Wa’alaykumussalam
To dan’uwa hadisi ya zo daga Umar- Allah ya yarda da shi- cewa: “Annabi s.a.w. idan ya daga hannayansa ya yi addu’a ba ya mayar da su, har sai ya shafa su a fuskarsa” Sunanu Attirmizi : 3386.
Wannan... moreWa’alaykumussalam
To dan’uwa hadisi ya zo daga Umar- Allah ya yarda da shi- cewa: “Annabi s.a.w. idan ya daga hannayansa ya yi addu’a ba ya mayar da su, har sai ya shafa su a fuskarsa” Sunanu Attirmizi : 3386.
Wannan hadisin ya zo da hanyoyi masu yawa, saidai dukkansu suna da rauni, wannan yasa malaman hadisi suka yi sabani game da ingancin shi, Ibnu Hajara ya kyautata shi, saboda ya zo ta hanyoyi da yawa, kamar yadda ya bayyana haka a Bulugul-maraam a hadisi mai lamba ta : 1345.
Akwai wadanda suka raunana shi saboda suna ganin hanyoyin da yazo da su masu yawa, ba su kai su karfafe shi ya zama Hasan ba, wannan shi ne ra’ayin Ibnu Taimiyya kamar yadda ya bayyana haka a Majmu’ul fataawaa 22\509, haka Albani a Silsila Sahiha 2\146.
Malaman Fiqhu sun yi sabani game da shafar fuska bayan addu’a, wasu sun tafi akan mustabbancinsa, saboda sun gamsu da kyautatawar da Ibnu-hajar ya yiwa hadisin, kamar Ibnu Bazz a daya daga cikin fatawoyinsa, akwai... less
Assalamu alaikum inayiwa malan fatan alkhairi, tambayata iyace :- Azumi uku na tsakiyar wata wanda ake kira " Ayyaamul beed " na watan Rajab. To ya hallata a muslunci?.
Amsa
Wa alaikum assalam,
Ya tabbata a cikin hadisin Tirmizi mai lamba ta: 761: Annabi s.a.w. ya cewa Abu-zarrin idan za ka yi azumi, to ka azumci ranar sha uku da ranar sha hudu da sha biyar daga kowanne wata, watan Rajab Daya ne dağa cikin watannin musulunci za'a iya azumin da ya tabbata a ragowar watanni a cikinsa, saidai kawai watan bai kebanta da Wata falala ba.
Tambaya
Assalamu Alaikum... moreSHAFA FUSKA BAYAN KAMMALA ADDU'A
Tambaya
Assalamu Alaikum
Malam menene hukuncin shafa hannu a fuska bayan gama addu'a.
Amsa:
Wa'alaykumussalam,
To dan'uwa hadisi ya zo daga Umar- Allah ya yarda da shi- cewa: "Annabi s.a.w. idan ya daga hannayansa ya yi addu'a ba ya mayar da su, har sai ya shafa su a fuskarsa" Sunanu Attirmizi : 3386.
Wannan hadisin ya zo da hanyoyi masu yawa, saidai dukkansu suna da rauni, wannan yasa malaman hadisi suka yi sabani game da ingancin shi, Ibnu Hajara ya kyautata shi, saboda ya zo ta hanyoyi da yawa, kamar yadda ya bayyana haka a Bulugul-maraam a hadisi mai lamba ta : 1345.
Akwai wadanda suka raunana shi saboda suna ganin hanyoyin da yazo da su masu yawa, ba su kai su karfafe shi ya zama Hasan ba, wannan shi ne ra'ayin Ibnu Taimiyya kamar yadda ya bayyana haka a Majmu'ul fataawaa 229, haka Albani a Silsila Sahiha 26.
Malaman Fiqhu sun yi sabani game da shafar fuska bayan addu'a, wasu sun tafi akan mustabbancinsa, saboda sun gamsu da kyautatawar da Ibnu-hajar ya yiwa hadisin, kamar Ibnu Bazz a daya daga cikin fatawoyinsa, akwai kuma wadanda suka tafi akan cewa ba za'a ayi ba, saboda rashin ingancin hadisan da suka zo akan haka.
Abin da na fahimta a wannan mas'alar shi ne ba za'a aibanta wanda ya shafa fuskarsa ba bayan addu'a, tunda yana da magabata .
Assalamu alaikum, Malam mutum ne yana da chemist yana sayar da magunguna. Ya halatta ya sayar da maganin qarfin maza ga wanda yake so ya biya bukatar iyalinsa? Allah ya qarawa Dr. Jameel imani da lafiya da ilimi, gaskiya muna amfana
Amsa:
Wa alaikum assalam, In har an jarraba an samu yana amfani kuma likitoci sun tabbatar ba ya cutarwa ya halatta a siyar da shi don aure ya gyaru, a kara samun donkon soyayya, saboda saduwa tsakanin ma'aurata turke ne tsayayye, wanda in ya goce aure ba zai tafi saiti ba, yana daga cikin ka'idojin Sharia duk harkokin mutane na yau da kullum wadanda ba ibada ba ne sun halatta, in har ba'a samu nassin da ya hana ba.
Addinin musuluci ya haramta duk abin da yake cutarwa, kamar yadda nassoshi masu dinbin yawa suka tabbatar, wannan yasa duk maganin da likitanci ya tabbatar cutarsa ta fi amfaninsa yawa ya wajaba a guje shi, Tunkude cuta ginshike ne a cikin addinin musulunci.
Assalamu alaikum. Malam menene hukuncin 'yan matan da suke bada hotunansu ga tsofafi don su nema musu mijin aure ?
Amsa
Wa alaikum assalam Addinin musulunci ya haramta kallo zuwa ga matar da ba muharrama ba, sai in akwai lalura, amma ya halatta ka kalli mace, idan kana so ka aure ta, kamar yadda ya zo a cikin hadisi, inda Annabi s.a.w. yake cewa : "Idan dayanku yana neman aure, to in ya sami damar kallon abin da zai kira shi zuwa aurenta, to ya aikata hakan" ABU DAWUD.
Malamai sun yi sabani akan wurin da ya kamata mutum ya kalla a jikin mace lokacin da ya je neman aure :
1. Akwai wadanda suka ce zai kalli fuska da tafin hannu ne kawai.
2. Wasu malaman sun tafi akan cewa : zai kalleta a kayan da take sawa a cikin gida, ta fuskace shi ya kalle ta, sannan ta juya baya ya kalleta.
Wannan ra'ayin shi ne ya fi dacewa, saboda ta haka mutum zai san yanayin matar da zai aura.
Ta hanyar bayanan da suka gabata, za mu iya fahimtar cewa aikin dalilin aure ya hallata, amma da sharuda, ga wasu daga ciki :
1. Ya zama hoton ya fito da asalin fuskar matar, bai KWARZANTA ta ba, ta yadda za'a iya yaudarar namijin, ko a rude shi.
2. Ya zama wacce za'a bawa hoton mai amana ce, ta yadda ba za ta nunawa wanda ba shi da nufin aure ba, saboda asali ya haramta ayi kallo zuwa ga matar da ba muharrama ba, sai in akwai lalura, sai ga wanda yake nufin aurarta, wannnan yana nuna cewa, bai halatta asa irin wannan hoton na neman aure ba , a face book, ko a jarida.
3. Ka da hoton ya kun shi fito da tsaraici, ya wajaba a tsaya a iya inda shari'a ta bada umarni.
4. Zai fi dacewa ace mace ce za ta yi dalilin aure, saboda in namiji ne, zai iya fitinuwa da hotunan da yake gani, sai barna ta auku, don haka ita ma macen ya wajaba ta ji tsoron Allah a cikin aikinta.
Shafin Dr. Jamilu Zarewa INA SHIRIN YIN AURE, SAI TSOHON MIJINA YA CE DAMA CAN YA YI MIN... moreINA SHIRIN YIN AURE, SAI TSOHON MIJINA YA CE DAMA CAN YA YI MIN KOME
Tambaya:
Malam mijina ya sake ni bayan na kammala idda, saura kwana uku na yi aure sai ya zo ya ce dama ya yi min kome, amma bai sanar da ni ba ne, don Allah malam yana da hakki, ko kuma na kyale shi na yi aurena? saboda gaskiya ina son wancan, amma kuma ba na so na sabawa sharia?
Amsa:
To 'yar'uwa tabbas miji yana da damar da zai yiwa matarsa kome mutukar tana cikin idda, kamar yadda aya ta :228, a suratul bakara take nuni zuwa hakan, Amma mutukar bai yi mata kome ba har ta kammala idda to ba shi da dama akan ta, amma zai iya shiga cikin manema.
Idan ya yi da'awar cewa ya yi mata kome tun tana idda, amma bai sanar mata ba ne sai bayan ta kammala idda, to ba za'a gaskata shi ba, sai ya kawo shaidu, wadanda za su tabbatar da faruwar hakan.
Yana daga cikin ka'idojin sharia toshe duk hanyar da za ta kai zuwa barna, idan aka bar abin a bude, wanda yake kin matarsa, zai iya mata mugunta, ta wannan hanyar, hakan yasa malamai suka ce sai ya kawo shaidu za'a gaskata shi, idan kuma bai kawo ba za ta iya zuwa ta yi auranta.
Saidai wasu malaman suna cewa : idan har matar ta gaskata shi, to ya isa, ko da bai kawo shaidu ba.
Slm. malam ko akwai nassi da yake nuni akan halarcin yin walimar saukar alqur'ani?
Amsa
To dan'uwa malamai suna cewa : Yin walimar saukar Alqur'ani ta kasu kashi biyu:
1. Wanda ya sauke Alquir'ani ya yi walima saboda godiya ga Allah, wannan kam ya halatta, saboda nassoshin da suka zo wadanda suke kwadaitarwa akan godewa Allah akan ni'imominsa.
2. Yin walimar saboda riya cewa ibada ce mai zaman kanta, wannan kam bidi'a ne tun da ba'a samu Annabi ﷺ da sahabbansa sun yi ba, don haka yana da kyau wanda ya yi walima ya bayyanawa mutane cewa ya yi ne don godewa Allah, ba wai don kasancewar hakan ibada ce mai zaman kanta ba.
Amma abin da aka rawaito cewa: Umar R.A ya yanka rakumi bayan ya gama haddace & kiyaye suratul-bakara, to wasu malaman hadisin sun raunana shi kamar Ibnu-kathir A Musnadul-farouk 21, saboda a cikin sanadinsa akwai Abu-bilal Al-ashhary, wanda Dara-kudni ya raunana.
Don neman Karin bayani duba fatawaa Allajna Adda'imah 28.
Ya kamata a ce na yi istibra'i kafin na yi aure, amma ban yi ba, har na yi aure, yanzu haka ina jini na farko ban yi tsarki ba, amma ba da wanda na aikata laifin na yi aure ba. Ya ingancin aure na? Gani nake kamar babu auren.
AMSA:
To farko dai ina miki wasici da tsoron Allah saboda zunubin da kika aikata, amma game da aure, to aurenki ya yi, saidai yinsa bayan istibra'i shi ne ya fi, sannan ya wajaba mutukar kin san kina da ciki to bai halatta ki bawa sabon mijinki dama ya take ki ba, saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: "Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa" Abu-dawud : 1847.
Don haka ya wajaba a gare ki ki yi stibra'i kafin mijinki ya sadu da ke, sannan istibra'i jini daya ne , idan kuma har kin dauki ciki, kafin ki yi istibra'i, in kin haihu kafin wata shida to ba dansa ba ne, amma in har kin haihu bayan wata shida daga fara saduwarku, to dansa ne, mutukar ba'a samu shaidar da take nuna kina da ciki ba, tun kafin ku fara saduwa .
Don neman Karin bayani duba : Al-mugni na Ibnu kudaamah 8.
Assalamu alaikum malam, ina tambaya ne akan yiwa yaro kaciya shekara nawa ya kamata ayi masa?
Amsa
Wa alaikumus salam,
To malam babu wani hadisi ingantacce wanda ya kayyade wani lokaci da za'a yiwa yaro kaciya, saidai malamai suna cewa : babbar manufar yin kaciya ita ce katanguwa daga najasar da za ta iya makalewa a al'aura, wannan ya sa ya wajaba a yiwa yaro kaciya dab da balagarsa, saboda idan ya balaga shari'a za ta hau kan shi kuma tsarkinsa ba zai cika ba, in ba'a yi masa kaciyar ba, daga cikin ka'aidojin malamai shi ne duk abin da wajibi ba zai cika ba sai da shi, to shi ma ya zama wajibi, amma mustahabbi ne ayi masa, tun yana dankarami, saidai wasu malaman sun karhanta yin kaciya ranar 7\ga haihuwa, saboda akwai kamanceceniya da yahudawa.
Don neman karin bayani duba Fathul-bary 10/349.
Assalamu alaikum, Allah ya jikan Malam, shin ya halatta na biyawa mahaifiyata aikin hajji kafin naje?
Amsa
Wa alaikum assalam, Mutukar babu halin da za ka biya muku ku biyu, to abin da yake daidai shi ne ka fara zuwa kafin ita, saboda kai ya wajaba akanka, ita kuwa bai wajaba akanta ba, tun da ba ta da hali.
Allah madaukakin Sarki ya wajabta aikin hajji ne ga wanda ya samu iko a suratu Al'imraan aya ta (97).
Fifita wani da gabatar da shi akanka wajan biyayya ga Allah Makaruhi ne kamar yadda Suyudi ya yi bayanin wannan Ka'idar a littafinsa "Al'ashbahu wannaza'ir"
الإيثار في القرب مكروه وفي غيره محبوب.
Makaruhi ne ka tura wani sahun farko, kai ka tsaya ana biyu, amma a wajan sanya sutura da Ciyarwa ya abin so ne ka FIFITA waninka, shi yasa Allah ya yabi mutanen Madina a suratul Hashr akan haka.
Shafin Dr. Jamilu Zarewa → Filin Fatawa: MATAR DA BA TA DA AURE, ZA TA IYA SANYA TURARE TA FITA... moreMATAR DA BA TA DA AURE, ZA TA IYA SANYA TURARE TA FITA UNGUWA?
Tambaya:
Assalam malam muna san karin bayani akansa turare gamata sufita, wani malami yace wadda ba matar aure ba zata iya sawa?
Amsa:
Wa'alaikum assalam, To 'yar'uwa ya HARAMTA ga mace Baliga ta sanya turare, ta fita unguwaa, saboda fadin Annabi S.A.W : "Duk matar da ta sanya turare, ta wuce ta wani majalisi, to ta zama mazinaciya, kamar yadda Abu-dawud ya rawaito. A wani hadisin kuma yana cewa: "Duk matar da ta sanya turare, kar ta halarci sallar Isha tare da mu.
Nassoshin da suka gabata suna haramta sanya turare ga mace balagaggiya idan za ta fita, kuma ba su bambance tsakanin matar aure ba da budurwa ko bazawara, wannan sai ya nuna gamewarsu ga dukkan mata wadanda sharia ta hau kansu, tun da ba'a samu abin da ya kebance wasu nau'i ba, sannan kuma an haramta sanya turaren ne: saboda yana kaiwa zuwa tada sha'awar Maza, wannan kuma baya bambanta tsakanin matar aure da wacce ba ta yi ba
Amma za ta iya sanyawa ta zauna a gida mijinta ya ji kamshi, in ta yi hakan za ta samu lada, haka ma budurwa, za ta iya sanyawa a tsakanin 'yan'uwanta mata, ko gaban muharramanta wadanda ta san ba za su yi sha'awarta ba
Malam Mutum ne ya bar kakansa da mahaifiyarsa da ]an’uwansa da suka ha]a uba, yaya za’a raba... more8. Tambaya
Malam Mutum ne ya bar kakansa da mahaifiyarsa da ]an’uwansa da suka ha]a uba, yaya za’a raba gadon?
Amsa:
To ]an’uwa za'a kasa dukiyar kashi uku, a bawa mahaifiyarsa ]aya bisa ukun abin da ya bari, sai a bawa kakansa ]aya bisa uku, ]an’uwansa shi ma sai a ba shi ragowar ]aya bisa ukun, Allah ne Mafi sani.
Mutum ne ya rasu ya bar mahaifinsa da mahaifiyarsa da }annansa wa]anda suke uwa ]aya uba ]aya da wa]anda suke uba ]aya, Malam yaya za’a raba dukiyar da a ka bar... more7. Tambaya
Mutum ne ya rasu ya bar mahaifinsa da mahaifiyarsa da }annansa wa]anda suke uwa ]aya uba ]aya da wa]anda suke uba ]aya, Malam yaya za’a raba dukiyar da a ka bar musu?
Amsa:
To ]an’uwa, za’a raba dukiyar kashi shida, a bawa mahaifiya kashi ]aya, sai a bawa uba ragowar kashi biyar ]in, }anne ba su da komai saboda uba ya katange su, Allah ne Mafi sani.
Amsawa:
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
2715
December 7, 2020
Shafin Dr. Jamilu Zarewa IDAN AKA YI KISAN KUSKURE, WA ZAI BIYA... moreIDAN AKA YI KISAN KUSKURE, WA ZAI BIYA DIYYA?
Tambaya
Assalamu Alaikum, Dr. ina da tambaya wai lalle ne idan mutum ya kade wani ya mutu idan za'a biya diyya wai duk kudinsa ba'a yarda ya biya shi kadai ba sai anbi dangi an harhado kudin sannan za'a biya.
Amsa
Wa alaikum assalam,
Mutukar diyyar kisan kuskure ne, to dangi na wajan uba su ne za su biya, saboda hakan zai sa şu hana wawayen cikinsu sakaci da yin abin da bai kamata ba, sannan dangin Wanda aka kashe musibar za ta musu sauki, sannan akwai koyawa mutane taimakekeniya a ciki.
Amma Idan kisan ganganci ne to diyyar za ta kasance a dukiyar mai laifin, in har dangin Wanda aka kashe sun yarda a biya diyya. Don neman karin bayani Duba : Makasidussharia Indassa'ady na Dr. Jamilu Zarewa shafi na: 303.
Tambaya:... moreMACE ZA TA IYA DAGA MURYARTA DA KARATUN SALLAH?
Tambaya:
Assalamu alaikum Malam barka da yau, tambaya zan yi malam. Shin ya halatta mace ta daga murya a cikin karatun sallah kuwa?
Amsa:
Wa alaikum assalam To dan'uwa ya halatta a gare ta ta daga muryarta yayin karatun alqur'ani a sallah, sai in akwai wanda ba muharrami ba a kusa, to sai ta yi kasa da muryarta, don kar ya fitinu.
Wasu malaman sun haramta mata bayyana karatu, in ta ji tsoran fitina, saboda Annabi s.a.w. ya umarci mata da yin tafi a sallah, lokacin da liman ya yi rafkannuwa, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta :1145, sai suka fahimci cewa: Annabi ya umarce su, su yi tafi ne, don kar wadanda ba muharramai ba, su ji sautinta.
Mace tana daukar hukuncin namiji a cikin dukkan hukunce-hukuncen shari'a, in har ba'a samu nassin da ya kebance ta ba, wannan ya sa za ta bayyana karatu a wuraren da yake bayyanawa, in ba'a ji tsoron fitina ba .
Shafin Dr. Jamilu Zarewa YA YA KAMATA NAYI DA RIBAR BANKIN DA NA... moreYA YA KAMATA NAYI DA RIBAR BANKIN DA NA AMSA?
Tambaya
Assalamu alaikum malam Menene ra'ayin malaman Sunna akan kudin da banki suke karawa mutane a cikin Saving account? Ya yakamata ayi amfani dasu? Allah ya karemu daga aikata kuskure.
Amsa
Wa'alaikum assalam Farko dai ya haramta ga musulmi ya bude account din da za'a dinga saka masa kudin ruwa a ciki, saboda Allah ya haramta cin riba ya kuma yi shirin yaki da Wanda bai daina ci ba à cikin aya ta 275 a Suratul Bakara da ayoyin da suka zo bayanta.
Annabi ﷺ ya la'anci mai cin riba da wanda ya rubutata da wanda aka wakilta da wanda ya yi shaida akanta. Kamar yadda Tirmizi ya rawaito a hadisi ingantacce.
Idan mutum ya amshi Interest din Banki to ya wajaba ya tuba ga Allah da niyyar ba zai sake amsa ba, tun da Allah ya Hana.
A zance mafi inganci zai iya amfani da kudin wajan yin aikin da zai amfani jama'a kamar gina Asibitoci ko kwatar da ruwa zai wuce ko kuma hanyoyin da mutane za su bi su wala, saidai ba shi da ladan wannan aikin da ya yi, saboda ba dukiyarsa ba ce.
Wannan ita ce maganar manyan malaman musulunci na wannan zamanin kamar Sheik Ibnu Bazz da sauransu.
Wannan zaure ne da zai kawo muku muhimman FATAWOWIN RABON GADO GUDA 212 wadanda aka tattaro su daga amsoshin tambayoyin da Dr. Jamilu Yusuf Zarewa ya amsa a kafofin sada zumunta (Social Media).