Mai girma Alkalin muhawara, mai kula da lokaci, ‘yan uwana abokan muhawara, ina yi muku barka da wannan lokaci.
Sunana Maryam Suleiman Indabawa daga kungiyar Hakuri da Juriyya, na tsaya a nan ne domin bada hujja ta akan batun da ke fadin "Karatu a cikin kasar mutum da Karatu a kasar waje wanne yafi?"
Ina zaka hada, ai karatun da akayi shi a kasar waje yafi Wanda aka yishi cikin kasar Nigeria, domin ko makaho ne ya shafa ya shafo yasan banbancin a bayyane yake, meyasa masu kudin mu basa barin yaransu yin karatu a cikin kasar nan? Yawa yawan su kasashen waje suke dibar yaran su kai. saboda me? Saboda sun san zallar Madara karatun Yana kasar waje. Ku biyo ni sannu a hankali dan jin dalilai na. less less