• Contrast
    • Font
    • A
  • Sign In
  • Sign Up
    Loading ...
View All Updates Mark All Read
Bakandamiya
  • Home
  • Rubutu
  • Bidiyoyi
  • Sautuka
  • Hotuna
  • Zauruka
  • Profile Type: Personal
  • Profile Views: 4,242 views
  • Followers: 21 followers
  • Last Update: January 24, 2021
  • Last Login: November 14, 2020
  • Joined: November 14, 2020
  • Member Level: Basic
  • Update
  • About

Update

The post was not added to the feed. Please check your privacy settings.
  • samira ibrahim
    samira ibrahim liked Nana Aicha Hamissou's post.
    January 24, 2021
    Nana Aicha Hamissou → ZAUREN KACI-CI-KACI-CI:
    Assalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu. 'yan'uwa barkarmu da war haka.

    KA-CICI-KA-CICI
    Tsarawa...  more
    Nana Aicha Hamissou → ZAUREN KACI-CI-KACI-CI:
    Assalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu. 'yan'uwa barkarmu da war haka.

    KA-CICI-KA-CICI
    Tsarawa :
    Rukkaya...  moreAssalamu alaikum warahmatullahi wa barkatuhu. 'yan'uwa barkarmu da war haka.

    KA-CICI-KA-CICI
    Tsarawa :
    Rukkaya Ibrahim Lawal
    Real Nana Aisha
    Hauwa'u Salisu

    Ɗaukar nauyi : Manhajar Bakandamiya

    Tukuici: dubu uku ga mutum biyar na farko.


    Tambayoyi:

    Q1: menene sunan marubucin littafin bugyatul-musulumina?

    Q2:kawo sunayen tsuntsaye uku a cikin tsuntsaye 10 da aka faɗa a alqur'ani.

    Q3: Me Yasa ba'a ambaci sunan Imam Ali (a.s) da sauran a'immai ba a cikin Alqur'ani?

    Q4: gabobin sujjada guda nawa ne? Kawo su.

    Q5: Miye tsakanin Kano da Katsina?

    Q6. Kawo ma'anar waɗannan kalmomin masu zuwa:

    Farka, Farfanfana, kasgi, Malallota, Tabahuwa.


    Q7. Kawo sunayen kungiyoyi takwas da suka zo zagaye na uku a wannan muhawarar ta Manhajar Bakandamiya.


    Q8. A zagaye na biyu na wannan muhawarar ƙungiyar Kainuwa ita da wacce kungiya suka kara? Kuma wacce kungiya ta yi nasara?

    Q9. Faɗi sunayen waɗannan kofofin da suke garin kano a halin yanzu:

    Kofar Adama
    Kofar Dogo
    Kofar Ɗanƙwai
    Ƙofar Lunkui
    Kofar kawaye.


    Q10. Kawo jam'in waɗannan kalmomin masu zuwa :

    1. Jimina
    2. Ɗawisu
    3. Mai
    4. Talatalo
    5. Babba-da-jaka.

    A tura amsoshin ta...    less
    • 11 people like this
    • samira ibrahim
      Salisu Abdullahi 👍👍👍
      • January 25, 2021
      • -
      • Report
  • samira ibrahim
    samira ibrahim liked Haleema Hassan Leemat's post.
    January 10, 2021
    Haleema Hassan Leemat joined the group Sababbin Litattafan Halima K/Mashi
    • samira ibrahim and Haleema Hassan Leemat like this.
  • samira ibrahim
    samira ibrahim joined the group TSEGUMI ZALLA
    December 20, 2020
    • Ummyter Abdallah likes this.
  • samira ibrahim
    samira ibrahim liked Haupha123's post.
    December 20, 2020
    Haupha123 → ZAUREN KACI-CI-KACI-CI:
    *YA GAZA YI MIN UZURI*
    ...  more
    Haupha123 → ZAUREN KACI-CI-KACI-CI:
    *YA GAZA YI MIN UZURI*
    Na

    *HAUWA'U SALISU*
    ...  more*YA GAZA YI MIN UZURI*
    Na

    *HAUWA'U SALISU*
    (HAUPHA)


    *بسم الله الرحمن الرحيم*
    *____________________________________*


    *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
    ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
    https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

    *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

    https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

    *____________________________________*


    *MARUBUCIYAR.*
    Da Aurena
    Mamana ce
    Wani Malamin
    Kisa ko Aure?
    Sanadin mulki
    Akan Ɗa
    Ni da Kakata
    Mamaya.



    07081095452

    My Gmail👉🏻
    *Hauwausalisu407@gmail.com*


    My Facebook 👉🏻
    *Hauwa'u Salisu(Haupha)*


    My Wattpad 👉🏻 *Hauwausalisu*
    https://my.w.tt/P1yNEVRFl3

    My You tube channel 👉🏻https://youtu.be/h6gc8ahxrmM


    __________________________________


    Page 25


    Wannan littafin na kuɗi ne, ku biya Naira ₦200 kacal don ku sha karatu cikin natsuwa da kwanciyar hankali ta hanyar tura kuɗin ta wannan account ɗin 3121773501 Hawwa'u Salisu First bank.
    Sai ku tura shaidarku ta wannan lambar 07081095452 .


    Abduljalal


    Tsakani da Allah yake son Badiyya amma ita ko muryarshi bata buƙatar ji kusa da ita sam.

    Ba ƙaramin girgiza yayi ba da ganin mahaukacin mutumin nan cikin gidan ba, kuma wai Badiyya ce ta kawo shi cikin gidan take ba shi kulawa da duk kan wani abin a zo a gani.
    Ranar da ya fara ganin mahaukacin cikin gidan bai gane shi ba, domin sai ya hango shi kamar Aiman daga nesa, har zuciyarshi ta sauya bugawa ya fara tunanin abin da zai ce ma Aiman ɗin.
    Sai da ya daure ya isa gab da shi ya gane ba Aiman bane tsabar kama ce kawai, sai yayi tunanin ɗan'uwansu Aiman ɗin ne domin kamar har tayi yawa, don haka ya miƙa masa hannu da nufin su gaisa, amma ko kallo bai ishi gayen ba.
    Hakan yasa ya ɗan sha jinin jikinshi ya sake miƙa ma shi hannu sai kawai ya ga ya raɓa shi ya wuce ko waige babu.
    Lado mai guga ne ya lura, don haka ya shaida masa ai bai da hankali, kuma Badiyya ce ta kawo shi, domin sun shaƙu da juna tuni ita ce ke ba shi abinci da duk suturu yana sawa, don haka ake ganinsa kamar mai hankali.

    Ba ƙaramin ɓacin rai ya ji ba, a ransa me yasa ta kawo shi gidansu? Me ye haɗin ta da mahaukacin ? Lallai kam dole yasan yadda zai yasa ya bar gidan, domin ba zai bari ta cigaba da kulawa da ƙaton banza ba, yana ji yana gani, ga shi yana masifar sonta, ita kuma sai gara ma shi kai take .

    Cikin gidan ya nufa, yana cigaba da saƙe-saƙen zuciya dangane da Badiyya da mahaukacin.
    Yana shiga ya ja yayi tsaye kamar marar numfashi, ganin Badiyya zaune tana karatu mahaukacin ya kwanta kan kujera ya ɗora kansa bisa cinyarta yayi shiru.

    Cike da fusata ya daka ma shi tsawa.
    "Kai maza tashi ka bar nan, mahaukacin banza mahaukacin wofi."

    Shi dai ko a jikinsa, yayin da Badiyya taji tamkar ya watsa mata garwashin wuta, don munin maganarsa akan Ameer ɗin.

    Ta ɗago rai ɓace ta ce, "To kai kuma miye damuwarka da shi ? Dangin Iya ko na Baba?

    Sakin bakinsa yayi yana kallonta cike da mamakinta, wai shi ne ta ke gayama magana don mahaukaci ?

    Sai dai ko mi zatai ba zai iya kauda kai akan mahaukacin ba, don haka ya shareta ya sake daka masa tsawa.
    "Kai jakin ina ne wai ? Maza ka bar falon nan kafin ranka ya ɓaci, ka je can gun mahaukata nan masu hankali ne."

    Ba ita Badiyyar ba, hatta Ameer ɗin babu wanda ya sake kallon inda yake tsaye, sai ma tari da Ameer ɗin ya fara da sauri Badiyya ta ɗauki ruwa ta nufi bakinsa, shi kuma ya buɗe bakin yana kallonta ido cikin ido.

    Dafe kanshi yayi ya nufe su a fusace ya buge ruwan ya zube masu a jiki.

    Ameer ya dubi Badiyya ya yamutsa fuska, alamar bai ji daɗin hakan ba.

    Kallon Abduljalal ɗin tayi ranta yayi mugun ɓaci ta ce,
    "Na rantse da Allah akan Ameer zamu kwashi ƴan kallo da kai a gidan nan.
    Babu ruwanshi da kai, to kaima kayi tamkar baka ganin shi a cikin gidan nan, idan ba haka ba zan matuƙar baka mamaki domin ni ba Yaya Aiman bace ba."

    Ta ja hannun Ameer ɗin suka fice ta ƙofar baya, ko bai tambaya ba yasan lambu za ta kai shi.

    Sau nawa yana kiranta lambun su yi fira tana ƙin zuwa ?
    Sau nawa yana isketa ciki tana ganin shi take barin wajen, amma yau tsabar rainin hankali da mahaukaci taje gun.

    Haka ya wuce ɗaki ransa a jagule yana jin tamkar yayi ihu ko ya samu sauƙin zuciyarsa.

    Sai dai ya kasa natsuwa sai juyi yake a kan gadon, shi kam mahaukacin bai ma shi ba, ga shi kyakkyawan gaske, yana matuƙar kama da Aiman, kowa yasan Aiman kyakkyawan gaske ne kuma nesa ba kusa ba.
    Hakan yasa ya miƙe ya nufi lambun shi ma don ganin abin da suke ko ya samu natsuwa.


    Lambu

    Suna shiga ya ja yayi tsaye, ya haɗe rai yayi kicin-kicin da fuska, duk da dama bai cika fara'a ba amma dai yana sakar mata fuska yadda ya kamata, domin suna wasa da dariya yadda ya kamata da shi, amma daga ba ita ba bai sakarma kowa fuska asalima bai haɗa ido da mutane,ko da yaushe kansa a ƙasa yake bai kallon fuskar mutum.

    Ganin bai walwala sai taji duk ba daɗi don haka sai ta fara zolayarsa tana rugawa, nan da nan kuwa suka dinga zagaye lambun suna ɗibar ganye suna watsama junansu, ita dai sai dariya take sosai, shi kam murmushin ne mai sauti ke fita a fuskar shi.
    Duk wanda ya gansu kallo guda zai ɗauka masoya ne masu matuƙar ƙaunar junansu.

    Ƙasan bishiyar mangaro ta zauna tana dariya, shima ya zauna yana kallonta yana murmushi.

    Kallonsa ta yi ta ce, "Ameer ka dinga min magana idan nayi maka ka ji ?
    Shi dai kallonta kawai yake, ba alamar zai furta ko da kalma ɗaya.

    Zoben azurfar dake hannunta ya kai hannu akai yana taɓawa ga alama bai san ko miye ba, don haka ta cire ta kama hannunshi ta saka ma shi a yatsanshi tana murmushin yadda yayi ma shi kyau a hannun .

    "Kana so na bar maka shi ? Ta tambaye shi tana kallon shi.

    Murmushi yayi mata har kumatun shi ya lotsa.

    Hakan yasa ta fahimci cewar yana son zoben, don haka dinga cewa, "Inye Ameer yayi zobe mai kyau, inyee Ameer yayi zobe mai kyau."

    Shi kuma sai ƙara murmushi yake yana taɓa zoben.

    Kayi kyau sosai Ameer ɗina ka dinga fara'a tana maka kyau sosai ka ji ? Kan shi ya ɗaga mata alamar to.

    Sumar kanshi ta ga tayi yawa, don haka ta kai hannu tana taɓawa, ta ce "Ameer anjima zan kai ka aski kana so ai ko?
    Bakinsa ya zumɓura alamar bai so, dariya tayi ta ce, " Baka wani abu bane wannan gashin za a cire yayi yawa Ameer."

    Kanta ya fara taɓawa yana murmushi nufinshi itama kenan za ai mata abin da za ai mashin kenan.
    Ta fahimce shi sosai don haka ta fara nuna ma shi ban da ita shi dai za a yi ma wa ba ita ba.

    Duk abin da suke Abduljalal na tsaye yana kallonsu, fuskarshi babu alamar fara'a, domin ji yayi tamkar ya je ya shaƙe shegen ya wurga waje kowa ya huta ma.

    Yadda yake ganinsu haka itama Badiyya ke kallonsa ta ganshi sarai kawai bata da lokacin shi ne ita.
    Hakan yasa ta zaunar da Ameer ta dube shi da alamar lallashi ta ce, "Ka zauna a nan na shiga na fito mu je shagon aski ai maka mai kyau."

    Ɗaga mata kanshi yayi alamar to, ta shafa fuskarshi tana murmushi ta nufi hanyar cikin gidan.

    Abduljalal mamaki ya kashe shi a tsaye, ganin yadda Badiyya ta raɓa shi ta wuce bata kalli ko inda yake ba ta shige ciki.

    Cike da zafin zuciya ya isa gaban Ameer ɗin ya ɗaga hannu ya wanke ma shi fuska da mari ya fisgo ma shi riga ya zare ma shi idanuwa yana ma shi kashedi.

    "Idan baka bar gidan nan ba tabbas zan maganinka duk taurin kanka, kana mahaukaci kana shigema wadda nake so ?

    Duk maganar da yake ba wadda Ameer ya nuna ya san abin da yake cewa, hakan yasa ya sake kwashe shi da mari, dai-dai lokacin Badiyya ta sawo kai tana ganinsu.

    Da gudu kuwa ta iske shi ta janye Ameer ɗin dake sosa kumatun da ya mare shi.

    Har bata gani ta janyo Ameer ɗin hawaye na zubowa a idanunta tana taɓa inda shatin sawun hannun Abduljalal ɗin ya kwanta a fuskar Ameer ɗin.

    Sai da ta zo ya ɗago fuskarshi ya kalli Abduljalal ɗin ya sauke idonshi akan Badiyyar.

    Zabura yayi da yaga hawaye na zubowa daga idanunta, nan take ya runtse idonsa yana ƙanƙame jikinsa kamar mai jin sanyi.

    Ba ta ankara ba sai ganin Abduljalal tayi kwance ƙasa Ameer ya take ma shi maƙoshi da ƙafarsa sai mutsu-mutsu yake irin na azaba.

    Mamaki yasa ta kasa magana ko alama, kenan idan shi akai ma abu bai damuwa sai idan ita akai mawa yake damuwa ?

    Ko ko duk wanda akai mawa yake damuwa ban da shi ?

    Sai ga Abduljalal na neman sumewa yadda ya take ma shi cikin yasa numfashinsa neman ɗaukewa nan take.

    Ganin yana neman yi ma shi lahani yasa ta ce, "Ka rabu da shi mu tafi ka ji Ameer ɗina?
    Ko alamar jin ta bai ba, sai da ta yi murmushi ta tallabo fuskarsa ta ce, "Ba kyau faɗa mu je inda za mu kawai."

    Ganin tana fara'a yasa ya kama hannunta suka wuce, suka bar Abduljalal ɗin kwance yana dafe da cikin shi.


    Ko a hanya sai kallonta yake yana ƙara goge mata fuskarta, shi nufinshi hawayen yake goge mata.

    A shagon askinma ansha daru, domin ta ga maza ciki don haka ta ƙi shiga ta ce ya shiga, amma yayi biris da ita ya ƙi shiga.
    Mai askin ya leƙo yayi juyin duniyar nan amma Ameer ya ƙi yadda ya shiga ya barta a waje shi.

    Ƙarshe dai dole itama ta bi shi suka shiga cikin shagon tare.
    Kuma za ai askin shi bai yadda ita za tai ma shi wai.

    Ba ƙaramin artabu aka sha ba ya amince amma fa tana tsaye gabanshi ya riƙe mata hannuwa duka biyu sannan mai askin ya samu damar yi ma shi askin.
    Mutanen shagon su kai ta kallonsu shagon yayi tsit ana al'ajabin abin, domin basu gane mahaukaci ba ne, saboda shigarshi da natsuwarshi a fuska .


    Haka aka gama askin suka dawo gida ko takan Abduljalal bata sake bi ba ta wuce ɗakin da ta gyara ma shi ta kai shi ya kwanta ta fice zuwa nata ɗakin.





    Kano



    "Rayuwa kenan yau ni ne Maryam tai ma wannan abin ? Ashe daman Maryam bata da mutunci ? Yanzu kenan ni da Inteesar duk mun zama ɗaya tunda abin da tayi nima nayi shi ?
    Idan kuwa haka ne ya kamata na koma ga Inteesar mu cigaba da soyayyarmu cikin rufin asiri." (Shawarar da Imam ke yi kenan duk lokacin daya zauna shi kaɗai)
    "Sai dai kuma na daina ganinta, ko a hanya, tun ranar da ta maido min duk abin da na taɓa siya mata ban sake ganinta ba, ko tana ina yanzu ?

    Ƙanwarsa Yusrah ce ta shiga ɗakin cikin kukanta, ta tsugunna gabansa ta ce, "Yaya haƙiƙa na yadda kai baka da tausayi, haka baka sona, kanka kawai kake so, nayi nadamar zamowa ƙanwa a gareka !
    A yau ina jin cewa inama ace ni ce Inteesar ?
    Inama ace ni ce na samu Yayye irin nata ?
    A duk lokacin da na ga yadda Yayyenta suke mata rana sai na samu kaina da jin inama ace ni ce ita ? Saboda farin cikinta babu wanda bai sadaukar da nashi farin cikin ba a cikin Yayyenta, amma kai fa ?
    Kanka kawai ka sani sai soyayyar yarinyar da kowa yasan bata da kamun kai kake ta dako.
    Ka ci mutuncin Inteesar ka ci mutuncin Iyayenta hakama Yayyenta yau ga shi ni ƙanwarka na kamu da soyayyar Yayanta Yusuf .
    Ka sani Yaya Imam kayi babban rashi na masoyiyar kirki da daraja, haka ka rasa macen kirki macen ƙwarai wadda zata kula da kai harma da mu ahalinka.
    Amma Wallahi Tallahi ni ba zan yadda na rasa wanda nake so ba, ko da hakan na nufin bankwana da kai ne Yaya Imam !

    Idan bacin Inteesar da ahalinta mutanen kirki ne kai ka isa kai mata abin da kayi mata ne Yaya ?
    Miye laifinta don ta soka ? Ashe laifine don Inteesar ta nace ma soyayyarka ?
    Haƙiƙa ka shirya zuwan mummunar nadamar abin da ka aikata gareta Yaya.

    Kuma da gaske nake idan dai har ka ɗauke ni ƙanwarka kamar yadda Yayyen Inteesar suka ɗauke ta ƙanwa to ka je ga Yusuf ka shaida masa cewar ina sonsa idan ba haka ba komi zai iya faruwa kuma kai ne sanadi." Ta cigaba da rairo kuka mai tsuma zuciyar mai saurarenta.

    Baki ɗaya sai ta sanya ya sake faɗawa cikin wani mugun yanayin.
    Wai ya akai duk hakan ta faru ma?
    Shi fa yana da gaskiya kan lamarin nan, kawai tsabar kishinta ne yasa yayi duk abin da yayi mata, amma me yasa mutane suka gaza ganewa ne ?
    Mutanen da sukai masa magana kan Inteesar sun fi a ƙirga, musamman da tana gadon asibiti, to amma shi bai jin zai iya mata uzurin cigaba da soyayya da ita tunda yayi arba da hoton nan ya ji cewar ba zai iya cigaba da soyayya da ita ba ko alama.
    Ko yanzu da yake tunanin komawa gareta don kawai ga abin da ya faru ne tsakaninsa da Maryam bayan haka ina shi ina ita ?

    Yusrah ganin yayi banza ya ƙyaleta yasa ta tashi da gudu ta faɗa cikin gidan tana kuka sosai kamar ranta zai fita.

    Mahaifiyarsu ce ta nufeta da tambayar abin da ke faruwa amma ina kafin ta ida isa inda take ta yanke jiki ta faɗi ƙasa ba numfashi.




    Inteesar cikin ikon Allah ta dage karatunta take hankali kwance, duk weekend tana zuwa gida tayi abin ta, a nan ne take samun labarin Imam ya rabu da wadda zai aura wai ƴar iska ce, taɓa bakinta tayi ta dubi Kakar ta ce, "Shi dai ya sani, ni kam ko a hanya bani fatar abin da zai haɗani da Imam balle labarinsa da ɓata lokaci ne a gareni."

    Sosai manema ke zuwa gun Inteesar amma sam ta ƙi saurararsu domin akwai abin da ta saka ma ranta, wanda tana ganin shi ne kawai zata yi ya zama ta ɗauki fansar abin da Imam yayi mata, don haka take ba kowane saurayi haƙuri idan ya zo gareta.

    Kasancewar anyi na farko ba a ji da daɗi ba yasa kowa na gidan saka mata idanuwa, har zuwa lokacin da zata kammala karatun ta sai a yi mata maganar fidda miji tai aurenta.

    Ko da yaushe takan fiddo wayarta ta kalli hoton tayi murmushi, ba shakka zata guma ma Imam takaici da wannan hoton, tabbas zata sa ya shiga mafiyin halin da ta shiga sanadin hoton nan, dole shima na shi zagayen ya zagayo .

    "Ban sanka ba, haka jikina na bani baka Sanni ba, to waye yayi mana wannan aikin ?

    Tabbas a baya na tsaneka haka na ji ban da maƙiyi sama da kai a rayuwata, amma a yanzu nemanka nake ido rufe domin ramuwar gayya ga Imam."

    Ban san ko zaka aminta da ni ba amma ina fatan ka amintar domin samun biyan buƙatar da nake nema.

    Tabbas ba zan iya yafe ma Imam tozarci da wulaƙancin da yayi min ba !

    Fansa zan ɗauka ta gasken-gaske a garesa don Allah ka bayyana gareni da gaggawa."

    Ko da yaushe maganarta kenan idan tana kallon hoton wanda har zuwa yanzu ko mai kama da shi bata taɓa gani ba, duk kuwa da yadda take ankare da mazajen da take gani .



    Bauchi


    Aiman kai tsaye ya shige gidan, da tunanin nan ne gidan da tsohuwar da ta kai ma shi abinci take.

    Da sallama ya shiga gidan, kamar jira ya ji muryar yarinyar nan mai shegen surutu ta amsa, bigit sai gata ta fito tana kallonsa tana murmushi.

    Da ƙyar ya iya yi mata magana.

    "Ina tsohuwar take ?

    Ɗakin tsohuwar ta nuna ma shi da yatsa tana sake ƙunshe dariya a fuskarta.

    Girgiza kanshi yayi ya nufi ɗakin, (ita komi sai ta saka wasa)a cewar shi.

    Kaka na zaune ta yi zugudum tana tunanin jikanta, ta ji sallamar shi, da sauri ta amsa tana ƙare ma shi kallo, tabbas komi na shi irin na marigayi Muhseen ne.

    Zama yayi ya gaidata, sai ya samu kanshi da jin matuƙar tausayin tsohuwar ganin tana tsohuwa amma ga damuwa nan kwance a kan fuskarta .

    Cikin lokaci kaɗan ya bayyana mata ko waye shi, da kuma cewar ya zo ne wani aiki a garin wanda bai san lokacin da zai kammala ba.

    Ba ƙaramin murna ya gani a fuskarta ba, hakan yasa shima ya ji nan take tsohuwar ta kwanta ma shi a ranshi.

    A hankali ya dinga janta da labari, nan da nan kuwa sai ga su kamar sun saba da juna, abin har mamaki ya dinga ba shi a ƙasan zuciyarshi yadda ya saki jikinsa da tsohuwar daga ganin farko.

    Ya jima suna tare kafin ya miƙe yace zai fita ya dawo.

    Kai tsaye ya fice daga gidan ya hau napep yace a kai shi kasuwar garin.

    Ba ɓata lokaci sai ga shi sun isa, ashe ma babu nisa tsakaninsu da kasuwar.

    Nan fa ya dinga siyayyar kayan abinci masu yawa ya koma ɓangaren lemuka da kayan shayi.

    Ya gama tsab ya biya kuɗin kai kayan aka biyo shi da su sai gida.

    Yana zuwa ya nuna sashen tsohuwar yace a shiga da su.

    A lokacin kuma Kaka da Zainab na ta shawarar abin da za su ba shi ya ci, domin dai babu komi a gidan na su na abinci , sun tabbatar da yadda ba a ba su shima ba zai samu ba.

    Kawai sai ga kaya ana ta shigowa da su na abinci iri-iri abin da ya ba su mamaki kenan.
    Suka ce ba nan bane za a kawo cikin babban gidan ne.

    Masu shigar da kayan suka ce nan aka ce masu.

    Hawayen daɗi suka cika idanunsu, Kaka ta fara tunanin Allah Ya shirya mata ɗanta ya gane gaskiya kenan tunda ya karkato kanta yau.

    Sai ga Aiman ya shigo ɗauke da wata leda babba ya miƙa mata yana ce ma Zainab, "Ki duba abin da babu a samo maku."

    Sai lokacin suka fahimci daga gareshi kayan suke .

    Kaka ta fara yi ma shi faɗa, daga ƙarshe ta koma kan Zainab tana cewa ita ce ta gaya ma shi babu kayan abincin.

    Taita rantsuwa babu ruwanta, sai da ya kalli Kakar yace, "Ki yi haƙuri ni ma Babana ya aiko ni ba daga gareni bane ."

    Abin da basu sani ba shi ne lokacin da yana zaune suna fira da Kakar ya lura da Zainab ta fice ta dawo ɗauke da garin kwaki a leda fara ta shige ɗakin.
    Nan take ya fahimci babu wadataccen abinci a gidan, ganin kuma ta jiƙa ta kawo ma Kakar ta ce ta sha, ita kuma ta amsa ta ɗan sha ta miƙa mata, sai ta miƙa ma shi, wai ya sha.

    Nan take ya ji tausayinsu ya kama shi, yake jin cewar suna cikin matsala, ba shakka sai ya binciki damuwarsu kafin ya bar garin ya magance masu ita, duk da bai damu da shiga sabgar mutane ba, amma sai ya ji tasu ta dame shi .

    Cikin kwana biyu da yayi a gidan ya gama fahimtar komi na gidan da yadda yake tafiya.

    Wato ita Hajiya ƙarama ita ce matar gidan kuma Alh ɗane ga Kaka ita kuma Zainab ba ta da mahaifiya ta rasu, a cikin lokacin ne kuma ya ga abin da yayi matuƙar ba shi mamaki wato ganin hoton mahaifiyarsu Zainab ɗin kamar Ummar shi sak kama suke sosai wadda kallo guda take bayyana.

    A lokacin ne dai ya ga hoton marigayi Muhseen ɗin da suke cewa yana kama da shi sosai, sai dai shi bai ga kamar ba ya ga dai yayi kama da ƙanwarsa Badiyya sosai duk da tana mace yana namiji.


    Ta ɓangaren Hajiyar gidan kuma abin ba daɗi domin bata da kirki ko kaɗan bata da mutunci, sannan ta raina maigidan sosai, abin takaicin ma yadda sai abin da ta ce ake aikatawa a cikin gidan.

    Gaban kowa take rashin mutuncinta, ta zagi Kaka ta zagi maigidan a gabanshi bai iya cewa komi, sai ma haƙuri da yake bata wai bai son ɓacin ranta.

    Ranar da rashin mutuncinta ya juyo kan Aiman ɗin ta sha mamakin yadda yayi kunnen uwar shegu da ita da tana gaya ma shi ya bar ɗakin Muhseen ya koma ɗakin da ke kallon nata ɗakin.

    Shi kuma ya shaida mata ɗakin yayi ma shi sosai don haka ba inda zai koma.

    Ba komi yasa ta ce ya bar ɗakin ba sai bokanta da ya shaida mata cewar yaron dake ɗakin na gab da tona asirin dake rufe cikin ɗakin yadda ko da yaushe yake kan karatun Alkur'ani da yawan sallah tare da sadakar da yake yi.

    Sannan ya gaya mata cewar a gun da suka rufe asirinsu yake aiwatar da sallar shi wanda hakan barazana ce ga aljanin dake tsaron wajen.

    Hakan yasa ta ce ya bar ɗakin shi kuma haka kawai sai ranshi ya ba shi cewar akwai abin da yasa ta ce ya bar ɗakin ba kamar da Kaka ta na shi labarin asalin mai ɗakin da yadda akai ya rasu.

    Hakan yasa ya ɗauki alwashin bincikar ɗakin da kyau don ganin abin da yasa take son ya bar ɗakin.


    To fa ko ya zata kaya ?


    Haupha ✍️  less  less
    • 7 people like this
    • samira ibrahim
      Ameera Garba Tnx
      • December 20, 2020
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • samira ibrahim
      Salisu Abdullahi Jinjina gareki daughter 👍
      • January 2, 2021
      • -
      • Report
  • samira ibrahim
    samira ibrahim joined the group ZAUREN RUFAIDA UMAR
    December 16, 2020
  • samira ibrahim
    samira ibrahim → ZAUREN KACI-CI-KACI-CI:
    Assalamu Alaikum

    Samira...  more
    Assalamu Alaikum

    Samira Ibrahim

    Amsoshin kacici-kacici

    Q1.Kainuwa writers Association

    Q2.1-Haske writers Association

    2-Nguru writers Association

    3-Gaskiya writers Association

    4-Strong pen writers Association

    5-Zaman Amana writers Association

    Q3.Adams Garba

    Q4.Maryam Haruna
    Hauwa'u Muhammad

    Q5.1 Aisha shafa'i
    2 Bello Hamisu IDA
    3 Zaidu Ibrahim Barmo
    4 Muttaka A Hassan
    5 Fatima Ibrahim Garba (Dan borno)

    Q6. Dakashi nonon akuya Wanda ake tatsa na sabuwar haihuwa Ana soyashi kamar cuku.

    -Aya-Aya kuma dakkuwa
    -salga kuma Ana nufin Masai.

    Q7. Idan ansha fura xa'a kai ga dallaki

    Idan ansheka mata ruwa zai zama farau-farau

    Idan an shanye farau-farau za'a sami tsaki.

    Q8.Kwaruru -Kuriga
    Sha bulta -itama tana nufin kuriga Amma wadda aka riga aka cire bawonta.
    -kwaras kwaras kuma ita ce busassar kuriga
    -Lubbatu kuma itama dafaffiyar kuriga ce.

    Q9.Tatsuniya kirkirarran labarine da ake yiwa yara
    - Ana kiranta Gatanan gatanku.

    Q10.Fatima
    Rukayya
    Zainab
    Ummulkursim
    Abdullahi
    Qasim
    Ibrahim.  less
    December 14, 2020
    • Hafsat Umar, BILKISU ZAKARI BK, and nusaiba sani like this.
  • samira ibrahim
    samira ibrahim joined the group ZAUREN LAMTANA BINGEL/NOVELS ONLY
    December 13, 2020
    • BILKISU ZAKARI BK, Ummyter Abdallah, and Zainab Isa Ahmad like this.
  • samira ibrahim
    samira ibrahim liked Aisha Abdullahi's post.
    December 8, 2020
    Aisha Abdullahi → MARUBUTA:
    SAMA TA YI WA YARO NISA, SAI DAI YA MIƘA KAI YA YI...  more
    Aisha Abdullahi → MARUBUTA:
    SAMA TA YI WA YARO NISA, SAI DAI YA MIƘA KAI YA YI KALLO!


    Hujja ta...  moreSAMA TA YI WA YARO NISA, SAI DAI YA MIƘA KAI YA YI KALLO!


    Hujja ta uku


    Makaho yana abubuwa da yawa waɗanda kurma ba shi da su; yana da haƙuri, kawaici, hangen nesa, ilmi, kamala, hikima da sauransu. Ko a cikin al'umma an fi lissafa makafi cikin mutane kammalalli, domin makaho zai iya bayar da shawara kuma idan aka yi amfani da ita sai ta amfanar da al'umma, amma wani kurma an fi lissafa shi cikin yara ko jerin gama-gari.
    Haka zalika a zamantakewa makaho yana da hikimar tsara zance, wannan dalilin ya sa ko saɓani makaho ya samu da abokiyar rayuwarsa zai rarrashe ta cikin kalamai masu sanyaya zuciya, waɗanda za su yi tasiri a zuciyarta sosai saboda kalamai ta hanyar furuci suna matuƙar tasiri ga wanda aka faɗa wa su. Amma kurma fa? Ba zai iya rarrashin matarsa ba cikin daɗin rai.

    A ɓangaren tarihi kuwa har zuwa duniyarmu ta yanzu, an yi makafi mawaƙa masu hikima. Ko a mawaƙan Hausa akwai irin su Dr Aliyu Na Mangi Zaria wanda har gobe malamai suna sharhi a kan waƙarsa, da Ali Makaho da sauransu.

    Da waɗanan hujjojin ya isa mu fahimci cewa makanta ta...    less
    • 44 people like this
    • View all 37 comments
    • samira ibrahim
      Nura Ismail Gaskiya ne wannan makafi suna da tarin baiwa.
      • December 9, 2020
      • -
      • 2 like this
      • -
      • Report
    • samira ibrahim
      nafiu Muhammad Magana mai ma'ana, jinjina
      • December 9, 2020
      • -
      • 4 like this
      • -
      • Report
    • samira ibrahim
      nafiu Muhammad Allah ya bada nasara
      • December 9, 2020
      • -
      • 3 like this
      • -
      • Report
    • samira ibrahim
      Hafsat Umar MashaAllah tabbas makanta tafi kurumta Allah y bada nasara
      • December 9, 2020
      • -
      • 4 like this
      • -
      • Report
    • samira ibrahim
      Samira Hamissou Amine yayana
      • February 21, 2021
      • -
      • Report
  • samira ibrahim
    samira ibrahim liked Aisha Abdullahi's post.
    December 8, 2020
    Aisha Abdullahi → MARUBUTA:
    Hujja ta farko

    Bari mu fara da Alƙur'ani mai girma, sau da yawa idan za a yi bayanin ni'imomin da Allah Ya yi wa ɗan Adam akan fara da ni'imar ji sannan gani. Haka kuma idan ana aibantar da kafurai, akan buga misali da...  more
    Aisha Abdullahi → MARUBUTA:
    Hujja ta farko

    Bari mu fara da Alƙur'ani mai girma, sau da yawa idan za a yi bayanin ni'imomin da Allah Ya yi wa ɗan Adam akan fara da ni'imar ji sannan gani. Haka kuma idan ana aibantar da kafurai, akan buga misali da cewa sun kurumce sannan a ce...  moreHujja ta farko

    Bari mu fara da Alƙur'ani mai girma, sau da yawa idan za a yi bayanin ni'imomin da Allah Ya...    
    • 36 people like this
    • View all 41 comments
    • samira ibrahim
      Samira Hamissou Wannan zance naki gaskiya 'yar'uwa.

      Fatan alheri da fatan nasara.
      • December 9, 2020
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • samira ibrahim
      Mariam Harounz Ma sha Allah!\n\nKa ji zance na gaskiya da gaskiya. Fatan nasara
      • December 9, 2020
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • samira ibrahim
      Aliyu Labaran Balarabe Masha Allah wannan zance haka yake
      • December 9, 2020
      • -
      • 2 like this
      • -
      • Report
    • samira ibrahim
      Aliyu Labaran Balarabe A gsky makaho yafi kurma sbd Mafi yawanci bazaka samu kurma ba Akan hanyar neman ilimi ko son cigaba na harkar rayuwa Sai dai kagansu wajen wanki da guga Amma Akwai makahi masu karatu Arabi da boko wannan kadai ta ishemu hujja
      • December 9, 2020
      • -
      • 2 like this
      • -
      • Report
    • samira ibrahim
      Maman twins Wannan haka yake Masha Allah
      • December 9, 2020
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
  • samira ibrahim
    samira ibrahim liked Aisha Abdullahi's post.
    December 8, 2020
    Aisha Abdullahi → MARUBUTA:
    WITSIYAR RAKUMI TA YIWA KASA NISA

    Hujja ta...  moreWITSIYAR RAKUMI TA YIWA KASA NISA

    Hujja...  more
    Aisha Abdullahi → MARUBUTA:
    WITSIYAR RAKUMI TA YIWA KASA NISA

    Hujja ta...  moreWITSIYAR RAKUMI TA YIWA KASA NISA

    Hujja ta biyu

    Babban abun birgewa za ka sami makaho a islamiya aji ɗaya da masu gani yana kwasar ilmi. A makarantar boko ma aji ɗaya da masu gani sannan kuma a tare ake faɗa masu darasi suna rubutawa, masu gani suna amfani da biro da takarda, shi kuwa cike da birgewa yana amfani da na'ura wacce duk harafin da ya danna ya san shi. Amma kurma fa? Sai dai a ware masa karatunsa daban da 'yan'uwansa kurame.

    Ƙarin abun ban shawa ga Makaho shi ne za ka same shi yana koyarwa a ɓangaren addinin islama da boko don a kwai makafi mahaddatan Alk'ur'ani, da wannan koyarwa zai iya riƙe kansa da iyalansa har ƙarshen rayuwarsa. Amma kurma fa? Ina! Ba zai iya ba!
    Haka zalika makaho yakan yi limanci masu gani su bi bayansa, saɓanin kurma da babu ta yadda zai iya yin limanci sai dai ya zo ya ya bi jam'i bayan makaho. Har a Saudiyya an yi wani makaho mai suna Abdul'Aziz Bn Bazz wanda yake jagorancin sallah. Haka zalika a zamanin Manzon Allah (SAW) a kwai wani sahabi makaho mai suna Ibn Ummul Makhtum wanda yake kiran sallah. Da wannan hujjar nake ƙara tabbatar da cewa makanta ta fi kurumta, don makafi suna da tarin...    less
    • 35 people like this
    • View all 44 comments
    • samira ibrahim
      Aliyu Labaran Balarabe Tabbas makaho zai iya zama aji daya da masu gani wannan kadai iya ishemu hujja Akan ladanin manzon Allah (SAW) Alhmdllh muna godiya Allah ya qara nasara
      • December 9, 2020
      • -
      • 2 like this
      • -
      • Report
    • samira ibrahim
      Aliyu Labaran Balarabe Ga wani misali zan buga A jaharmu wato zamfara state kam zamfara Wanda yafi kowa ilimin hadisi da sanin sa makawo ne Ajahar mu kunga ko tabbas makaho yafi kurma sbd babu ta inda za ace gawani kurma Wanda ya rika wani matsayi na fanin ilimi malamin...  moreGa wani misali zan buga A jaharmu wato zamfara state kam zamfara Wanda yafi kowa ilimin hadisi da sanin sa makawo ne Ajahar mu kunga ko tabbas makaho yafi kurma sbd babu ta inda za ace gawani kurma Wanda ya rika wani matsayi na fanin ilimi malamin hadisin nan shine malan haruna hizburahim makaho Nagode  
      • December 9, 2020
      • -
      • 3 like this
      • -
      • Report
    • samira ibrahim
      Samira Harouna Allah yasa mu dace, hak'ik'a Allah yana rufe musu ido amma kuma zuciyarsu a bud'e take da kwakwalwarsu, suna da saurin d'aukar abu da basira nesa ba kusa ba
      • December 9, 2020
      • -
      • 3 like this
      • -
      • Report
    • samira ibrahim
      Aisha Abdullahi Tabbas hakan ne, ai akwai makafi manyan malaman addini ko masu ido ba za su nuna masu ilimi ba
      • December 9, 2020
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • samira ibrahim
      Samira Hamissou 😅
      • February 21, 2021
      • -
      • Report
  • samira ibrahim
    samira ibrahim liked Aisha Abdullahi's post.
    December 8, 2020
    Aisha Abdullahi → MARUBUTA:
    Gabatarwa.

    Amincin Allah Ya tabbata a gare ku ya ku ahalin wannan zaure mai tarin albarka. Kama daga: Mahukunta, Alƙalan wannan gasa, masu gabatarwa, abokan karawa, da kuma masu bibiyar wannan gasa.
    Na...  more
    Aisha Abdullahi → MARUBUTA:
    Gabatarwa.

    Amincin Allah Ya tabbata a gare ku ya ku ahalin wannan zaure mai tarin albarka. Kama daga: Mahukunta, Alƙalan wannan gasa, masu gabatarwa, abokan karawa, da kuma masu bibiyar wannan gasa.
    Na tsaya a nan ne da nufin bayyana gamsasun...  moreGabatarwa.

    Amincin Allah Ya tabbata a gare ku ya ku ahalin wannan zaure mai tarin albarka. Kama daga: Mahukunta, Alƙalan wannan gasa, masu gabatarwa, abokan karawa, da kuma masu bibiyar wannan gasa.
    Na tsaya a nan ne da nufin bayyana gamsasun...    less
    • 39 people like this
    • View all 21 comments
    • samira ibrahim
      Samira Hamissou Wannan gaskiya ne!
      • December 9, 2020
      • -
      • Report
    • samira ibrahim
      Mariam Harounz Wannan zance naki gaskiya ne fatan nasara
      • December 9, 2020
      • -
      • Report
    • samira ibrahim
      Aliyu Labaran Balarabe A gsky Nima Ina bayanki Akan wannan magana makanta tafi kurumta Allah yabaki ikon kawo hujjoji masu inganci ya Kuma shiga cikin lamarin ya bada nasara mai dorewa Amin
      • December 9, 2020
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • samira ibrahim
      Haupha123 Ameen-ameen.
      • December 9, 2020
      • -
      • Report
    • samira ibrahim
      Samira Harouna Allah ya bada sa'a
      • December 9, 2020
      • -
      • Report
  • samira ibrahim
    samira ibrahim → ZAUREN KACI-CI-KACI-CI:
    Samira Ibrahim umar

    Q1. Mutane dubu...  more
    Samira Ibrahim umar

    Q1. Mutane dubu saba'in

    Q2.Sayyidina Abubakar
    Sayyidina Umar
    Sayyidina Uthman
    Sayyidina Aliyu

    Q3. Dawwama a wurin biyayya ga iyaye
    Sallah cikin lokaci

    Q4. Allah ( S W T)

    Q5.1-son iyalan gidan Annabi.
    2-Soyayyar Annabi (S.A.W)
    3-Karatun alqur'ani.

    Q6.Munkar wa manakiri

    Q7.Dharham

    Q8. C 79

    Q10. Ranar juma'a
    Abu hisham.  
    December 7, 2020
    • Nana Aicha Hamissou and Ameera Garba like this.
  • samira ibrahim
    samira ibrahim joined the group KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
    December 3, 2020
    • Nana Aicha Hamissou likes this.
  • samira ibrahim
    samira ibrahim joined the group Sababbin Litattafan Halima K/Mashi
    November 22, 2020
    • nafisa Abdullahi, Zaharadden Nasir, and safnah Aliyu jawabi like this.
  • samira ibrahim
    samira ibrahim → ZAUREN KACI-CI-KACI-CI:
    Assalamu alaikum
    ...  more
    Assalamu alaikum

    Q1.114

    Q2.Abay hasan almaliki asshazali.

    Q3.Sayyidina uthman
    Saboda ya auri 'yayan manzon Allah S .A.W.

    Q4.Nasir Muhammad Abu Alayth Al-samar gandi.

    Q5.Bazara

    Q6.Hankaka

    Q7.Benin

    Q8.1960.  
    November 16, 2020
    • Nana Aicha Hamissou and Rahmatu Lawan like this.
  • samira ibrahim
    samira ibrahim → ZAUREN KACI-CI-KACI-CI:
    Assalamu alaikum
    November 15, 2020
    • 5 people like this
    • samira ibrahim
      Nana Aicha Hamissou Wa aleikissalam
      • November 15, 2020
      • -
      • Report
  • samira ibrahim
    samira ibrahim joined the group ZAUREN KACI-CI-KACI-CI
    November 15, 2020
    • Nana Aicha Hamissou and Haupha123 like this.
View More
Loading ...

About

Personal Information

  • Sunan Farko samira
  • Jinsi Mace
  • Ranar Haihuwa October 10, 1993
  • Takaitaccen Bayani Ni sunana Samira Ibrahim an haifeni a garin birnin kebbi inada Aure da yara biyu.

Contact Address

  • Sunan Gari kebbi state
  • Karamar Hukuma birnin kebbi
  • Sunar Jaha birnin kebbi
  • Sunar Kasa Nigeria
© 2022 Bakandamiya About Terms Privacy Subscription Earn Money Advertise Contact
  • Facebook
  • Twitter
  • Linkedin
  • Youtube
  • Pinterest
  • Instagram