kalla ba har zuwa kan 'yan karkarar da kuka ta haƙilon ba su da talabijin. less
Ai yanzu ci gaba ya zo, babu wani gidan talabijin da ba su da manhaja ta waya, wacce za ka sauke ka riƙa kallon labaransu. Ni ina da manhajar Arewa 24 wanda da shi na kalli Maryam Umar taku a tattaunawar da aka yi da ita ta ZOOM... moreAmrah (Takwarar 'ya ta)
Ai yanzu ci gaba ya zo, babu wani gidan talabijin da ba su da manhaja ta waya, wacce za ka sauke ka riƙa kallon labaransu. Ni ina da manhajar Arewa 24 wanda da shi na kalli Maryam Umar taku a tattaunawar da aka yi da ita ta ZOOM a arewa.
Don haka batun wai a ɗauke wuta kana kallo duk bai taso ba, ki dai sake wata makamar, wannan makamar ta ki ganyen iska kawai kika riƙe, kina sake masa nauyi faɗowa za ki yi.
Maryamerh AbdulKana yi kaman baka san tattalin arzikin najeriya ta yi qasa ba. Wa yake da datar kalle kalle a waya bayan ga sauki? Ana ta abinci ko ana ta data? Wai ni ko malam Jibrilla ko dai Gwamnatin nan ta masu kudi ne kawai da kake ta nanata telbijin, waya da... moreKana yi kaman baka san tattalin arzikin najeriya ta yi qasa ba. Wa yake da datar kalle kalle a waya bayan ga sauki? Ana ta abinci ko ana ta data? Wai ni ko malam Jibrilla ko dai Gwamnatin nan ta masu kudi ne kawai da kake ta nanata telbijin, waya da abubuwan da ba kan gado.
Da kake cewa masu talbijin ne suka gani kuma suka isar da sako ko suka bada labari, wannan magana taka karya ce, sanin kanka ne masu bada labarin da suka ji a gidan rediyo sun rinjayi masu badawa don sun gani a telbijin. Yoo yawanci masu kallon talbijin ‘yan birni ne da hira tsakaninsu ke musu wahala, kowa da wayarsa hannu ko an shiga kalle kallen televista. Amma mu mutanenmu kullum cikin zumunci da hira ake yi, in ba a bada labaran rediyo ba ma ai ka san zaman... less
Rabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Biyu:
Sakonnin gwamnati suna isa ga al'umma ta hanyar nishadantarwa, ko ilmantarwa da makamantan haka, to idan ana son a sami duk wadannan sai an garzaya zuwa ga shirye-shiryen da ake yi a gidajen radiyo.... moreRabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Biyu:
Sakonnin gwamnati suna isa ga al'umma ta hanyar nishadantarwa, ko ilmantarwa da makamantan haka, to idan ana son a sami duk wadannan sai an garzaya zuwa ga shirye-shiryen da ake yi a gidajen radiyo. Misali a gidajen radiyo ne ake... moreHujja Ta Biyu:
Sakonnin gwamnati suna isa ga al'umma ta hanyar nishadantarwa, ko ilmantarwa da makamantan haka, to idan ana son a sami duk wadannan sai an garzaya zuwa ga shirye-shiryen da ake yi a gidajen radiyo. Misali a gidajen radiyo ne ake samun wasannin kwaikwayo wadanda kacokan gwamnati ce ke daukar nauyinsa domin isar da wani sako na musamman wanda zai amfani al'umma, kamar wasanni domin kawo karshen cutar foliyo ko tarin fuka ko zazzabin maleriya, uwa-uba kuma kariya daga kamuwa da... less
Jibrin Adamu RanoNa fahimci kin tsani talabijin, da alamu shi ya sa ba kya kallonta. Shi kuwa hukunci ba a yankewa bisa ra'ayi, abin da ka gani kake iya ɗorarwa.
WASAN KWAIKWAYO.
Ai daga sunan kawai kin san cikar fahimtarsa sai an kalla a talabijin, ba wai ji a rediyo... moreNa fahimci kin tsani talabijin, da alamu shi ya sa ba kya kallonta. Shi kuwa hukunci ba a yankewa bisa ra'ayi, abin da ka gani kake iya ɗorarwa.
WASAN KWAIKWAYO.
Ai daga sunan kawai kin san cikar fahimtarsa sai an kalla a talabijin, ba wai ji a rediyo ba. Wannan shi ya sa ita kanta gwamnatin a talabijin take ƙarfafa saka shi, don a can ne za a faɗaku ba rediyo ba.
Rabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Farko:
Bahaushe ya ce mutane su ne kasuwa ba tarin rumfuna ba! A kiyasi na baya-baya da aka yi an gano cewar a daukacin mutane masu bibiyar labarai a kowace kafa, idan aka raba su gida goma, bakwai suna amfani... moreRabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Farko:
Bahaushe ya ce mutane su ne kasuwa ba tarin rumfuna ba! A kiyasi na baya-baya da aka yi an gano cewar a daukacin mutane masu bibiyar labarai a kowace kafa, idan aka raba su gida goma, bakwai suna amfani da radiyo ne a Nijeriya. Yayin da... moreHujja Ta Farko:
Bahaushe ya ce mutane su ne kasuwa ba tarin rumfuna ba! A kiyasi na baya-baya da aka yi an gano cewar a daukacin mutane masu bibiyar labarai a kowace kafa, idan aka raba su gida goma, bakwai suna amfani da radiyo ne a Nijeriya. Yayin da gwamnati ta zo da wasu sababbin tsare-tsarenta wadanda take son su karade ko'ina, idan ta yi amfani da gidajen radiyo to mutane bakwai cikin goma da ke bibiyar labarai za su riski wannan sabon tsari, idan... less
Jibrin Adamu Rano → MARUBUTA:
KAMMALAWA:
TAƁA KIƊI, TAƁA KARATU.
Zan ɗabbaƙa wannan karin-maganar na jingine misalai na azanci a gefe, mu ɗakko zantukan masana irin su Belle Beth Cooper (2013).
"A... moreJibrin Adamu Rano → MARUBUTA:
KAMMALAWA:
TAƁA KIƊI, TAƁA KARATU.
Zan ɗabbaƙa wannan karin-maganar na jingine misalai na azanci a gefe, mu ɗakko zantukan masana irin su Belle Beth Cooper (2013).
"A ɗabi'a ta ɗan'adam, ya fi sharɓar saƙo da romo idan yana ji yana ganin mai... moreKAMMALAWA:
TAƁA KIƊI, TAƁA KARATU.
Zan ɗabbaƙa wannan karin-maganar na jingine misalai na azanci a gefe, mu ɗakko zantukan masana irin su Belle Beth Cooper (2013).
"A ɗabi'a ta ɗan'adam, ya fi sharɓar saƙo da romo idan yana ji yana ganin mai isar masa." Wannan maganar tata hatta hadisi ya ƙarfafe ta. Da hadisin da Ma'aiki S.A.W yake koya wa Sahabbai salla zan ba wa zantukan nata kariya. Idan Annabi (S.A.W) ya yi musu bayani da baki (irin yadda ake yi a rediyo), ba ya barin su haka saboda ya san an fi gane abin da aka ji aka gani. Sai ya hau kan mambari ya siffanta musu yadda ake yi, (irin yadda ake siffanta saƙonni a talabijin).
(Ihkamul'ahkam 1/332).
Wannan allurar hujjojin nawa kaɗai ta isa ta huda fata, ta ratsa tsokar mai larurar da bai... less
Nura IsmailMalama Maryam maganar Annabi (S.A.W) har gobe muna amfani da ita, ta hanyar wanda suka gan shi. Tambaya ɗaya da zan miki ita ce, za ki iya koyon Alƙur'ani ba tare da kina ganin malami yana ganin ki ba? Za ki iya koyon salla ba tare da malami ya nuna... moreMalama Maryam maganar Annabi (S.A.W) har gobe muna amfani da ita, ta hanyar wanda suka gan shi. Tambaya ɗaya da zan miki ita ce, za ki iya koyon Alƙur'ani ba tare da kina ganin malami yana ganin ki ba? Za ki iya koyon salla ba tare da malami ya nuna miki yadda za ki yi ba? Malaman su ne magada Annabawa. Don haka su za mu riƙe a madadin Annabi da ba mu riske shi ba. Su ne madubin da za mu kalla, mu ga duk abin da sahabbai suka ga ni.
A Nijeriya, radiyo ta samu a shekarar 1933 da wani fasali na yada ayyukan da manufofin Turawan Mulki. 'RDS' ko 'Radio Diffusion Service' shi ne farkon abinda ya samar da gidajen radiyo... moreRabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Gabatarwa.
A Nijeriya, radiyo ta samu a shekarar 1933 da wani fasali na yada ayyukan da manufofin Turawan Mulki. 'RDS' ko 'Radio Diffusion Service' shi ne farkon abinda ya samar da gidajen radiyo sama da 200 yau a Nijeriya.
Zan... moreGabatarwa.
A Nijeriya, radiyo ta samu a shekarar 1933 da wani fasali na yada ayyukan da manufofin Turawan Mulki. 'RDS' ko 'Radio Diffusion Service' shi ne farkon abinda ya samar da gidajen radiyo sama da 200 yau a Nijeriya.
Potiskum gari mai rahma
Ga matasa masu himma
Da dattaɓai masu hikima
Matansu ma'abota... morePotiskum gari mai rahma
Ga matasa masu himma
Da dattaɓai masu hikima
Matansu ma'abota islamiya.
Matasan su zakakurai
Aure kamar tattabarai
Basa halayen bunsurai
Ga riƙe aure babu murɗiya.
Kullum neman na kansu
Ɓangaren ilmi da Asusu
Shine ɗabi'un ɗaukacinsu
Ga zaman lafiya ba hayaniya.
Af! Ashe fa bakin abinda aka iyakance na lokaci yana tunkarowa, sai dai a yadda na shawo gangara da za a kyale ni to hujjoji yanzu ma aka fara; me aka yi da maza? In ji karya! Kodayake hakan ma na tabbata duk wanda ya karanta zai...