• Contrast
    • Font
    • A
  • Sign In
  • Sign Up
    Loading ...
View All Updates Mark All Read
Bakandamiya
  • Shafin Farko
  • Mambobi
  • Zauruka
    • Browse Groups
  • Tambayoyi
  • Ra'ayoyi
    • Browse Polls
  • Makalu
    • Browse Entries
  • Bidiyoyi
    • Browse Videos
  • Sautuka
    • Nemo Sautuka
  • Hotuna
    • Browse Albums
    • Browse Photos
  • More
    • Kasuwa
      • Stores Home
      • Browse Stores
      • Browse Locations
      • Products Home
      • Browse Products
      • Products Pinboard
      • Categories
      • Browse Reviews
      • Wishlists
    • Sana'o'i
      • Browse Listings
    • Sanarwa
      • Bukukuwa Masu Zuwa
      • Past Events
  • Updates
  • About
  • Abokai(23)
  • Zauruka(1)

Updates

About

Personal Information

  • Suna Safiyya
  • Jinsi Mace

Abokai

  • Lawan Dalha Ya Allah Ka sada mu da alkhairan da ke cikin wannan rana; ka tsare mu daga sharri duniya da lahira. #JummaaMubarak
  • Abdullah m bature
  • Rahma kabir *AKAN IDO NA* Na Rahma Kabir (Mrs MG) Whattpad @rahmakabir 15 *Last free page* Anty Amarya ta shiga tsananin rudani, ta rasa wani irin tunani zata fara, tana da tarin tambayoyi amma ba tada mai amsa mata. Koda Alhaji ya dawo ya kwanta tana jinsa har barci ya sake daukarsa tana jin saukar numfashinsa, hakan ne ya bata dama ta tashi zaune a hankali ta mike ta shiga bayi tayi fitsari kana ta dawo ta kwanta, da kyar barci ya dauke ta. ****** Washe gari. Da safe bayan mutanan gidan sun kammala karin safe gaba daya, sai suka tattara suka koma falo saboda Alhaji yace zai yi magana dasu, ya kai dubansa ga Majaheed wanda yake sanye cikin blue din riga da bakin wando da alama ya gama shiryawa fita aiki kawai zai yi. Kai Mujaheed ya zancen yarinyar nan daka kai station dinku? Tana nan a hannunmu har yanzu bata bada wani bayani ba, ina ga nan da wasu kwanaki zan mikata kotu, sannan zamu yi bincike akan wanda suka yi silar kawota gidan nan. Ayya ina ganin ba za ayi haka ba, ka sake ta kawai ta tafi tunda mu mun yarda da kaddara, duk kuma mai son ganin bayanmu Allah ba zai barshi ba koya kika ce Hajiya. Yayi maganar yana duban Ummi. Hakane Alhaji amma daka barshi yayi aikinsa dan amfanin naka yana waje kenan. Ni kam nafi amincewa da arufe maganar, insha Allah asarar da muka yi zai dawo Amma Baba ina ganin yin hakan kamar an kara mata wani karfi ne wanda nan gaba zata iya sakewa. Mujaheed umarni na baka ka saketa ta tafi ba wai niman shawararka nake ba. Meye duniyar da har zamu tsaya muna zafafa abu. Shikenan insha Allah zanyi yadda kace. Yauwa, sannan batun Haj. Kausar shima ya kare tunda ita aiki ta dauketa bata san cewar da wani nufi ta shigo gidan nan ba, tsawon zaman dana yi da Kausar ban taba kamata da wani laifi mai muni ba, kun san dai halinta Yayi maganar yana kallonta, Anty Amarya tayi murmushin yake ita kadai tasan halin da take ciki na rudani. Ummi taja guntun tsaki. Ai ita dama bata laifi a gunka, waya sani ma ita ce tasaka kace a saki yarinyar Babu ruwanta ganin damana ne yasa nace a saketa, kuma ai na isa da gidana na yanke hukunci, bana son irin wannan maganganun. To ai shikenan Allah ya kyauta na gaba Cewar Ummi tana kawar da kai gefe, nan Alhaji ya mike tare da yi musu sallama akan shi ya fita kasuwa, Anty Amarya ta bi bayansa dan yi masa rakiya kamar yadda ta saba kullun. Suna fita Mujaheed ya mike jiki a sanyaye Umminsu ta kalleshi cikin kulawa. Sai dai kiyi hakuri da halin Babanku tunda ya riga ya yanke hukunci Ai wlh wani lokacin lamarin Baba sai a hankali Cewar Amina itama tana mikewa cike da jin haushi. Kar na sake jin bakinki a nan kin san bana son raini, mahaifinmu ne ya isa ya zartad da duk hukuncin da yaso a gidansa kuma dole muyi masa biyayya, shiyasa kullun nake bambantaki da Aisha dan ta fiki hankali. To to ni me nace ai gaskiya na fada Tace tana turo baki sai ta wuce zuwa dakinsu da sauri dan karya kai mata hannu. Tsaki kawai yaja ya girgiza Kai. Ummi ina zuwa Ka fasa fitan kenan? A'a zan yi wani abu ne Yace yana haurawa sama, yana isa dakinsa ya kira station dinsu ya basu umarnin su dauko Saufyan su kawo shi gidansu yana jiransu. Bayan minti goma sha biyar sai gasu sun karaso, Mujaheed ya fita zuwa farfajiyar gidan sai gasu sun shigo tare da Sufyan da suka sanyawa ankwa a hannu, ya yi baki ya rame jikinsa duk ciwuka gwanin tausayi, Mujaheed ya karasa gabansa ya kwance masa ankwan yace yaran aikinsa su jirashi, sai ya cewa Sufyan yabi bayansa, ba musu ya bishi suka isa dakin baki ya nuna masa wani daki yace ya shiga ciki yayi wanka, ba musu Sufyan ya shiga ciki dan yana bukatar yin wankan ko zaisa jikinsa ya rage yi masa tsami, yana shiga Mujaheed ya fito ya nufi dakinsa ya dauko wani shadda ash color daga cikin kayansa ya fito ya koma dakin bakin ya ajiyewa Sufyan a gefen gado ya zauna yana jiran ya fito. Ya dauki kimanin minti ashirin yana gasa jiki a cikin shawa, wannan ne karonsa na farko daya taba yin wanka a irin wannan bayi mai kyau na masu kudi, banda yana cikin halin tashin hankali da ba karamin kallo zai tsaya yasha a gidan ba, amma ina hankalinsa gaba daya yayi gida yana tunanin irin halin da mahaifiyarsa take ciki, ya maida kayansa ya fito sai yaci karo da Mujaheed suka hada ido ya sakar masa murmushi, kamar ba shi ne mara mutuncin nan ba da yasa aka yi masa dukan kawo wuka. Ga wasu kaya na kawo maka ka sanya su dan wannan na jikinka sun baci sosai, in ka kammala ka fito ka karya. Mujaheed yana gama fadar haka ya mike ya fice ba tare daya jira amsarsa ba, da kallo Sufyan ya bishi harya fice yana mamakin sauyawar da ya gani, haka dai ya zame kayan jikinsa ya sanya wannan da ya bashi, sun so suyi masa yawa da yake Mujaheed yanada tsayi shi kuma baida tsawo sosai sai dai kaurinsu zai zo daya, yana gama shiryawa ya fito ya samu an tsake masa center table da abinci, ya karasa ya zauna, Mujaheed ya mike yaja table din zuwa gaban Safyan. Ka ci ka koshi amma kayi sauri dan zamu je asibiti a duba lafiyarka Galala Sufyan ya kalle shi ya kasa yin shuru wannan karan, sai yace cikin raunin murya. Dan Allah ka gaya min dalilin wannan sauyawar haka? Meyasa kake kokarin yimin kirki? me yake faruwa? Babu komai sai alkhairi, bincikenmu ya tabbatar mana da ba kada laifi, kasantuwar ni na jawoka kazo garin, shiyasa nake son kyautata maka koda sau daya ne, kayi sauri ka kammala cin abincin lokaci na tafiya. Sai ya fice ya barci, Sufyan bai kuma cewa komai ba ya dauki kofin tea da aka hada masa mai kauri ya fara sha yana kallon irin tagomashin da aka hada masa, wanda duk mugun cinsa sai ya barshi, soyayyar Irish da kwai, indomie wanda yaji kayan hadi, farfesun naman kaza, nan take ya hadiye wani yawu dan gaba daya yaji sha'awar yaci su duka, sai a lokacin bakin yunwar da yake ji ya taso masa, aiko haka ya saki ciki ya kwashi girki, harya nima mance a ina yake dan ba karamin yunwa yake ji ba, duk kuwa cinsa sai da ya hakura ya bar abincin. bayan ya kammala sai ga Mujaheed ya shigo yace masa suje, haka suka fito ya sashi a motar office dinsu shi kuma ya shiga nashi suka wuce asibitin murtala, sai driver din gidan shima ya bi bayansu dan cika umarnin Mujaheed. Koda suka je likita ya duba Sufyan sosai ya rubuta masa Magani, sannan ya hada su da wata nurse suka wuce dakin dressing aka wanke masa ciwukan daya ji a jikinsa, bayan an gama masa suka siya magani sannan suka fito haraban asibitin, a nan Mujaheed ya sallami yaransa suka wuce, sai ya sanya Sufyan a motar gidansu ya mikawa driver kudi. Wannan kasha mai dasu, sai sauran kaci abinci ka tabbatar kayi tuki a hankali, kuma ka kaishi har kofar gidansu, in dare yayi maka ka kwana gobe in Allah ya kai mu ka dawo. To insha Allah nagode Driver yace sai ya shiga motan, Mujaheed ya sunkuya windon baya in da Sufyan ke zaune ya mika masa kudi duba ashirin da wata leda wanda yake dauke da kayansa da wayarsa da kuma duk abinda yake nashi wanda suka cire masa lokacin da suka kai shi station. Kayi hakuri da abinda ya faru, insha Allah yau zaka koma gida, ga kayanka nan, wannan kuma ka sha ruwa a hanya. Nagode Allah ya saka da Alkhairi, sai dai ina son tambayarka labarin Mubeena. Zata dawo itama insha Allah karka damu. Sufyan zai kuma magana, Mujaheed ya daga masa hannu alamar baya son wani zance, sai ya umarci driver daya ja su wuce. Akan idonsa suka bar cikin asibitin kafin shima ya koma mota ya shiga ya tayar ya kama hanyar station dinsu, yana sauke wani irin murmushi wanda shi kadai ya barwa kansa sanin yinsa. Yana isa station dinsu yasa aka fito masa da Beena, ya tasa keyarta har zuwa wajen motarsa ya bude mata mazaunin baya ya ce ta shiga, ta kama marfin motar tana kallonsa. Ina Sufyan? Bazan iya barin gurin nanba ba tare da shi ba Na sallama shi ya tafi Amsar daya bata kenan yaje mazaunin driver ya bude ya shiga, ganin babu wasa a fuskarsa shiyasa zuciyarta ta yarda da abinda yace sai ta shiga ta zauna, Mujaheed bai ji wani haushi ba danya kasance driver dinta, bazai iya jure ganinta a gaba kusa da shi ba shiyasa ya gwammaci ta zauna a baya ya jata. Suna fitowa yaran Alh. Maina suka shaida masa a waya cewar sun ga Mujaheed ya fito da wata mace a bayan mota, sai yayi musu umarnin su bisu a baya. Mujaheed gidansu ya wuce da Beena, suna isa yayi parking ya karba key wajen mai gadi yace ta fito, ya tasa keyarta suka isa sashin ma'akaita har zuwa dakinta, ya bude ya fara shiga ta bishi a baya. Ki kwashe duk kayan da kika san naki ne ina jiranki Bata tanka shi ba ta shiga hada kayanta ta tusa a jaka, kana suka fito har zuwa harabar gidan, sai suka iske mutanen gidan cirko cirko sai kallonsu suke yi, Anty Amarya taji kamar ta jawo Mubeena ta boyeta a dakinta, gaba daya babu wanda ya iya magana, har sun gota su zata wuce Beena ta juyo ta kallesu tace cikin sanyin murya. Labarin dana baku cewar daga kauye na fito ba gaskiya bane, hasalima ban taba yin rayuwa a kauye ba, shigata da kwalliyata duk shiri ne, asalin sunana Mubeena. Anty Amarya nagode da karamci, ba dan ke ba da ban kasance a cikin gidan nan ba. Sai ta juya ta cigaba da tafiya, gaba dayansu sun kasa magana kamar babu wani halitta a gurin, sun tsorata sosai da zancenta, Anty Amarya kuwa taji kamar ta dakatar da ita dan tana so ta sanar mata asalin labarinta da dalilinta na zuwa gidan, akwai tarin tambayoyi data so Beena ta amsa mata su sai dai kash ba hali, Mujaheed kuwa wani bacin rai yaji yana taso masa, yana matukar jin zafin abinda mahaifinsa yasa shi yayi, sai dai bai da yadda yaso dole yayi masa biyayya, shiyasa har ya iya daukarta a motarsa suka zo gidansu ta kwashi kayanta ta kara gaba, sai dai akwai wani sirri daya barwa zuciyarsa wanda yake ganin me bullewa ce a gareshi, dan in har ya bar Beena ta tafi tofa taci bulus. Akan idonsu ta fita daga gidan sai a sannan ne Ummi ta furta. A gayas Allah ya mayar miki sharrinki Su Inna Hauwa da sauran ma'aikatan gidan suka amsa da Amin. Mujaheed shine ya tare mata napep ya ciro dubu daya ya mika masa yace ya kaita duk inda take so. Sai ya tsaya ya kama karfen Napep din ya kalli Beena yana wani shu'umin murmushi, itama ta bishi da kallo cike da harara, haka ya saki karfen mai napep ya jata suka wuce shi kuma ya koma cikin gida. Tunda suka kama hanya mai napep ya kula da wata bakar jeep tana binsu a baya, hakan yasa ya kara gudunsa dan su shiga cikin mutane ba tare daya sanar da Beena ba. Koda suka shiga cikin mutane still jeep din na binsu harya isa hotel din data ce ya sauke ta, ya ciro canjin dari biyu ya bata tace ya barshi sai ta dauki kayanta ta shige ciki, mutane sai kallonta suke ganin jikinta duk datti ga ciwuka a fuskarta duk ta kubbura, haka ta ratsa ta wuce ko a jikinta, mai napep kuwa tuni ya bace ya tafi yana mai sauke numfashi zuciyarsa cike da sake saken ko meyasa wannan bakar jeep ke binsu. Su kuma ganin ta shiga hotel din suka tsaya daga nesa suka yi parking dan zaman jiran fitowarta. Tana isa ta bude dakinta ta shiga ta kulle, ta shiga toilet ta yi wanka ta gasa jikinta sosai kana ta fito ta dauro alwala, zama tayi kan dadduma ta gabatar da sallah a zaune dan gaba daya jikinta babu karfin da zata iya tsayuwa, ga bakar yunwa tana ji, haka ta jima a zaune tana rama sallolin da ake binta, kana ta kira room service suka kawo mata abinci tea ne mai kauri da soyayyar plantain da kwai. Bata bukatar abu mai mauyi saboda ba zata iya ci ba, tana kammalawa ta sanya doguwar jallabiyarta ta gyara kayanta ta kwashe na gana mazgo ta mayar cikin trolley ta ninke jakar tasa a ciki, wannan lu'u lu'un daya zama dutse data gani a cikin kayanta ta sanya a aljihun trolley da nufin in sun isa wani rafi zata jefa a ciki. Cikin sauri sauri ta kammala shirinta saboda tayi matukar damuwa da halin data jefa Sufyan, ba zata iya kwana a kano ba dole ta bi bayansa dan sanin a halin da yake ciki. Ta sanya dogon hijab dinta ta rufe fuskarta da nikaf nan take tayi badda kama, taja trolley dinta ta fito ta rufe musu daki kana ta isa reception ta basu key ta wuce. Tana isa bakin gate ta samu napep ya sauke wani mutum sai kawai ta tare shi ta shiga tace masa ya kai ta kano line suka wuce. Bangaren yaran Alh. Maina kuwa suna nan a inda suka tsaya suna jiran fitowarta wanda harta fito ta wuce basu sani ba. ****** Gidan Alh. Nasir Suna zaune a falo gaba daya, suna zancen askin da Shukura ta yiwa kanta, Abbansu shi kadai ne ya goyi bayanta da cewar. Karku takurawa Autata, in dai gashi ne nan da wasu lokacin zai kara fitowa. Ai dama kai baka ganin laifinta Cewar Mami. Mustapha yace. Ai bari Mami zan fadawa saurayinta cewar kwaikwaido zai aura To kayi ta fada mana Tace tana turo baki, sai duk suka sanya dariya. Shigowarsu Saifu ne ya dakatar da hirarsu, nan da nan Abba ya shiga natsuwarsa ya daga jarida ya rufe fuskarsa ya soma karatun dole, dan yana mugun jin kunyar hada ido da Aisha. Suka shigo ciki suka zauna sai suka gaishesu duk suka amsa, Abba dai da jarida a fuskarsa ya amsa, itama Aisha taji dadin haka dan bata son ganin fuskarsa saboda irin tsanar data ke masa, Saifu ma tunda yazo gidan ya kuda da Abbansa ya kasa sake jiki da shi suyi hira, shiyasa bai damu da shiga lamarinsa ba iyaka suka gaisa ya wadatar, yace. Abba, Mami mu mun fito zamu tafi Au komawar taku yau ne ko? Cewar Mami Insha Allahu yau ne har mun sanya kaya a mota, To Allah ya tsare ya kaiku lafiya Cewar Abba, Mami tace. Zaku biya gidansu Aisha ko? Ai tun jiya munyi sallama dasu wucewa kawai za muyi. To Allah ya tsare. Suka amsa da Ameen, kana suka mike su Mami suka rakosu har wajen mota Amma banda Abba, Shukura kamar zata yi kuka saboda taso ta bisu amma ba hali, suka shiga mota suka suna dagawa su Mami hannu har suka fita daga gidan suka kama hanya. Bangaren Beena ma ta samu mota drop sun kama hanya, tafiyarta kusan lokaci guda ne dana su Saifullah.   *Ko me zai faruuu...?* #Lastfreepage #Rahmace            ______________ Dan samun cigaban wannan labari da zakinsa hade da warwara ku biya cikin fara shi mai sauki N200. Ku tura ta wannan account number din. 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access (Diamond) Bank. In an biya a turo screen short din alert ta WhatsApp chart a Numberta 07036993733. Ko MTN card N200 ta wannan number 07036993733. Insha Allah zan yi Adding mutum zuwa group d'in littafin.
  • Meemi Bashir Assalamu alaikum barkanmu da warhaka
  • Aisha Sa'eed Abubakar (Aishan Umma) *AHALINA* *Na* *Aishan Umma* *???????? ZAMAN AMANA WRITER'S (Z.A.W)* https://www.facebook.com/ZAMAN-AMANA-Writers-FANS-311893699485963/ 2019 1 Cike da zumud'in yau zasu zauna da mahaifansu ababen alfaharinsu suka tashi daga bacci, sakamakon yau babu makaranta. A gaggauce Fahat yayi wanka yasa Aida ma taje tayi sannan yayiwa sauran k'annensa guda biyu, duk suka shirya sannan suka fito. Fahat ne yayi saurin shiga kitchen dan anan ya jiyo motsin Amminsu, har k'asa ya tsuguna ya gaisheta, suma sauran k'annensa da suka shigo kitchen d'in yadda suka ga d'an uwansu yayi hakan sukayi, ta amsa cike da fara'a had'i da kulawa, duk seda ta shafa kawunansu tana mai karanta musu addu'ar da Annabi Sallalahu alaihi wa sallam yake karantawa Hassan da Hussaini (u'izukuma bi kalimatillahi tammat min kulli shaid'anin wa hamma, wa min kullu ainin lamma). Tana matuk'ar son yaranta, sosai take k'aunarsu, har wani lokacin takanyi tunanin Kodai mutuwa zatayi ta barsu ne?. Fahat ne ya katse mata tunaninta ta hanyar cewa "Ammi bari naje na gaida Abbu na dawo na tayaki da wani abin mana se mufi yin sauri". "A'a d'an albarka jeka ku gaisa d'in daga nan kuje ku gyara d'akunanku tukunna ni na k'arasa wannan" cewar Ammi Kafewa yayi yace "ai tunda babu school yau to zan tayaki aiki insha Allah, Habibtyna ina k'aunarki, bana son naga kina gajiya da yawa. Mene amfanin Allah ya baki ni amma na gagara taimaka miki, gaskiya inde kina so na samu lada ki bari na tayaki kinji Ammi na?" Tayi murmushi had'e da shafa kanshi tace "na amince to yaron kirki, kaida kake namiji kaine me son shiga kitchen ita kam Aida ko a jikinta, yanzu ko nace tazo muyinma se raina ya kusan b'aci, ban san inda ta koyi k'uiya ba. Allah ya raya mana ku, ya tsareku ya kare ku, Allah yayi muku albarka ya kareku dukkan sharri, ina alfahari da samunku masoya na sanyin idaniyata." Daga haka ya je ya gaida mahaifinsu, se gashi ya dawo tare da Aida suka ci gaba da aikinsu suna hirarsu ta tsakanin uwa da yaranta. A haka ta dad'a samu tayi ta yi musu nasiha akan halin rayuwa. Su ko su Sa'eed da Alim suna can wajen mahaifinnasu suna tayashi hira sakamakon weekend baya zuwa ko ina. A haka suma suka kammala aikinsu suka fito da komai suka jere a dinning area, kowa kuma ya hallara akayi bismillah aka fara cin abinci cikin ladabi. Haka rayuwar gidan take tafiya cikin aminci gashi dai ba wani me kud'i bane me gidan sedai rufin asirin Allah da kuma wadatar zuci, amma zuciyar mutanen gidan tana cike da k'aunar juna da kuma tausayawa. Iyayen suna k'ok'arin ganin sun bawa yaransu tarbiyya daidai gwargwardo, haka ma yaran suna biyayya ga iyayen nasu, duk kuwa da irin soyayyar da suke nuna musu hakan besa raini ya shiga tsakaninsu ba. Rayuwar gidan abar sha'awa ce ga duk wanda ya gani sedai san barka. Alhaji Nasir Aliyu (Abbu) shine mahaifinsu Fahat, se mahaifiyarsu Maryam, sunyi aure tsawon shekara goma sha bakwai kenan a yanzu. Allah ya azurtasu da yara hud'u Fahat shine babba wanda yake da shekara goma sha shida, se Aida take bi masa ita kuma tana da shekara goma sha d'aya, se Sa'eed me shekara bakwai, sannan auta Alim me shekara hud'u a duniya. A yanzu haka Fahat yana SS 2 a makaranta sannan yayi saukar Al Qur'an tun yana shekara sha hud'u yanzu hadda yake, ita kuma Aida tana Pri. 6 itama takai kusan izifi 30 a Al Qur'an, Sa'eed yana Pri. 2 yana uzifi 10 a Al Qur'an, se auta Alim yana Nur. 2 shi kuma izifi biyu a Al Qur'an Kwatsam wata ranar Juma'a bayan su Fahat sun tafi makaranta wani irin ciwon ciki ya taso Ammi a gaba, da k'yar ta iya lalubar wayarta ta kira Abbu ta sanar masa, cikin tashin hankali shima ya baro office domin yaga meke damunta har haka?, dan tabbas duk ciwon da Maryam zata bud'e baki ta fad'a harta kira a waya ba k'aramin ciwo bane. Da hanzari ya shiga d'akin ganin halin da take cikine ya sashi fita nemo mota dan baze iya d'aukarta a babur ba cikin wannan halin. Allah sarki Ammi! Allah ya baki lafiya ???? *Aishan Umma* ??????????????
  • Bashir Adam BAKANDAMIYA (1) ???? IN KA ?I JI.... ???? GABATARWA: Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin ?ai, Tsira da Aminchi su Tabbata ga Shugabammu Annabi Muhammadu (S.A.W) Da Alaye Da Sahabbansa baki ?aya, Amin. Bayan haka: IN KA ?I JI... Labari ne akan wani matashi mai suna Gagare, wanda ya gagari mahaifanshi, ya zama ri?a??en mashayi ?an bangar Siyasa. Abubuwa marasa kyau na wa'azi sun same shi amma bai tuba ba, ya biye wa Shai?an har ya ?auracewa iyayensa. Dalilin hakan ne a ?arshe har ?waya ta sanya ya haukace ya zama wula?antacce a cikin al'umma. Ina fatan labarin zai nisha?antar, ya ilmantar kuma ya fa?akar. A sha karatu lafiya. Bashir Adam. *** *** *** A DANDALIN SHAYE-SHAYE Zaune a dandalinsu na shaye-shaye suna fuskantar juna kamar yadda suka saba zama, matasa ne guda uku: Gagare, Goje da ?azaza, kowanne ya tuzgu?e dafe da hannu guda a ?asa, gudan hannun kuma rike da tsumma yana zu?ar Sholisho. Hira suke yi irin tasu ta bugaggun mashaya wa?anda suka yi nisa cikin harkar chaskalewa. Gagare ne ya fara magana cikin murya irin ta bugaggu, ya ce, Kai! Wallahi bb ba abinda ya fi rusu da?i! Don ni in har ina da ?waya ba ni da wata matsala! Wallahi ni fa da in rasa ?waya gwamma in rasa abinci! Goje shima cikin muryar makakku, yace: ?warai kuwa bb, Wallahi gwamma rashin abinci da rashin ?waya! Ai ni shi yasa ma kuka ga kwata-kwata ba na bari ?waya tana yanke min! Loading...
  • Zuuz Alhassan
  • Mrs Sadiqq Ja'afar
  • Pharty Bb I just published "7." of my story "MADUBIN GOBE!". https://my.w.tt/iVBD7rFeEbb MADUBIN GOBE 7. Pharty Bb. Wattpad phartybb. .... Littafin kyauta ne. .... "Nuratu?" Da kyar ta buɗe idanunta da suka fara canza launi ta dubi Mami dake zaune gefenta bayan sun shigo gidan ta zube saman kujerun falon tayi kwanciyarta. Hannu Mami ta saka ta kamo hannuwan Nuratu da ta bita da ido. "Bana hana ki saka damuwa a ranki ba, bana son ciwon ki ya tashi dan Allah ki daure ki kawar da komai a ranki, ki duba halin da muka shiga dalilin haka, Nuratu in bana ganin dauriya tattare dake bana jin kwanciyar hankali a rayuwa ta, sai in ga har yanzu baki gama warkewa ba. Duk da nasan kina ƙoƙari, ki daure ki ƙara. " Mami ta ƙarasa maganar cikin ƙarayar murya. Murmushi Nuratu tayi ta damƙe hannun Maminta. "Mami kai na yake ciwo, amma babu komai." "Shikenan to tashi muje ganin babyn Hasiya, waya sani ma ko sabon miji na samu." Mami tace tana dariya dan kawarwa Nuratu damuwarta. Itama dariyar Nuratu tayi tana ƙoƙarin danne damuwarta, ta tambayi Mami. "Sun koma gidane?" "Eh muje can, in zaki zauna mata zuwa bayan suna sai ki ɗauki kaya." To Nuratu tace ta miƙe ta shiga ɗakinta ta ɗauki kayanta cikin kits ƙarami ta fito suka fita. ... Gidan har ya fara cika da mutane suka karɓi baby suna gani, babynta mace kyakkyawa fara tasha kayan sanyi farare. Bayan Mami ta miƙawa Nuratu babyn ta hana kowa karɓa. Mami bata jima ba ta koma gida ganin su kansu sun isa kula da mai jego, ga Aunti Rahma ga Walida da Ameera mai bin ta ga Nuratu da Aunti Rukayya. "Ki kula da ita Rahma dan Allah. Ki tabbatar tasha maganinta a kan lokaci." Mami take faɗawa Aunti Rahma kafin ta wuce. "Mami menene? Wani abun ya faru." Aunti Rahma tace cikin damuwa. "Kusan hakan ne, lafiyarta ƙalau ta dawo daga gidanki amma zuwanmu asibiti ya kusan dawo mana da aiki baya, ki kula da ita kar ku barta cikin damuwa." "InshaAllah Mami komai zai wuce." Aunti Rahma tace cikin tausayin ƙanwarta da wannan ƙaddara ta gifta a rayuwarta da nasu gaba ɗaya. Tun da Mami ta tafi Rahma ta saka ido akan Nuratu har dare da ta lura ta kasa walwala gaba ɗaya ta zauna ta zuba jaririyar ido, Walida da Aunti Hasiya sai hira suke Ameera da Rukayya sun koma gida. Da ido Aunti Hasiya ta nunawa Aunti Rahma Nuratu ta ɗaga mata kai alamar ta ganta. "Ƙanwata!" Aunti Rahma tace tana zama gefen Nuratu da ta juya a ɗan firgice ganin Aunti Rahma ne ya sata sauƙe ajiyar zuciya. "Wa kike tunani? Yaya Al-ameen ko sauran samarin ki?" Ɓata rai Nuratu tayi tana yamutse fuska. "Babu kowa ciki. Ni fa ba samarina bane, dukkan su mutunci muke, kuma kun sani." "Hakane kuma fa." Aunti Rahma tace tana murmushi tare da ɗaga kai. Turo baki Nuratu tayi ganin Aunti Rahma ta maida abin wasa. "Tashi kiyi wanka ki kwanta, ga kuma can maganin ki yana jiranki." Miƙewa Nuratu tayi ta shiga wanka, data fito ta saka kayan baccinta tasha maganinta kafin ta kwanta gefen baby. Wayarta ta ɗauka ta ƙira Dr Awwab tunawa da ya ƙirata ɗazu. "Har na cire rai da ganin ƙiran ki Noor." Dr Awwab ya amsa mata dashi bayan ya amsa sallamarta. Murmushi Nuratu tayi. "Ina Hanan? Ya aiki?" "Lafiyar ta lau, tayi rigama ta gaji tayi bacci duk ta ishe ni in kawota gurin ki." Har lokacin murmushi bai gushe saman fuskarta ba dan tana girmama Dr Awwab. "Allah sarki My Baby, yaushe zaka kawo ta?" "Duk lokacin da kike da free har Daddyn Hanan na son ganin ki ba ita ɗaya ba." Shuru Nuratu tayi kamar ba zata amsa ba kafin ta sauƙe numfashi. "Ni dai Hanan zan gani." "Ni fa?" Yace mata da sauri har ya bata dariya ta ɗan dara. "In na samu time zan sanar da kai." "Godiya muke ranki daɗe, ya jiki fatan babu wani matsalar?" "Babu komai sai godiyar Allah." "To allahamdulillahi haka ake so, Allah ƙara lafiya." Ameen ta amsa dashi su kayi sallama ta kashe wayar tana kwanciya. Tun tana jin hiransu Aunti Rahma da Hasiya har bacci ya ɗauketa. "Tausayi take bani Aunti Rahma." Aunti Hasiya tace tana kallon Nuratu dake bacci. "Addu'a za muyi ta mata, Allah zai yaye mata komai." "Hakane Allah kawo mata sauƙi." Ameen Aunti Rahma ta amsa mata dashi tana shirin kwanciya ita ma dan ba zata koma gida ba ta bar yaranta da mai aikinta ta kula dasu, babansu yayi tafiya. Gidan bai rabu da mutane ba har ranar suna Baby taci sunan kakarta ta wajen uba, dangin mijin Aunti Hasiya sun yi murna sun haɗa mata kayan goyo duk da haihuwa na biyu ne. An yi taro lafiya an watse, ƙannenta sun zage sun mata aiki, Mami ma ta haɗa nata kayan ba laifi, Amma Jidda ma haka da ita ta tsaya kan komai. Haka Abban su ma ya aiko mata kuɗi masu yawa. Washegarin Aunti Rahma da Rukayya da Walida da Ameera suka tattare komai suka gyara mata gida kafin su watse dan an nema mata dattijuwa da zata zauna mata. *** Sati ɗaya da haka Nuratu suka fara final exam, ta maida hankali tana karatu sosai bangare ɗaya kuma tana ƙoƙarin ganin ta kawar da duk damuwar da yake damunta, ga maganinta da bata bari ya wuce ta tana sha akan lokaci. Hakan yanama Mami daɗi ganin tana ƙoƙarin kauda komai a ranta ta maida hankali kan karatunta. Sati biyu da kwanaki suka gama sai fatan samun sakamako mai kyau. Agajiye lis ta dawo gidan cike da murnar yau ta kare exam ɗinta. Cikin falon ta shiga ganin wanda yake zaune ya sa murmushin fuskarta ya ɗan gushe ta ɗan haɗa fuska. Shi ko ido kawai ya saka mata komai zai faru da Nuratu ba zai taɓa daina sonta ba, ba zata taɓa tashi daga Nuratun daya sani ba ta koma wata Nuratun da ƙaddara ta faɗa rayuwarta ba. "Ƴan makaranta." Yace mata ganin bata da niyar mishi magana. "Ina wuni Yaya Al-ameen." Ta faɗa ganin irin kallon da Mami ta watsa mata. Bata jira amsar shi ba ta wuce ɗakinta. Duk fa ta gane take taken su musamman shi da yasha furta mata yana sonta kuma ta amince tun kafin ƙaddara ta faɗa rayuwarta. Babu wani ɗa namiji a rayuwarta yanzu ko zuciyarta da zata iya so har ta aura. Matsalar rayuwarta da damuwar da take ciki ma kaɗai ya isheta balle wani namiji da sanadin shi duk wani farin cikin rayuwarta ya tarwatse. Ta tsani duk maza in ka cire mutane ukun da take ganin mutuncinsu suka taimaka rayuwarta sai shi da take ganin girmansa matsayin Yayanta. Babu aure a tsarin rayuwarta burinta tayi ta karatu ta gama ta samu aikin yi ta kula da maihaifiyar ta data sha wahala a kanta tun haihuwarta har girmanta, a dalilinta duk wani kadara nata ta siyar dan ta sama mata rayuwa mai kyau mai inganci, a dalilinta taƙi zaman aurenta, a dalilinta ta rabu da ƴaƴanta a dai-dai lokacin da suke buƙatar ta. Kwanciya tayi ta ƙi fita tana jiran ya tafi. .... "Bari in ƙirata ku gaisa." "A'a Mami ki barta in ta gama ta fito babu matsala zan jira ta." Yaya Al-ameen yace duk da yana son ganinta da sauri dan yana da gurin zuwa. Mami bata jira mai yake faɗa ba ta shiga ɗakin Nuratu. "Kin zo kin kwanta, kin san dai dan ke yake zuwa gidan nan." Rai Nuratu ta ƙara haɗawa. "Ni Mami kin san dai.." "Na san me? Tashi dalla kije. Al-ameen ɗin ne zaki fara nuna hali. In bakya son sauran maza ai shi baya cikin su saboda ya nuna miki so da kauna duk da abinda ya faru bai gujeki ba." "Kiyi hakuri Mami bari in je." Nuratu tace ta miƙe ta ɗauki mayafinta ta fita. A falon ta sameshi zaune ta zauna tana sake gaishesa. "Na takura miki ko na hanaki hutawa." Kai Nuratu ta girgiza cike da kunya dan tana jin nauyin shi ita kanta bata san lokutan da take mishi haka ba. So take ya gane yanzu da baya ba ɗaya bane. Wannan wata Nuratu ce da duniyarta ta canza mata. Ba zata iya cigaba da soyayya dashi ba, ƙaddara ta hana hakan baya gani ne. Koma waye yanzu bata da lokacin ɓata mishi lokaci domin aure baya tsarin rayuwarta. "Ƙanwata!" Yaya Al-ameen ya ƙira ta ganin ta faɗa tunanin da baya so. Murmushi yaƙe tayi tace. "Na'am Yaya Al-ameen. Ya gida dasu Amma Jidda?" "Lafiyarsu ƙalau, kina bani wahala ƙanwata har yanzu kin ƙi bani lokaci muyi magana. Karatu kullum shine uzirin ki, yanzu kuma gashi kuna exam in ma baku gama ba." Kan Nuratu ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta kasa bashi amsa dan yasha neman lokaci suyi maganar da bata da amsar shi. "Ke nake saurara ƙanwata. Zan wuce wani guri nace bari in shigo miki in miki zuwa bazata." "Za muyi magana ta waya ko WhatsApp." Amsar da ta iya bashi dan neman mafita ma kanta. Murmushi yayi yana miƙewa. "Shikenan Allah yasa in ga canji, zan wuce sai munyi magana." Itama miƙewa tayi tana bin bayan shi lokacin da ya nufi kofa. "Nagode ka gaishe da Amma dasu Walida." "Za suji." Yace ya fita kafin ta koma falon ta samu Mami ta fito zata wuce ɗakinta Mami ta bata umarnin ta zauna za suyi magana. Zama tayi ta san dai kullum maganar ɗaya ne ta bashi dama da ita kam bata jin zata iya haka. "Mai yasa kike bawa yaron nan wahala ne Nuratu, kina ganin dai shekarunsa sun kai aure har sun wuce shekara talatin da biyu, dalilin ki har yanzu ya kasa hakura yana binki kina mishi wulaƙanci." Idanun Nuratu cike da hawaye take duban Mami data haɗa rai. "To ni kam Mami na nuna mishi bana so ya yake so in mishi." "Auren ne ba za kiyi ba?" Kai Nuratu ta ɗaga hawayema zuba saman kuncinta. "Babu aure cikin tsarin rayuwata Mami, ba zan yi ba." "Saboda abin da ya faru?" Mami ta tambayeta itama da dauriya take ganin hawaye saman fuskar ƴartan da tasan dole in ta tuna abinda ya faru da ita sai ta zubar da hawaye balle kuma maganar aure. Ajiyar zuciya ta sauƙe. "Ba zan miki dole ba Nuratu, amma duk da abinda ya faru aure shine mutuncin ki, ki cire komai a ranki ki cigaba da rumgumar Ƙaddarar ki. Shi Al-ameen ɗin ya san abin da ya faru kuma ya yarda a haka zai aure ki to ki godewa Allah, kiyi ta addu'o'i in da alheri tsakanin ku Allah tabbatar muku in kuma babu Allah muku canji mai alheri. Share hawayen ki Noori." Murmushi Nuratu tayi jin maganar Mami na ƙarshe dan ta kwantar mata da hankali. Nasiha ta mata kamar kullum dan yadda da ƙaddara duk da itama Mami dauriya take. Sai lokacin Nuratu taji nutsuwa ta samu cin abinci taci ta wuce ɗakinta ta kwanta dan jiran ƙiran sallar magriba. Yaya Muhammad Al-ameen shi ya fara nuna mata menene so, ɗa namiji da ta fara saka sonshi cikin zuciyarta da rayuwar ta. Har yanzu tana son shi tana kaunar shi amma Ƙaddarar da ba zata iya goge shi ba ya rabata dashi. Ba auren shi ne ba za tayi ba abinda zata tarar gaba take tunani, balle bata tsammanin danginshi zasu barshi ya auri mace irinta, duk da Amma Jidda ta nuna itama tana son auren su. Tunani ta faɗa na abinda ya wuce. *** Shekaru biyu kenan da gama makarantar su Rahma da Hasiya suka shiga makarantar gaba da sakandare dan ci gaba. Suna aji biyu a lokacin samari suka dame su dan son aura ganin haka Alhaji Mamman ya ce su fitar da mazajen aure. A ciki suka zaɓa ko wanne ya turo aka saka ranar auren su. Daga lokacin Alhaji Mamman ya fara shirin aurar da yaranshi, kaya ya musu na gani na faɗa dan arziki shi sai bunƙasa yake. Mami sai a bakin Amma Jidda taji da yaranta, dan su Rahma har gidanta suka kawo samarin da zasu aura suka gaisheta. Ta yaba da tarbiyyarsu dukkansu biyu ta musu addu'a da samun zaman lafiya. Lokacin Rukayya tana ajin ƙarshe na sakandare, Walida da Nuratu suna aji biyu. Muhsin yana aji ɗaya a digiri nashi. Amma Jidda ta sake haihuwar ƴa mace Ameera. Biki saura sati yan uwa daga Gombe sun zo dangin Alhaji Mamman haka Amma Jidda tayi nata gayyar dan wasu ma sun ɗauka itace mahaifiyarsu. Anan Amma Jidda ta samu Mami ta roƙeta ta bar Nuratu ta zo gidan dan ayi biki da ita dan ta ɗinka mata har anko na aure da dinner party. Mami bata so ba amma ganin itama Nuratu tana so ta barta akan ranar wuni maza ta dawo dan tana guje mata haɗuwa da Abban ta gudun wulaƙanci ko zagi. Amma Jidda itama ta san nufin Mami dan haka ta mata alƙawarin ba abinda zai faru. Nuratu a gidan Alhaji Mamman. Like. Comments. Share.
  • Zubairu Garba Dalau
Previous
Next

Zauruka

  • HASKE WRITERS ASSOCIATION
    s
    K'ungiyar Marubuta Don Wayar Dakan Al'umma
Previous
Next
© 2021 Bakandamiya  -  About Us  -  Terms  -  Privacy  -  Advertise  -  Support Center  -  Mobile Apps  -  Contact Us
  • Facebook
  • Twitter
  • Linkedin
  • Youtube
  • Pinterest
  • Instagram