Masha Allah! Mambobin babban kwamitin shiryawa da tsarawa da alkalantawa da gudanar da muhawarar Bakandamiya 2020 daga farko har zuwa taron kammalawa jim kadan a ofishin Ado Ahmad Gidan Dabino, MON bayan sun kammala meeting na bitar nasarori da matsaloli... moreMasha Allah! Mambobin babban kwamitin shiryawa da tsarawa da alkalantawa da gudanar da muhawarar Bakandamiya 2020 daga farko har zuwa taron kammalawa jim kadan a ofishin Ado Ahmad Gidan Dabino, MON bayan sun kammala meeting na bitar nasarori da matsaloli da aka samu da kuma yadda za a kara inganta taro na gaba.
Allah Ya sakawa wadannan jajirtattun marubuta da mafificin alkhairi. Amin.
Don nuna karin farin cikinmu duk wanda ya fara kawo...
faridat sweery
Ado Ahmad gidan Dabino.\nMukhtar Musa karami.\n\u018Aanladi Haruna.\nMuttaƙa A Hassan.\nZaraddin Nasiru.\nAlmustapha Adam Muhammad.\nBilkisu Muhammad.\nSumayya Ibrahim Gambo.\nZarah Bello Bala.\nUmmita Abdullahi Ibrahim.\nUmmi Tasi'u Abiha.
Rabee'atou A Oumar (Pinky)
Almustapha Adam Muhammad \nZahradden Nasir\nMuttaka A Hassan\nDanladi Haruna\nMukhtar musa Karami\nAdo Ahmad Gidan dabino\nBilkisu Muhammad Garkuwa\nSumayya Ibrahim Gambo\nFatima Bello Bala\nAsma'u Abdullahi Ibrahim\nUmmi Tasiu Abdul mumini
Hauwa'u Muhammad Almustapha Adam Muhammad
Zahradden Nasir
Muttaka A Hassan
Danladi... moreAlmustapha Adam Muhammad
Zahradden Nasir
Muttaka A Hassan
Danladi Haruna
Mukhtar musa Karami
Ado Ahmad Gidan dabino
Bilkisu Muhammad Garkuwa
Sumayya Ibrahim Gambo
Zahra BB
Fulani Bingel
Ummi Zee Aflam
Masha Allah! Mambobin babban kwamitin shiryawa da tsarawa da alkalantawa da gudanar da muhawarar Bakandamiya 2020 daga farko har zuwa taron kammalawa jim kadan a ofishin Ado Ahmad Gidan Dabino, MON bayan sun kammala meeting na bitar nasarori da matsaloli... moreMasha Allah! Mambobin babban kwamitin shiryawa da tsarawa da alkalantawa da gudanar da muhawarar Bakandamiya 2020 daga farko har zuwa taron kammalawa jim kadan a ofishin Ado Ahmad Gidan Dabino, MON bayan sun kammala meeting na bitar nasarori da matsaloli da aka samu da kuma yadda za a kara inganta taro na gaba.
Allah Ya sakawa wadannan jajirtattun marubuta da mafificin alkhairi. Amin.
Don nuna karin farin cikinmu duk wanda ya fara kawo...
faridat sweery
Ado Ahmad gidan Dabino.\nMukhtar Musa karami.\n\u018Aanladi Haruna.\nMuttaƙa A Hassan.\nZaraddin Nasiru.\nAlmustapha Adam Muhammad.\nBilkisu Muhammad.\nSumayya Ibrahim Gambo.\nZarah Bello Bala.\nUmmita Abdullahi Ibrahim.\nUmmi Tasi'u Abiha.
Rabee'atou A Oumar (Pinky)
Almustapha Adam Muhammad \nZahradden Nasir\nMuttaka A Hassan\nDanladi Haruna\nMukhtar musa Karami\nAdo Ahmad Gidan dabino\nBilkisu Muhammad Garkuwa\nSumayya Ibrahim Gambo\nFatima Bello Bala\nAsma'u Abdullahi Ibrahim\nUmmi Tasiu Abdul mumini
Hauwa'u Muhammad Almustapha Adam Muhammad
Zahradden Nasir
Muttaka A Hassan
Danladi... moreAlmustapha Adam Muhammad
Zahradden Nasir
Muttaka A Hassan
Danladi Haruna
Mukhtar musa Karami
Ado Ahmad Gidan dabino
Bilkisu Muhammad Garkuwa
Sumayya Ibrahim Gambo
Zahra BB
Fulani Bingel
Ummi Zee Aflam
Rabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Farko:
Bahaushe ya ce mutane su ne kasuwa ba tarin rumfuna ba! A kiyasi na baya-baya da aka yi an gano cewar a daukacin mutane masu bibiyar labarai a kowace kafa, idan aka raba su gida goma, bakwai suna amfani... moreRabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Farko:
Bahaushe ya ce mutane su ne kasuwa ba tarin rumfuna ba! A kiyasi na baya-baya da aka yi an gano cewar a daukacin mutane masu bibiyar labarai a kowace kafa, idan aka raba su gida goma, bakwai suna amfani da radiyo ne a Nijeriya. Yayin da... moreHujja Ta Farko:
Bahaushe ya ce mutane su ne kasuwa ba tarin rumfuna ba! A kiyasi na baya-baya da aka yi an gano cewar a daukacin mutane masu bibiyar labarai a kowace kafa, idan aka raba su gida goma, bakwai suna amfani da radiyo ne a Nijeriya. Yayin da gwamnati ta zo da wasu sababbin tsare-tsarenta wadanda take son su karade ko'ina, idan ta yi amfani da gidajen radiyo to mutane bakwai cikin goma da ke bibiyar labarai za su riski wannan sabon tsari, idan... less
Rabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Biyu:
Sakonnin gwamnati suna isa ga al'umma ta hanyar nishadantarwa, ko ilmantarwa da makamantan haka, to idan ana son a sami duk wadannan sai an garzaya zuwa ga shirye-shiryen da ake yi a gidajen radiyo.... moreRabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Biyu:
Sakonnin gwamnati suna isa ga al'umma ta hanyar nishadantarwa, ko ilmantarwa da makamantan haka, to idan ana son a sami duk wadannan sai an garzaya zuwa ga shirye-shiryen da ake yi a gidajen radiyo. Misali a gidajen radiyo ne ake... moreHujja Ta Biyu:
Sakonnin gwamnati suna isa ga al'umma ta hanyar nishadantarwa, ko ilmantarwa da makamantan haka, to idan ana son a sami duk wadannan sai an garzaya zuwa ga shirye-shiryen da ake yi a gidajen radiyo. Misali a gidajen radiyo ne ake samun wasannin kwaikwayo wadanda kacokan gwamnati ce ke daukar nauyinsa domin isar da wani sako na musamman wanda zai amfani al'umma, kamar wasanni domin kawo karshen cutar foliyo ko tarin fuka ko zazzabin maleriya, uwa-uba kuma kariya daga kamuwa da... less
Jibrin Adamu RanoNa fahimci kin tsani talabijin, da alamu shi ya sa ba kya kallonta. Shi kuwa hukunci ba a yankewa bisa ra'ayi, abin da ka gani kake iya ɗorarwa.
WASAN KWAIKWAYO.
Ai daga sunan kawai kin san cikar fahimtarsa sai an kalla a talabijin, ba wai ji a rediyo... moreNa fahimci kin tsani talabijin, da alamu shi ya sa ba kya kallonta. Shi kuwa hukunci ba a yankewa bisa ra'ayi, abin da ka gani kake iya ɗorarwa.
WASAN KWAIKWAYO.
Ai daga sunan kawai kin san cikar fahimtarsa sai an kalla a talabijin, ba wai ji a rediyo ba. Wannan shi ya sa ita kanta gwamnatin a talabijin take ƙarfafa saka shi, don a can ne za a faɗaku ba rediyo ba.
Rabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Uku:
A shekarar 2004 zuwa 2005 al'ummar garuruwan Agbowo da Orogun da ke jihar Oyo sun fuskanci matsaloli na mummunar ambaliyar ruwa. Gwamnati ta yi ta kokarin shawo kan matsalar, ta kuma zage dantse wajen... moreRabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Hujja Ta Uku:
A shekarar 2004 zuwa 2005 al'ummar garuruwan Agbowo da Orogun da ke jihar Oyo sun fuskanci matsaloli na mummunar ambaliyar ruwa. Gwamnati ta yi ta kokarin shawo kan matsalar, ta kuma zage dantse wajen yin shirye-shirye na fadakarwa da... moreHujja Ta Uku:
A shekarar 2004 zuwa 2005 al'ummar garuruwan Agbowo da Orogun da ke jihar Oyo sun fuskanci matsaloli na mummunar ambaliyar ruwa. Gwamnati ta yi ta kokarin shawo kan matsalar, ta kuma zage dantse wajen yin shirye-shirye na fadakarwa da wayar da kai ga al'umma domin su fahimci illar da ke cikin toshe magudanan ruwa. A duba fa, gwamnati ba ta yi amfani da sojoji ko 'yan sanda ko wata hotiho wai ita talbijin ba, amma... less
Jibrin Adamu RanoKun bar bugun jaki, kun ɓige da bugun taiki. Ni fa abu ɗaya na ce, in da a ce gwamnati bata yi amfani da talabijin wajen nuna ainahin abin da ya faru ba, da babu wanda iya jin maganganun da kunne zai saka ya yarda kai tsaye.
Bayan na ga sanarwar a... moreKun bar bugun jaki, kun ɓige da bugun taiki. Ni fa abu ɗaya na ce, in da a ce gwamnati bata yi amfani da talabijin wajen nuna ainahin abin da ya faru ba, da babu wanda iya jin maganganun da kunne zai saka ya yarda kai tsaye.
Bayan na ga sanarwar a talabijin na ji babu daɗi sosai, har da safe nake ba wa abokaina labarin abin da na gani gwanin ban tausayi. To kamar yadda na faɗa wa abokaina, haka duk masu talabijin za su faɗa wa abokanan su na karkara da kuke da'awar cewa ba su da talabijin ko lantarkin da za su gani. less
Jibrin Adamu RanoNi fa magana ɗaya na yi, na ce muku na san lokacin da wannan matsalar ta faru.
Ban manta ba ina gida a zaune ina kallon talabijin na ga ana ta nuna irin ta'adin da ruwa ya yi musu.
Idan a rediyo za a faɗa, wa ye ma zai gane ainahin buƙatar taimakon da... moreNi fa magana ɗaya na yi, na ce muku na san lokacin da wannan matsalar ta faru.
Ban manta ba ina gida a zaune ina kallon talabijin na ga ana ta nuna irin ta'adin da ruwa ya yi musu.
Idan a rediyo za a faɗa, wa ye ma zai gane ainahin buƙatar taimakon da suke yi? Ai gani a talabijin ne ya jawo aka tausaya musu sosai suka samu wannan gudummawar.
Washegari da safe kuwa cikin alhini nake labarta wa abokaina irin asarar da waɗanda ambaliyar ta shaf. To idan ba ku sani ba ku sani, kamar yadda na ba wa abokaina labari, haka duk mai talabijin ɗin da ya kalla ya gamsu da gaske ne zai faɗa wa wanda bai kalla ba har zuwa kan 'yan karkarar da kuka ta haƙilon ba su da talabijin. less
Ai yanzu ci gaba ya zo, babu wani gidan talabijin da ba su da manhaja ta waya, wacce za ka sauke ka riƙa kallon labaransu. Ni ina da manhajar Arewa 24 wanda da shi na kalli Maryam Umar taku a tattaunawar da aka yi da ita ta ZOOM... moreAmrah (Takwarar 'ya ta)
Ai yanzu ci gaba ya zo, babu wani gidan talabijin da ba su da manhaja ta waya, wacce za ka sauke ka riƙa kallon labaransu. Ni ina da manhajar Arewa 24 wanda da shi na kalli Maryam Umar taku a tattaunawar da aka yi da ita ta ZOOM a arewa.
Don haka batun wai a ɗauke wuta kana kallo duk bai taso ba, ki dai sake wata makamar, wannan makamar ta ki ganyen iska kawai kika riƙe, kina sake masa nauyi faɗowa za ki yi.
Maryamerh AbdulKana yi kaman baka san tattalin arzikin najeriya ta yi qasa ba. Wa yake da datar kalle kalle a waya bayan ga sauki? Ana ta abinci ko ana ta data? Wai ni ko malam Jibrilla ko dai Gwamnatin nan ta masu kudi ne kawai da kake ta nanata telbijin, waya da... moreKana yi kaman baka san tattalin arzikin najeriya ta yi qasa ba. Wa yake da datar kalle kalle a waya bayan ga sauki? Ana ta abinci ko ana ta data? Wai ni ko malam Jibrilla ko dai Gwamnatin nan ta masu kudi ne kawai da kake ta nanata telbijin, waya da abubuwan da ba kan gado.
Da kake cewa masu talbijin ne suka gani kuma suka isar da sako ko suka bada labari, wannan magana taka karya ce, sanin kanka ne masu bada labarin da suka ji a gidan rediyo sun rinjayi masu badawa don sun gani a telbijin. Yoo yawanci masu kallon talbijin ‘yan birni ne da hira tsakaninsu ke musu wahala, kowa da wayarsa hannu ko an shiga kalle kallen televista. Amma mu mutanenmu kullum cikin zumunci da hira ake yi, in ba a bada labaran rediyo ba ma ai ka san zaman... less
Rabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Rufewa:
Tun daga 1933 har zuwa yau ina kalubalantar duk wani mai bayyananniyar hujja wadda za ta fifita wata kafar isar da sakon gwamnati wacce ta shallake radiyo, ko ma wacce kafa ce mu zube ta a faifai mu gani idan... moreRabiatu SK Mashi → MARUBUTA:
Rufewa:
Tun daga 1933 har zuwa yau ina kalubalantar duk wani mai bayyananniyar hujja wadda za ta fifita wata kafar isar da sakon gwamnati wacce ta shallake radiyo, ko ma wacce kafa ce mu zube ta a faifai mu gani idan akwai riba. Ba domin hujjojina sun... moreRufewa:
Tun daga 1933 har zuwa yau ina kalubalantar duk wani mai bayyananniyar hujja wadda za ta fifita wata...
Jibrin Adamu Rano
Abu na gaba da nake so ku kai hankalinku kai. A cikin ku ai akwai wacce ta samu nasarar zama zakarar BBC Hikayata ta bana. Shin ta murya Maryam ta zagaya duniya kowa ya gan ta ko kuwa ta bidiyo na talabijin da wayoyi?
Maryamerh AbdulArewa dai arewa dai, arewa kuma me alaqanta da sakon Gwamnati? Duk kallonka da arewa, yaushe ka ga sun sako sakon Gwamnati? Tambaya ta Allah da annabi kenan. Da kake maganar cancer, kafin cancer ta kama mutum biyu, ciwon ido ta kama mutum goma. Me zaka... moreArewa dai arewa dai, arewa kuma me alaqanta da sakon Gwamnati? Duk kallonka da arewa, yaushe ka ga sun sako sakon Gwamnati? Tambaya ta Allah da annabi kenan. Da kake maganar cancer, kafin cancer ta kama mutum biyu, ciwon ido ta kama mutum goma. Me zaka ce da wannan? Ko kwana zamu yi a nan, ina tabbatar maka bazan gaji da baka hujja kan hujja akan rediyo ta fi talbijin tura sakon Gwamnati ba, sannan ba zan...
Amrah Auwal → MARUBUTA:
Hujja Ta Biyu;
Idan direbobi suka sheka da gudu kai ka ce da iska suke tsere! Ci-da-zuci yana d'aukar su a ga suna fera wuta tare da daukar kasadar kutsawa hannun da ba nasu ba (Overtaking), su a dole sai sun isa inda... moreAmrah Auwal → MARUBUTA:
Hujja Ta Biyu;
Idan direbobi suka sheka da gudu kai ka ce da iska suke tsere! Ci-da-zuci yana d'aukar su a ga suna fera wuta tare da daukar kasadar kutsawa hannun da ba nasu ba (Overtaking), su a dole sai sun isa inda suka yi wa tsinke da wuri. A... moreHujja Ta Biyu;
Idan direbobi suka sheka da gudu kai ka ce da iska suke tsere! Ci-da-zuci yana d'aukar su a ga suna fera wuta tare da daukar kasadar kutsawa hannun da ba nasu ba (Overtaking), su a dole sai sun isa inda suka yi wa tsinke da wuri. A irin wannan gudun kuskure kadan za a yi shi... less
Rabiatu SK MashiSosai ma kuwa, wani direba da irin hakan ta taba faruwa dashi, garin saurin yayi accident mota tayi rugu-rugu shi dinma yasha jinya, ke kince bazai kara yarda yayi sauri ba balanta na tuqin ganganci, anma wallahi har yanzu tuqi yake da sauri kamar zai... moreSosai ma kuwa, wani direba da irin hakan ta taba faruwa dashi, garin saurin yayi accident mota tayi rugu-rugu shi dinma yasha jinya, ke kince bazai kara yarda yayi sauri ba balanta na tuqin ganganci, anma wallahi har yanzu tuqi yake da sauri kamar zai tashi sama, sannan ba ruwanshi da bin dokokin hanya, toh ina laifin gwamnati anan da ba itace zata mishi tuqin ba?
Maryamerh AbdulHanzari fa, idan da Gwamnati ne mai laifi da a garin Abuja baza a taba hatsari ba kenan. Amma kulli yaumin sai an yi hatsari, kuma kaf najeria babu inda ake da titina masu kyau, street light, tsagar hanyan nan fari, kai komai na tuki Gwamnati ta sa. Har... moreHanzari fa, idan da Gwamnati ne mai laifi da a garin Abuja baza a taba hatsari ba kenan. Amma kulli yaumin sai an yi hatsari, kuma kaf najeria babu inda ake da titina masu kyau, street light, tsagar hanyan nan fari, kai komai na tuki Gwamnati ta sa. Har yanzu Gwamnati ko? Don an renata komai sa a makala mata. Direbobi ne masu laifi babu shakka
Amrah Auwal → MARUBUTA:
Hujja Ta Farko:
Direbobin zamani babu ruwansu da bincikar bukatun ababen hawansu, da sun tashi da safe sun cika cikinsu, sai su fita su shige gidan gaba su jefa wa mota makulli su garkama giya. Wannan halin ko-in-kula da... moreAmrah Auwal → MARUBUTA:
Hujja Ta Farko:
Direbobin zamani babu ruwansu da bincikar bukatun ababen hawansu, da sun tashi da safe sun cika cikinsu, sai su fita su shige gidan gaba su jefa wa mota makulli su garkama giya. Wannan halin ko-in-kula da sakaci na direbobi suna janyo... moreHujja Ta Farko:
Direbobin zamani babu ruwansu da bincikar bukatun ababen hawansu, da sun tashi da safe sun cika cikinsu, sai su fita su shige gidan gaba su jefa wa mota makulli su garkama giya. Wannan halin ko-in-kula da sakaci na direbobi suna janyo... less
Maryamerh Abdul
Haka fa, daidaikun direbobi ne zaki ga da safe suna duba motar nasu, wanda wurin ruwa ya riga ya lalace ki ga an fara qiqarin qara masa ruwa. Abun fa ba dadi
Af! Ashe fa bakin abinda aka iyakance na lokaci yana tunkarowa, sai dai a yadda na shawo gangara da za a kyale ni to hujjoji yanzu ma aka fara; me aka yi da maza? In ji karya! Kodayake hakan ma na tabbata duk wanda ya karanta zai...
Amrah Auwal → MARUBUTA:
Hujja Ta Uku:
Cikar kwari da ake yi wa motoci da fasinja ko kayan fasinjoji yana janyo a sami mummunan hatsari. Mota ce, watakil ma Baturen da ya yi ta kawai saboda a je cefane a dawo ne, amma sai a cusa mutane har a but,... moreAmrah Auwal → MARUBUTA:
Hujja Ta Uku:
Cikar kwari da ake yi wa motoci da fasinja ko kayan fasinjoji yana janyo a sami mummunan hatsari. Mota ce, watakil ma Baturen da ya yi ta kawai saboda a je cefane a dawo ne, amma sai a cusa mutane har a but, kafafu na reto, cikin motar kuwa... moreHujja Ta Uku:
Cikar kwari da ake yi wa motoci da fasinja ko kayan fasinjoji yana janyo a sami mummunan hatsari. Mota ce, watakil ma Baturen da ya yi ta kawai saboda a je cefane a dawo ne, amma sai a cusa mutane har a but, kafafu na reto, cikin motar kuwa an dora mutane wani... less
Rabiatu SK Mashi
Da naga wannan hujjar sai da nayi dariya, saboda tunawa da nayi da wani direba shima mai irin wannan zalamar daya taba tsayawa daukarmu😆
Rabiatu SK MashiMota cike da mutane, an maida kaya can sama an saka mutane a but, maza ne su hudu cikin but dinma wai ya tsaya d’aukarmu, ina zaku? Dakyar na iya fada mishi ina riqe dariyata, yana jin inda zamu yace to ku taho mu tafi, wallahi saboda dariyar data... moreMota cike da mutane, an maida kaya can sama an saka mutane a but, maza ne su hudu cikin but dinma wai ya tsaya d’aukarmu, ina zaku? Dakyar na iya fada mishi ina riqe dariyata, yana jin inda zamu yace to ku taho mu tafi, wallahi saboda dariyar data kamamu muka ma kasa haqura muga inda zai sakamu cikin wannan mota😆😆 daga cikinta har but mutane, ko saman ma cike da kaya, yaga yanda muke dariya kawai yaja motarshi ya qara gaba🤣🤣🤣.
Amrah Auwal → MARUBUTA:
Direba! Ga ka mutum amma ka rike kambun mutuwa (sitiyari).
Direba! Kana gudu bisa iska (tayoyi), makamashin wuta gefenka (fetur).
Kara wuta direba, Aljanna ta mai rabo... moreAmrah Auwal → MARUBUTA:
Direba! Ga ka mutum amma ka rike kambun mutuwa (sitiyari).
Direba! Kana gudu bisa iska (tayoyi), makamashin wuta gefenka (fetur).
Kara wuta direba, Aljanna ta mai rabo ce!
Direba kenan... Me zai hana wadannan maganganu su hau kansa har ya ji kamar shi... moreDireba! Ga ka mutum amma ka rike kambun mutuwa (sitiyari).
Direba! Kana gudu bisa iska (tayoyi), makamashin wuta gefenka (fetur).
Kara wuta direba, Aljanna ta mai rabo ce!
Direba kenan... Me zai hana wadannan maganganu su hau kansa har ya ji kamar shi kadai ne bisa hanya a yayin da yake famfala gudu kamar wanda ya hau Dokin Iska Danfilinge?!
A yi mini afuwa na fara da sambatu ba tare da gaisuwa ba. Tsananin mamaki ne ya cika ni, jin har akwai masu tunanin wai laifin Gwamnati ne ke kawo yawaitar hatsari, ana neman a bar jaki a koma dukan taiki!
Masu girma alkalai, jagorori, abokan karafkiya, masu bibiya, ina nema mana amincin Allah Madaukakin Sarki. Sunana Amrah, daga kungiyar Nagarta. A karo na biyu na zo domin wakiltar kungiyata.
Tabbas direbobi ke da laifi a hatsarin da ke afkuwa a... less
"Fad'i dukkan sharad'inka a shirye nake domin cika maka su ko da kuwa fansar raina ne, indai zaka amince da bukata ta".
Tsaraki ya yi gajeriyar dariya kafin ya sake daidaita tsayuwarsa yakai dubansa fuskar Dan Zabuwa a karo na kusan hudu, kafin ya fara magana da fadin.
"Tabbas zan amince da Manya ya auri Mairamu idan har zaka dawo da kambun tsarafi gare ni, zan yarda na sadaukar da fansar gaba idan har ka amince ka damka kambun sarautar ahalin mu guda biyu a hannuna, wanda kakanmu ya kwace daga hannun Mahaifina, zan yarda da auren ne kawai idan ya kasance ka durkusar da karfi da iko na Manya, idan har ka aminta da wadan nan sharadin to shirye nake ko yanzu basai anjiba ba ko gobe a daura wannan aure".
Dan zabuwa ya zubawa Tsaraki idanuwa tsayin wasu dakikai yana nazartar gaskiyar al'amarin daya zo masa da su wanda bai yi tunanin hakan daga Tsaraki ba, domin abin da ya bukata abubuwa ne masu matukar wahala, amma da ya tuna da gudan jininsa tilo daya tal a duniya mafi soyuwa a gareshi sai ya ji a shirye yake ya sadaukar da komai daya mallaka domin samun lafiyarsa, dago kai ya yi yakai dubansa ga Tsaraki wanda shima kallon nasa yake yi fuskarsa fal murmushi domin yasan ko babu komai ya yi abin da zai wulakantar da Dan Zabuwa a kauyen Maina, shi kuwa Dan Zabuwa ba tare da sake nazartar yanayin Tsaraki ba ya cigaba da fadin.
"Zan baka dukkan abin da ka ambata, amma akan sharadi guda daya".
"Ina jinka".
"Sai idan ka yi alkawari da kambun tsafi ba zaka cutar dani da yarona ba*.
"Na yi alkwari, kuma kasan nasan girman alkawari zan rike kalmar da yakininta, bazan canja abin da na fada ba".
"Shi kenan zuwa daren yau ka zo gidana zan baka dukkan abin da ka bukata"
"An gama"
Da ga haka suka yi sallama kowa ya yi hanyarsa, Tsaraki cike da dumbin farin ciki da murnar cin galaba akan Dan Zabuwa, Dan Zabuwa kuwa abin duniya ya yi masa yawa, yana ganin zai aikata babban kuskure ne zunubi mai girma, amma idan ya tuna lafiyar yaronsa sai ya ji a ransa hakan ba komai ba ne.
KANO.
WASHE GARI.
Bayan ta idar sallar asuba tana zaune kan abin sallar tana addu'o'inta, saboda sabo da tashi a gidan su Salima, har ta soma zame mata jiki, bacci ne ya sace ta anan inda take zaune, kamar daga sama taji yo tashin bugun kofar dakin nata, firgigit ta farka tare da murje ido ta nufi bakin kofar da fad'in.
"Waye ne?".
"Hafsy ce".
Ta bata amsa a daidai sanda ta bude kofar, da murmushi suka dubi juna Ishatu na fad'in.
"Bismillah shigo mana".
Hafsy ta sanya kai cikin dakin tana mai cigaba da fad'in.
"Kin jini shiru sai yanzu Allah ya yi dawowar mu, kai amma dakin naki ya yi kyau wallahi".
Ta kare maganar tana mai ajiye manyan ledojin data shigo da su kafin ta nemi gefan katifa ta zauna, ta sake duban Ishatu dake tsaye tana binta da kallon mamakin jin cewar tun daren jiya sai yanzu ta dawo.
"Ishatu lafiya kuwa?".
Ishatu ta dawo daga duniyar tunanin da murmushi shimfide saman fuskarta kafin ta ce.
"Kenan ba gida kika kwana ba?".
Hafsy ta yi dariya ba tare da ta bata amsa ba ta cigaba da magana.
"Kin ga duba cikin waccan karamar locker akwai plate da sauran kayayyaki kitchen dauko nan mu yi breakfast dan wallahi da yunwa na dawo, wannan shegiyar dinner a bushe basu tanadi abincin kirki ba sai kayan shaye-shaye na banza".
Ita dai Ishatu tuni ta dauko mata abin da ta bukata ba tare da ta damu da son jin inda zancen nata ya nufa ba, ta ajiye mata kayan a gabanta tana cewa.
"Yunwa tun yanzu Hafsy?".
Baki sake Hafsyn ke dubanta da mamaki kafin ta daga kai takai dubanta jikin bangon dakin inda agogo yake kafe lokaci guda ta dawo da kallonta ga Ishatu da fadin.
"Kika san yanzu karfe nawa?".
Sai lokacin Ishatu takai dubanta wajen agogon karfe tara har da wani mintuna lokacin, Ishatu ta zaro ido da fadin.
"Ikon Allah ashe bacci na yi sosai haka?".
Hafsy ta girgiza kai da murmushi ba tare da ta sake magana ba, ta cigaba da juye musu kayan makulashe kala-kala wanda Kamal ya biya ya siya Mata, saboda mitar yunwa data cika shi da ita suna hanya.
"Ya kamata a ce an kawo miki kayan tea fa? Babu wanda ya shigo wajenki ne?".
"Aa Aunty ta shigo tun jiya da dare".
"Ok may be ina jin ta yi aike kina bacci, dan nasan ba zata bari a tashe ki ba".
"Ai tana da kirki Aunty sosai".
Hafsy ta gimtse dariyar dake shirin kufce mata jin maganar da Ishatu ta yi akan Aunty har tana shirin kwarewa a daidai sanda takai cokali bakinta dauke da farfesun kayan jiki, a jiye cokalin ta yi tare da yafito Ishatu da hannu ta zaunar da ita gefanta da fadin.
"Zan gaya miki wani abu a game da zaman gidan nan amma kafin nan na tambayeki abu daya zuwa biyu, idan kin ga dacewar ki sanar da ni ina maraba da hakan, idan kuma abin ya kasance sirri ne a gareki to kibar abin a cikin ranki".
Ishatu ta gyada kai alamun ta gamsu da batun nata, Hafsy ta zubawa Ishatu nata naman a dayan plate din tana mai cigaba da cewa.
"Mene dalilin da ya fito dake daga gida, sannan kuma kin shiryawa zama a cikin gidan nan?".
Ishatu ta yi shiru tsayin wasu dakiku tana nazari da tunanin amsar da zata bata, kafin ta yankewa kanta hukuncin sanar da Hafsy wani abu a dangane da ita, nan dai ta fara bata labarin zuwanta gidansu Salima da shiga dakinta da ake yi da yanda aka yi ta baro gidan, Hafsy ta girgiza kai kafin ta ce.
"To ni a ganina nan din ma da kika zo duk kanwar ja ce, amma kafin na ce wani abu bani amsata ta biyu".
Ishatu ta gyara zama kafin ta cigaba da magana.
"A shirye nake na cigaba da zama anan, domin idan har nabar nan bansan inda zan nufa ba".
Hafsy ta girgiza kai da murmushi kwance saman fuskarta, kafin ta kama hannun Ishatu ta rike a cikin nata ta dubeta da kulawa kafin ta ce.
"Kinsan abin da zan fada miki da zaman gidan nan? Babu ruwanki da shiga harkar da bata shafeki ba, haka kuma duk wacce ke nemanki da rigima ki bawa banza ajiyarta, Aunty na son girma da iko, ki girmamata ki yabeta a gabanta, idan kin bi wannan zaki zauna kafiya kalau da kowa cikin gidan nan, sannan kuma a labarin da kika bani kamar kin boyemin abubuwa da dama, amma karki damu kanki nasan may be sirrinki ne, nasan kuma akwai lokacin da zaki yarda dani ki sanar dani, Bismillah muci abinci".
Tana kaiwa nan ta cigaba da cin abincinta, haka itama Shatun, amma a gefe guda tana mamakin saukin kai irin na Hafsy da yanda ta dauki rayuwa ba komai ba, tafiyar da rayuwarta take yi hankalinta kwance, alamun babu abin da yake damunta a fadin duniya, a haka suka kammala karyawa Ishatu ta kwashe kwanukan ta wanke kafin ta dawo ta nemi inda ya tashi ta zauna tana kallon Hafsy dake ta faman latse-latsen waya data gaji ta shiga daukar selfie har tana sanya Ishatu ta matso sunyi hotuna sosai masu kyau da yake wayar iPhone 11 ce ga kyau ga fidda hotuna masu kyau, Ishatu ta dubi Hafsy dake gyara kwanciya da shirin bacci tana fadin.
"Na tambayeki mana Hafsy?".
"Allah yasa na sani ina jinki".
Ta karashe maganar tana hamma alamun baccin take ji sosai, Ishatu ta gyara zama sosai kafin ta ce.
"Wai dan Allah mene Bariki ne? Kuma suwaye kadangarun Bariki kamar yanda na ji jiya suna maganar anan waje?".
Hafsy ta mike zaune tare da murje gidonta daga baccin dake fizgarta, ta kafe Ishatu da manyan idanuwanta sosai take yi mata kallon mamaki.
'Baya ga haka kuma bata zubi ga mutanen kauye bare ta kirata bakauya, kuma tasan a kauye ma yanzu yaro da babba babu wanda zai ce baisan me kalmar bariki take nufi ba amma da mamaki'
Hafsy ta gyara zama tare da fara yi mata bayani daya bayan daya ta cigaba da fad'in.
"Aunty zata yi alfahari da ke ne idan kin fita kin nemo mai yi Miki hidima tare da ita, haka kuma zata kaunace ki fiye da kowa idan farashinki ya haura na sauran matan dake gidan nan, ni nasan zaki yi kasuwa matukar kika waye a wannan harkar, sannan kuma kinsan wani abu?".
Ishatu ta girgiza kai alamu a'a.
"Na ji mamaki da kika tambaye ni game da abin da ake nufi da bariki, dama wai ba BARIKI KIKA FITO BA?".
Ishatu ta girgiza kai alamun zancen Hafsy ba haka bane.
"Shi yasa dama na tambayeki idan kin shiryawa zama anan domin babu macen da Aunty ke ciyarta da ita abanza matukar ba zata fita ta nema ba sunanta sorry, ki yi tunanin mafita Ishatu zan taimake ki da yardar Allah kin ji?".
Hafsy ta koma takwanta tabar Ishatu nan zaune zuciyarta cike da sake-sake kala-kala na neman mafita akan tudun data taka a yanzu, wanda tana ganin har kusan gara zamanta a gidan su Salima akan hanyar da rayuwarta take shirin bi yanzu, ko kusa ko da wasa bata fatan sake kazanta kanta domin Allah ya nufa ta tsabtacu akan addininta, tunani sosai take yi tare da neman mafita kamar yanda Hafsyn ta fada mata.
Hafsy ta sake yi mata magana a karo na biyu tare da jijjiga kafad'arta kad'an, Shatu ta dawo da ga dogon tunanin data fad'a, daidai sanda Hafsy ta kalleta da murmushi tare da bud'e Mata murfin motar gidan baya tana mai yi mata nunin ta shi ga.
Ishatu ta sanya kai cikin motar zuciyarta na cike da rera addu'o'i kala-kala na neman tsari.
Tun da ta shiga motar Ishatu kanta na k'asa, bata fatan driven ya ga fuskarta, Hafsy dake zaune kusa da shi suke ta hira tsayin mintuna kafin ya jefeta da tambayar.
"Ina kika samo wannan kuma?".
"K'awata ce".
"Karki raina min hankali mana, kina son nuna min bansan k'awayen naki ba ne?".
"Sai aka ce maka su kad'ai ne k'awayena?".
"Ba nufina kenan ba, amma alamu sun nuna yarinyar farin shiga ce, domin na yi la'akari da tsoron da yake tattare da ita".
Hafsy ta yi ajiyar zuciya tare da watsa masa wani irin kallo na cikakkun 'yan bariki kafin ta ce.
"A nan na sameta, niyata mu wuce can wajen dinner din da ita kafin a tashi sai mu je gida tare, to amma kuma ina ganin kamar hakan zai takura mata, ko wajen Aunty zamu fara zuwa ka ajiyeta?".
Shiru ya ziyarci motar tsayin lokaci kafin ta sake magana da fad'in.
"Kamal kana jina kuwa?".
"Ke ! Ni fa duk tunanina ya tafi akan samun sabon nama".
Hafsy ta galla masa harara kafin ta ce.
"Ka da ma ka fara tunanin hakan wallahi, domin bana tunanin yarinyar ta san wannan harkar".
"Sannu ko?".
Ya fad'a ta cikin mudubin yana mai karewa Ishatu kallo ba tare da ya kula da maganar Hafsy ba, kai tsaye ya juya kan motar zuwa gidan magajiyar kamar yanda Hafsy ta fad'a masa, tafiyar mintuna talatin ce ta sada su da kofar gidan, Hafsy ta fito daga motar tana fad'in.
"Ka jira ni na fito, Ishatu fito muje".
'Ishatu'.
Kamal ya yi maimaicin kalmar sunan a cikin ransa, har suka shige cikin gidan yana bin bayansu da kallo kafin ya yi ajiyar zuciya yana raya abubuwa da dama a k'asan ransa game da Ishatun.
Tun daga yanayin k'ofar gidan zuwa tsakar gida Ishatu tasha jinin jikinta da al'amarin gidan, tunani ta dinga yi kala-kala tare da rokon Allah yasa ta fad'a hannun na gari.
'Dakuna ne birjit a gidan tsakar gidan ya haske da kwan lantarki, Mata ne kala-kala zaune a zagaye da wata k'atuwar mace mai cikar zati da kwarjini, tasha ado leshin dake jikinta kawai abin kallo ne ban da sark'ar kwal d'in dake damb'are a wuyanta mai manyan d'an kunne, suna shiga aka dakata da kidan k'waryar da ake yi, kowa sai binsu da kallo yake fuskokinsu kad'ai zaka kalla ka hasaso abin da ke k'asan ransu na tambayar WACECE ITA KUMA WANNAN?.
MAINA.
Dan zabuwa ya nemi sa'a akan kud'urinsa bayan shafe tsayin kwanaki da ya yi yana nazari da lissafin wuta da taurari akan neman mafita bai samu ba, abin da ruhinsa da tunaninsa baya so dole shi ne mafitar, ba shi da zab'in da ya wuce yin hakan a gareshi, kai tsaye bishiyar da yasan kullum nan ne dandalin zaman Tsaraki ya nufa tun kusantuwarsa garesu suka zuba masa ido domin karantar da yanayin da yazo garesu, bayan ya k'araso kallan kallo aka fara yi, kafin Dan Zabuwa ya yi ajiyar zuciya ya dubi Tsaraki da fad'in.
"Magana na zo muyi cikin masalaha da sirri".
Tsaraki yakai dubansa ga sauran abokansa kafin ya mai da kai ga Dan Zabuwa yana karewa yanayinsa kallo, mik'ewa ya yi sauran abokansa suka suka mik'e da nufin bin bayansu ya dakatar da su da nunin baya buk'atar su zo garesu.
'Yar tafiya kad'an suka yi nesa da sauran abokan amma duk da haka hankalinsu yana garesu, tsayin dak'ik'u suka shud'e Dan Zabuwa ya kasa furta kud'urinsa ga Tsaraki tsoro da fargaba sai ziyartarsa suke akai-akai yana tsoron abin da zai je ya dawo, a hakan ya yi ta maza tare da neman jarumta ya sanya wa ransa kafin ya gyara tsayuwarsa da ya ce.
"Magana ce a tattare a bakina, haka kuma alfarma ce nake nema wacce bana fatan ka ce a'a shirye nake na d'auki dukkan hukuncin da ka yanke a gare ni matukar zaka amince ka yarda da ni, Tsaraki zan kashe wutar gabar da ke tsakanin mu, zan ajiye jiji da kai da tak'ama na fuskanceka indai zaka amsa da kalmar aminta a gare ni".
Dan zabuwa ya yi shiru tsayin lokaci yana karantar yanayin Tsaraki, wanda shima kallon Dan Zabuwan yake yi cike da mamakin kalaman hikimar dake fita da ga bakinsa, Tsaraki ya katse shirun da fad'in.
"Ina jinka fad'amin dukkan abin da kake son ka fad'a min, sanar dani wacce alfarma ce haka da har zata sanyaka ajiye mamakaman yak'i akanta?".
"Kasan cewar 'Dan wajena ya fad'a doguwar suma?".
"E na ji jama'ar gari na fad'a, amma ban tabbatar ba sai yanzu da naji a bakinka".
"To tabbas haka ne, na yi bincike cikin taurari da wuta amsar duk d'aya ce idan har Ina son dawowar hayyacin Manya dole sai dai ka yimin wata sadaukarwa".
"Sadaukarwa me fa?".
"Ka aurar min da Mairamu ta zamto suruka a gare ni, wato d'ana Manya ya auri Mairamu wannan ita ce warakarsa".
Wani mugun kallo Tsaraki ya wurgawa Dan Zabuwa yahau binsa da kallo sama da k'asa yana mai zagayeshi kamar mai yin dawafi, hankalin Dan Zabuwa idan ya yi dubu ya tashi, fargaba da tsoro sai k'ara shigarsa suke yi, da mamakinsa sai ji ya yi Tsaraki ya kaure da wata irin mahaukaciyar dariya, kafin ya lafa nad'an wani lokaci ya tsaya a gaban Dan Zabuwa yana fad'in.
"Wata sabuwar yaudara ce wannan kuma?".
"Ko kad'an ka da ka yi tunanin hakan, ba yaudara ba ce, gaskiya ce wannan ".
"To shi kenan idan na yarda da yarjejiyar auren Ishatu a da wannan dan bana sonta ne ita da Uwarta, Mairamu kuwa da Uwarta sune komai nawa a yanzu, sune duniyata da dukkan jindadi ne, taya kake tunanin zan iya sadaukarwa Tsohon makiya na bashi abu mafi soyuwa agare ni?".
Yana furta hakan Dan Zabuwa ya zube a gaban Tsaraki gwiwa k'asa yana afi da neman afuwa, da mamaki Tsaraki yake binsa da kallo yasan tabbas abin babba ne tun da har Dan Zabuwa ya iya ajiye girman kansa ya durk'usa masa, sosai ya bashi tausayi ganin ruwan hawaye akan fuskarsa amma duk da hakan ya danne domin cika alwashinsa, ya sanya hannuwa biyu ya d'ago Dan Zabuwa daga Kan gwiwa yana fad'in.
"Na yarda da kai, zan kuma amince da abin da ka zo min da shi amma akan sharad'i uku".
Dan zabuwa ya mai da hankali sosai yana fad'in.
"Fad'i dukkan sharad'inka a shirye nake domin cika maka su indai har zaka amince ko da kuwa fansar raina ne".
KANO.
Suna k'arasa wa aka basu waje gaban Magajiya suka zauna Hafsy ta kama hannun matar tayi mata kiss na girmama wa, kafin ta gyara zama da fad'in.
"Yau na yi tsuntuwar wani d'anyan nama ne Aunty".
Takai maganar tana duban Ishatu, matar har lokacin na kishingid'e irin kwanciyar sarakai, a tada hannu da filo, itama duban Ishatun take yi a nutse tana nazarinta kafin ta ce.
"Sunanta fa?".
"Ishatu".
Matar ta maimaita sunan tana d'an tab'e baki kad'an, kafin ta cigaba da magana.
"Shi kenan tashi ki je, za'a kula da ita".
Hafsy ta mik'e tana duban Ishatu da ta ce.
"Ki huta kafin na dawo".
Bata jira amsar Ishatu ba ta fice abinta, matar ta dubi d'aya daga cikin 'yan matan dake zagaye da ita da ta ce.
"Zeena kaita wancan d'akin".
Ta yi nuni da saban d'aki wanda yasha fenti, da alamu ma sabon gini ne, ba musu Ishatu ta mik'e tabi bayan yarinyar da aka kira da Zeena, saboda ji ta yi ba zata iya musu da Auntyn ba, saboda kwarjini ta yi mata sosai, ko da suka shiga cike da mamaki Ishatu kebin d'akin da kallo ganin komai an k'awata d'akin dashi katifa ce katuwa a jiye wacce ake kira gado huta tasha beedsheet mai kyau, d'akin shimfid'e da carpet sai wata karamar wardrobe da wani mirrow mai d'auke da shirgin kayan kwalliya kala-kala, d'akin dai babu abin da mace zata buk'ata a ciki na rayuwarta ta rasa, tamkar dama an tanadesu ne saboda zuwanta.
Zeena ta kalleta cikin wani irin yatsima tana taunar cingum kafin ta ce.
"Gaskiya kin taki babbar sa'a da alamu ke ta musamman ce da wuri tauraruwarki zata haska, kina mamakin d'akin ne ko?".
Ta cigaba da fad'in.
"Sai macen da takai ta kawo kad'ai Aunty ke bawa irin wannan d'akin, shekaruna uku a bariki amma har yanzu ban taka wannan matsayin ba, dan haka kibi a sannu".
Tana gama fad'in hakan ta juya ta fice daga d'akin, ba tare da ta jira amsar da Shatu zata bata ba, Ishatu na nan tsaye tana kalle-kalle ta hangi wata karamar kofa ta k'arasa gareta ta bud'e toilet ta gani madaidaici mai kyau, ta dawo ta bud'e k'aramar drower d'in nan kayan sawa ne ciki na mata kala-kala a d'aya b'angaren, d'aya b'arin kuma kayan sawa na maza wajen kala goma suma, Ishatu ta cika da mamaki kafin ta ajiye mamakinta gefe guda a cikin ranta tana fad'in.
'ko dai d'akin wata matar ne ta ara mata kafin ta dawo'.
Tunaninta ya katse a daidai sanda ta tuna da kalaman Zeena, zama ta yi gefan katifar tana tambayar kanta.
"Ko mene Bariki kuma oho?".
Ta fad'a tana mai cigaba da k'arewa d'akin kallo, kafin ta mik'e zuwa bakin k'ofa ta leka a hankali har yanzu suna nan zaune kamar yanda ta barsu, rufe k'ofar ta yi har da sanya makulle kafin ta shige band'aki domin yin wanka da alwala saboda yanda dare ya gabato sosai, ko da ta fito agogon d'akin dake bugawa kad'an-kad'an ya nuna karfe hud'u daidai, da yake Salima ta koya Mata agogo, gabanta ya fad'i a daidai sanda ta ji karat bugan kofar dak'in, ta window ta hangi Auntyn tasu kamar yanda ta ji Hafsy ta fad'a, ajiyar zuciya ta yi tare da k'arasa wa ta bud'e mata kofar, Auntyn ta shigo tana maiai k'arewa Ishatu kallo a ranta tana yaba sura da zubi irin na halittarta ko banza zata kwashi kud'i, ta yi maganar cikin ranta tare da neman guri ta zauna gefan katifa tana fad'in.
"Magana nazo muyi ko da yake na barki ki huta zuwa gobe da safe, duk abin da kike da buk'ata ki fad'amin karki ji nauyi, a nan gidan duk matan nan da kika gani ni ce Uwa da Ubansu komai nike yi musu, saboda haka kema ki saki ranki kamar kowa, ki manta da baya da abin da ya faru ki fuskanci gaba da abin da zai zo miki nan gaba kin ji?".
Ishatu ta gyad'a kai alamar gamsuwa da kalamanta.
"Ko kina jin yunwa ne?".
"Aa dare ne yanzu k'arfe hud'u yaushe mutum zai ci abinci idan ba azumi zai yi ba".
Magajiya ta yi 'yar dariya kafin ta ce.
"Nan gidan ai sai dare ake rayuwa, mun mayar da dare tamkar rana domin a lokacin muke bud'e shagunan kasuwancin mu, ko da yake mene nawa na b'ata baki wajen sharhi da sannu zaki fahimci komai".
Takai maganar tana mai mik'ewa tsaye, kafin ta cigaba da fad'in.
"Zo ki rufe k'ofarki, sai da safe ko?".
"Allah ya tashe mu lafiya".
Ishatu takai maganar daidai sanda ta fita daga d'akin ta mayar da k'ofar ta kulle tare da komawa tsakar d'akin tana mai ajiyar zuciya a fili, kafin ta nufi wardrobe d'in ta d'auko wata doguwar riga mai silky ta sanya da wani k'aramin hijab, ta shimfid'a abin sallah wanda ta gani cikin wardrobe d'in ta tayar da kabbarar sallah domin yin nafila.
ALHAMDULILLAHI
Ina mai ban hak'urin jinkirin da kuke ta samu hakan ya samu ne sakamakon binciken file nawa da aka yi na wasu kwanaki, amma ynz alhamdulillahi komai ya zama normal, inshaAllah zaku cigaba da jina ko da yaushe in dai ba wani uzuri ya rike ni ba, NAGODE SOSAI.
Mukhtar Musa Karami Abu Hisham → MARUBUTA:
Maso son su WASA TUNANINSU kuna ya jirana ko.
Afuwanku dai wato lokacin da mukayi da ku ya shude ban zo ba,hakan ya faru saboda wata matsala amma yanzu komai ya wuce,idan kun shirya zanyi sabon post na zabar lamba.
Mukhtar Musa Karami Abu Hisham → MARUBUTA:
11/1/2021
MU WASA TUNANINMU
Zaku samu kyautar kati cikin minti biyar...... moreMukhtar Musa Karami Abu Hisham → MARUBUTA:
11/1/2021
MU WASA TUNANINMU
Zaku samu kyautar kati cikin minti biyar... more11/1/2021
MU WASA TUNANINMU
Zaku samu kyautar kati cikin minti biyar .
Zabi lamba daga 1 zuwa 50 kowacce lamba da kalar tambayarta,za a tura tambayar a baka...
Mukhtar Musa Karami Abu Hisham → MARUBUTA:
INA HAUSAWAN MASU JI DA KANSU A KALMAR HAUSA?
Zaka iya amsa tambaya biyar a mintuna biyar kuma ka samu katin dari... moreMukhtar Musa Karami Abu Hisham → MARUBUTA:
INA HAUSAWAN MASU JI DA KANSU A KALMAR HAUSA?
Zaka iya amsa tambaya biyar a mintuna biyar kuma ka samu katin dari biyar?
Ko kuma ka amsa tambaya daya tal a minti goma itama ka samu katin dari... moreINA HAUSAWAN MASU JI DA KANSU A KALMAR HAUSA?
Zaka iya amsa tambaya biyar a mintuna biyar kuma ka samu katin dari biyar?
Ko kuma ka amsa tambaya daya tal a minti goma itama ka samu katin dari...
Takaitaccen Bayani
Haifaffiyar kasar Nigeriya, zaunanniyar Kano, ina rayuwa a karamar hukumar dala ta jahar Kano.
Sannan ni marubuciyar yanar gizo ce mai kishin kasa da addinina.
Almustapha Adam Muh'd
Zaharaddeen Nasir
Muttaƙa A... more
Zahradden Nasir
Muttaka A Hassan
Danladi... more