A makalar da ta gabata na dabarun rubutun labari, mun duba musamman ma’anar jigo da yadda ake samar da jigo. A yau za mu duba yadda ake girka jigo ya koma labari.
Da yake mun yi maganar girki, yana da kyau mu yi misali da wani nau'in abincin na Bah...
A makalar da ta gabata na dabarun rubutun labari, mun duba musamman ma’anar jigo da yadda ake samar da jigo. A yau za mu duba yadda ake girka jigo ya koma labari.
Da yake mun yi maganar girki, yana da kyau mu yi misali da wani nau'in abincin na Bah...
Jibrin Adamu Rano: Ina marubuta? TA YAYA MARUBUCI ZAI KAIFAFA FASAHARSA?
Ku fito mu yi washin... moreIna marubuta? TA YAYA MARUBUCI ZAI KAIFAFA FASAHARSA?
Ku fito mu yi washin ƙwaƙwalwa.🤗
Kamar Yadda @Yusuf Gumel ya faɗa ɗaya daga cikin hanyoyin kaifafa fasahar marubuci akwai yin karatu, amma wanne irin karatun? Irin karatun da yake kaifafa fasaha shi ne yin karatu irin na marubuci, ta yadda za ka riƙa yin karatu ko kallo kana ba wa kanka wani aiki a cikin ƙwaƙwalwarka.
Misali:
Idan ina karanta labarin marubuci, ina yi ne ina auna basirar marubucin. Duk gaɓar da na karanta kafin na tafi gaɓa ta gaba sai na tsaya na fara hakaito abin da nake zaton marubucin zai iya saƙawa a gaɓa ta gaba. A cikin raina zan ce, na san kaza da kaza da kaza zai yi a gaɓa ta gaba cikin rubutun.
Idan har na karanta gaɓar na ga ya dace da irin hasashena, to ina ba wa marubucin maki. Haka ma idan na karanta aka samu saɓanin hasashena ina ƙara masa maki ɗoriya a kan na farkon🙅♂️
Akwai gaɓar da na manta a nan. Tana iya yuwuwa fasahar marubuci ta ci karo da hasashenka, amma kuma koda za a ɗora tunanin naku biyu a sikeli naka yana iya rinjayar nasa, ta fuskar dacewa da zahiri da kuma abin da zai iya faruwa.
Marubuci yana samun alfanu sosai, da kaifafar fasaha idan har yana yin irin wannan karatun.
*Na farko dai idan ka iya hakaito abin da yake zuciyar wani marubucin ba tare da ka karanta abin da ya rubuta ba, hakan yana nuna cewa kana da hikima kwatankwacin irin ta marubucin.
*Na biyu kuma idan aka samu akasi ba ka iya hakaito inda ya dosa a daidai ba, to idan ka ga nasa salon ya zama ka ƙaru da hanyoyi biyu kenan, hanyarka da ka yi tunanin ita za ta faru, da kuma hanyar shi marubucin.
Hakan sosai yana taimakawa wajen kaifafa tunanin marubuci, *karatu irin na marubuta* da kuma *kallo irin na marubuta*.
Wanda yake ba marubuci ba shi ne yake yin karatu ko kallo na nishaɗi, amma shi marubuci kamata ya yi karatu da kallonsa duk su kasance ta sigar da zai ƙara kaifafa hangen nesansa.
Gaf da azumi mun yi wata semina ta marubuta, a wajen seminar an ba mu wani aiki na auna fahimta. Irin wannan aikin ni ma zan bayar yanzu.
Ina fata za a ba da haɗinkai wajen jarrabawa. Ina so kowanne marubuci ya jarraba samar da mafita ya turo mini da amsa ta pc ɗina, idan ya so daga baya sai mu zo nan gidan mu baje a faifai mu ga yanayin hangen kowa a cikinmu.
Sai ku zaɓi adadin tsahon lokacin da kuke so a ɗiba.
Bayan ruwa da aka tafka cikin dare kamar da bakin ƙwarya, an wayi gari irin iskar da ke haɗe da ruwan ta kayar da wata rusheshiyar bishiyar kuka.
Dayawan mutane ba su ji daɗin faɗuwar bishiyar ba, domin kuwa bishiyar irin tsofaffin bishiyun nan ce dasawar kaka da kakanni. Bugu da ƙari a lokacin da ta tara ganye mutane da suke wucewa a gefen titin da take, sukan samu mafakar rana su tsaya su tari mota ko adaidaita a ƙasanta.
Cikin hikima ta Ubangiji, da bishiyar ta tashi faɗuwa kawai sai ta faɗa a tsakiyar titi mafi zirga-zirga na garin. Kasancewar bishiyar rusheshiya shi ya jawo ta rufe titin gabaɗaya ta yadda bata bar hanya koda ta keke ba. Hatta mutum idan zai wuce sai dai ya haura ta saman bishiyar, sai kuma masu ƙarfi cikin masu kekuna da su ma suke ɗaga shi a hannu su haura ta saman bishiyar su wuce.
Ƙarin dalilin matsala cikin matsaltsalun da faɗuwar bishiyar ya haifar shi ne kasancewar garin ya waye ne a ranar litinin da Bahaushe yake yi mata kirari da 'litinin ranar aiki', aka ce wai ko bature yana tsoron litinin saboda ayukan da take zuwa da su. Shi ya sa kafin wani lokaci mai tsayi titin ya cika maƙil, ta kowanne ɓangare ababen hawa ne reras.
Da ma'aikata da suka fito aiki, da 'yankasuwa da za su tafi kasuwanni da shagunansu, da masu aikin hannu da za su tafi wajen ayyukansu, da ɗalibai da za su tafi makarantunsu, da sauran dukkan masu buƙatu da suka fito, su suka taru suka cushe hanyar aka tsaya cirko-cirko kowa yana tunanin mafitar da aka rasa.
Wasu masu girman uziri kuwa dama tuni sun faffaka motocin nasu a gefen titi sun tafi uzirinsu, yayin da wasu cikin ma'aikata har suka fara bacci kafin a samu a ɗauke bishiyar.
A matsayinku na marubuta ku ba wa waɗannan mutanen mafita ta yadda za su kawar da bishiyar, amma wajen samar da mafitar ku kula da waɗannan abubuwa.
*Bishiyar tana da girman da mutum ba zai iya ɗaga ta ba sai dai ko irin babbar motar nan mai ƙugiya.
*Ita ma mota mai ƙugiyar ba za ta iya shiga can wajen bishiyar ba saboda yadda kan titin babu masaka tsinke, ta ko'ina motoci sun cike shi fal.
Akwai mafita iri-iri na yadda za a kawar da bishiyar, amma ina da yaƙinin zai yi matuƙar wuya a samu wanda zai bayar da mafita iri ɗaya sak da ainahin abin da ya faru a labarin. Don haka a auna fahimta, a turo da mafitar ta lambar wayata 08132505026 ta whatsapp.
Domin ire-iren waɗannan da sauran dabarun rubutu, akwai zaure na musamman. less
Umar1984
اللهم صل علي محمد وعلي آل محمد كما صليت علي إبراهيم وعلي آل إبراهيم في العالمين إنك حميد مجيد . وبارك علي محمد وعلي آل محمد كما باركت علي إبراهيم وعلي آل إبراهيم في العالمين إنك حميد مجيد.
Bala Danfulani
Na duba iyakar iyawata na rasa inda rubutun yake. Matsalar na ga duk wani motsi da mutum ya yi, kama daga 'Like' da 'Comment' da kowane abu da ka taba, to yana zaune a kan 'Profile' ne, saboda haka yana matukar wahala ga mutum ya bibiyi 'posting' idan ya shude.
Nana Aicha Hamissou → MARUBUTA:
Assalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu. In sha Allah shirin yau sai dare kasancewar na koma makaranta, yanzu haka ma ina cikin aji. Na gode sai an jiman ku.
Mukhtar Musa Karami Abu Hisham
Na gaida Jamilu mai wakar Bakandamiya,
Lallai farar aniya dole mu kirata da Laya
Wakar ga tayi abin a duba sannan a biya,
Zan so ace a rera a taron ...
Mukhtar Musa Karami Abu Hisham
Na gaida Jamilu mai wakar Bakandamiya,
Lallai farar aniya dole mu kirata da Laya
Wakar ga tayi abin a duba sannan a biya,
Zan so ace a rera a taron ...
🍳 *_Mata ce su kayi sallama da Mijinta akan cewa za taje kauye dubo Mamanta kuma kwana biyu za tay_*i. *_Ta gama kwanakinta ta dawo, Mijin yace ya mai jiki? Sai tasa kuka wai jikin yayi tsanani amma zata koma takara... moreSadik
*_ME YAKAMATA TAYI?_*
🍳 *_Mata ce su kayi sallama da Mijinta akan cewa za taje kauye dubo Mamanta kuma kwana biyu za tay_*i. *_Ta gama kwanakinta ta dawo, Mijin yace ya mai jiki? Sai tasa kuka wai jikin yayi tsanani amma zata koma takara dubata wani... more*_ME YAKAMATA TAYI?_*
🍳 *_Mata ce su kayi sallama da Mijinta akan cewa za taje kauye dubo Mamanta kuma kwana biyu za tay_*i. *_Ta gama kwanakinta ta dawo, Mijin yace ya mai jiki? Sai tasa kuka wai...
Mukhtar Musa Karami Abu Hisham
Madallah.\n\n\nSalo da dabarun rubuta gajeren labari abubuwa ne masu sauki ga wanda ya fahimcesu,masu wuya ga wanda ya gaza fahimtarsu.\n\nTakaita kalmomi,fayyace komai a cikin kalmomi...
Amrah Auwal
Duk yadda kika yi daya ne. Kina iya yin salon dan magori ma'ana wanda marubuci zai rinka alakanta rubutun da shi kanshi. Kuma kowanne yana hawa da gajeren labari.