*_♠️Dedicɑted To♠️_*
👇
*My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll 😘😘💋💋💖💖💓✌👌*
*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*Dukkan godiya da yabo marasa iyaka sun tabbata ga Allah mahaliccin kowa da komai, tsira da amincin Allah su kara jaddada ga Annabi _MUHAMMAD_ ((Sallallahu Alaihi Wasallama)).*
*Pɑge 1 & 2*
“Usainah Usainah, tashi ki shirya mana mu fita da wuri, kin san fa idan muka makara shikenan ba zamu samu aikin nan ba ko? Dan Allah ki tashi kin ga shekaranjiya ma ba mu samu shiga ba sakammakon ba muje da wuri ba.”
Dakyar wacce ake tashi daga baccin wato Usainah ta mike idanuwanta a tamaimaye da bacci tamkar ma a lokacin ta kwanta, sannan ga wata azababbiyar gajiya da ta game mata gaɓɓan jikinta. Hatta da 'yan tsunta dakyar take motsa su.
Haka ta lallaɓa ta mike ta fito ta nufi bayin gidan, inda ta iske mutane uku na jiran na ciki ya fito sannan su shiga. Ita ma sai ta hau layi ta zama ta huɗu kenan, kusan mintuna ashirin tana jira sannan layi yazo kanta, ta shiga ta kamo ruwa ta fito tayi alwala tayi sallah lokacin har rana ta fara fitowa sosai kamar misalin karfe 7:00am na safe.
Tana idar da sallar Hassana tace, “To tashi mu tafi, kin ga har rana ta fara yi, shiyasa nake tashinki tun da asuba ki shirya kafin kowa ya tashi a fara wannan layin shiga bayin na ƙaddara.” Nan suka mike suka yiwa Inna mahaifiyarsu sallama suka fice.
Hanya suka mika santal suna ta sauri kamar zasu tashi sama, har da sassarfa suke haɗawa, sunyi tafiya kamar mintuna goma sha biyar (15) sannan suka isa wani kamfanin aikin barkono dake rukunin kamafanoni na unguwar Dakata.
Cikin sa'a suna shiga aka rufe gate ɗin, sune na ƙarshe da zasu samu damar yin wannan aiki a wannan rana. Ba tare da ɓata lokaci ba ƙaramin manajan ya rubuta sunayensu a wani littafi da ake ɗaukar sunayen wanda suka samu aikin, suka shiga cikin hall suka kama aiki.
Wadannan yara Hassanah da Usainah kamar yadda kuka ji sunansu, 'yan mata ne 'yan kimanin shekaru sha bakwai zuwa sha takwas (17-18). Zaune suke a unguwar Tudun Wada tare da iyayensu wanda suka kasance masu ƙaramin karfi ainin.
Rayuwarsu cike take da ƙunci da talauci da rashin tabbas me tsanani. Ɗaki ɗaya ne tak! suke rike dashi a gidan da suke haya, kuma su biyar ke kwana a cikin wannan daki wanda shima ba wani babba ɗaki bane. Hassanah da Usainah da Inna da babansu, sai ɗan ƙaramin kanensu ana kiran sa Khalid, duk da kasancewar su Hassanah baligai ne haka suke gwamutsuwa da mahaifinsu a wannan daki komai tsananin zafin da akeyi kuwa.
Mahaifin nasu ana kiransa malam Isah ya manyanta sosai sannan ya gamu da larurar cutar laka (spinal cord). Kafin ya gamu da cutar ya kasance me sana'ar wanki da guga ne. Mahaifiyarsu kuwa sunanta Saude amma Inna suke ce mata.
Ba iya kamfanin barkono kadai suke zuwa aikin ba, dukkan wani kamafani da ake daukar leburorin wucin-gadi, su Hassanah zuwa suke suyi aikin. Ya danganta da lokaci da kuma nau'in abinda ake sarrafawa a kamfanin. Sukanyi aiki a kamafanin Ƙaro, kamfanin Riɗi kamfanin Citta da dai sauransu.
Wannan aiki da su Hassanah suke shine cinsu, shine shansu, shine suturar da suke sawa, shine kudin maganin cuta karama idan ta same su, uwa uba shine kuma hanyar da suke samun kudin biyan hayar dakin da suke zaune, a takaice dai Hassanah da Usainah sune ke rike da iyayen nasu da kuma ƙanensu Khalid.
A yini ɗaya basa yin aikin da ya wuce naira ɗari biyar (N500) kowacce daga cikinsu komai kokarin da zasu yi. Sune ma masu kokarin, domin wasu basa wuce suyi aikin dari uku ko dari hudu .
A cikin dari biyar din nan zasu ci abincin rana bashi kafin a su gama aikin a biya su, abincin safe kuwa ba samu suke ba, sai kamar ranar da Allah yasa suka yi tuwo da daddare yayi saura ,to da safen sukan samu su ci koda babu ɗumame.
Idan suka fita tun safen nan suka kama aiki basa tsayawa sai misalin karfe ɗaya zuwa biyu 1-2 na rana, a lokacin ne zasu samu wani abin su ci, kamar dambu, alala, ɗanwake da dai dangain abincin garau-garau da masu sayarwa ke kaiwa kamafanin. Bayan sun ci wannan abinci, wasu kanyi sallah wasu kam babu ruwansu da sallar ma.
Bayan nan zasu koma su sake kama aikin sai kuma yammaci sosai misalin karfe 5:00pm sannan zasu dakata. Manajan zai zo da littafin nan da aka dauki sunayensu, zasu kafa layi ana kiran sunayen nasu ɗaya bayan ɗaya ana basu kudin aikin da suka yi.
Gwargwadon kokarin mutum gwargwadon abinda zai samu, Hassanah da Usainah kan dage sosai su maida hankali a kan aiki, domin indai har sun samu damar yin aikin, to ladansu ɗari biyar - biyar ne idan aka haɗa jumulla sun kama naira dubu ɗaya daidai (N1,000).
Da zarar sun karɓi wannan kudi sai masu abincin nan suma su taso domin su karɓi hakkinsu. Da yake Hassanah da Usainah ba wani zagewa suke su ci abincin ba sosai, bai fi su kashe naira ɗari da hamsin ba (N150), dan haka sukan koma gida da aƙalla naira ɗari takwas (N800).
Basu dawo gida ba sai dafda magariba, to da yake sun san yadda suka bar gidan nasu babu wani abun taɓawa. Naira ɗari da hamsin ce kacal a hannun Inna, da safen Khalid ya sayo musu koko da ƙosai na naira saba'in, da rana kuma ya sayowa baban nasu kunun tsamiya ya ɗan kurɓa. Saboda haka tun daga kan hanya Hassanah da Usainah suka auno garin kwaki suka yo cefanen miya.
Isowarsu gida keda wuya Usainah ta haɗa
wuta tayi musu teba suka ci. Bayan sun gama cin abincin sunyi sallar Isha, jim kaɗan Hassanah tace, “Usainah shirya mu tafi Islamiyya, kin san yau laraba akwai haddar Qurani kuma da wuri malam Musa yake shigowa.”
Usainah ta mike ta zura hijabinta suka dauki jaka suka fice. Misalin karfe 9😸0pm suka dawo, nan suka cigaba da hira da Innar tasu har kusan karfe 10:00pm na dare. Innar tace, “Ku tashi kuje ku kwanta ku huta domin ku tashi da wuri gobe.”
Wannan ita ce irin rayuwar da waɗannan 'yan mata suke yi tare da mahaifansu. Mahaifinsu ba mutumin Nigeria bane, daga Nijar yazo, sannan ba wasu 'yan uwa bane dashi sosai, domin ita kanta Inna bai fi sau biyu bane ta taɓa zuwa Nijar ɗin. Su Hassanah kam basu taɓa sanin cewa Mahaifin nasu mutumin Nijar ne ba.
Farkon da larurar ta same shi, an kaishi asibiti an nemi kudin da za'a masa aiki kusan naira milliyan ɗaya, kuma sai an aje wannan kudi, za'a taɓa shi. Wannan al'amarin ba ƙaramin tada hankalin Inna da su Hassanah ba yayi, shin ina zasu samu waɗannan kuɗaɗe haka da basu taɓa ganinsu ba balle su san ma yawansu.
Da farko dai Inna wajen wani wanta taje ta kai masa kukanta. Shi dai wannan wan nata ya kasance me hali ne sosai a kasuwar kofar ruwa yake ɓangaren 'yan rodi, babu shakka yana da kuɗi. To sai dai ya kasance irin mutanen nan ne mararsa adalci, marasa imani masu wulaƙanta zumunci, bashi da kirki ko kaɗan mutumin banza ne.
Bayan sun gaisa ta gabatar masa da ƙoƙon bararta da ya taimaka mata koda ma bai biya kudin duka ba, ya dan bada kafin alƙalami idan yaso ita ta shiga rigar arziki wajen masu hannu da shuni na unguwar tasu ta barato sauran. Mutumin nan sai ya ƙeƙasa-ƙasa ya murtike fuska ya haɗa girar sama da ta ƙasa, ya haɗe rai kamar wanda aka aikawa da labarin mutuwa yace, “Yanzu fa kasuwa babu ciniki, zama kawai ake yi idan anje, babu harka saboda haka ayi hakuri sai dai nan gaba. ”
Inna ta fara masa magiya dan Allah ya taimaka koda rabin kudin ne ya basu a samu a ceto rayuwar bawan Allahn nan. Matarsa ma tasa baki da cewa, “Alhaji dan Allah ka duba wannan buƙata ka ceci lafiyar mutumin nan, ka duba zumunci.”
Tsawa ya daka mata tare da cewa, “Ke dakata min dan Allah, ku me yasa mata yawancinku baku da tunani ne ko kaɗan, ta yaya kasuwa ba'a samun ciniki kawai sai a ɗebi kudi aje wani waje can daban inda ba'a da tabbas ɗin za'a amfane su. Karki sake min irin wannan, idan ina magana da mutane kada ki ƙara samin baki.”
Tace,“Allah ya huci zuciyarka kayi hakuri ba zan sake ba.”
Nan Inna ta taso gwiwarta a doke ta kamar ansa sanda an doke mata su, tayi dana sani da nadamar zuwa wajensa.
Aysha ALIYU GARKUWA
Da ace Bakadanmiya zata samar da tsaro ga groups da mazau cikinta suke ta yadda mutun zai iya killace abunsa ta yadda wani bazai samu damar fitar mishi da abinsa ba, sai da yardarsa ko sahalewarsa, in bai yardaba kuma babu mai... moreAysha ALIYU GARKUWA
Da ace Bakadanmiya zata samar da tsaro ga groups da mazau cikinta suke ta yadda mutun zai iya killace abunsa ta yadda wani bazai samu damar fitar mishi da abinsa ba, sai da yardarsa ko sahalewarsa, in bai yardaba kuma babu mai fiddawa. To da lallai... moreDa ace Bakadanmiya zata samar da tsaro ga groups da mazau cikinta suke ta yadda mutun zai iya killace abunsa ta yadda...
Bakandamiya
Wannan karin bayani ya kara karfafa mana guiwa matuka. Da ikon Allah za mu ci gaba da tattauna wannan, kuma duk abubuwan da mu ke yi na kara inganta Bakandamiya za mu kara kaimi akai.\n\nAllah Ya yi mana jagora baki daya. Mun gode.
Halima K Mashi Abdullahi → Sababbin Litattafan Halima K/Mashi:
ILLAR FURUCI
NA: Halima Abdullahi k/... moreILLAR FURUCI
NA:... moreHalima K Mashi Abdullahi → Sababbin Litattafan Halima K/Mashi:
ILLAR FURUCI
NA: Halima Abdullahi k/... moreILLAR FURUCI
NA: Halima Abdullahi k/ mashi.
1
Direban Motar ya fito da sauri ya bude bayan motar ya na dan dukawa alamun girmamawa, tare da fadin “Hajiya a fito a sannu.”
Hajiyar ta fito ciki leshi na alfarma gami da mayafin da ya da ce da shi, ta gyara tsaiwar ta sannan ta kalli sauran masu fitowa daga cikin motor. Jummai yar aiki ce ɗauke da Afrah a kafaɗa. Hajiyar ta ce “Jummai bani Afra sai ki goyo Afrin tunda ta na bacci."
“Tanti Dije mu barta a motar mana tun da ta na bacci mun huta da surutun ta.” Baba Bello ya fada lokacin da ya bude gaban motar ya fito.
Tanti ta dube shi da sauri “Haba Baba Bello da kanka kake faɗin haka? Ko kai ma ka na taya Fatima faɗa da yan biyu na ne?” Ya ce “Kin san ra 'ayinmu ɗaya ko da yaushe, har na ƙara ƙosawa in ga Fatin Mamma na yi kewar Fatima.” Tanti ta ce “Ai yanzun nan za ka gan ta.” Suka jera direban ya na biye da su dauke da ƙatuwar darduma suka nutsa cikin makarantar Hassan gwarzo, wadda ke a garin kano dan ziyarar Fatima. Iyayen yara ko ina tare da 'ya'yansu guraren da aka ware dan ganawa. Fadila ce ta fara hango su, Tanti Dije ta zo da gudu ta na dariya “oyoyo Momi!” Da hannu ɗaya Tanti ta rungumo Fadila ta na fadin “Fadila oyoyo.” Fatima cikin jin dadi ta nuna musu wani guri “Momi ga wani guri nan zaku sa kafet ne?” Habu direba ya shimfiɗa darduma suka zauna. Fadila ta miƙawa Afrah hannu "Zo mu je mu kira Aunty Fatima ." Afrah ta sa ke lafewa. Tanti ta ce “Dama Afrin ce za ta je wannan sarkin tsoro ce."
Bello ya ce “Ni bari in zo mu je". Fadila ta ce “Ai baza a barka zuwa gurin mata ba, yanzu zan kirata ku dan yi hakuri.” Cikin sauri ta nufi kiran Fatima.
Abin da Baba Bello ya yi tsammani shi ne ya ga Fatima da gudu za ta fada jikin Momi, ya san ta na ganinsa za ta fa sa, cikin ɗoki da ihu za ta fado jikinsa ya lumshe ido tare da kallon in da ya ke zaton ta nan za ta ɓullo. Fadila maimakon Fatima sai ya hango wata siririyar yarinya su na tafe tare da Fadila, yarinyar ta na tafiya tamkar mai tausayin kasa, fuskar ta sanye da gilashi wanda bai sani ba na ado ne ko kuwa na ƙarawa ido ƙarfin gani ne?
Ya mai da kansa ga Tanti. Ya ce “Ba ta ga Fatimar ba ke nan?" Tanti ta kai duban ta ga su Fadila ta ce “Ga su nan tare.” Bello ya sake ware ido ya na kallon su cikin tsananin mamaki.
“Baa Bellona!”
Fatima ta fada tare da dafa kirji bayan ta tsaya turus. Ya mike tsaye tare da isa gaban ta ido ya zuba mata, kamar mai son ganin wani abu, cikin sauri ya waiwayo tare da duban Tanti yana faɗin “Hatta muryar ta ta canza me yasa?” Fatima ta yi ɗan murmushi “Ba Bello na sannu da zuwa, wacce tsaraba ka wo min?” Ya ce “Kin san dole in zo da Kwasam.” “Mamma kuma me ta ba da a kawo min?” Tanti ta katse su. “To ku zo nan mana ku yi maganar daga zaune.” Fadila ta ce “Bari in koma na bar su Aunty.” Tanti ta ce “Hajiyarku ta zo ne?” Fadila ta ce “A'a su Yayanmu ne da matarsa." ta ce “To ki gaida su.” Fadila ta ce "Ai za su zo nan ku gaisa kafin su tafi.”
ILLAR FURUCI
NA: Halima Abdullahi K/Mashi.
2
Tanti Ta ce “Ban san za su zo ba ai da mun taho tare.” Fadila ta ce “Ai su a Kaduna su ke.” Tanti ta ce “Allah sarki.” Fatima ta zauna kusa da Tanti ta na faɗin “Ina Daddy haka mu ka yi da shi fisabilillahi? Momy harfa alkawari ya yi min ba wani uzri!” Tanti ta kalli Habu direba wanda ke zaune can gefe, ta ce “Dan Allah Malam Habu a fito da kayan motar nan ku je da Baba Bello.” Fatima ta tura baki ta na cewa “haka Daddy ya min ko?” Tanti ta ce" "Ina waya ta in kira shi , ya fada miki da kansa taro ne na gaggawa ya taso ya na Lagos, ina ta kin zancan amma kin nace, Bello zo ka faɗa mata sakon shi.” Fatima ta matse kafaɗa “Ni ba zan ji ba ai mun yi da shi babu uzuri.” Bello ya ce “Shagwabar ce kawai ba ta can za ba.” Habu direba ya ce uwar ɗakina ina ta miko gaisuwa tun ɗazun.” Fatima Ta dube shi “Sorry Malam Habu an zo lafiya ban ji ba ne.” “Lafiya lau.” Ya amsa daidai lokacin da su ke tafiya dan kwaso kaya a mota.
Fatima ta Ballawa Afrah harara wadda ke kwance jikin Momi tare da faɗin “Ke ku ma kallon fa?” Momi ta ce “Zaki fara ko Fati! Ina laifin wanda ya zo ya duba ka?” Fatima ta ƙara sakar ma Afrah harara “Allah Momi haushi suke bani...” “Kar in kuma jin haka ko kunyar ido na ba kya ji?” Fatima ta kuma tura baki cikin shagwaba ta na hararar Afrin. Bello ya zauna bayan ya aje kwalin hannun sa, ya ciro kwasam daga wata jaka Fatima ta amsa da sauri ciki kaguwa ta bude ta kalli Bello
“Ba Bello na kana son ka birge ni, kuma ka birge ni.” Ta soma ƙwalƙwala kamar ruwa ga ma abocin kishi. Bello wanda zuciyarsa ke cike da tambayoyi ya dubi Tanti “Wai Tanti wannan gilashi na idon Fatin Mamma fa?” Ya yi tambayar tare da cire gilashi. Fatima ta saki robar madarar tare da sa hannu ta rufe fuskar ta, Bello ya mike cikin tsananin Faɗuwar gaba ya na faɗin me zan gani haka? Me ya samu idanun Fatima?”
Tanti ta yi saurin cewa “Me ka gani! Ya za ka cire mata gilashin ta Bello? Me ye hakan kuma?” Fatima ta soma zubo da hawaye Bello cikin sauri ya ce “Yi hakuri Fatima ban zo dan in ba ta miki farin cikin ki ba.” Tanti wadda ke harararsa ta ce na nawa kuma?” Ta janyo Fatima zuwa jikin ta
“Yi hakuri bari in kira maki Daddy amma sai kin yi shiru.” Fatima cikin shashshekar kuka ta ce “Shike nan Momy ni idona ya lalace ke nan?” Tanti hankalin ta ya kuma tashi, ta ce "In jiwa? Shi ma Bellon wasa ya ke miki fa ko Bello?” Bello cikin in ina ya ce “Ni ni babu komai fa ni kawai ban san ki da gilashin nan ba ne, amma ki yi haƙuri ga idonki babu komai.” Sai lokacin Jummai 'yar aiki ta yi magana " Haba Aunty Fati kin ga su Afrin sai kallon ki su ke yi, gashi kin ta da wannan ma da ga bacci.” Fatima ta kalle su cikin harara sun zuba mata ido fuskar su ɗauke da rashin jin dadin ganin ta ta na kuka. Tanti ta ɗauki robar kwasam din tare da “Faɗin sha kayan ki kin ji.” Fatima ta amsa ta riƙe a hannu, Tanti ta buɗe jakar ta ta ciro tissue ta soma share mata guraren da madarar ta ba ta a jikin ta. Bello cikin son ya kawar da damuwar ya ce “Bari in ɗauko miki tsarabar Mamma ta ce kici ki ba wanda ki ke so.” Ya kai ƙarshen maganar ya na kallon fuskarta. Ta ɗauki gilashin ta ta mai da sannan ta ce "Momi kira min Daddy." Tanti ta ɗauko wayarta yayin da shi kuma Bello ya ci gaba da rarrashi ta har ta saki.
Sun ci sun sha Tanti ta ba wa Fatima abubuwan da suka kawo mata har da ƙawayanta, musamman Fadila wadda kusan komai tare a ka kawo musu. An kira Daddy In da ya yi ta lallashin Fatima ta re da faɗin “Uwata kiyi hakuri lokaci na gaba zan zo ni kaɗai.” Cikin shagwaba Fatima ta ce “Jarabawa fa za mu fara, sai dai in hutu a ka yi mana ka zo ka tafi dani.” Ya ce dole na in zo Uwata, sannan in ki ka yi ƙoƙari zan kai ki duk kasar da kike son ki je hutu.” Fatima ta saki dariya ta ce...
Mu je zuwa
ILLAR FURUCI
NA: Halima Abdullahi K/Mashi.
3
“Ummara zan je Daddyna.” Ya ce “An gama Uwata.” Fatima sai murna ta manta da damuwa sai farin ciki.
Haka nan wan Fadila da matar sa su ka zo su ka gaida Tanti, sannan su ka yi godiya su ka tafi. Fadila da sauran kwayansu su ka yi ta ɗaukar hotuna da kyawawan yan biyu, waɗanda in su ka ga waya za a yi hoto shi kenan babu sauran kiwa. Fatima dai cewa ta yi ba za ta ɗauki hoto da su Afrah ta ce ba za ta yi da su ba, dan ita ba sa'ar su ba ce. Sun ɗauka da Ba Bello sosai, ta ce “Jummai ki fita sabgar yaran nan ki zo mu yi hoto.” Jummai Ta ce “Uwar ɗakina ina ni ina fita sabgar iyayan ɗakina? A yi hakuri mu ɗauki hoton nan da su ko sa ƙara mana kwar jini a idon duniya." Cikin zolaya Jummai ta ke maganar. Fatima ta ce “To ba zamu yi da ku ba, Momi ki zo mu dauka.” Momi ta ce nima dai in ba bu yarana zan iya hakura.” Fatima ta tura baki tare da faɗin “To karsu tsaya kusa da ni.” Jummai ta ce “Uwar ɗakina yi murmushi mana fushi ba ya yi miki kyau, sai ki ke kama da mutanan Hindiya, amma in kina murmushi tamkar larabawan Chaina ko na Dubai.” Dariya Fatima da su Fadila suka saki. Fatima ta ce “Wai ke Jummai me ya haɗa chaina da larabawa?” Jummai ma cikin dariya ta ce “To koma dai su wane ne tun da dai na saka ki dariya ai shi kenan ,yanzu sai mu sha hoto.” Wannan ya na da ga cikin dalilan da suke sa Tanti ke son Jummai mai aiki, domin mace ce mai barkwanci da raha, kuma ta kan shawo mata kan Fatima da yan biyu a duk lokacin da suka soma rigimarsu ta shagwaba. Amina Sidi Ali ƙawar su Fatima sai sha'awar su Afrah ta ke yi, ta na faɗin "Ina ma a ce waɗanna ƙannai na ne masu kyau haka? Fatima maimakon ki na ji da su." Ko ta kan Amina Fatima ba ta bi ba bare har ta ba ta amsa. Sai ma cewa ta ke. " Momi ina kika samin sauran Madara ta Kwasam da kilishina, dan babu wadda zan sammawa.” Tanti ta du beta " harda Fafilarki? " Ta ce "Har ita Ba Bellona da Mammata su ka kawo min fa, kuma Fadila ko kallon Ba Bello ba ta yi ba bare ta gaida shi ya zo tun daga Maraɗi dan kawai ya ganni.” Fadila ta ce "Lah! Ashe shi ne? To ai laifin ki ne da baki gabatar min da shi ba, sannu da zuwa Ba Bellonmu." Yadda ta yi abin sai a ka sa dariya har shi Ba Bello.
Amina Sidi Ali ta ce “Ina miki maganar yan biyu kin min banza." Fatima ta ce “Hakan zai sa ki fahimci ni ɗin ba na son zan can ne.” Amina zata yi magana Fadila ta riga ta da cewa “Ke Amina kin fi ye da mu.” Bello ya ce “Ke ce babbar ƙawarmu ko?” Fadila ta ce “Aminiya dai.” Tanti ta katse musu hirar da faɗin “Kun ji mafi sauki ka wai mu yi sallah, mu kama hanya.” Fatima ta ɓa ta fuska tare da faɗin “Haba Momy ku kwana mana, anjima in lokaci rufe ziyara ya cika ba sai ku je Tahir guest ba, tun da lokacin da zaku kawo ni, ai a Tahir din kuka yi ta kwana sai da a ka gama min komai.” Momy ta ce “Amma lokacin yan biyu suna jarirai ILLAR FURUCI!
NA: Halima Abdullahi K/Mashi.
4
“Daddy dai ba ya son tafiyar dare, na sani ko yanzu ba da yawun sa za a yi wannan tafiyar ba.” Bello cikin dariya ya ce “Fatin Mamma kin fi Tanti gaskiya, mu ne mi masauki kawai.” Tanti ta ce “Ai dole in hakura tun da kun fini baki.” Haka dai suka zauna har zuwa lokacin da aka tsara cewa lokacin ziyara ya ƙare, dan haka suka kama hanya suka shiga cikin gari, dan neman masauki kafin washegari su kama hanya.
A hanya ne Bello ke nuna wa Tanti mamakin shi na canzawar Fatima matuƙar canzawa.
Tanti ta ce “Ai kullum girma ta ke yi, kuma wannan makarantar ta su ƙwarai ta taimaka, karatun addini su ke yi sosai sauka da hadda kamar yaro ya na gaban iyayansa, ga tsafta kuma ladabi abin har mamaki ya ke ba ni, na sama ya na tausayin na kasa, shi kuma na kasa ya na girmama na sama, kuma abinci kamar na gida. Kifi, nama, kayan marmari, irin su lemo da ayaba, kankana, kai hatta da agwaluma Fatima ta ce min in lokacin ta ya yi ana kawo musu.”
Bello ya ce “Gaskiya makarantar ta yi, su na da tsari da kula ga tarbiyya, amma duk da haka na yi matuƙar mamakin canzawar Fatin Mamma, to kuma me ya samu idanun ta?” Tanti ta yi saurin duban sa ta ce “Bello dan Allah ka dai na yin zancan nan musamman a gaban Fatima.” Haka Bello ya sake yin shiru zuciyarsa cike da tambayoyi, amma babu wanda zai bashi amsa.
****** ***** ******
KADUNA
Cikin sauri yarinyar ta fito daga wanka, daure da tawul dogon gashinta nade a cikin karamin tawul, da rawa gami da waka ta fito daga banɗakin, gaban madubi ta zame tare kallon kanta, ta na ci gaba da rawar, wakar ta na tashi daga cikin wayarta, wadda ke aje a kan gado ta ke bi.
Cikin yanayin rawa da waka ta yi duk shirinta, tun daga shafar mai har zuwa saka kayanta matsatstsun riga da wando ta saka tare da daure gashinta a tsakiyar kai ta kuma fesa turaruka, ta tsugunna ta na daura takalma masu dogayen igiyoyi har kwaurinta, sannan ta dauki ƙaramin mayafi ta yane kanta, tare da kallon madubi sannan ta ware manyan idanunta ta kalli suffarta, daɗi ya rufe ta ta sumbaci yatsunta ta hura a madubin tare da faɗin, “Gaskiya na yi kyau! Ina da kyau! Allah na gode maka ina son kai na.” Ta faɗa cikin murna da farin ciki, tana ɗaukar wayarta ta na soka earpiece a kunnuwan ta, sai ga kira ya shigo cikin sauri ta ɗaga ta na “Faɗin oga BY gani nan fitowa ."
Daga ɗayan ɓangaren ya ce “Yawwa dan Allah ki yi sauri yau studio ɗin akwai mutane da yawa.”
“Toh! Gani nan zuwa.” Ta dire maganar, tana nufa kicin in da mahaifiyarta ke shirin dora girkin dare. “Mama na tafi makaranta sai na dawo.” Ta faɗa daidai lokacin da ta ke gyara yar igiyar jakarta, da akewa lakabi da wankan gefe.
Tun daga sama Uwar take kallon ta har kasa, ta ke fuskarta ta canza. "Amma na hanaki saka kananan kayan irin haka ki fita ko da kofar gidan ko?” Ɓata rai ta yi tare da turo baki ta ce “Haba Mama yanzu ina laifin kayan nan? Kin gani fa ko ina nawa a rufe ya ke.” “Wuce ki je ki saka hijabi ki zo in gani.” Uwar ta faɗa a fusace.
Ciki ta koma ta na ƙunƙunai “Ita Mama ba ta ganewa ta ya ya mutum zai zama tauraro, in ba ya na shigar suwaga irin haka ba?” Ta sako katon Hijabi sannan ta koma cikin kicin din tana cewa “Gashi na saka.” Murmushi ta yi tare da kallon ta ta ce “Ko ke fa Mamana! Wannan ita ce shigar mutunci da addininmu ya amince, waccan shigar da ki ka yi irin ta marasa tarbiyya ce.” Ƙare tamke fuska ta yi, cike da jin haushi hatta maganar da ta yi ma ciki-ciki ta yi shi “To ni na wuce.”
“ Allah ya tsare Mamana, ki kula da kanki ki nutsu ki fahimci karatunki.” Da gudu ta fita ta na fadin “To Mama.” Sakamakon rurin da wayarta ke yi ta san oga BY ne ta daga ta na faɗin “Gani a bakin Gate.” Da gudu ta isa tare da bude gaban motar, cikin azama ta fada tare da rufe ƙofar, ta dube shi daidai lokacin da ya figi motar “Yi hakuri babban Yaya na bar ka tsaye.” Ya ce "Haba babu komai ina son dai mu yi beating tima ne, dan sun fada min akwai mutane kin gane ai?” Ya yi maganar cikin irin salonsu na matasa, yan wanka kuma sabbin mawakan hip hop. Ta cire hijabin jikinta ta wurga a kujerar bayan motar tare da faɗin “Mama ta matsa.” Ya ce “Sunan hijabin kenan?” Suka tuntsire da dariya a tare. Ta ce “Yanzu dai na raɗa masa.” Ya ce “To ni dai na yi mamaki a ce ke ce cikin wannan hijabin har ƙasa, farko ma da kika shigo na so in tsorata.” Suka ƙara tintsirewa da dariya, suka saki sauti suna bi su na rausaya.
Kai tsaye daga Unguwar Malali suka nufi Mogadishu, in da studio da za su buga wakar yake maimakon makarantar koyon na'ura mai kwakwalwa...”
Zan ci gaba ranar Asabar idan mai kowa da komai ya nuna mana, ku bi labarin a sannu dan yanzu muka soma.
Taku har kullum HALIMA K/MASHI.
Na gode.... less
Halima K Mashi Abdullahi → Sababbin Litattafan Halima K/Mashi:
Illar Furuci
Na Halima Abdullahi... moreHalima K Mashi Abdullahi → Sababbin Litattafan Halima K/Mashi:
Illar Furuci
Na Halima Abdullahi k/Mashi
8
Shawara mafi sauki Ashir ka kulle bakinka har zuwa ta kammala sakandire dan muga abin ko kuruciya... moreIllar Furuci
Na Halima Abdullahi k/Mashi
8
Shawara mafi sauki Ashir ka kulle bakinka har zuwa ta kammala sakandire dan muga abin ko kuruciya ce."
Ashir ya maida bayansa jikin kujera ya tare da lumshe idanu ya soma tuno gargadin da Fatima ta zabga masa a wani hutun karshen mako da ta je yi a gidansu. Ya tuna yadda ya zauna a bakin gadon mahaifiyarsa lokacin Fatima ta idar da salla ta dago kai ta kalle shi "Ya Ashir ka dawo kenan? Cikin sassanyar muryarta da ya ke matukar so." Na dawo Fatima kin san duk inda na je ba zan iya zama ba matsawar kina cikin gidan nan." Take ya ga ta canza fuska ta kuma gyara hijabinta ya kara rufe jikinta. Bai daddara ba ya sake fadin "Fatima bansan menene dalilin da ya sa zuciyata take damuwa da lamarinki har na ke kasancewa da yawan tunaninki ba." Zaraf Fatima ta mike a fusace cikin muryar nan ta ta mara kara ta ce "Yakama ka gargadi zuciyar nan taka tayi kokari ta samu nutsuwa kafin ta jefa rayuwarka cikin hadari da nadama, shawara ta biyu zai fi kyau ka rike girmanka ni kuma na baka girman dan kar a samu Marsala." Dogon tsakin da tayi a lokacin sai ya ji tamkar yanzu ta jashi har ya firgita ya tashi zauna ya kalli Tanti wadda ta kalleshi cikin sauri ganin ya zabura. Ta ce "Ya dai Ashir?" Ya ja dogon numfashi. Momi dan Allah in lokacin ya yi ke ce zaki tsaya min na dogara ga Allah na dogara gare ki." Maimakon amsa sai Tanti ta ce "Ka amshi wayarka fa domin su Afra fasa waya su ke yi." Ya lumshe ido cikin damuwa bai damu su fasa wayar ba duk da tsadarta shima sai ya ce "Mami ba ki yi magana ba." Ashir ka rike Allah ka dogara dashi ka kuma nemi zabinshi, shine kadai zai iya yi maka komai ni babu abinda zan iya, shawara ta karshe ka dai na saka abu a cikin zuciyar ka yadda ko ka rasa shi damuwa za ta zo maka da sauri." Zai yi magana sallamar maigida ta dakatar da shi dole ya canza maganar zuwa mika gaisuwa. Daddy ya tambayi yan gidan Ashir ya ce kowa kafiya. Dole ya maida hankalinsa ga 'yan biyu ya na ta musu hotuna kala kala. Mami ta mike tare da fadin "Ashir muje tebur abinci gashi can." Shima ya mike "Mami tafiya zanyi nima cikina a cike yake." Ta ce "Shike nan ka gaida min da Maminka ka ce wai jiya bata ga kira na bane?" Ya ce " tom zan fada mata."
'Yan biyu suka sa daru wai sai ya basu waya ko kuma ya ci gaba da daukarsu hoto sai da kyar akayi musu dabara ya tafi. Daddy ya na cin abinci ya ce "Hadiza ina mamakin yadda yaran nan suka san waya suka kuma saba da ita." Tanti ta ce "Kasan tun suna kanana kowa ya zo sai ya dauke su hoto shiyasa idon su ya bude da hoto kaga kuwa yadda horunansu ke yawo a yanar gizo?" Ya ce "Kaha kike fada min zan dai sai musu wayoyin nan su dai na kuka a kan na mutane." Tanti ta ce "Kawai ka bari su dan kara girma nan da shekara mai zuwa sai ka saya musu." Ya ce to Allah ya kaimu." ****** *****
Dogo ne sankacece mai cikar zati yana da kyau bayyananne duk iya kallonka da wahala ka gano
Illar Furuci
Na Halima Abdullahi k / mashi.
9
muninsa, haka farar fatarsa zai wahala ka gano kabilarsa a tsakanin larabawan Sudan da Indiyawan kudanci, bakin gashin da ya taso tun daga kansa zuwa gefen fuskarsa da kasan hancinsa har kan habarsa su ne suka sa wasu ke masa kallon Balaraben Madina mai cike da nutsuwa. Yadda ya ke tafiya cike izza da kuzari ba sai ka wahala ba za ka gano cewa shi din lafiyayye ne, amma a fuska ba za ka tantancen shi a cikin hudun nan ba, wato miskili mafadaci maijinkai ko mai shiru shiru ba. Shine wanda zai ja jirgin daga kasar Najeria zuwa kasar Saudi Arabia Muhammad AA shine rubuce a jikin yar falmaran din da ke saman kayan da ke jikinsa wandon Jeans da riga mai dogon hannu. Shi din ba bako bane a gurin mamallaka jiragen sufuri, hazikin matukin manyan Jirage ne shi mai zaman kansa ne kamfanoni suna daukarsa ya na tuka musu jirgi. Bisa ga dukkan alamu ya na matukar son aikinsa, haka masu jirage su na jin dadin aiki da shi in aka yi la akari da yadda kullum ya na cikin aiki tare da yiwa wasu alkawura. Dan haka ya ware lokuta uku a rayuwa wadanda ba ya wasa da su. Na farko lokaci sallarsa sai lokacin cin abinci da lokacin bacci. Banda wannan duk sauran lokutansa ya zuba su ne a cikin aikinsa. Wannan ya sa ya ke da mahaukatan kudi a asusun sa na banki, dan haka matashin ya ke jin cewa babu wata rana da za ta zo ya ji aikin ya gundire shi.
Karfe sha biyu ya gani a jikin agogon hannunsa, ya sa makulli ya bude dakin da ke cikin shararren hotel din da ke birnin na Makka. Wanka yayi tare da alwala ya saka fara kar din jallabiyya da hula samfurin tashi ka fiye naci, ya fita zuwa harami wanda ba shi da nisa da hotel din. Bai dawo ba sai lokacin da zaiyi sahur ya koma sashen abinci a cikin hotel din kasancewar duk nau in abincin da kake bukata za ka sameshi a wannan hotel din na kasashe da ban da ban. Ya zabi abinda ya ke so aka kawo masa ya zauna, ya na kurbar shayi ya na tura wani sako wanda ya ya maida shi wajibi a kansa ya ware wasu kebantattun lokuta dan aika su. Da ya kammala haramin ya koma, bai dawo ba sai karfe shidan safe inda ya koma ya bude dakin na sa ya kwanta don ya danyi bacci, a kwai jirgin da zai ja zuwa Etopia da ga can zai dauka zuwa Lagos ta Nigeria.
Maimakon bacci sai ya dakko wayar sa ya soma hawa yanar gizo,Instagram ya shiga dan ya fison manhajar, ya juya kwanciyar zuwa rigingine dan ya ji dadin nutsawa cikin manhajar. Duk da shi bai damu da yin posting ba yana son kallon hotuna tare da jin abinda duniya ke ciki ta wannan fanin.
Idanunsa su ka tsaya kyar akan wani hoto na yaran yan biyu masu matukar birgeshi. Musamman ya ke bin account din mai dauke da suna Ashir KTK dan kawai ya kalli yan biyun masu tsananin kama da juna ga kyau, Mamakinsa shi ne yadda yaran su ka iya salo salo na kalolin daukar hoto ya na kaunar yaran ya aje hotuna masu yawa na yaran wanda bai san iyakaci ba, ya sumbaci hoton cikin kauna. Ya aje wayar ya lumshe ido cikin wani yanayi mai wuyar fassara. Gabobin yatsunsa ya ke... less
Halima K Mashi Abdullahi → Sababbin Litattafan Halima K/Mashi:
Salam
Na zo muku da wata yar shawara ku kasance kuna bibiyar labarin nan na Illar Furuci tun daga farko har karshe zan yi tambayoyi bayan na mamma wanda in ka...
Halima K Mashi Abdullahi → Sababbin Litattafan Halima K/Mashi:
Illar Furuci
Na Halima... moreIllar... moreHalima K Mashi Abdullahi → Sababbin Litattafan Halima K/Mashi:
Illar Furuci
Na Halima... moreIllar Furuci
Na Halima k/mashi
5
Cikin Farin ciki Yarinyar ta sauka a kofar gidan su su ka yi sallama da BY, lokaci kannanta sun dawo da ga masallaci sallar isha i. Faruk Ya ce "Yaya Fati ashe bakya zuwa makaranta, to Baba ya na ciki ya na jiranki." duk da cewa gabanta ya yi mummunar faduwa amma sai ta da ke, ta zabga masa harara tare da fadin "Zan mare ka Faruk! Ni tsararka ce?" Ya sa yatsunsa guda biyu ya kama lebunansa. Ta ja tsaki sannan ta nufi ciki. Ya bi ta a baya ya na fadi a hankali "Wata za ta sha fada." Dakin Mama ta nufa kai tsaye, ta samu Mama ta na salla dan haka ita ma sai ta nufi dakinsu dan ta yi salla. A dakinsu ta samu Nafisa ta na salla, sai da ta sha rawarta sannan ta zo za ta wuce ta gaban Nafisar, cikin sauri ta yi alamar karta keta mata gaban salla. Ta ce "Sorry sannan ta koma ta bayanta ta fada bandaki dan dauro alwala. Ta idar da salla sannan ta sake nufar dakin mama dan tabbatar da abinda Faruk ya fada mata. Sam ba ta son duk wani abu da zai bata ran Mama. Tana fitowa bakin kofa mama ta na isowa, dan haka su ka yi kicibis a bakin kofa. Gaban Fati ya fadi. Ta ce " Mama sannu da gida, na dawo ki na salla ne. Mama ta ce "Muje ciki." Ta kalli Nafisa wadda ke karatun azkar dinta na yamma. Ta ce " Ki je ki zuba wa su Faruk abinci kema ki sa, zanyi magana da yayarku. Nafisa ta mike a hankali ta fita. Mama ta kalli Fatima. " Kinsa bana son karya ko kame kame ?" Fati ta ce " Na sani Mama." Ta ce " To fada min gaskiya ina ki ke zuwa da sunan makaranta?" Fati ta zaro ido "Ina kuwa za ni Mama." Mama ta daga murya "Amsa za ki ba ni Fatima ba ki jeho min wata tambayar ba." Cikin Fati ya kada domin in ba yau ba Mama ba ta taba kama sunanta tsirara haka ba. Duk da ba ta son yiwa Mama karya dole ne ta yi ko don ta baiwa burinta kariya na zama shahararriya Domin tasan yanzu mama za ta ka tse ma ta burinta hakuri kawai Mama za ta yi. " Bangane hakuri zanyi ba." Fati ta zaro ido ko dai ba a zuci take nazarin ba. Mama ta ji dukkan tunaninta ke nan! Inko haka ne lamari ya baci. Mama ta tashi ta dawo kusa da Fati ta zauna ta tausasa murya tare da dafa mata kafada. "Uwata na shede ki bakya karya ki fada min ko kin fara bin wani ne?" Da sauri ta dubi mahaifiyar tare da fadin Allah ya tsare ni Mama karki min wannnan fatan." Mama ta ce to " 'Ya ta fada min ina ki ke zuwa?" Fatima ta sunkuyar da kai "Makaranta na ke zuwa Mama, waye ya ce ba na zuwa?" Mama ta ce "Babanku ya je har makarantar fa." Fatima ta ce "Mama kin san Baba fa kullum ya na neman laifina ne, ga su Nafisa nan ba ya cewa ga abinda sukayi, ni bànsan dalili ba Baba ba ya so na." Uwar ta kama hannun yar "Haba 'ya ta, kin taba ganin uban da baya son 'yar sa? Ke ce kin cika rawar kai dole ya sa ido sosai a kanki, kuma na hanaki yin zantukan rashin ladabi ga mahaifinki." Fati ta ce "To kiyi hakuri Mama gaskiyar magana ina zuwa makaranta." Mama ta mike "Shike nan amma ki kula sosai kuma ki dage." Fati ta shiga
Illar Furuci
Na Halima Abdullahi k / mashi
6
rawa bayan fitar Mama bata da matsala in dai Mama ba ta fushi da ita, sai dai kuma ta san dole ne wata rana asiri ya tonu, dan gaskiya duk rintsi sai ta yi halinta domin karya fure ta ke amma ba ta 'ya'ya.
Uban ya jima tsaye ya na kallon yadda Fati ke rawa a kan gado tare da rera wakar da su ka yi dazu. "Subahanallahi! Fatima ta tsaya can cikin fargaba. Ya ce " Lallai kullum shedancin ki ga ba ya ke yi, to ko koyon rawar ki ke zuwa ne ki ke karya cewa kina zuwa makarantar koyon computer? " Ta soma kir kirar kukan karya. "Can ni ke zuwa Baba kila ba gurin kaje ba." Ya shiga dakin a fusace ya yin da ta nufi bandaki da gudu. Ya ce " Inje in yi miki rijista da hannu na amma ki na fada min cewa ko ba can na je ba! Nufin ki gurin ya ma ba ce min kenan? Sun fada min cewa tun da aka sa ki a makarantar ba ki yi zuwa ya kai biyar ba. Ta ce "Karya su ke min gobe mu je tare tunda karya za su yi min." Ya ce "Ke za ki fada min a bin da ya kamata inyi? Uwarki ta goye miki baya dole ki ce kina zuwa abinda ki ke so shi ki ke yi, dan haka ba zan dauki rashin mutunci da zub da mutunci a idon duniya ba. Ya juya ya fita ya na me ci gaba da fada.
Da safe duk su ka fito cikin kayan makarantar boko na Kaduna Capital school Fatima ce babbarsu ta na aji biyu na babbar sakandire Nafisa ta na aji uku na karamar sàkandire, Faruk ya na aji daya, sukuwa Amir da Kabir duk yan primary ne. Kabir ya shige gaban mota shi da Amir. Nafisa ta ce " Baba ba ka bamu rasit din da ka biya mana kudi ba, yau za a iya ha na mu shiga aji. " Ya ce "Ai kuwa gara da ki ka tuna min Faruk yi gudu ka ce Mamanku ta duba kan durowar gefen gadona ta dakko maka. Ya tafi da gudu ya yin da shi kuma Baban ya dubi Fatima zan dawo daukarku zanje ajujuwanku da kai na kuma ni zan kai ki computer school din za ki ga ne kurenki. Fatima ta zaro ido ta tuna in har Baba zai je ajinsu yanzu to kuwa akwai matsala. Domin ta gudu a ajin kusan so hudu a satin nan su na zuwa gurin kallon daukar wasu sabbin wakoki da za a fitar da video din su domin ta na son ta samu kwarewa so sai, in sun tashi daukar na su ta riga ta gogu. Nafisa ta yi murmushi "Baba zan ji dadi in ka je da kanka ka kai rasit din ba sai munbi layi ba, in iyayen yara su ka zo anfi kula su. " Faruk ya ce " E mana." Fatima dai ta kasa magana sai zaro ido take cikin far gabar abinda zai je ya dawo.
Abuja
Tanti Dije ta na fitowa wanka cikin sauri ta shirya ba ta son mijinta ya karaso ba tare da ta shirya ba, domin Habu direba ya tafi dakko shi da ga filin jirgin sama, ya dawo da ga Lagos. Ta na fesa turare ta jiyo muryarsa ya na fadin "Hadiza!" Cikin sauri ta nufi dakinsa Indi ta jiyo muryarsa da ga can. Ta shiga ta samu ya na kokarin cire malun-malun , cikin sauri ta nufe shi ta na fadin "Sannu da zuwa yallabai sannunka da hanya." Ya shafi kumatuta "Sannu da wanka Hadiza kina ta kamshi." Ta kama hannunshi "Bari in ta ya ka cire kayan domin na san kaima wankan ka ke muradin yi ko?" Ya ce " "Ba ni ne zanyi ba, matata ce za ta yi min don na gaji ." Ta ce "Aiki na ne mijina muje in maka yanzu." Bayan ta gama masa ta baro shi ya na alwalla domin dab a ke da kiran magariba, ta kalli ledojin da ke zube a kan gado duk kayan tarkace ne na tsarabar yaran, kayan zaki da kayan wasa. Ta yi murmushi " Oga kenan shi dai duk inda ya je sai ya yo wa yan biyu tsaraba." Ta nufi gurin da ya ke aje jallabiyunsa ta ciro masa daya mai gajeran hannu da gajeran wando ta feshe su da turaruka masu kamshi ta aje a kan durowar gefen gadon wadda ke daf da kofar bandakin, ta ciro Laptop din sa daga cikin jaka ta aje gurin da ya yi mata mazauni. Ya fito ya na saka kayan gami da tambayar "Ina yan biyu na?" Ta ce "Za ka gaji da su yau domin sun sha baccin rana."
Illar Furuci
Na Halima Abdullahi / mashi.
7
Ta zauna a bakin gadon tare da janyo ledojin "Kai kam ko ina kaje sai kayi tsaraba?" Shima ya zauna. "Wannan tsarabar da ga Hajiya Maimuna taki ta ke, ta ce a kaiwa yan biyunta." Ta daga ta na fadin lallai Hajjaju, ta gidan ka bi ke nan?" "Ya ce " Ba na fada miki na je duba Hajiyar Alhaji Kabiru da jiki anyi mata aiki a ido ba, kinsan ta na gidan sa gurin Hajiya Maimuna." Ta ce "Ai ka kyauta dubi lokacin da Mamma tayi ciwon nan shi ne har Maradi ya je duba jikinta." Ya ce "Alhaji Kabiru ya wuce aboki sai dai dan uwa na jiki." Ta ce "Tabbas haka ne tamkar dai ni da Hajiya Maimuna." Ya mike tare da fadin bari in dawo daga masallaci insha labarin Uwata Fatima na san ta sha fushi banje ba." Ta saki dariya tare da fadin "Kai Uwarnan ta ka da fitina ta ke, gashi Bello ya so ya tsokalo mana sama da tsinke ya cire mata gilashi ya na neman ba a sin yaya a ka yi idanunta su ka koma haka!" Ya rike baki "Tofa!" Ta bi bayansa ta na bashi labarin har su ka sauka kasa, ta raka shi har kofar falon kasa ya nufi masallaci.
Da kanta Tanti Dije ta ke jera kayan abincin Jummai me aiki ta na miko mata daga katon tiren da ta jero su. Duk da shekaru sun ja sam Tanti ba ta wasa da kula da mijinta wan da ta ke kallo kamar jiya aka daura musu aure, burinta guri ya yi tsaf kafin ya dawo salla dan in ya fita magriba sai bayan isha i ya ke dawowa domin su na daukar karatu a tsakanin magriba da isha 'i a gurin limamin masallacin wanda ya kasance makocinsu ne, duk da ba su da yawa bawan Allahn ya jure gurin samun ladansu, haka suma sun jure koyo matsawar su na gari.
Aka kwankwasa kofar falon ta dubi Jummai wadda ta kawo su Afra da Afrin sun sha gayu cikin wasu tsadaddun riguna da takalma sai ka ce za su je gidan shi a ni. Ta ce "Ki duba ana kwankwasa kofa."
Ya shigo sanye cikin kananan kaya ya yi kyau dan matashi Ashir kenan dan wan Tanti Dije ne. Ta kalle shi da fara a "Ashir daga ina haka kamar an jeho ka?" Ya nufi kujera daidai lokacin da su Afrin su ka ruga su ka kama kafafunsa su na fadin "Oyoyo Yaya!" Ya dora su a hannuwa kujerar da ya zauna gefe da gefe ya na fadin "Daga gida nike Mami ina yini." Nan suka gaisa, ya mikawa yanbiyu wayarsa da su ke ta kokarin amsa da ga hannusa, sannan ya soma antayo korafinsa ga kanwar mahaifin nasa. "Mami ba dole inzo a wannan lokacin ba, don Allah mami banji dadin yadda kuka min ba." Ta tattara hankalinta gareshi. "Me a kayi ne dana fadamin inji." "Kuka tafi ziyarar Fatima bayan kin san na ce zanje." Ta yi dan tsaki gami da sakin dariya. "Har ka fadarmin da gaba, na zaci wani abu ne daban da na ga duk ka marairaice." Ya ce "Mami kin san dai ina son Fatima sosai zan iya rasa rai na a kanta bana son a samu matsala ne Mami dan Allah." Ta danne rashin jin dadin kalaman nasa ta yi dan yake. "Ka gane ko Ashir ka bi a hankali na fada maka ka saurara da wannan zancan domin fa sanin kankane Fatima ta tsani jinsin maza musamman wanda zai kusanto ta, ina son ka sani Fatima ta na da mabanbancin ra ayi da sauran mata in har ka yi kuskuran bayyana manufarka har ta gane to babu shakka za ta yi maka tsana mai... less
Halima K Mashi Abdullahi → Sababbin Litattafan Halima K/Mashi:
Illar Furuci
10 Kaduna
... moreHalima K Mashi Abdullahi → Sababbin Litattafan Halima K/Mashi:
Illar Furuci
10 Kaduna
Fatima kwance a falo ta na kallon tashar wakokin turanci, har kullum ta na son ta kara gogewa a fannin rawa domin nan gaba kadan ta na son ta fara wakarta ta kanta, wannan dalilin yasa ta... moreIllar Furuci
10 Kaduna
Fatima kwance a falo ta na kallon tashar wakokin turanci, har kullum ta na son ta kara gogewa a fannin rawa domin nan gaba kadan ta na son ta fara wakarta ta kanta, wannan dalilin yasa ta matsawa kanta a duk lokutan da take gida kuma Mama bata nan, ta na amfani da wannan damar ta kalli tashar rawa ko da kannanta za suyi zuciya su bar mata falon. Kamar yau ma suna kallon wani cartoon wai shi Oscar osis sai, kawai ta zo ta canza tasha. Nafisa Ta ce "Haba Yaya Fati dan Allah wannan fa ba adalci ba ne fa." Fati ta ce " Ku baza ku gane ba, kunfi son kallo mara amfani gara ku bari in koyi abinda ya kamata harka ce ta girma, kuma TV dai sai an saka shi a kowane daki a gidan nan." Faruk ya tafi da dan kukansa dakin Mama ya nufa, Nafisa ta ce "garama ka hakura domin ba lallai Mama ta amshi uzrinmu akan Yaya Fati." Haka kuwa ya na cewa Mama kinga Yaya Fati muna kallon Oscar ta zo ta can... "Ka gama Homework din ka ne?" Mama ta katse shi da tambaya. Ya ce "Ai ana gamawa zan yi." ta ce to, je kayi."
Wayar Fati ta yi ringing ta duba da sauri kawarta Sumayya ce.Ta daga tare da fadin "Shegiya Sumy ina kika shige kwana biyu?" Daga can Sumy ta amsa da cewa "Teema Celebrity ina kika shiga ne?" Fati ta ce " kin san yanzu na ke tunanin kiranki in fada miki munfa buga wakar nan, kuma zamuyi Videos kwanannan, an kusa haska ni." Sumy ta saki shewar murna sannan ta ce " Ke Teema kira na yi in fada miki gidan hoton nan na kan titin Isa kaita sun manna hotunan nan da mukaje muka dauka, amma na ki kadai suka manna a bangon gidan hoton ta kan titi." Ihun murna ta saki wanda ya sa Mama fitowa da sauri gami da rawar jiki ta na zaton ko wani abinne ya samu Fatin. Sai ta ji ta na fadin "Dole inzo ki raka ni in gani, gaskiya sun min komai wallahi na ji dadi sosai, kin ga nasara ko Sumy ina ji a jikina zan cimma burina zan zama tauraruwa." Juyin da ta yi cikin rawa sai suka hada ido da Mama, take ta ji gabanta ya fadi. Mama fuskar ta babu fara a ta ce "Menene aka miki da ki ke fadin za ki je ki gani?" Cikin in ina ta ce "Wannan ce fa da mukayi test ita ce na cinye Sumayya ke fada min ta amso min ne shine zan je in gani." Mama ta ce "Ban gamsu ba domin Sumayya yanzu ba a makarantarku ta ke ba, F.G.C Malali ta ke sannan ba Islamiyyarku da ya ba." Fati cikin fargaba ta ce Mama a Computer fa ni ke magana kinsan ta shiga makarantar ba na fada miki ba tun kwanan baya." Yadda Fatin ke magana ci ke da karfin gwiwa, sai uwar ta shiga waswasi kamar sunyi zancan. Ganin haka sai Fati ta samu kwarin gwiwar ci gaba da fadin. Test mukayi to shine ta ke min albishir." Mama ta ce Allah ya ba da sa a ni danaji kina fadin burinki har na tsorata domin na jima da sanin ki na son zama shahararriya amma ban san a wane fanni zaki zama ba. Na ce likita ko lauya ko malama duk kin ce ba daya. Ta ce "A computer zan zama." Mama ta ce "Allah ya taimaka, to kannanki kuma da kika canza musu tasha ki ka sa arnan nan kina kallo fa?" Ta ce "Na yi musu alkawarin TV kowa da tasa." Tsaki Mama ta ja sannan ta dauki remote ta canza zuwa sunna tv sannan ta ce ban
Halima k/mashi
11
da abin ki Mamana kina dalibar ilmi me zai hada ki da kallon rawa da waka?" Ki ke yin abin da kannanki za su koya. Fati ta ce "To Mama ni ce Uwarsu wata rana tunda ni ce babbar yaya.ko" Mama ta yi murmushi ta re da fadin "Insha Allahu" ta koma dakinta."
Washegari Fati ta nemin iznin Mama ta nufi gidan su Sumayya, da ke Unguwar dosa dan suje gurin mai hoto don ta ga hotunanta. Suna isa masu gidan hoto su ka amshi Fati cikin fara 'a da murna domin hotunan ta sun kawo musu mutane kowa ya zo kalolin salonta su ke yi. Sun bukaci in za ta yarda su kuma daukarta wasu kaloli amma da kaya irin na al 'adun yarukan kasar nan irin na Hausa Igbo Yoruba da sauran su. Take ta amince musamman da mamallakin shagon ya fada mata cewa zata iya samun talloli da ga kamfanoni in suka ga hotunan.Dama da kayansu nan suka nemi mai kwalliya, cikin sa'a ta na kusa, dan haka tazo ta shiga zayyanawa Fati kwalliya ciki gwanin ta. Haka duk shigar da ta yi sai ayi mata ado irin na kabilar sai kaga ta tashi tamkar su.An daukii hotuna sosai kuma sun amshi lambarta za su tura mata a wayar ta dan ta samu damar sawa a shafukanta sun ce za ta iya samu tallar ko da ga bangaren ta ne wa su za su tuntube ta. Sai kusan magariba sannan su ka bar shagon Sumayya ta na ta mitar za ayi mata fada. Suna fita Sumayya ta hauta da fada, ta ce amma gaskiya Teema ke banza ce, har yaushe zaki bari suyi miki hotuna ba tare da sun biya ki ba!" Ta zungure mata kai tare da ci gaba da fadin "Kudi fa za su nema da ke!" Fati ta yi shewa sannan ta ce " Nima suna zan samu ta dalilinsu, ki gane mana kawata nasara ke bina taurarona ya soma haske in ya fara kyalli, wayyo Allahna Sumayya nan gaba kadan cikin alfahari za ki ke fadin Teema Celebrity kawata ce lokacin ma wasu za su ce karya ki ke yi, amma in lokacin ya yi ki kira ni zan fidda ke in ce sa a hand's free in fada musu Sumy aminiyata ce." Tsaki Sumayya ta ja, "Ina tausayin ki duk ranar da Mama ta san abinda kike ciki." Fati ta gatsina fuska. "Na zaci zaki ce ya zanyi yanzu na yi dare, domin nan gaba din ai ba ta zo ba tukunna ko?" Sumayya ta ce ni dai ki raka ni gida ki fiddani a gurin Mamanmu." Fati ta ce nan fa daya, kowa tashi ta fishheshi nima fadan zanci, amma ga shawara, kawai ki ce bani da lafiya nima zance baki da lafiya." Sumayya ta ce "Ba zancan karya hoto na raka ki haka zan fada kema ya rage naki ko ki fadi gaskiya ko ki yi karya ita fure ta ke ba ta 'ya'ya." Haka dai suka rabu su na yiwa juna tsiya.
Fati ta na isa gida ta shirga wa mahaifiyarta... less
lubabatu lawal
Masha Allah Aunty halima novel fa yadauko dad I\uD83E\uDD11\uD83E\uDD11\uD83E\uDD11\uD83D\uDE0D\uD83D\uDC83\uD83D\uDC83\uD83D\uDC83\uD83D\uDC83\uD83D\uDC83\uD83D\uDC83\uD83D\uDC83\uD83D\uDC83
Halima K Mashi Abdullahi → Sababbin Litattafan Halima K/Mashi:
IILLAR... moreIILLAR... moreHalima K Mashi Abdullahi → Sababbin Litattafan Halima K/Mashi:
IILLAR... moreIILLAR FURUCI.
Na
Halima Abdullahi k/ mashi.
13
Takwas na dare Fatima tana ta faman daukar hoto a waya tana editing tana yin posting a shafukanta.
Nafisa ta leka ta kalli fuskar wayar, sannan ta dubi Fati ta ce "Yaya Fati malam ya yi mana nasiha akan daukar irin wadannan hotunan a gantsare ba bu kyau, kuma ya ce duk yarinyar da.....
"Yimin shiru mayyar sa ido kawai, ni tauraruwa ce, mutane suna son kallon hotunan taurari kuma suna kwaikwayon irin salon daukar hotonmu da irin sa kayanmu."
Nafisa ta sake duban ta cikin yar dariyar zolaya ta ce "Su tauraruwa manyan gari, to Film ki ke yi ko waka?"
Fati ta ce. "Ina ruwanki ne wai!" Nafisa ta ce " babu ruwa na."
Faruk ya shigo da gudu. "Mama tana kiran kowa a zo a ci abinci.'
Nafisa ta dube shi. " Faruk so nawa zan fada maka, ka daina shigowa da gudu babu sallama ne? Oya koma ka yi sallama tukunna."
Ya koma ranshi a bace sannan ya sake yin sallama. Nafisa ta amsa sannan ta ce "Gamu nan zuwa yanzu."
Bayan fitar shi, ta dubi Fati Ta ce " "Tauraruwa ki tashi mu je mu ci abinci." Fati ta ce "Ni ba zan ci da kowa ba."
Nafisa ta bata rai tare da fadin. " Baba bayason abin da kike yi sam, mu fa kannanki ne amma bakya janmu a jiki ba na jin dadi nima."
Fati ta maido kallonta ga Nafisa. "Amma ba ki lura da Baba ya fi son ku fiye da ni ba? Ya takura min yasa idon sa a kaina, ku kuma baya yi muku haka, shiyasa nake janye jikina daga cikin ku na tsaya ga Mama wadda ke sona."
Nafisa ta ce "Yaya Fati duk Baba ya fi son ki kalli can." Ta nuna mata hoton da ke manne a bango.
Ita ce da Baban a lokacin bikin tunawa da zagayowar ranar haihuwarta, yar shekaru biyar ce lokacin ga Cake ga
kalolin lemuka sannan ga yar karamar mota wadda Baban ya sai mata .
ILLAR FURUC
Na Halima k/mashi
14
Fati ta tsurama hoton idanu, tana tuna lokacin a idon zuciyarta. Ta numfasa sannan ta ce "Nafisa hakika Baba ya so ni amma a da, bansan meyasa yanzu ya tsane ni ba."
Nafisa ta ce "Har yanzu Baba yana sonki fiye da kowa a gidan nan, halayanki ce bayaso in ya ce ki bar abu ba kya bari kuma sai Mama ta na goyon bayanki."
Fati ta taba baki. "Ni banga wani abu da nike yi ba."
Nafisa ta ce " Yaya ko ni nasan da dama cikin abubuwan da ki ke aikatawa, kuma har yanzu hankalin su Baba bai kai gurin ba. Kina gudu daga makaranta, kina hotuna marasa dacewa ki na posting din su, kuma ba kya zuwa computer school kuma 'yan ajinmu sun fada min sun ga hotunanki a manne a titi duk da ban gani ba na san cewa ke din ce."
Fati ta ware ido cikin mamaki tana kallon Nafisa. Sannan ta ce "wai dama Nafisa haka kika sa min ido ke ma?"
Nafisa ta ce " Ban sa miki ido ba Yaya, abin da kike yi a bayyane ya ke, ki daina ki koma kamar yadda muka taso."
Mama ta yi sallama. kafin Fati ta furta wani abu. Dukkansu su ka kalle ta tare da amsawa, ta ce "Wai zaman me kukeyi ba za ku zo ku ci abinci ba?" Nafisa ta ce "Mama Yaya ce wai Ita bazata ci da kowa ba."
Mama ta ce "Kutaso muje."
Dukansu babu wadda ta ce uffan haka suka mike zuwa gurin cin abincin.
Katuwar tabarma ce
aka shimfida a gurin da aka tanada domin cin abinci. Faruk da Kabir da Amir suna ci a kwano daya. Fati ta kalli abincin.
Faten doya ne na
mangyada ya ji kifi bushashshe.
Wani irin kallo Baba ya watsoma Fati, ta sunkuyar da kai cikin fargaba. "Sannu da gida Baba." Ta furta cike da in ina. Ya amsa cikiciki. Suka zauna su ka dauki na su kwanon su ka bude kular abincin su ka zuba su ka koma gefe.
Wayar Fati ta soma ruri ta kalli fuskar wayar, gabanta ya fadi ta kalli Mama da wadda ke cin abincinta, ta maida idanunta ga Baba ya zuba mata idanu cikin tuhuma ta kuma kallon fuskar wayar GIDAN HOTO haka ta rubuta da manyan baki.
Kiran ya na daf da zai tsinke ta daga. "Hello ya ku ke?" Ta furta cikin nuna rashin tsoronta dan kar iyayenta su fahimci wani abu. Ya ce "Za ki iya zuwa yanzu kuwa?" Ta ce "Akwai wani abu ne?" Ya ce. "E wasu ne za ayi musu hoton tallar atamfa, to yariyar ta karya musu alkawari sun gaji da jiranta.
Ta mike da sauri ta nufi dakinsu ta na fadin "Yanzu haka kuna tare ne?" Ya ce "Muna tare da su yanzu haka." Ta ce "To ganinan zuwa." Ta shiga kai kawo a cikin dakin ta na tunanin yadda za ayi ta fita. Can dabara ta fado mata cikin sauri ta nufi gurin iyayanta dauke da karyar da za ta shirga... less
Halima K Mashi Abdullahi → Sababbin Litattafan Halima K/Mashi:
ILLAR FURUCI
Na Halima... moreILLAR... moreHalima K Mashi Abdullahi → Sababbin Litattafan Halima K/Mashi:
ILLAR FURUCI
Na Halima... moreILLAR FURUCI
Na Halima /Mashi.
14
Tana isowa ta dubi Mama tare da mika mata wayar "Ga mamansu Sumayya za kuyi magana."
Mama ta amshi wayar ta saka akunne ta na fadin salamu alaikum jin shiru yasa ta dubi fuskar wayar tare da fadin "La kinga ta katse."
Fati ta amshi wayar ta na fadin Network ne yau mtn abin na su babu sauki, dama a jakata ranar da naje Sumayya ba lafiya wai ashe ta saka sakamakon gwajin ta na asibiti a jakata kinsan irin ta ta ce, shine gobe za su koma ta ce ko zan kawo mata...
"Babu inda za ki." Baba ya tari numfashinta.
Mama ta ce "Garin yaya har takardun asibiti su ka shiga cikin jakarki?" Fati ta dan razana a zatonta ko Mama ta soma tuhumarta, amma sai ta boye razanar da nuna ko in kula ta ce
" Ina zan sammusu Maman su ta ce Anty yayar su Sumayya ta taho zata amsa, in ta iso zata kirani in ta sauka a unguwar nan tunda bata san gidan nan ba."
Mama ta ce "To babu laifi, je ki ciro kafin ta kira." Fati ta juya ta koma cikin jin dadin ta samu damar saka kafa a waje.
Mama ta kalli Baba. "Ka ga irin gajen hakurin har kana babu inda zataje, to gashi aikowa za a yi." Ya ce "Data canza salo ba." Mama ta bata rai tare da "Fadin shike nan kaci gaba da zargin da ka ke mata".
Bai sake fadin komai ba sai ma wayarsa da ya dauka ya na dannawa.
Fati ta koma daki cikin sauri ta saka hijabi da takalmi da naira dari ta jefa wayarta a karamar jaka ta fi ce da sauri sauri gudu gudu.
KANO
Acikin makarantar Hassan Gwarzo Fatima da Fadila suna tafe cikin jerin daliban da suka fito dan zuwa masallaci yin sallar isha i daga can su wuce gurin cin abincin dare.
Fadila ta dafa kafadar Fatima ta ce "Kawata dan Allah in mun dawo suratul Maryam zaki kara min tilawarta." Cikin mamaki Fatima ta waiwayo ta dubi Fadila ta ce "sonawa zan koya miki suratul Maryam?"
"Wai ma ina hankalinki yake lokacin da ake koya Mana karatu! Gaskiya na gaji."
Fadila ta marairaice tana fadin "Haba kawata wannan shine karo na karshe akan wannan surar bazan kuma tambayarki ba, da asubahin gobe zan kawo haddarta zan sha duka in ban kawo ta ba."
Fatima ta yi dan tsaki, sannan ta ce Allah kin saka wani abu a ranki ne wanda ya hana ki rike abinda ki ka zo don shi, wancan satin fa an dakeki kafin ki kawo hadda kuma ada ba haka ki ke ba."
Fadila ta danyi shiru kamar me nazarin maganar Fatiman.
Can ta ce. " Ina zaton wannan matsalar tana da nasaba da labarin da Anty matar Yayana ta zo min dashi lokacin ziyara."
Fatima ta ce "Wane
labari kenan?"
Cikin mamaki Fadila ta ce "Ban fada miki ba?" Kai Fatima ta girgiza tare da fadin "Bana zaton munyi maganar."
Fadila ta ce "To bari in munje kwanciya zan fada miki."
Bayan sun kammala komai suna zaune bakin gadon Fatima wadda ta zaku ta ji labarin da ya taba lissafin kawarta har ya sa ta kasa rike karatu.
Fadila ta ce "Ai na zaci na fada miki ashe ba muyi zancan ba, amma na taba baki labarin Ya Hashim ?"
Fatima ta danyi shiru alamun son ta tuna domin tabbas ta san sunan.
Can ta ce. "Na tuna da wanda suka taba zuwa da Yayanku har ki ka ce dan wan Babanku ne amma a gidanku ya girma ko yana karatu a Dubai?"
Fadila ta ce "Shine kuwa a nan BUK ya yi Degree dinsa masters dinsa ce ya yi a Dubai." Yana aiki a Central bank .
Fadila ta numfasa sannan ta dafa kafar Fatima ta ci gaba da fadin. "Kawata tunda na taso tun ina karama komai na Ya Hashim barge ni ya ke yi daga baya sai na fahimci son Ya Hashim nakeyi, nayi matukar kokari gurin boye wannan son yadda ba bu wanda ya gane har shi.
Addu "a ta daya kullum nakeyi Ubangiji ya taimake ni ya cusa masa sona ya kasance shine mijina.
To zuwan su Yaya da Anty sai Anty ke bani labarin wai an saka masa ranar aure da wata yarinyar abokin mahaifinsa ce.
Na tambayesu kuma ya na sonta ne tunda naga shi bai damu da harkar mata ba.
Sai suka ce min sosai kuwa, kinga yadda ya ke mutuwar sonta. Fatima kinji masifar dana fada cikinta." Fadila ta kai karshen maganar cikin shashshekar kuka.
Ga mamakin Fadila sai ta ji muryar Fatima wadda tasani da taushin murya gami da sanyi ta canza zuwa mai kauri.
"Ke Fadila karki fara kiyi min kuka saboda da namiji!" Fadila ta ware ido cikin mamaki ta na kallon Fatima sai kuma ta sake fashewa da kuka.
"Fatima ki barni domin bani da zabi a duniya banda wannan kukan kila... less
Halima K Mashi Abdullahi → Sababbin Litattafan Halima K/Mashi:
. ILLAR FUTUCI
Na Halima Abdullahi ... more. ILLAR FUTUCI
Na Halima Abdullahi ... moreHalima K Mashi Abdullahi → Sababbin Litattafan Halima K/Mashi:
. ILLAR FUTUCI
Na Halima Abdullahi ... more. ILLAR FUTUCI
Na Halima Abdullahi k/mashi
16
Fatima ta sauke ajiyar zuciya sannan ta dubi Fadila "Dan girman Allah ki min shiru muyi magana, wallahi dan ke ce amma bana tattauna maganar jinsin namiji in har shi din ba ahalina ba ne."
Fadila ta numfasa cikin dashashshiyar murya ta ce "Fadamin wata shawara da za ta sa zuciya ta tayi sanyi"
Fatima ta ce "Tambayarki zanyi ko ya taba cewa ya na sonki?" Fadila ta girgiza kai tare da fadin "A a, sai dai ina kallon bani da wata makusa don haka kowane namiji zai iya cewa ya na so na."
Fatima ta ce. "Kin tafka kuskure sosai! Amma ga shawara me zai hana ki share batunsa ki saka karatun ki a gaba, duk shekarunmu nawa nema kam da zaki damu da namiji, ni a halin yanzu maza ko birge ni basayi matsawar ba 'yan 'uwana bane ko a yan uwanma bana son wanda zai nemi wuce guri, ke kanki kin sani ko fara a malami ya cika yimin yanzu zan dauki matakin daina gaida shi... Ta numfasa sannan ta ci gaba da fadin.
" Fadila ki yi tunani sosai kar ki kai kanki ga halaka kan wanda bai san kina yi ba, ki shafe babinsa ki kalli gobenki ki yi kokari ki zama cikin matan da al ummar ki da zauri'arku za suyi alfahari da ke."
Cikin kuka Fadila ta kwantar da kanta a cinyar Fatima ta damki gefen hijabin Fatima cikin wani irin kunci wanda ba za ta iya fassara shi ba, ta ce
Bazaki taba fahimtar halin da nake ciki ba,
tare da soyayyar Ya Hashim na girma da shi na soma mafarki ranar da balaga ta fara riskata, sonsa a jinin jiki na yake!"
Fadila ta fara shafa mata kai cikin tausayawa.
Fadila ta ci gaba da fadin ki taya ni da addu a Allah ya ya ye min ko kuma ya saukaka min ya zo ya so ni nima."
Fatima cikin siririyar murya ta ce "To ya isa tashi ga wata shawara." Zaraf Fadila ta tashi zaune ta na kallon Fatima.
"Kin manta jiya bayan mun idar da salla malam ya yi mana nasiha har yake cewa dukan wanda ke da wata matsala mai sarkakiya acikin mu ya yi sallar istihara sannan ya barwa Allah zabi kintuna?"
Fadila ta mike da sauri cikin rawar jiki tana fadin na tuna bari kawai inyi tun yanzu, domin in ban manta ba bai fada mana cewa ga lokacin yi ba, ko da wane lokaci za a iyayinta. Zan bawa Allah zabi dan shine mai karfin ikon sarrafa zukatan bayinsa."
Fatima ta ce "Haka ne." Tabi Fadila da kallo wadda ta nufi daura alwala duk namiji ya susuta ta, abinda ta ke ganin ba zai yiwu gare ta ba, domin namiji in ba dan uwanta bane kallo ma bai isheta ba.
Ciki kwanakin da su ka biyo baya Fatima ta tsaya sosai dan ganin ta ceto Fadila daga cikin wannan hali ta hanyar ba ta shawarwari da nace mata sai ta rike haddarta hakan ya taimaketa matuka amma fa game da son Ya Hashim za ta ce sai abinda ya karu. Domin dan ma makarantar basa barin kwakwalwar dalibi ta huta sam.
Tun karfe hudu su ke tashi suyi wanka su gyara shinfidunsu lokacin salla yanayi zasu nufi masallaci daga can su wuce kara tun kur ani masu hadda kuma su shiga.
Bakwai za su shiga karin kumallo da sun fito sai aji haka daki daki har yamma.
Haka dai Fatima ta yi ta fama da Fadila har tsawon sati biyu. Abin ya kan lafa kuma ya na tashi kamar mai aljanu.
Fatima Muhammad tana jin dadin rayuwar makarantarta sosai, sannan ta na godiya ga iyayanta da suka tsaya mata dan ta samu ilmi wanda zai amfane ta duniya da lahira.
Burinta shine ta zama kwararriyar likita ko kwararriya a kan magungunan sai dai tabarwa Allah zabi.
Abuja
Tanti Dije ta na kwance akan kujera a falo tana kalon tashar sunna TV sama sama taji kwankwasa kofa dan haka ta kalli hanyar kicin ta kwalawa Jummai kira, ta fito daga kicin tana cewa "Gani Tanti."
Ta ce. " ki duba kofa na ji kamar ana kwamkwasawa." Jummai ta bude Hajiya Asiya ta shigo da sallama. Tanti ta amsa tare da mikewa zaune ta dora da fadin "Antyna ta kaina kece haka da rana face fece."
Hajiya Asiya ta nemin guri ta zauna tare da yaye mayafinta ta na fadin "Bari ke dai zuwan na danki ne shi ya taso ni."
"Allah ya sa lafiya!" Inji Tanti ta fada ta na kallon Hajiya Asiya zuciyarta tana fada mata kan batun Fatima ne Ashir ya taso mahaifiyar sa.
Jummai ta dire tire kato dauke da ruwa da leman roba gefe kuma ga kayan marmari dangin Ayaba da abarba.
Suka sake gaisawa take kuma Hajiya Asiya ta shiga zayyanawa Tanti sakon Ashir. "Yaro ya hana mu sakat ko wane lokaci magiya yanzu yau tun safe ya ke shige da fice shifa sai nazo muyi magana kwakkwara ki masa alkawarin bashi Fatima."
Tanti ta yi shiru tana sauraron wannan mawuyaciyar maganar kuma tana nazari.
Hajiya Asiya ta tsiyayi lemo a kofi ta daga ta shanye ta dire kofin sannan ta dubi Tanti.
"Hadiza Ashir dai danki ne na tashin alkiyama domin dan zumucin ki ne kuma cikin Ummanki ke da ubansa ku biyu ne iyayanku suka haifa baki da bukatar sai kin yi wani bincike akansa ko halinsa."
Haba Hajiya Asiya ya ki ke irin wannan magana haka in har Ashir ya na da wata uwa ai abayana take, domin babansa ma yanzu ubane a gurina tun da iyayan namu sun mutu sun barmu, batun in bincike ko na san halin Ashir wannan ma ai batsa kike yi.
Nazari nake yi akan ita kanta Fatima halinta da dabi arta, Ashir ya san komai na yi masa bayani duka na ce ya hakura zuwa ta gama sakandire muga ko zata canza.
Hajiya Asiya ta ce "Mecece matsalar ta ne?"
Tanti ta ce "Bata son soyayya batayi bata son namiji ya kulata matsawar shi din ba, ahalinta ba ne."
"To menene dalilinta?" Hajiya Asiya ta tambaya cikin mamaki.
Tanti ta ce "Oho ni dai na barshi a kiruciya ne kawai duk da ina girmama ra ayin yaro tun yana karami."
Hajiya Asiya ta ce "Wannan ai duk laifinki ne, ke ce zaki fada mata cewa jinsin... less
Halima K Mashi Abdullahi → Sababbin Litattafan Halima K/Mashi:
ILLAR FURUCI
Na Halima Abdullahi k/... moreILLAR... moreHalima K Mashi Abdullahi → Sababbin Litattafan Halima K/Mashi:
ILLAR FURUCI
Na Halima Abdullahi k/... moreILLAR FURUCI
Na Halima Abdullahi k/ mashi
17
In babu daya rayuwar daya ba za ta taba inganta ba." Suka saki dariya tare da tafawa. Hajiya Asiya ta ce "Ai gaskiya ce, kinsan Allah ke ce zaki ke nuna mata."
Tanti ta ce kin san zamanmu da ita ba sosai ba ne, ta na makaranta ko yaushe sai dan hutu in tasamu."
"To ai a irin wannan lokacin ne za ku samu ku tattauna ke da ita, dan Allah ki fadaw Dadyn su bukatar Ashir."
Hajiya Asiya ta fada cikin son a taimaki danta.
Tanti ta zaro ido tana fadin "Saya ki rufani zai ce dan Ashir da na ne shiyasa zan kawo maganar duk da na san irin cakwakiyar da ke kan ta."
Wace irin chakwakiyar ce akanta?"
Hajiya Asiya ta tambaya cikin tsananin son ta ji zan can.
"Ashir shi ne na hudu a masu son auren Fatima, kuma dukansu na gida ne, kinga dan Abokinsa, kanin amininsa, sai kuma wani abokin kuma maigidansa a fannin harkokinsa. Sai kuma dan kawata Hajiya Nana."
"Faruk?" Hajiya Asiya ta tambaya da sauri. "Shifa inji Tanti ta amsa tare da daga hannu alamun tabbatarwa.Ta ci gaba da fadin kinsan ya na aiki a NNPC yana samun kudi sosai yarinyar nan duk ta ki su."
Hajiya Asiya cikin sanyin jiki ta ce "Lallai yarinya ta yi kasuwa ko da yake ai da kyanta, to kuma duk ciki babu wanda ta fidda ko ta nuna ra ayi?"
Tanti ta girgiza kai tare da fadin "ko zanca ba mu taba yi mata ba domin bata sonji, addu a mukeyi dai Allah ya bata nagari domin Fatima yarinya ce yar sha shida kacal saurin girma ne, yanzu kuma kibar nan da kika sani duk bata yansu sam ta sirance, don haka ki ce da Ashir ya yi hakuri kuma ya yi addu a ya kwantar da hankalinsa Allah shine mai yi."
Hankalin Ashir ya yi matukar tashi da jin bayanin da mahaifiyarsa ta dawo masa da shi. Ya ce "Momi ina zaton lokacin mutuwa ta ne ya ke gabatowa domin inna rasa Fatima ba bu shakka zan iya rasa raina."
Cikin sigar lallashi ta ce "Kayi hakuri ka dage da addu a, sannan kayi sallar istikhara." Da kyar ta shawo kan sa ya hakura. Daga ranar ya maida gidan Tanti gurin zuwa kowane lokaci duk da cewa Fatima bata nan.
Tanti ta san dalilin zuwan sa amma Dadi bai sani ba, ya zata saboda yan biyu ya ke zuwa wadan da kullum ya na cikin daukarsu hotuna tare da koya musu kalolin tsayuwa irin na yaran turawa da larabawa.
Ashir yana son yaran so sai shafin sa na Instagram mutane suna tururuwar dan gwalawar yabawa tare da daukar hotuna zuwa ga wayoyinsu.
Yaran suna da kyau matuka farare tar ga dogon gashi har bayan su, in ka gan su da Tanti baza kayi zaton su din tsatsonta ba ne, amma kana ganin su da Dadi kasan yayansa ne kyawawan asalin buzayen Agadas.
Kaduna
Fati ta tare dan achaba sai da ta hau sannan ta ce "Isa kaita za ka kai ni." Tana isa sun fito gurin motarsu za su tafi, ganin maigidan hoton ya sa ta sha jinin jikinta cewa su dinne.
Ta nufi gurinsu bayan ta sallami dan achaba ta ce "Oga gani na zo." Tare suka waiwayo ya ce "Yawwa ga ta nan ta iso." Kallo daya wanda aka kira Manaja ya yi wa Fati sai yaji ta kwanta masa ya ce "Kin bata mana lokaci." ta ce "kuyi hakuri muna da dan tazara ne." Nan suka koma ciki aka soma maganar yadda su ke son aikin na su duk ta amince sannan aka yi maganar kudi.
Dubu dari uku suka ce za su bata tunda ita din sabuwar fuska ce. Fati bata ko ja ba mamaki ma ta yi kuma ga tsoron ina zata kai kudin.
Sai ta ji maigidan hoto ya na fadin haba ku kara mata sannan kuma bakuyi maganar lokacin da za a cire tallar ba.
Suka ce to sun kara hamsin nan dai aka shiga daukar hotuna sannan... less
Halima K Mashi Abdullahi → Sababbin Litattafan Halima K/Mashi:
ILLAR FURUCI
Na
Halima Abdullahi... moreILLAR... moreHalima K Mashi Abdullahi → Sababbin Litattafan Halima K/Mashi:
ILLAR FURUCI
Na
Halima Abdullahi... moreILLAR FURUCI
Na
Halima Abdullahi k/mashi
18
Ba su gama ba har karfe goma da minti ishirin, sai da suka kammala sannan hankalin Fati celebrity ya dawo jikinta sun rabu akan zata tura musu lambar asusun da za su tura mata kudinta.
Ta dubi wayarta, kira ne sama da hamsin gasu nan ba su Mama da Baban su ba har Sumayya, duk da haka Fati ba ta karyar da zuciyarta cewa asirinta zai tonu ba. Kuma bata ji a jikinta cewa burinta ba zai cika ba.
Ta kalli mai gidan hoton bayan tafiyar su Manaja ta ce "Oga dan Allah zan bar wayata a nan sai ka bani naira dari in hau mashin.
Ya ce "Haba kanwata akan naira dari zan karbi wayarki muje in kaiki gida ya kamata insan gidanku."
Fati ta ce "Oga na sani ba don kudin bane kawai ina son shirya wata dabara ce, za a ce na dade za a min fada ne, (ta mika masa wayar) ka amsa zan zo gobe ko an kira karka daga amma gobe zan maka text in ka gani to sai ka daga kiran."
Ya ce "Ban gane ba." Ta ce "Oga na jima a waje kuma in fada maka gaskiya ba a san na fito ba, kuma Mamana ta yarda da ni duk da ina boye mata abubuwa yanzu haka nasan ta na cikin damuwa da kuma fuskantar kalubale daga Babana.
Don Allah ka taimaki Mamana bata san komai game da wannan abubuwan da nakeyi ba zance na yarda wayar ne na tafi dubawa.
Gobe inna kira sai ka daga ka ce ka tsinta zanzo in karba, kilama Babanmu ya ce shine zai kawo ni don ya kure ni."
Oga ya yi jugum ya na kallon Fatima a azuciyar shi ya na tsoron abinda zai je ya zo.
Can ya ce "Shikenan kawo Allah ya kyauta amma zan baki shawara gara ki fadawa Mamanki gaskiyar duk abinda ki ke yi, domin dolene a sani duk lokacin da Duniyar shahararki ta dago ki sama."
Cikin zakuwa ta mika masa wayar tare da fadin na gode zanyi yadda ka ce, ka bani kudin zan tafi."
Ya bata dari biyu tare da fadin shikenan sai goben."
Duk ta gama shirya karyar ta kafin ta isa gida dan haka ta shiga gidan a firgice hankali ta she. A farfajiyar gidan ta samu iyayan nata cirko cirko, ta na shiga mahaifinta ya daina latsa wayar sa ya zuba mata ido dan jin karyar da zata zabgo.
Da gudu ta rungume Mama tana rusa uban kuka. Jikin Mama ya hau tsuma ta shiga jijjiga ta tana fadin "Me yafaru da ke Innalillahi! Dan Allah ki fada min."
Cikin kuka Fati ta ce "Wayata ce ta fadi bayan da 'yan shara suka shigo da gudu cikin layin nan lokacin da ta kira wayata ta ce inzo in shigo da ita sai ga su da adda ."
Innalillahi amma ba su miki komai ba dai ko?
Kuma dan shakiyanci Sumayyar ta nuna bata san maganar magani ba?"
Gaban Fati ya fadi ta tsaida kukan ta cikin far gaba ta ce. "Ina ki ka samu lambarta?" Ta ce "Nafisa ce ta ciro da ga cikin karamin littafin ki."
Fati ta girgiza kai ba lambar Sumayya ba ce gaskiya domin ban rubuta lambarta a ko ina ba sai a waya."
Mama ta ce "Na yi zaton haka amma na ji muryar kamar ta ta." Fati ta ce ina lambar ba ni wayarki in gani, ta fada ta re da amsar wayar.
Tsaki uban ya ja, sannan ya juya zuwa cikin gida. Mama ta bishi da kallo tare fadin "Wai wannan tsautsayin ma duk cikin laifine Babansu?"
Bai tanka ba ya fada cikin falon. Fatima ta yi amfani da wannan damar ta fashe da kuka tare da fadin "Baba baya so na, bai damu da ni ba."
Nafisa ta baro inda ta ke a tsaye ta zo ta kama hannun Fati ta ce, "Yaya Fati baba ya damu da ke fa, domin bai zauna ba tunda ki ka fita shima hankalinsa a tashe ya ke."
Mama ta ce "Muje ciki tunda Allah ya sa basuyi miki komai ba."
Mama ta kalli Baban ta ce "Me yasa kullum baka yiwa yarinyar nan adalci sai ka ke kallonta a mara gaskiya ba na jin dadi domin tana tashin hankalinta, kukan ta akan baka damu da ita ba."
Ya daga mata hannu, "Dakata ki ji, in har ki na son mu tattauna akan batun Fatima ki bari sai... less
Halima K Mashi Abdullahi → Sababbin Litattafan Halima K/Mashi:
ILLAR FURUCI
Na Halima Abdullahi... moreILLAR... moreHalima K Mashi Abdullahi → Sababbin Litattafan Halima K/Mashi:
ILLAR FURUCI
Na Halima Abdullahi... moreILLAR FURUCI
Na Halima Abdullahi k/mashi
19
Mama ta ce "Kash! Bana son kasa zuciyata ta zargi wani abu, nafi son ka kwantar da hankalinka mu hada kan yaranmu."
Ya ce "Ai bazamu iya hade kan yaranmu ba sai kin ba ni naki hadin kai kin yarda cewa Fati ta na yin wani laifi a boye sai muyi kokarin gano menene kuma mu dawo da ita akan hanya."
Cikin takaici Mama ta ce "Shike nan ka ci gaba da bayyana banbancin karakara."
Ya juya ya kwanta ya bar Mama tana ta mita. Daga bisani ta mike daga kan gadon ta fita cikin fushi. Dakin su Nafisa ta nufa ta samu Fatima kwance lamo cikin tausayi ta kira sunan ta. Fati wadda ta yi nutso a cikin tunanin yadda zata ga hoton ta a allon tallar akan babban titin Zaria Kano Abuja.
Kiran Mama ya sa ta dakata da murmushin dake kan fuskarta. Ta dago ta dubi mama wadda takaici gami da tausayi ya sa duk ta yi wani iri, ta ce "Mamana ki yi baccinki Allah zai kawo yadda zamu sake saya miki wata wayar."
Fati ta ce " Harsai zuwa yaushe kenan domin ban manta yadda ki ka matsa kanki ki ka canza min wayar nan ba, na dai hakura Allah ya saka min kawai in kuma da rabo na Allah ya bayyana min."
Mama ta ce "Ameen zan tayaki da addu a ni ma, ta dubi Nafisa ki rufo muku kofar sai da safe."
Sai da safe Mama."
Nafisa ta fada bayan ta sakko dan ta rufe kofarsu.
Abuja
Momin su Fadila ta kawo ziyara ga Tanti lokacin ana sauran kwana biyu su Fatma su samu hutun makaranta ta roki arzikin in za su dakko Fatima su hado da Fadila domin ita zatayi tafiya zuwa Zaria ita da direba don yin gaisuwar mutuwar kanwar mahaifiyarta.
Tanti ta yi mata gaisuwa sannan ta dora da fadin "Ina amfanin zaman tare in har ba za a amfani juna ba, bai dace ga baki ga hanci unguwarmu daya amma sai direban kowacce ya tafi tun daga Abuja har Kano ba, na jima ina son in miki wannan zancan."
Ashir da ke lissafi tun daga ranar da ya ji batun zuwa dakko su Fatima ya makale shima sai ya je
ita kam Fatima tun da idanunta suka sauka a kan Ashir ta ji wani kunci dakyar ta iya amsa gaisuwar da ya yi mata, suka ci gaba da sallama da kawayansu.
Haka a mota Fadila ke zubar ta amma Fatima da ga um sai um um, sai ma littafin ta da ta dakko ta na karantawa duk nisan Kano zuwa Abuja.
Ashir jiki babu karfi ya sauka a hanyar uguwarsu tun daga irin kallon da Fatima ta watsa masa wanda ya sa shi shiga taitayinsa , ga wani kwarjini da ta yi masa.
Sun sauke Fadila sannan su ka nufi gida.
Da gudu Tanti ta fito ta rungume Fatima wadda ta daure fuska ta ki dariya.
Tanti ta ce "Me kuma ya faru ne 'ya ta?"
Cikin tura baki ta ce "Akan me zaki bari Ashir ya je makarantarmu? "
Tanti ta ce "To ni ya ya zanyi ya dage ko da baki nan kullum yana hanyar gidan nan ina ga kin dawo!"
"Inko zai ci gaba da zuwa babu shakka zan nemi gurin da zanyi hutu."
Fatima ta fada cikin sauri tare da kawo ruwan hawaye.
"Sai ki je Maradi ki sha hutu dama Ba Bello ya ce a kai ki."
t
Ta fada tare da amsar gilashin da Fatima ta ciro daga idon ta.
Hanyar dakinta ta nufa tana fadin "Bana tsammanin kafa ta zata kara taka Maradi har abada."
Tanti ta bi bayan ta tana fadin muje kiyi wanka ki ci abinci ki huta kinji 'ya ta, daga baya sai muyi maganar dalilinki na tsanar Maradi."
Tare suka saka kafa a dakin dai dai lokacin da Fatima ta ke fadin "Wai Momi kin kasa gane cewa inna tsani abu iya gaskiya na tsane shi ko?"
Jummai ta iso bakin kofar ta na fadin "Lale marhabun da zuwa uwar dakina, na shirya kalolin abincin da ki ke so dan kawai in burge ki shugabata."
Ta koma da sauri ba tare da jin abinda Fatima za ta fada ba.
Tanti ta dubi Fatima wadda ta baje akan gadonta tace kije ki watsa ruwa.
Jummai ta kara shigowa da 'yanbiyu tana fadin "Ina gabatar miki da iyayen dakina sunzo su kwashi gaisuwa."
...Sa'adda ta isa ga shimfidar, sai taga ashe ba ƙwakwalwa ce a cikin ƙoƙon kan ba, abince ne wani iri kamar biski, aka cika a ƙoƙon kan mutum din, harda katon nama yanka guda, da kuma tataccen ruwan inabi a wani kokon da ya mata yanayi... moreDANDANO...
...Sa'adda ta isa ga shimfidar, sai taga ashe ba ƙwakwalwa ce a cikin ƙoƙon kan ba, abince ne wani iri kamar biski, aka cika a ƙoƙon kan mutum din, harda katon nama yanka guda, da kuma tataccen ruwan inabi a wani kokon da ya mata yanayi da na giwa saboda girmansa.
Ta waigo ta kalle shi sa'illun da halittun cikinta suka yamutse kamar za ta yi amai, ya sakar mata murmushinsa mai sanyi yana takowa zuwa gabanta ya duka, masifaffen ƙamshin turarensa ya daki hancinta, ta yi azamar rufe idanuwanta jin xuciyarta na shirin tarwatsa allon kirjinta ta fito...
"Ki ci mana Ziyada..."
"Ko na ba ki a baki...?"
"Ko in tattauna miki in dura miki a bakin..?
"Wanne kike so?"
"Dan Allah...Dan Allah Hussain ka mai dani gida, wallahi Allah ba zan ƙara zuwa dakinka ba, kai ko club ban kara zuwa, kai ko kofar gida ban sake fita, na tuba! Na bi Allah!! Na bi ka!!!
"Shitttttttttt!"
Ya furta yana ɗora yatsansa a bakinta.
"Na fahimce ki, na fahimta, dama kin faɗa ba wannan kike so ba, da kika kira ni shawarma kika ce ko? Pizza da Rufaida Yoghurt Mai kankara ko? Zo mu je Sahiba...!"
Kafin ta farga ya hura mata iskar bakinsa, idanuwanta suka rufe ruf! Kunnuwanta suka ɓame ɓam!
"Buɗe ki gani, ire-iren wuraren da na Miki alƙawarin zuwa, mun iso guri na takwas yanzu."
Ba ta taɓa haɗa guri da makaho ba, makafi na cikin halittun da take tsantsanin cin karo da su, sai kawai ta samu kanta da tuna tsohon saurayinta Habu Makaho da ta faffallawa mari dan ya ce da gaske aurenta ya zo yi, a yanzu sai ta ji dama ta koma shi, dama kar idanuwanta su buɗe har abada!
Sai dai fatanta bai kai ba...
...Ita da kanta ta buɗe su tana sauke su a tsakiyar makeken kogin da ke gabanta....
Da ta zaro idanun sai taga jefi-jefin turawa na giftawa ta gabanta da ɗan bante...A sannan kuma ta ji sanyi a jikinta, sanyi irin wanda ba ta saba ji ba, sai ta dubi jikinta da niyyar ganin me ya samu atamfarta da ta saka mai zanen kwando, ba tada kome...Tik! Take... Daga ita sai irin tufafin da ke jikin turawan.
Ko da take karuwar kauyensu mai lasisi, ko da take tantiriyar karuwa... Ko a sa adda Jummai ACi Duniya ta bata lasisi ta hanyar gwaji, ba a saka ta yin tik a gaban karti ba, da sutturarta aka yi kome aka gama!
Sai ta ji dama...
"Sahiba... Idan wandancan larabawan sun fito mu shiga cikin ruwan mu ma...muna fitowa zan kawo miki shawarmar...
Da wannan, sauran numfashin da ya rage mata ya dakata.