Awowina dubu daya da dari hudu da arba’in ina kutsawa a cikin dokan daji da kafa. Kwanaki sittin kenan ko nace watanni biyu. Na lashi tokobin gwara na mutu da na koma ba tare da na samu ganin boka kallamu ba. Kudi shine burina, wallahi na gaji da ba...
Maimarta Sarkin Bauchi Dr Rilwanu Suleiman Adamu C.F.R ya kafa Gidauniya Domin Tallafawa ma Yayan marasa Galihu Dan su samu ingantaccen Ilimi kan
Kulawarsa Sarkin Bauchi ya kaddamar da
tsarin yanda masarauta da Attajirai zasu Tallafi yaran Talakkawan jihar sa Domin taimakawa da kuma kara zumunci tsakanin masu sarauta Attajirai da kuma marasa Galihu,
Bude Gidauniyar mai suna (Amir (Dr) Rilwanu Suleimanu Adamu foundation)
Kai tsaye Sarkin yayi Umarnin a nemo yaran Talakawa guda 30 wanda zasuyi Jarrabawa ta Jamb aka biya musu tare kuma da Daukar nauyin karatun su har su kammala jami'a wannan a matakine na Gwaji wanda Gidauniyar zata cigaba da Daukar nauyin yaran marasa karfi iyakar I yawanta har sai an tabbatar da samun nasarori,
"Daga cikin mutanen da aka zaba an zabi mata guda goma sha tara 19 maza guda Goma sha daya 11, wanda Zaa fara Wannan shiri dasu,
Lokacin da yake jawabi a wajen mai martaba sarkin Bauchi farko ya mika Godiyarsa ga Allah daya nuna masa wannan rana mai dauki da dunbin tarihi da kuma bashi ikon kaddamar da wannan GIDAUNIYYA, sai ya zarce da kira ga daliban dasu kasamu wannan TALLAFI da suyi amfani da wannan dama na kara azaman yin karatu da sadaukarwa don samun ilimi mai Albarka maimartaba yace jihohin kudanci sunyi mana nisa wajen Irin wannan Gidauniyar wanda mune mukafi chanchanta wanda muke kan koyarwa ta Addinin Musulunci da ke koyar da tausayi tsakanin Al'umma wajibi ne Shugabanni su zamo rahama wa marasa karfi da suke karkashin su shine ke samar da kauna tsakanin Al'umma