Bakandamiya
GORON JUMMA'A
Assalamu alaikum Malam,
Mutum ya rasu sai ya bar yayye biyu maza, da yayye mata wadanda suke uba daya, da kuma mahaifiyar sa, ya za a raba musu gadon?
Amsa:
Wa alaikum assalam,
Za’a raba dukiyar kashi shida, a bawa uwa kashi daya, ragowar kashi biyar din a bawa yan'uwa su raba, namiji ya dauki rabon mata biyu.
Amsawa:
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
Daga zauren Fatawowin Rabon Gado Guda 212