A kowace shekara miliyoyin mutane ne suke kamuwa da son juna. A kowace shekara kuma miliyoyin aure ake daurawa. Amma abin takaici kuma a kowace shekarar dai miliyoyin auren ne suke watsewa! Saboda wancan son da suke yi wa juna a baya, yanzu ya gushe! Daga...
Shin wai ni yau bari na tambayeki. Shin wai Hameedu ƙafar Habu Maharbi ya cire ko kuwa ta Bawa? Shin wai Hameedu dukiyar Ladi ya cinye ko kuwa ta Bawa? Shin shi Bawan me yake zame miki ne banda miji? Shin akwai wani jini guda ko da na halittar kaza ne da ...
Barkanmu da sake kasancewa a wannan fili na muhawara wanda ke zuwa daga taskar Bakandamiya, inda marubutan Hausa suka wasa ƙwaƙwalensu wajen kawo hujjoji masu kare ra’ayinsu a kan batutuwa mabambanta da suka shafi rayuwarmu ta yau da kullum. A yau z...
_As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah._... more#SIFFAN SAHIHIN TSARKI
... moreMustapha musa abu Aisha
#SIFFAN SAHIHIN TSARKI
_As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah._... more#SIFFAN SAHIHIN TSARKI
_As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah._
Malam, ina da tambayoyi ne:
(1) Yaya ake yin sahihin wankan janaba?
(2) Yaya ake sahihiyar taimama?
(3) Yaya ake sahihin addu’ar saduwa da iyali?
*AMSA A159😗
_Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh_ .
Ga abin da na kalato daga cikin littafina: *Zuwa Ga Sabon Saurayi* da *Zuwa Ga Sabuwar Budurwa* a kan hakan:
*[1] SIFFAR KAMA-RUWA*
Yadda musulmi zai kama-ruwa a sunnace shi ne:
(1) Ya yi nesa daga mutane domin kar su ji ƙara ko wari ko kuma su ga tsiraicinsa.
(2) Ya nemi wuri mai laushi don ya kare jikinsa daga tartsatsin najasa, mai aukar da Azabar ƙabari.
(3) Ya yi addu’ar Sunnah kafin ya shiga wurin biyan buƙatar, ya ce:
اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْخُبُثِ وَالْخَبَائِثِ
Ya Allaah! Ina roƙon ka tsare ni daga shaiɗanu maza da mata
_(Sahih Al-Bukhaariy: 142, Sahih Muslim: 375)._
(4) Ya fara shiga makewayin da ƙafar hagu, saɓanin yadda yake shiga masallaci.
(5) Kar ya ɗage tufafinsa har sai ya yi daf da ƙasa domin ya kare su daga shafar najasa, kuma ya kare tsiraicinsa daga idon mutane.
😈 Kar ya fuskanci Alƙibla kar kuma ya juya mata baya a duk inda yake biyan buƙatarsa.
(7) Kar ya shafi al’aurarsa da hannun dama a wurin biyan buƙatarsa, ko kuma a lokacin tsarki.
🎵 Ya fara yin tsarki da wanke hannunsa na hagu ne bayan ya gama biyan buƙatar.
(9) Ya fara wanke mafitan fitsari ne da farko kafin ya koma ga na bayan-gida.
(10) Ya tabbatar wuraren sun fita fes kafin ya daina zuba ruwan.
(11) Ya goge hannunsa a kan ƙasa ko turɓaya, ko ya wanke shi da sabulu sosai.
(12) Yana iya amfani da _tissue paper_ ko makamancinsa tare da wankewa ko kuma a maimakon wankewar, in ji waɗansu malaman.
(13) Ya kammala gogewar a kan wutri ne, watau a na uku ko na biyar ko fiye da haka, har sai ya fitar da na ƙarshe babu komai a jikinsa.
(14) Ya fito da ƙafar dama daga ban-ɗakin saɓanin yadda yake fita daga masallaci.
(15) Ya yi addu’a bayan fitowa daga makewayin, ya ce:
غُفْرَانَكَ
Ina neman gafararka (Ya Allaah)
_(Sahih Al-Jaami’: 4714)._
*[2] SIFFAR ALWALA*
Yadda za ka yi alwala a Sunnace shi ne:
(1) Ka fara da yin aswaki kamar yadda Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya koyar.
(2) Ka tabbatar ruwan yin alwalar mai tsarki mai tsarkakewa ne tun farko.
(3) Ka ɗaura niyyah a cikin zuciyarka, mai ƙunshe da neman yardar Allaah Ta’aala.
(4) Ka fara aikin alwala da ambaton Sunan Allaah Ta’aala, ka ce:
بِسْمِ اللهِ
Da sunan Allaah
_(Sahih Ibn Maajah: 320)._
(5) Ka wanke hannuwanka guda biyu a haɗe har zuwa wuyan hannuwan.
😈 Ka kurkure bakinka, ka shaƙa ka fyace da tafin ruwa guda ɗaya.
(7) Ka wanke dukkan fuskarka daga goshi zuwa ƙarshen haɓa, daga kunnen dama zuwa na hagu.
🎵 Ka wanke tsintsiyar hannunka na dama, tun daga kan yatsun har ya haɗa da gwiwar hannun.
(9) Ka tsettsefe tsakanin yatsun hannunka, ka kula da kan gaɓoɓin yatsun su ma.
(10) Ka wanke hannunka na hagu kamar yadda ka wanke na dama, ba bambanci.
(11) Ka jiƙa tafukanka, ya shafi dukkan kanka gaba-ɗaya daga goshi har zuwa ƙeyarka, sannan ya dawo zuwa goshin.
(12) Ka shafi ciki da wajen fatun kunnuwanka da danshin ruwan da ya rage a hannuwanka daga shafar kai.
(13) Ka wanke kafarka ta dama tun daga kan yatsu, ya haɗa da idanun sawunka.
(14) Ka tsattsefe tsakanin yatsun da ƙaramar yatsar hannunka, kuma ka goggoge duddugen ƙafarka ta dama da kyau.
(15) Ka wanke ƙafarka ta hagu, kamar yadda ka wanke ta dama ita ma ba bambanci.
(16) Kana iya yin shafa a kan safa ko takalma maimakon wanke ƙafarka, idan ka sanya safar ko takalman a bayan tsarki ne.
(17) Kana yin shafar har kwana uku, in a halin tafiya ne, ko kuma kwana ɗaya kawai in a halin zaman-gida ne.
(18) Ka wanke dukkan gaɓoɓinka a cikin zama guda kawai, kuma kar ka yi ɓarnar ruwa, amma ka kyautata wankewa sosai.
(19) Kana iya maimaita wanke dukkan gaɓoɓin alwalar sau biyu-biyu ko uku-uku.
(20) Ka kammala alwalarka da addu’ar da ta tabbata a cikin Sunnah kawai, ka ce:
أَشْهَدُ أَنْ لَآ إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّداً عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ
اللَّهُمَّ اجْعَلْنِي مِنَ التَّوَّابِينَ وَاجْعِلْنِي مِنَ الْمُتَطَهِّرِينَ
Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allaah, shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, kuma na shaida lallai Annabi Muhammad Bawansa ne kuma Manzonsa ne.
Ya Allaah! Ka sanya ni a cikin masu yawan tuba, kuma ka sanya ne a cikin masu neman tsarkaka.
_(Sahih Muslim: 234, Sahih At-Tirmiziy: 55)._
*[3] SIFFAR TAIMAMA*
Yadda kuma zai yi taimama a sunnace shi ne:
(1) Ya tabbatar kan ƙasar da zai yi taimamar wuri ne mai tsarki mara ƙazanta.
(2) Ya fara da faɗin *‘Bismil-Laahi’* yana mai ɗaura niyyar taimamar a cikin zuciyarsa.
(3) Ya ɗora cikin tafukan hannuwansa biyu a kan ƙasar da zai yi taimamar.
(4) Ya ɗago hannuwan daga kan ƙasar, kuma ya hure tafukan da bakinsa.
(5) Ya shafi dukkan fuskarsa tare da hannuwansa guda biyu, har zuwa wuyan-hannuwa kawai.
😈 Kar ya ɗora tafukan hannunsa a kan ƙasa fiye da sau ɗaya a taimama guda.
(7) Kada ya shafi fiye da wuyan-hannuwa a wurin shafar hannuwa a taimamarsa.
🎵 Yana iya yin taimama a jikin bango, ko da kuwa an shafe shi da siminti kuwa.
(9) Yana iya yin taimama daga gida sannan ya tafi masallaci, kamar dai alwala.
(10) Ya yi alwala ko wanka a lokacin da ya samu ruwa domin salloli masu zuwa.
_(Dubi ƙarin bayani a cikin Al-Wajeez Fee Fiqhis Sunnati Wal Kitaabil Azeez, shafi: 70-73)._
*[4] SIFFAR WANKA*
Kuka yadda zai yi wanka a sunnace shi ne:
(1) Mutum ya ɗebi ruwa mai tsarkakewan da zai ishe shi yin wankan, ba tare da ɓarna ba.
(2) Kar ya yi wanka tsirara a cikin jama’a, sai dai in shi kaɗai ne, ko kuma in yana tare da Muharrami ko Muharramarsa.
(3) Ya fara da yin tsarki, ya wanke duk ƙazantar da ke jikinsa, sannan ya goge hannunsa a kan ƙasa ko ya wanke da sabulu.
(4) Ya yi alwala cikakkiya kamar irin alwalar da ka ke yi saboda Sallah.
(5) Ya jiƙa tafukansa ya murtsuka gashin kansa, sannan ya kwara ruwa a kansa ya wanke shi har zuwa wuyansa sau uku.
😈 Ya kwara ruwa a kafaɗarsa ta dama, ya wanke har zuwa ƙasa, kuma ya wanke bayansa, kamar yadda ya wanke gaba.
(7) Ya kwara ruwa a kafaɗarsa ta hagu, ya wanke sashin jikinsa na hagu, kamar dai na dama.
🎵 Ya matsa daga inda ya yi wanka, ya wanke ƙafafunsa sosai da sasai.
(9) Mai wankan haila ta fara da warware kitson gashin kanta domin ta samu damar cuccuɗa kanta, har ta tabbatar ruwan wankan ya samu shiga zuwa ga ƙoƙon kanta.
(10) Dalili, in ji wasu Malaman: Saboda hadisin A’ishah _(Radiyal Laahu Anhaa)_ inda ta ce Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya umurci Asma’u Bint Shakal _(Radiyal Laahu Anhaa)_ a wurin wankan haila da cewa:
ثُمَّ تَصُبُّ عَلَى رَأْسِهَا فَتَدْلُكُهُ دَلْكًا شَدِيدًا
Sai kuma ta kwara ruwa a kanta, ta cuccuɗa shi, cuccuɗawa mai tsanani.
Amma a wurin wankan janaba sai dai kawai ya ce:
ثُمَّ تَصُبُّ عَلَى رَأْسِهَا فَتَدْلُكُهُ
Sai kuma ta kwara ruwa a kanta, ta cuccuɗa shi
_(Sahih Muslim: 332)._
Watau a nan bai ce: *‘cuccuɗawa mai tsanani’* ba a wankan janaba!
*[5] ADDU’AR SADUWA DA IYALI😗
Amma yadda ango zai yi addu’ar Sunnah a lokacin haɗuwa da amarya shi ne:
(1) Lokacin da ya shiga wurin amarya a daren farko sai ya dafa goshinta, ya yi wannan addu’ar domin fatar samun daidaituwar al’amura a tsakaninsu:
اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا وَخَيْرَ مَاجَبَلْتَهَا عَلَيْهِ ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا وَشَرِّمَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ
Ya Allaah! Ina roƙonka alherinta da alherin kyawun ɗabi’arta, kuma ina roƙon ka tsare ni daga sharrinta da sharrin mugun ɗabi’arta.
_(A cikin Sahih Abi-Daawud: 2160 As-Shaikh Al-Albaaniy ya ce: Hasan ne)._
(2) Daga nan kuma kafin fara kowace saduwa sai ya ce:
بِسْمِ اللهِ ، اللَّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا
Da sunan Allaah. Ya Allaah! Ka nisantar da shaiɗan daga gare mu, kuma ka nisantar da shaiɗan daga abin da ka azurta mu da shi.
_(Sahih Al-Bukhaariy: 5165, Sahih Muslim: 1434)._
_Wal Laahu A’lam._
Muhammad Abdullaah Assalafiy
25/10/2019
11: 13pm. less less
INA YAWAN FITAR DA MANIYYI SABODA MIJINA BA... moreGORON... moreRahmatu Lawan
GORON JUMMA'A
INA YAWAN FITAR DA MANIYYI SABODA MIJINA BA... moreGORON JUMMA'A
INA YAWAN FITAR DA MANIYYI SABODA MIJINA BA LAFIYA
Tambaya:
Assalamu Alaikum , Dr macece mijinta ba yada lafiyan aure tsawon lokachi, sai ya zamana tana yawan releasing ba sai tayi wani dogon tunani na sha'awaba, ya matsayin ibadarta yake?
Amsa:
Wa alaikumus salam
To gaskiya abin da yake daidai shi ne: ya nemi magani, in kuma bai samu ba, ana iya raba auran, tun da yana daga cikin manufofin aure, katange ma'aurata daga fadawa haramun, kamar yadda shararren hadisinnan ya tabbatar.
Yawan fitar maniyyi zai iya zama lalurar da za ta iya haifar da saukin sharia, saidai na ki ba zai zama lalura ba, saboda iyayenki za su iya wajabtawa mijin neman magani, in kuma bai samu ba, za ku iya rabuwa, Allah ya azurta kowa dağa falalarsa.
Cigaba da zamanku a wannan halin yana iya jefa ki cikin hadari, mata nawa ne suka zama mazinata ta hanyar wannan sababin?
Ya wajaba ki yi wanka duk sanda maniyyin ya fita, tun da ya fita ne ta... less
Auwalu Adamu SabongidaHaƙiƙa ana fama da wannan matsalolin a yanzu.\nSai dai mazan ne suke jefa matan cikin haɗarurruka saboda wani shi bai ma yarda ya na da matsalar ba, wani kuma ya na ganin kashi ne ya ce ba shi da lafiya.\nNa amsa wannan dabbarwar da bada shawarwari ga... moreHaƙiƙa ana fama da wannan matsalolin a yanzu.\nSai dai mazan ne suke jefa matan cikin haɗarurruka saboda wani shi bai ma yarda ya na da matsalar ba, wani kuma ya na ganin kashi ne ya ce ba shi da lafiya.\nNa amsa wannan dabbarwar da bada shawarwari ga wasu, mafi akasari akwai rashin fahimta da rashin sanin haƙƙin farko na aure ga mazajen. Allah ya kyauta.
Bad friends are like the waves in the sea,
They keep hitting us all the time with... moreBad Friends, Good Friends
Bad friends are like the waves in the sea,
They keep hitting us all the time with glee,
But good friends are like the stars in the sky,
The stay with us forever and teach us how to fly.
I'm glad that I have found such a lovely friend in you,
When you are around, I never find myself sad or blue.