Rufaida Umar
NADAMAR FURUCI
©Rufaida Umar.
"Hoo! Ka ji kunya! Wallahi ka ji kunya! Tirr! Da miji irinka!"
Wata siririyar mace ce ta ci ɗamara a daidai majalisar wasu dattawa tana sababi. Wanda ake dominsa, ya sunkuyar da kai yana jin wani raɗaɗi a ƙasan ransa. Ga yara da manya an taru ana kallonsu.
Wani tsamurmurin dattijo dake gefensa ya dubi matar yana nuna ta da yatsan shi manuniya.
"Wallahi Asabe ki ji tsoron Allah, ki tuba tun kafin lokaci ya ƙure miki! Wane irin wulakanci ne za ki biyo mijinki bainar jama'a ki ci mutuncinsa? Ƙarin aure a kansa aka fara ne?"
Jin haka ya sa ta yi kan Dattijon nan da sababi.
"Kai Amadu! Wallahi ka yi gaggawar fita daga idanuna na runtse! Dama ai ko ba ka nuna hali ba na san ku ne munafukan da ke hure mishi kunne! Wato ga annoba, yana kawo muku karya da gaskiya a kaina kuna haɗuwa ku zage ni tas! Hakan kaɗai bai yi muku ba sai da kuka ga zai auro min sa'ar ɗiyata. Kai ai da ace ma na samu ciki da wuri da tuni na aurar da Yaha. Amma tsabar wulaƙanci, a rasa wa za a haɗa ni kishi da ita sai yarinya ƴar bana-bakwai! To wallahi karr nake kallo ku! Aure ne dai ina raye Murtala bai isa ya yi shi ba. Idan kuwa yana ja da ni to mu zuba mu gani! Ya dai ji kunya wallahi, an girma ba a san an girma ba!"
Ran dattijan ya ɓaci, Sule wanda ya fi su harzuƙa ya miƙe tsaye jiki yana rawa.
"Mutuniyar banza da wofi! Yau kin ƙara tabbatar da ko ke wace ce! Na yi tirr da shawarar da na ba Murtala na aurenki, da ace na san za ki zame mishi bala'i da masifa da ban soma ba! Kuma Asabe mutuwa ce sai dai ki yi, aure dai babu fashi! Ɗan'uwanmu ba zai mutu da annoba irinki ba! Shashasha kawai!"
Wata irin shewa ta sanya gami da sakin guɗa tana rausaya kai kamar taɓaɓɓiya.
"Ayyiriri nanaye! Yaro bai san wuta ba sai ya taka wallahi! Mu zuba mu gani Sule, gobe dai za a daura aure ko? To, ni Asabe na ce mu zuba, na ga uban da ya isa ya ɗaurawa Murtala aure. Zan kashe mutum na kashe banza wallahi! Duk abin da ya biyo baya ka yi kuka da kanka!"
Daga haka ta bar wajen tana sababi da kururuwa da cika-baki. Murtala har lokacin bai ɗago ba sai zubar da hawaye, sai da Amadu ya kori dukkan jama'ar da suka taru kafin ya soma yi wa Murtala magana cikin faɗa-faɗa.
"Me ya sa ba za ka iya sakin wannan matar ba? Haƙuri na me kake yi da ita har haka Murtala? Cin mutumcin da take maka ya yi yawa kai kuwa kamar ma ba gani kake ba! Akan wane dalili? Idan yara ne Allah Ya raya maka su. Amman wannan cin mutumcin da me ya yi kama?"
Sule ya yi ƙwafa.
"Ka ƙyale shi! Tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka ai, na ce ka rabu da shi kawai Amadu! Kunnen Murtala ba ya jin laifin Asabe, idanuwansa ban ce suna gani ba. Amman na rantse da Allah ba macen da ta isa na zauna ta ci mutumcina irin haka! Ka zama namiji, kuka aikin banza ne! Wannan ba matar rufin asiri ba ce."
Shi dai Murtala ba baka sai kunne, ya gama sauraronsu, da ƙyar ya saki ransa bayan sun ƙarashe da yi mishi nasiha mai kwantar da zuciya kafin daga bisani su hau zolayarsa akan amaryar da zai yi. Nan ya ɗan sake amman labarin zuciya a tambayi fuska.
***
Washegari da misalin ƙarfe takwas, Asabe ce tsaye ƙiƙam a ƙofar ɗakin Murtala tana dakon fitowarsa duk kuwa da ta sanya sakata ta rufe ɗakin gam tun daren jiya da ya dawo gida. Bugun duniya ya yi bata buɗe ba, abinci ma cewa ta yi wanda su Amadu suka ba shi a majalisa ya ishe shi. Da Asuba ma bata buɗe ba shi ma bai ƙwanƙwasa ba. Wannan ya sa tana tashi, ta kasa, ta tsare a bakin ƙofar. Yaranta sai safa da marwa suke yi suna masu jin takaicin halin uwarsu, yayin da masu goya mata baya na yi.
Atika wacce ta fi kowannensu tausayin baban nasu ta dube ta.
"Haba Umma, don Allah mene ne haka kike yi? Kin hana Baba fita alhalin kin san yau..."
"Atika zan ci ubanki! Zan ci ubanki wallahi muddin ba ki fita a hanyata ba. Shegiyar yarinya marar kishin uwa. Ku wuce ku tafi makaranta tun ban karya ƙafafunku ba."
Atika ta goge hawayenta, ta ja hannun ƙannenta su biyar suka fice daga gidan. Suna fita ta ci karo da Amadu da Sule sai wani Kawun babansa Murtala a waje. Ta gaishe su.
"Kira mana Babanku mana, lokaci na ƙurewa."
A sanyaye ta labarta musu abin da ke faruwa. Wannan ya sanya suka shiga gidan da sallama, musamman ma Sule wanda ya fi su shaƙa. Asabe na zaune saman kujera tana girgiza ƙafa tana cin ƙosai mai zafi, ba ta ko jin zafinsa saboda yanda ranta ke suya. Kallon tara saura ta yi musu kafin ta kau da kai tana ƙwafa.
"Asabe wace irin mata ce ke? Me ya sa ba kya jin bari?!"
Kawu ke wannan maganar cikin tausasan lafazi don a tunaninsa zai sa ta tausaya. Ta miƙe tsaye gami da furzar da ƙosan bakinta, harara ta watsa musu da jajayen idanunta waɗanda kishi ya rinar.
"Lamido kake ko Rilwan? To wallahi ba ka isa ka aurar da mijina ga kowace shegiya ba, ba zan yarda ba! Mutu ka raba ni da Murtala! Ba wanda ya isa ya..." Ai bata kai ƙarshe ba, Sule ya dauke ta da kyakkyawan mari yana huci. Wani irin hantsilawa ta yi, ta daka tsalle ta miƙe ta yi kansa tana kantara ashariya.
"Ni! Ni za ka mara har gidan aurena Su.."
Bata kai ga ƙarasawa ba ya ƙara dauketa da wani marin, ya angiza ta gefe.
"An mare ki asararriya! Na ce an mara ɗin! Banza da bata san darajar aure ba! Kuma wallahi kika yi wani yunƙurin hana mu fid da Murtala daga gidan nan sai na zage na ci ubanki!"
Ya dubi Amadu.
"Amadu buɗe min ƙofar nan!"
Amadu ba musu ya ƙarasa ya zare sakata, shi kuwa Sule suna faɗi in faɗa da Asabe wadda ta koma tamkar zararriya.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Furucin Amadu ya maido da su hayyacinsu. Gabaɗaya suka dube shi. Kawu ya ƙarasa ɗakin da sauri. Ganin haka duk suka shiga ciki. Abin da suka gani ya yi matuƙar gigita su.
Murtala ne kwance, jini na fita ta kunne da hancinsa. Iyakar ruɗewa sun shiga. Wata irin azabbabiyar ƙara Asabe ta saki. Ta juya da zummar fita daga ɗakin sai dai cikin zafin nama Amadu ya tare ƙofar.
"Annamimiya! Ina za ki?! Ina za ki je bayan kin kashe shi?!! Babu inda za ki fita!!"
Asabe ta fashe da kuka.
"Wallahi na rantse da girman Allah ban kashe Murtala ba! Wallahi ban kashe shi ba!"
Kawu wanda ke fid da hawaye jikinsa har rawa yake ya dubi Sule.
"Sulaimanu, kira ƴansanda."
Jin haka gabaɗaya Asabe ta ƙara rikicewa tana haɗa su da Allah su rufa mata asiri, rantsuwa sosai ta shiga yi akan ba ita ta kashe Murtala ba, amman ina! Babu mai sauraronta.
Atika na cin karo da gawar Babanta ta fasa ƙara ta faɗi anan ta sume.
Hayaniyar ta jawo hankalin makwabta, sai ga shi an soma cika gidan. Babu jimawa Sule ya dawo tare da ƴansanda, Asabe na ta rantsuwar ba ta kashe mijinta ba sai dai babu wanda ya saurareta. Kowa ma ya buɗe baki cewa ya ke yi za ta aikata duba da irin furucin da ta dinga yi na kashe rai. Har tana ikrarin MU ZUBA MU GANI.
Da wannan aka tafi da Asabe ofishin 'yansanda. Iyakar binciken ma'aikata ba su gano taƙaimaiman abinda ya kashe Murtala ba.
Haka aka ci gaba da tsare Asabe kafin a kammala shari'a. Iyakar gaskiyarta ta faɗa akan ba ta kashe Murtala ba, sai dai babu wanda ya saurareta ballantana ya yarda duba da munanan kalamanta waɗanda da su lauyan dake kare haƙƙin Murtala ya ci galabar da Alƙali ya sa a tsare ta.
Kwananta uku a gidan yari, tana zaune zugum tana tunanin munanan halayenta, aka aiko tafiya da ita ta yi baƙo. Bata ta6a zaton akwai wanda zai duba maraicinta ya ziyarce ta ba, haka nan Atika tun a harabar kotu ta ce babu ita ba ita saboda ta kashe ubanta.
Bayan an kai ta ɗakin ganawa da baƙi, ta saki baki ganin ba kowa ba ne sai Sule. Wani irin murmushi yake yi mata na mugunta har ta samu wuri ta zauna. Bayan idanu sun ɗauke a kansu ya soma magana.
"Asabe kenan, sannu kin ji? Ai dama wanda ya riga ka kwana to zai riga ka tashi. Har kina zaton Ni zan mance irin tsantsar yaudarar da kika yi min a zamanin samartaka? Wannan kaɗan kika gani, sai na sa an kashe ki kamar yanda na ba da Murtala ga Dodon tsafi."
Ya dan yi waige-waigensa kafin ya dube ta yana murmushi cikin raɗa ya ce.
"Ni ne silar mutuwar mijinki, kuma ni zan zama silar taki mutuwar. Ko a haka na bar ki na kashe ki Asabe! Wannan somin ta6i ne daga ni Sule."
Cikin rawar murya ta nuna shi da yatsa.
"Kai.. kai...ne..su..?"
Dariya ya saki a hankali.
"Ƙwarai kuwa, ni ne nan silar mutuwarsa domin a duniya babu abin da nake so ban da shahara da dukiya. Ko ta wane hali sai na samu."
Wata razananniyar ƙara ta saki, ta cakume shi da hannayenta tana kuka.
"Sule ɗan'uwansa?! Ɗan'uwansa?! Allah Ya isa tsakanina da kai!"
Ganin tana neman tona asirinsu ya yi saurin fincikewa, gandiroba ta yi saurin zuwa ta rirriƙeta. Tana zage-zage da tsinuwa sai dai ba wanda ya kula da sambatunta. Sun ga fin haka a gidan yari, Sule na murmushin mugunta har aka shige da ita ciki sannan ya juya ya fice daga wurin zuciyarsa tas ya bar Asabe cikin NADAMAR FURUCI.
*KARSHE*