Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuh. Barkanmu da yau barkanmu da sake kasancewa cikin wannan rana ta Talata inda muke gabatar muku da shirin filin baƙon mako. Shiri ne dake zaƙulo manya-manyan Marubuta don tattaunawa dasu wanda ni Maryam Haruna... moreAssalamu alaikum warahmatullah wabarakatuh. Barkanmu da yau barkanmu da sake kasancewa cikin wannan rana ta Talata inda muke gabatar muku da shirin filin baƙon mako. Shiri ne dake zaƙulo manya-manyan Marubuta don tattaunawa dasu wanda ni Maryam Haruna da abokiyar aikina Hauwa'u Muhammad ke gabatarwa. Ku biyomu ciki don ji daga bakin baƙuwar. Ummyter Abdallah Hauwa'u Muhammad Mukhtar Musa Karami Abu Hisham kuna kusa?
Bala Danfulani
To ki kara dagewa; idan Hausar, Hausar, idan Ingilishin, Ingilishin. Akwai wuraren da babu laifi a sirka Hausa da wani harshen, inda laifin yake haka nan babu gaira ba dalili a rinka rubuta kalmomin Ingilishi saboda feleke. Allah ya kara basira.
Nana Aicha Hamissou → MARUBUTA:
Assalamu alaikum warahmatullahi wabarkatuhu ƴan'uwana barkarmu da warhaka barkarmu da sake kasancewa da ku a wannan filin na MUTUM DA AL'ADUNSA.
Za mu ɗora... moreNana Aicha Hamissou → MARUBUTA:
Assalamu alaikum warahmatullahi wabarkatuhu ƴan'uwana barkarmu da warhaka barkarmu da sake kasancewa da ku a wannan filin na MUTUM DA AL'ADUNSA.
Za mu ɗora daga inda muka tsaya. In ba ku manta ba mun tsaya wajen da ake fitar da sakamakon jarabawar... moreAssalamu alaikum warahmatullahi wabarkatuhu ƴan'uwana barkarmu da warhaka barkarmu da sake kasancewa da ku a wannan filin na MUTUM DA AL'ADUNSA.
Za mu ɗora daga inda muka tsaya. In ba ku manta ba mun tsaya wajen da ake fitar da sakamakon jarabawar BACCALAURÉAT (Senior).
Bayan an fitar da sakamako rana washegarin ranar waɗanda suka faɗo ORAL (Ƙamar yadda na yi bayani a makon da ya wuce) za a ba su result ɗinsu don su ga aikin da suka yi da kuma nazarin darasin da za su sauya. Washegari ko kuma da yamma a ba waɗanda ba su samu ba nasu requis ɗin don wanda yake ganin an yi masa manaƙisa ko kuma bai yarda ba ya shigar da ƙorafi. In ya ga makin da bai yi masa ba sai ya rubuta letter ya aje sai a sake duba masa paper ɗinsa da kuma sauran maki.
(Kuma wani lokacin ana dacewa in aka yi korafin don lokacin da muka yi jarabawar BACCALAURÉAT ƙawata ba ta samu ba amma tana shigar da ƙorafi ashe ta samu kuskure ne wajen lissafin maki sai ga shi ta samu ta wuce.)
Washegari kuma wadanda suka samu ECRIT sai a ba su result dinsu da da satifikat dinsu.
Su kuma Oral bayan kwana uku da fitar da sakamako sai su kara shiga aji su sake darasi bibbiyu na ɓangarensu cikin waɗanda ba su yi aiki ba ko kuma waɗanda suka fi iyawa in har suna da kwarin gwiwar in sun sauya za su fi samun aiki. Waɗanda suka ɓangaren science watau série C da E sai su zaɓi maths, Physics-chemestry ko sciences, sannan su haɗa da History-Geography. Su kuma waɗanda suke banagen arts kuma sai su sauya ko falsafa ko history ko kuma history sai su haɗa da harshe (in farko sun yi Larabci yanzu ORAL Ingilishi za su yi, in kuma farko Ingilishi suka yi sai su yi Larabci. ) Ya zama dole in sauya sai sun haɗa 10/20 a makin gabaɗaya da ake so, in mutùm bai yi ba dole sai ya sake shekara. Wannan kenan
Bayan fitar sakamako wasu su ga samu su ha rashi, mutum yana jin daɗin ya ci ORAL kuma ya sha ƙasa, wasu kuma sai su wuce jami'a gidan ban kashi.
Washegari aka ba su result da satifikat su kama gabansu sai gyaran takardu.
Ba zan samu yin ɓangaren jarabarwa 'yan technology ba saboda ban san yadda suke yi ba amma dai tare suke farawa.
*************
Bayan an ba wa kowa satifikat ɗinsa sai a fara gyaran takardu na scholarship. Kowa zai kai takardun da ake buƙata a makarantarsu. Yadda tsarin schoolship yake shi ne:
Sciences
1. Matuƙar mutum ya samu ECRIT wajen jarabawa zai samu schoolship kodakuwa ba shi da maki ko daya a aji, in har ɗan kasa ne shi, kuma bai wuce shekara 24 ba za a ba shi schoolship in ya shiga jami'a. (Wooo mu 'yan science jinjina gare mu)
2. In kuma mutum ya samu ORAL zai hada abin da yake da aji Ss3 da kuma abin da ya samu a jarabawa zagaye na biyu watau Oral sai a raba biyu. In Namiji ne sai ya samu 10/20, mu kuma mata 9,5/20 saboda rauninmu. Sannan zai samu schoolship ɗinsa.
Arts
1. Ko da mutum ya samu ECRIT in har a aji Ss3 ba shi 10/20 to ba zai samu ba. Sai dai haƙuri.
2. Ko da mutum yana da 19/20 a aji matuƙar bai samu ECRIT ba ya fado Oral to ba shi da schoolship.
3. Dole ne mace ta samu 10/20 a aji kuma ta samu ECRIT.
4. Dole ne namiji ya samu 11/20 a aji kuma ya samu ECRIT ki zai samu.
Tun kafin fitowar sunayen sunaye mutum yana da masaniya in zai samu saboda ya riga da ya yi lissafin abun da ya samu. Ko ba a dauki mutum ba wajen schoolship akwai kuɗin da ake ba su ƙarshen shekara jikka ɗari da hamsin. Su kuma masu schoolship duk bayan wata uku ana ba su jikka ɗari da jikka biyar, cikin wata biyu na hutun ƙarshen shekara kuma sai a ba su jikka hamsin da biyu da rabi.
†***************†
Daga jigilar ɗora schoolship kuma sai shirye-shirye dora karatu a jami'ar da mutum yake muradun karatu. Kowa zai... less
Ummyter Abdallah
Kai! Amma tsarin schoolship dinnan ga dan kasa ya burgeni wallah, wato har kudi ake baku, ke Nana in zo ki maidani yar kasa dan karatu?
Mukhtar Musa Karami Abu Hisham → MARUBUTA:
KAMMALAWAR MUHAWARAR YAU 17/1/2021
(ZAGAYE NA... moreMukhtar Musa Karami Abu Hisham → MARUBUTA:
KAMMALAWAR MUHAWARAR YAU 17/1/2021
(ZAGAYE NA II)
Alhamdulillahi mun godewa Allah da yasa wannan Muhawara ta kammala cikin aminci,za mu yi amfani da wannan dama mu mika sakon bangajiya ga Alkalai da wakilan kungiyoyi da suka fafata a wannan... moreKAMMALAWAR MUHAWARAR YAU 17/1/2021
(ZAGAYE NA II)
Alhamdulillahi mun godewa Allah da yasa wannan Muhawara ta kammala cikin aminci,za mu yi amfani da wannan dama mu mika sakon bangajiya ga Alkalai da wakilan kungiyoyi da suka fafata a wannan muhawara,tare da sauran dukkanin mahalarta da akayi komai akan idonsu, da ma duk wadanda suka samu halartar wannan Muhawara muna yi musu bangajiya.
Insha Allahu gobe Alkalai za su zo mana da sakamakon muhawarar da akayi yau 17/1/2021 kafin muhawara ta... less
Ummyter Abdallah → TSEGUMI ZALLA:
Don Allah kiboye sunana.
Mijina ne yanada gemu kuma na kula budurwar shi nason gemu sosai, saina aske masa gashin yana bacci saboda na lura inyazo taje gemun har wani jan gemunsa yake yana murmushi in zaije zance.... moreUmmyter Abdallah → TSEGUMI ZALLA:
Don Allah kiboye sunana.
Mijina ne yanada gemu kuma na kula budurwar shi nason gemu sosai, saina aske masa gashin yana bacci saboda na lura inyazo taje gemun har wani jan gemunsa yake yana murmushi in zaije zance. Inajin takaicin hakan wallahi,maganar da... moreDon Allah kiboye sunana.
Mijina ne yanada gemu kuma na kula budurwar shi nason gemu sosai, saina...
Fita karatu wata ƙasa yana dasa girman kai matuka a zuciyar wanda ya fita ɗin. Daga sadda ɗalibi ya fita ya yi alaƙa da jinsin mutanen da ba nashi ba, sai ya rinƙa ganin jinsinsa a banza, ya rinƙa kallon su... moreKabir Layuza → MARUBUTA:
Hujja Ta Uku:
Fita karatu wata ƙasa yana dasa girman kai matuka a zuciyar wanda ya fita ɗin. Daga sadda ɗalibi ya fita ya yi alaƙa da jinsin mutanen da ba nashi ba, sai ya rinƙa ganin jinsinsa a banza, ya rinƙa kallon su matsayin ba su iya ba, ya... moreHujja Ta Uku:
Fita karatu wata ƙasa yana dasa girman kai matuka a zuciyar wanda ya fita ɗin. Daga sadda ɗalibi ya fita ya yi alaƙa da jinsin mutanen da ba nashi ba, sai ya rinƙa ganin jinsinsa a banza, ya rinƙa kallon su... less
amyra gwadabeAkwai ja a maganarki ,duk Wanda yai ilimi a kasar waje to ina mai tabbatar miki da cewa musamman ma ilimin lafiya ko na shari:'a ya karanta wani kwas akan tattali da kula da Mara lfy ko mai kawo kara ,duk da dai a kasar tamu akwai amma ba'a aiki da shi... moreAkwai ja a maganarki ,duk Wanda yai ilimi a kasar waje to ina mai tabbatar miki da cewa musamman ma ilimin lafiya ko na shari:'a ya karanta wani kwas akan tattali da kula da Mara lfy ko mai kawo kara ,duk da dai a kasar tamu akwai amma ba'a aiki da shi Sam ,Dan in ban manta ba muna makaranta in munji irin hakkokin da Mara lfy keda shi a kan likita hangame baki muke Dan mun San ba'a yin su ,amma ki bincika wani Abu yawanci likitoci masu kula da Mara lfy sunyi karatu a kasar waje ne ,Dan a can sukaga ana aiwatar... less
Ama Kabir
Sannan ga rashin ganin mutuncin mutake , kai hatta iyayen da suka tsugunna suka haifeshi ma ba ya ganin girmansu muddin suka fita karatu waje idonsu ya buɗr
Aisha Aliyu
Ai bama iya girman kai ba harda tarwatsa tarbiya wallahi zaki dauki shekaru sama da ashirin kina baiwa ɗiyarki tarbiya amman cikin kwanaki ƙalilan idan taje ƙetare zata manta da wannan shekarun da kika ɗauka kina bata tarbiyya.
Gwamnati zata yi iya ƙoƙarinta wajen kafa dokokin da suka dace, amma kuma na ƴan kwanakine al'umma zata yi wasarere da su taƙi bin doka.
Idan... moreRUFEWA
Tabbas cin hanci laifin al'ummane, domin asalin kafuwarsa daga tushiya ya soma.
Gwamnati zata yi iya ƙoƙarinta wajen kafa dokokin da suka dace, amma kuma na ƴan kwanakine al'umma zata yi wasarere da su taƙi bin doka.
Idan gwamnati nada ikon saka doka, bata da ikon tusassa al'umma kan sai ta bi domin ba kowa ne yake yi wa gwamnati biyayya ba.
Idan muka haɗu muka jajirce kan ƙin bada cin hanci, to tabbas za a gauda matsalar har a Gwamnatin ma, domin al'umma ita ce Gwamnati!
SanahHaƙƙun ina tare da ke. Matuƙar al'umma zata jajjurce ta ƙi bada cin hanci to kuwa gwamnati bata da dogon hannun amshewa. Domin dai sai ka bayar za a amsa. Idan baka bayar ba zata ƙwaci cin hanci hannunka ta ƙarfi ne? Ko kuma zata fito ta shaidawa... moreHaƙƙun ina tare da ke. Matuƙar al'umma zata jajjurce ta ƙi bada cin hanci to kuwa gwamnati bata da dogon hannun amshewa. Domin dai sai ka bayar za a amsa. Idan baka bayar ba zata ƙwaci cin hanci hannunka ta ƙarfi ne? Ko kuma zata fito ta shaidawa duniya cewa ta koreka saboda baka karɓar cin hanci?
Hassana Zakariyya MAIDARU → MARUBUTA: HUJJA TA GABA:
Mu yi aiki da hankali da kuma lura. Shin idan gwamnati ta bawa masu bata cin hanci abinda suke so mu kuma sai mu biye mata duka mu zama abu ɗaya.
Idan gwamnati ta karɓa mu kuma ai muna da ikon daƙilewa muƙi bayarwa. Laifinmu ne da... moreHUJJA TA GABA:
Mu yi aiki da hankali da kuma lura. Shin idan gwamnati ta bawa masu bata cin hanci abinda suke so mu kuma sai mu biye mata duka mu zama abu ɗaya.
Idan gwamnati ta karɓa mu kuma ai muna da ikon daƙilewa muƙi bayarwa. Laifinmu ne da muke bawa gwamnatin, tunda da zamu haɗa kai mu kaucewa afkuwar hakan da gwamnatin ta saduda, da ba a samu yawaitar masu bayarwarba da gwamnatin bata samu ƙarfin guiwar cigaba da aiwatar da haramtaciyyar hanyarta ba.
Annabi S.A.W na cewa, ka kaucewa saɓon Allah ta hanyar hani da furucin bakinka, ko kuma ka ƙi abun a zuciyarka idan baka da yadda zaka yi. To mu muna da yadda zamu yi idan muka kaucewa bayarwar ai zamu yi nasarar taƙaita abun.
Wanda ya daka ta bado... less
Fadima
Shi mutun ai yana buƙatar ya rayu, wannan yasa yake hakuri tunda Gwamna ba Adala ba ce yake haƙura ya bayar ko ya karba da tana adalci shi da zai fitar a aljihunsa ai bama zai ciro ba bare ya bada
Hassana Zakariyya MAIDARU → MARUBUTA: MAHANGA TA GABA:
Al'ummah ta taka muhimmiyar rawa wajen ba wa cin hanci duga-dugan zama a zuƙatan mutane da yawa. Cin hanci asali ya samo tun daga mu'amalarmu ta yau da kullum.
Idan muka koma gida zamu ga cewar matakin farko da ake ɗora yara shi ne... moreMAHANGA TA GABA:
Al'ummah ta taka muhimmiyar rawa wajen ba wa cin hanci duga-dugan zama a zuƙatan mutane da yawa. Cin hanci asali ya samo tun daga mu'amalarmu ta yau da kullum.
Idan muka koma gida zamu ga cewar matakin farko da ake ɗora yara shi ne ummul'aba'isin kafa cin hanci me lasisi.
Uwa ce zata aiki ɗa, amma sai ta fahimci yana noƙewa sai ka ji an ce,
"maza ka dawo in baka alawa"
Ko kuma, "un go ka siyi cingum"
Yaro zai zo da rawar jiki ya amshi wannan aike ya ce. To idan mukan yi karatun ta nutsu a nan zamu fahimci abubuwa biyu zuwa uku. Ita uwar ta bada wannan alawa ko kuɗi ne domin san yaro ya cika mata uzurinta kan lokaci. Shi kuma yaron nan ya je wannan aike ne saboda wannan abu da aka ba shi. To daga wannan lokaci sai ka ga yaro duk ƙanƙantar aike sai an haɗashi da wani hasafi zai je, daga nan ma zai gane duk abinda kake so idan ka biya za a maka.
Kunga tun daga nan an ɗora tarbiyar yaro kan turba mara kyau, Kunga ko mun ƙi ko mun so cin hanci ya samu foruwar turba ne daga gida.
Babu laifin Gwamnati a nan! less
Hassana Zakariyya MAIDARUTabbas bada kyauta abu ne mai kyau da addini da al'adarmu ta koyar, amma bada abu a matsayin abin da zai sa a maka wani abu wanda ba dan shi ba ba za a maka ba, wannan cin hanci ne.
Duk yaron da kika ji ance yi min kaza ga kaza lallai idan ba a bashi... moreTabbas bada kyauta abu ne mai kyau da addini da al'adarmu ta koyar, amma bada abu a matsayin abin da zai sa a maka wani abu wanda ba dan shi ba ba za a maka ba, wannan cin hanci ne.
Duk yaron da kika ji ance yi min kaza ga kaza lallai idan ba a bashi ba ba zai yi ba, ko kuma ya yi ba yadda ake so ba.
Nura Ismail
Wannan bayani ya kama zuciyata ƙwarai da gaske. Tabbas a wannan zamani aiken yara ɓacin rai ne, musamman idan suka san ba su da wata mamora. Kuma iyayensu ne suka taka muhimmiyar rawa a kasantuwar hakan.
Hassana Zakariyya MAIDARU → MARUBUTA: Cin hanci nada ma'ana da yawa ta fanin addinni da kuma al'ada. Cin hanci ɗabi'ace mara kyau, wadda ta haɗa duk wata mu'amal wace babu tsoron ubangiji a cikinta.
A ɓangaren addinni mun sani cewa musulunci ya samar da cikakkiyar fayyatacciyar mafita... moreCin hanci nada ma'ana da yawa ta fanin addinni da kuma al'ada. Cin hanci ɗabi'ace mara kyau, wadda ta haɗa duk wata mu'amal wace babu tsoron ubangiji a cikinta.
A ɓangaren addinni mun sani cewa musulunci ya samar da cikakkiyar fayyatacciyar mafita ba ma ga cin hanci ba kawai ba, har da duk wata matsala data adabi al'umma take barazana ga kwanciyar hankalinsu. Sai dai a yanzu kam cin hanci shi ne abu mafi muhimmanci da al'umma suka saka a gaba. Sun sa ƙafa sun doke dokar da addinni ya gindaya. Komai ƙanƙantar sana'a sai ka samu ɗan cin hanci cikinta. less
Sanah
Tabbas kuma babu kunya babu tsoron Allah haka suke miƙashi ba tare da tunanin cewa za a iya yaɓa musu taɓo a fuska a dawo da shi ba. \nMu muka asassa cin hancin ya yi ƙarfi a tsakaninmu saboda son zuƙatanmu.
Sunana Hassana Zakariyya ni ce wakiliyar Gamzaki writer's association. Na tsaya ne domin kare ɓangaren da ya... moreAssalamu alaikum warrahamatullahi. Ƴan kallo, alƙlan muhawara, abokan karawata duka ina miƙo saƙon gaisuwa da kuma fatan alkhairi gareku.
Sunana Hassana Zakariyya ni ce wakiliyar Gamzaki writer's association. Na tsaya ne domin kare ɓangaren da ya zamo mallakina wato cin hanci ba laifin gwamnati bane. Ku biyoni in gamsar daku bisa doron gamsassun hujojina masu zuwa.
Kungiyoyi su sake duba kaidojin wannan zagayen da kyau musamman wajen adadin kalmomi. Idan kungiya ta kara kalmomin da suka zarce yadda aka tanadar, za a zaftare mata maki kamar...... moreAlmustapha Adam Muhammad → MARUBUTA:
Tunatarwa
Kungiyoyi su sake duba kaidojin wannan zagayen da kyau musamman wajen adadin kalmomi. Idan kungiya ta kara kalmomin da suka zarce yadda aka tanadar, za a zaftare mata maki kamar... moreTunatarwa
Kungiyoyi su sake duba kaidojin wannan zagayen da kyau musamman wajen adadin kalmomi. Idan kungiya ta kara kalmomin da suka zarce yadda aka tanadar,...
Jibrin Adamu Rano → MARUBUTA:
ZUWA GA ALƘALAN MUHAWARA
Aminci ya tabbata a gare ku, tare da fatan kuna lafiya. Dalilin rubuto muku wannan wasiƙa shi ne: Don na danni ƙirjin ku bisa al'amuran da ke faruwa game da gasar nan. Na sha yin alƙalancin... moreJibrin Adamu Rano → MARUBUTA:
ZUWA GA ALƘALAN MUHAWARA
Aminci ya tabbata a gare ku, tare da fatan kuna lafiya. Dalilin rubuto muku wannan wasiƙa shi ne: Don na danni ƙirjin ku bisa al'amuran da ke faruwa game da gasar nan. Na sha yin alƙalancin gasa, don haka na san irin... moreZUWA GA ALƘALAN MUHAWARA
Aminci ya tabbata a gare ku, tare da fatan kuna lafiya. Dalilin rubuto muku wannan wasiƙa shi ne: Don na danni ƙirjin ku bisa al'amuran da ke faruwa game da gasar nan. Na sha yin alƙalancin gasa, don haka na san irin yanayin da ake tsintar kai a yayin bayyana sakamako, musamman ma a rintsi irin wannan.
Ranar yaƙin Hunain Annabi (S.A.W) ya raba ganima. Bayan ya kammala wani sai ya ce, "Ba a yi rabon adalci ba". Ran Annabi (S.A.W) ya ɓaci; ya ce: Wane ne zai yi adalci, idan Allah da manzonSa ba su yi ba?
Wani ya nemi ɗan'uwansa ya yi masa iso wajen Sayyadi Umar lokacin yana halifanci. Da aka kai shi wajen Sayyadi Umar sai ya ce: Kai ba adalin shugaba ba ne; ba ka hukunci da gaskiya. Sayyadi Umar ya fusata ya mike zai ɓarar da shi. Sai ɗan'uwan mutum da ya yi wannan katoɓarar ya janyo wa Umar aya.
_"Ka yi riƙo da afuwa; ka yi umarni da kyakkyawa kuma ka kau da kai ga barin wawaye"_ (Aaraf aya ta 199)
Sayyadi Umar ya kasance mai tsayuwa a kan Alƙur'ani. Don haka da ya ji wannan tunatarwa sai jikinsa ya yi sanyi. Ya ƙyale wannan mutumin. Shi ya sa irin wannan ba yau aka saba ba.
A madadina da duk wani ɗa na MARUBUTAN HAZAƘA muna sanar da ku cewa ko a gobe idan aka kara da mu muka faɗi za mu haƙura mu zo a ci gaba da damawa da mu, tunda dama an ce MAKASHIN MAZA, MAZA KAN KAR SHI. Kafin a kayar da... less
Nura IsmailMadalla da wannan tunatarwa abokina.\n\n\"Idan Allah Ya taimake ku, to babu mai iya rinjayar ku. Idan kuwa Ya yarɓe ku, to babu mai iya taimakon ku. Ga Allah ne kaɗai muminai suke dogara\" (Aali Imran aya ta 160).\n\nNasara da faɗuwa duka suna tafiya... moreMadalla da wannan tunatarwa abokina.\n\n\"Idan Allah Ya taimake ku, to babu mai iya rinjayar ku. Idan kuwa Ya yarɓe ku, to babu mai iya taimakon ku. Ga Allah ne kaɗai muminai suke dogara\" (Aali Imran aya ta 160).\n\nNasara da faɗuwa duka suna tafiya ne, da izinin Ubangiji. Wanda ya yi tutsu to kamar bai yadda da hukuncin Allah a kansa ba. Duk da cewa faɗuwa tana da cin rai, amma haƙuri yana ƙara martaba da ɗaukaka.