Kallon ta Abu takeyi, in da wani yace zata taba kallon Dije da irin wannan idanuwan zata karyata, saboda Dije ce, Dije da ko lokacin da Datti ya auro ta da kuruciya bata ga alamar hauka a tattare da ita ba. Ashe dai hauka bashi da alaka da shekaru? Ashe h...
Tsaye yake ba don babu wajen zama ba, idan ya juya a cikin gidan da zai iya kira da nashi yanzun sai yaji shi a cikin wata duniya ta daban. Duniyar da kamar idanuwa ya rufe ya bude ga ganta a ciki. Nisan daya hangone ya hade da shi kamar almara.
Zaman da Asma'u ta yi don chat ɗin bai mata daɗi ba, kasantuwar jikinta bai iya ɗaukar sanyin da ke ratsa ƙafufunta yana shiga cikin jikinta, naɗe kafafuwan ta yi a kan kujerar one seater da take zaune, lokaci ɗaya kuma ta lulluɓe kaf jikinta da marron Hi...
A shekarar 2008 wani babban kamfanin zuba hannun jari da harkokin banki a Amurka mai suna Lehman Brothers ya durƙushe, lokacin kuwa yayi kimanin shekaru 158 yana aiki. An kafa bankin ne a shekarar 1850 kuma sannu a hankali ya zama wani ginshikin haɓaka ta...
Ruwan da Julde yayi nufin hadiyewa ne yaji ya zarce yana bin wata kofar da ba hanyar shi ba, ya kuma toshe masa wucewar iska, abinda ya saka shi fara tari babu kakkautawa a lokaci daya yana kokarin ganin numfashin shi ya saitu, ruwan ya kara sha yana jan ...