Bakandamiya
GORON JUMMA'A
BA A YIN WUTRI BIYU A DARE DAYA
Tambaya:
Assalamu alaykum, Malam don Allah Malam amma naji wasu sunce wai idan mutum yayi wuturi a lokacin da ya yi sallan tarawi, toh wai idan zai yi nafila a cikin dare zai kara raka'a daya ya cika wuturin da ya yi da sallah tarawi. shine nake neman karin bayani plxx malam.
Amsa:
Wa alaikum assalam,
Annabi S. A. W. yana cewa ba a wutiri biyu a dare daya, Na'am akwai malaman da suka faɗi siffar da ka ambata, saboda in ka yi hakan zai zamar da waccan ta farkon shafa'i, tun da wutiri daya ake yi a dare.
Amma abin da yafi shi ne ko dai barin wutirin tare da liman ko kuma in ka san za ka sake wata sallar daren In liman ya yi sallama kai sai ka tashi ka karo wata raka'ar don ta zama shafa'i kai a wurinka kafin ka yi sallama ,, wannan zai sanya ya zama ba ka yi wutiri ba a lokacin Annabi S. A. W. yana cewa: "Ku sanya sallarku ta karshe da daddare wutiri".
Allah ne mafi sani.
Amsawa:
Dr Jamilu Zarewa
07/06/2017