>>Previous page
Tsammanin Abbas dariyar jin daɗi ce Asma'u ke yi, wanda kuma haka yake fata ya ga ya yi mata abin da zai faranta mata zuciya, tambayarta ya yi "Yau ne sunan; ko yaushe?", ta ce "Gobe ne", d'an nazari ya yi kafin ya ce "Aaa! Ba gobe ...
"Ban damu da duk wani sharad'i naka ba, in dai bu'katata zata biya", cike da gadara ta 'karashe maganar, tare da yi mashi kallo mai cike da tsangwama. Murmushin da ya fi kukan da yake ciwo ya yi,...
Wani irin masifaffen son shi ne ya cigaba da azalzalarta a zuciya, sake sumbatar hoton ta yi kafin ta yi save. cigaba da gamsar da zuciyarta ta yi da kallonsa, a fili ta ce "Mutumin nan ya had'u", a rant...
A wannan karon ma, Asma’u bata ji me ya ce ba saboda komai nata ya d’auke in banda bugun zuciyarta dake ta ‘karuwa. A tsammanin Abbas miskilancinta ne ya motsa, don haka ya zuge bakins...
"Wato titsiye ni zaki yi ko?", bakin Asma'u dauke da dariya ta jefo ma Khadijah wannan tambaya, kai Khadijah ta girgiza "A'a waace ni, kawai dai dan in san irin shawarar da zan baki wadda zata fisshe ki ne."
'Dan rausaya kai Asma'u ta yi "Auho!". Shiru ...
Idanun likitan cikin nata ya bata amsa da "Yeah, kina da juna biyu Madam."
Tamkar wadda aka tsikara ta miƙe gami da dafe ƙirjinta dake luguden faɗuwa ta ce "Na shiga uku ni Asma'u", a yadda ta ƙarashe maganar kai ka ce faɗowa ƙwayoyin idanunta zasu yi ...
Da akace komai na da lokacin shi, a cikin lissafin mutuwa, aure, haihuwa da arziki sune sama. Komai sai yabi bayansu har suna danne wasu abubuwan, a shafuka na kwakwalwar Julde yanda lokaci ya kasance a bangarenshi saiya sha shi tunanin ba zai taba nuna m...
Kallon ta Abbas ya cigaba da yi, lokaci ɗaya kuma yana murmushin da shi kansa ya san yaƙe ne, don ko kaɗan bai ji daɗin yadda ta yi ƙerere a gabansa tamkar sandar rake ba, sai dai ya danne rashin jin daɗin saboda ya fahimci ɗanyen kan yarinta na ɗibar ta,...
Yelwa take kallo, idanuwanta a rufe, Saratu da take gabanta tana mata kwalliya, ta diga mata kwallin daya fara tun daga goshinta zuwa karan hancinta, da alama digon zai dire ne har habarta cikin kwalliyar su ta fulani, bakinta ma a zane yake da bakin kwal...
Zaman da Asma'u ta yi don chat ɗin bai mata daɗi ba, kasantuwar jikinta bai iya ɗaukar sanyin da ke ratsa ƙafufunta yana shiga cikin jikinta, naɗe kafafuwan ta yi a kan kujerar one seater da take zaune, lokaci ɗaya kuma ta lulluɓe kaf jikinta da marron Hi...
Kashedin da Babanta yayi mata yana dawo mata yana kuma saka zuciyar ta dokawa a cikin kirjinta a lokacin da take tsaye tare da Dattin, yana mata murmushin shi da zaka hango kyallin shi har cikin idanuwan shi ...
Aisha Sarkinyaki: Slm aunty hadiza ya gida ya aiki? Allah ya taimaka. Dan Allah muna jiran update din cikin baure mun ji ki shiru, Allah yasa lfy. Nagode
Tun bayan da Abbas ya taya Asma'u kimtsa jikinta take kwance a yalwataccen ƙirjinsa tamkar ƙaramar yarinya, cike da so gami da tausayin ta ya kai bakinsa a masarrafan sautinta, sassauta murya ya yi sannan ya ce "Ba zan hana ki kuka ba Asmy, amma don Allah...
Yau da gobe abin tsoro, ba a yanda ranaku suke karewa zuwa daren da yake wayewa da safiya ba, ba kuma a yanda kowacce rana take kara kusanta dan Adam da kabari ba, rashin tabbas din da yake cikin yau da gobe yafi komai tsorata Dije da dan ta ya makalawa D...
Kallon ta Abu takeyi, in da wani yace zata taba kallon Dije da irin wannan idanuwan zata karyata, saboda Dije ce, Dije da ko lokacin da Datti ya auro ta da kuruciya bata ga alamar hauka a tattare da ita ba. Ashe dai hauka bashi da alaka da shekaru? Ashe h...
Dalilan da suka hanata yi ma maza kudin goro akan cewa basu da adalci, zuciyoyin da suke kirjin su bangaren tausayi na wasu da yawa a mace yake kadan ne, mahaifinta baya cikin wannan dalilan, saboda shima ya kalle ta yace
Cike da kaɗuwa nake bitar takardar da na kasa gazgata baƙin saƙon da take ɗauke da shi. Jiki a mace na juya akalar ganina zuwa ga mijina da muke tsaye a tsakar gida, "Menene haka Aminu?", a taƙaice ya ce "Saki biyu ne". Haƙiƙa zuciyata ta jijjiga bisa ga ...