• Contrast
    • Font
    • A
  • Sign In
  • Sign Up
    Loading ...
View All Updates Mark All Read
Bakandamiya
  • Shafin Farko
  • Mambobi
  • Zauruka
    • Browse Groups
  • Tambayoyi
  • Ra'ayoyi
    • Browse Polls
  • Makalu
    • Browse Entries
  • Bidiyoyi
    • Browse Videos
  • Sautuka
    • Nemo Sautuka
  • Hotuna
    • Browse Albums
    • Browse Photos
  • More
    • Kasuwa
      • Stores Home
      • Browse Stores
      • Browse Locations
      • Products Home
      • Browse Products
      • Products Pinboard
      • Categories
      • Browse Reviews
      • Wishlists
    • Sana'o'i
      • Browse Listings
    • Sanarwa
      • Bukukuwa Masu Zuwa
      • Past Events
  • Updates
  • About
  • Abokai(22)
  • Hotuna(1)

Updates

About

Personal Information

  • Suna usman
  • Jinsi Na miji
  • Ranar Haihuwa November 21, 2000
  • Relationship Status Single

Contact Address

  • Sunar Unguwa Zoo Rd [map]
  • Sunan Gari kano
  • Karamar Hukuma municipal
  • Jaha kano
  • Kasa Nigeria

Abokai

  • Bakandamiya Muna matukar godiya, jinjina da ban gajiya ga duk waɗanda suka samu damar halartar taron bada kyautuka na Muhawarar Bakandamiya 2020, harma da wadanda suka yi ta aiko mana da sakonnin farin ciki da fatan alkhairi. Allah Ya sa kowa ya koma gidansa lafiya. Mun gode, mun gode. Allah ya bar zumunci.
  • Rahmatu Lawan Barkanmu da Jumma'a 'yanuwa. Allah Ya sada mu da albarkatun da ke cikinta!
  • Lawan Dalha Ya Allah Ka sada mu da alkhairan da ke cikin wannan rana; ka tsare mu daga sharri duniya da lahira. #JummaaMubarak
  • Sani Mohammed Sadiya Sms
  • Jamila Mustapha Iskokai Sun Kori Shugaban Kasar Brazil Daga Fadar Gwamnati Kwanaki 10 kacal bayan shi da iyalinsa sun koma fadar gwamnatin kasar, shugaban Brazil Michel Temer ya tattara ina sa ina sa ya koma fadar mataimakin shugaban kasa. Ya bayyana dalilinsa da cewa akwai iskokai mara sa kyau a gidan. Ya ce shi da matar sa da dan sa mai shekaru 7 ba sa iya barci da daddare saboda wasu irin motsi motsi da suke ji, kuma tun da suka shiga fadar gwamnatin, jikinsu bai gamsu da shi ba. Fadar shugaban kasar wanda ake kira Alvadora Palace dai katafaren gida ne wanda ya kunshi abubuwan more rayuwa da dama. Sai dai shugaban ya ce shi da iyalinsa sun fi sakewa a fadar mataimakin shugaban kasar mai suna Jaburu Palace wanda ya fi kankanta. Toh dama dai shugaban shi ne mataimaki kafin majalisar kasar ta tsige tsohuwar shugaban kasar, Dilma Roussef a kwanan nan, kuma iyalinsa sun riga sun saba da fadar ta Jaburu.
  • Hadiza Balarabe Wata budurwa nahango tsaye Bakin titi da Jan kaya da farin hijab dagani makaranta zata Hmm FAUZA YAR WANKA kenan kubiyomu donjin ya zata kaya zata MAKARANTAR kuwa? https://youtu.be/BZsKZJhHjOU
  • Zahra A. Alkali ???? _*????????a? ????r??er'? ??????oc?a??on*_ ????( _*K?ng?ya Daya Ta??ar D???*_) Hikmahwritersassociation2019@gmail.com load?ng...........????? ???? *R??A??Y??U??W??A??R?? Z??A??M??A??N??I??* ( _K??O?? S??O??N?? Z??U??C??I??Y??A??_) W??r??i??t??t??e??n?? b??y?? _*Z??a??h??r??a?? A?? A??l??k??a??l??i?? (D??i??d??e??e??y??l??o??v??)*_ Dedicated to Autan Hikima???? _B??I??S??M??I??L??L??A??H??I??R?? R??A??H??M??A??N??I??R?? R??A??H??I??M??_ 3??4? Raihan na komawa office ya aiki masinga akan yaje yace ma head din ko wani department yana son ganinsa aconference hall, babu 6ata lokaci duk yabi ya fadamusu kafin ya koma ya sanar da zuwansu. Yana zaune a office kafin ya fara komai yaga hoton kannen nasa dake cikin karamin frame fuskar Muhievert ya shafa yace "I love you sister but you won't understand why am always harsh toward you change for good please (inasonki kanwata amma ba zaki gane mai yasa nake takuraki ba, dan Allah ki chanja hali)" ya fad'a yana murmushi sallaman Baba masinja ne ya katse mishi tunani bayan ya amsa masa sai yace ya duba mishi office din Abbu koya iso bai dade ba ya dawo yace ya iso, tashi yayi ya wuce conference hall bai kai minti goma ba yaji sun shigo tashi yayi ya kira Abbu kafin ya dawo ya zauna ajerin kujerun da ke jikin babban table din babu dadewa Abbu ya fito atare suka tashi sai da ya zauna sannan suka gaisheshi suma suka zauna babu 6ata lokaci kowa ya gabatar da duk ayyukan da akayi acikin Department dinsa da yake duk sun saba da barin record hakan ya saukaka musu k'ar6a Abbu yayi ya fara gani, inda za'ayi signing yayi inda yaga da bukatan karin bayani sai ya sake tambaya kafin Raihan yayi stamping sannan ya k'ara musu albashi daga kan k'ananan maaikatan zuwa manya kafinnan ya sallame su sosai sukayi murna tare da mishi fatan alkairi. Ammi ce a kitchen tana dafa abinci dan duk kudin su bata wasa da damarta wajen yima mai gida girki in dai ba abunda yaran suke sonci ba duk wani girkin Abbu ita takeyi bata sakaci da hurumin mijinta tana aikinta tana ta salatin Manzo (s.a.w). Chan dai tayi shiru tana tunanin yarta kafin tayi ajiyar zuciya sai da ta gama komai ta kwashe na Abbu akularsa wanda yake daban dana yaran gida harma dana bak'i kafin ta kira kande cikin dadin murya ba cikin nuna isa ba tace idan sun gama gyaran cikin gidan su jera abincin a dining na Abbu su kai sama na yaran abari ak'asa sai su saka turaren wuta aduk kusurwan gidan domin ya fitarda kamshin daya shigo daga kitchen sai Ac shima su kunna dan kamshin ya bada abu mai dadi kafin ta wanke hannunta ta nufi sama. Dakin Abbu ta shiga ta k'ara gyarawa tare da sanya turaren wuta sai d'akinta shima ta gyara ta saka turaren wuta ta kunna Ac kafin ta shiga band'aki ta wanke tas ta fesa airfreshner daganan ta shiga wanka tare dayin alwala fitowa ta shiga shafe shafen su humra don lokacin sallah bai karisa ba, kaya ta saka riga da zani mai manyan pattern wanda akayi design din jikin kayan da pattern din bayan tayi simple makeup ta duba agogo taga har lokacin salla yayi da sauri tasa hijab dinta tayi kabbara bayan ta idar ta dad'e tana yiwa iyayenta da yaranta da mijinta addu'a kafin ta tashi daga kan darduman. Tana idarwa taji horn din mota ajiye hijab din tayi ta fita danyi musu sannu da dawowa. ??? Yana karasawa ya bar gurin da gudu saboda ya san halin Goggo sarai yanzun nan sai ta daka mai dundu kama baki tayi tana cewa "yau ni dannan zau ce dama ni na mutu, lallai ubanka zai zo yatarar dani wato har ya haifi dan da zai iya fadamin haka da sauri ta kwalawa Ibro kira ta mika mishi waya ungo danno min layin balarabe yi abu da jiki maza-maza karka 6atamin lokaci" ringing daya biyu ya dauka yana cewa "hello Goggo" tace "elon ubanka, eh nace elon ubanka ko kanada magana ne sai kuma ta fashe da kuka, wato d'an nan katuromin hatsabibin yaronnan saboda yazo ya cimin mutunci koh? ya zageni tatas daga ni har zuria ta balarabe kayi kokari da kai da wannan munafukar matar taka". Kukan data k'ara sawa ya d'aga hankalin Malam Balarabe arikice yace "haba Goggo dan Allah kiyi haku..." bata bari ya karasa ba tace "nace hakurin ubanka wallahi zan tsine maka tunda baka da mutunci" ta fada tana wurga wayan. Goggo! Goggo!! Goggo!!! Da sauri ta fito tana cin goro tana kokarin gyara zaninta "nace lafiya daiko kake min kira haka ubana dan ko ubana ne kawai zai kirani irin haka banza gantalalle mara mutunci" Hararanta yayi kafin yace "ba lafiya ba Goggo taya za'ayi ke kici abinci ki rage sannan wai inci? ai wannan ci bayane kawai cin abincin da kika rage haka kawai nasan ba wai wani wanke hannu kikayi ba kilama kinaci na bakin naki na komawa ciki but you're expecting me to eat this haba ai wannan abincin dabbobi ne kawai zasu iya ci ni kuma kinga mutunne ba dan kuikuyo ba" salati Goggo tayi ta rike baki tana kallonsa har zata d'auko muciya ta bi bayansa sai kuma ta fasa tace "lalle dannan wuyanka yayi kyauri ya isa yanka, wato nikake fadawa haka saboda ka mugun rainani wlh ba laifinka bane laifin uban kane daya aikoka kaci zarafina kuma na gode amma dan uwarka mai zakaci inba wannan din ba sai dai idan zaka dafa danwake inkuma ba haka ba sai dai fa ka kwana da yunwa". Hararanta yayi yace "cin abincin gidanki ko virus ni kinga tafiyata zanje naci indomie da kwai awajen mai shayi koba komai yafi wannan dattin tuwon da kika rage". Haushine ya kama Goggo kawai ta saka kuka tana cewa "oni yau naga yaro jarababbe aiko iyayenka zan sama duk sai naci mutuncin su". ??? Awani babban mall suka tsaya koda taga haka ba tace komai ba dan tasan suna da bukatan sayan kaya saboda haka itama ba tace kala ba ta fita suka shiga kantin vibration din wayanta ne yasa ta tsaya ganin mai kiran yasa tayi murmushi. "Hello darling brother my one and onl...." bai bari ta k'arasa ba azuciye ya amsa da cewa "waye darling din naki kina matsayin kanwata gida daya muke kwana muke tashi but you cant check on me kullun banganinki da safe, da dare kuma kinyi barci shin me kike nufi me kike tunani kina koyawa yan uwanki eh?" Marairaicewa tayi kafin tace "Yaya plx am sowie yaukan zan jira kadawo cox i really missed you dear kayi hakuri zan kiyaye ba zan sake haka ba kaji" ok kawai yace har zai kashe wayan sai kuma ya sake cewa "kar ki kuskura ki kai 6 awaje baki dawo gida ba" kafin ma ta amsa ya kashe ta6e baki ta ajiye wayan ta shiga ta iske harsun gama jakarta ta fitar ta cire makudan kudi ta mika musu sannan tace "gashi idan ya rage sai ku raba chanjin. Zaune yake a farfajiyar gidansa yana shan iska Hajiya ta shigo rike da tray babba "barka da hutawa baban Raihana" murmushi yayi kafin yace "yawwa barka dai uwar 'ya'yana wani beta kika had'omin tun dazu kamshi ke tashi? Alhaji kenan baka rabo da zolaya. "Ammi me kika dafa mana" Zahra data dawo daga makaranta kenan ta hangosu a gurin shan iska shine ta nufi gurin dan ta gaishesu hannu ta mika zata bude flask din cikin zolaya Hajiya ta buge hannunta tana cewa "ban sani ba yar nema kije dinning naku yana chan "haba Ammi ni gaskya da Abbu zanci koh Abbuna? ya amsa mata da eh yana murmushi. Ammi tace "haba dan Allah wallahi kai kake shagwaba su da yawa saboda meye ba zataje gurin yan uwanta ba?. "Yawwa ai naji dadin haka gwanda data zauna kinga Ammi shikenan sai in had'a da nata da nawa duk saina cinye" Raihan ya fad'a dan neman tsokala. Ammi tace "gaskiya kam gwanda kayi hakan" aiko tanajin haka ta ta6e baki tayi kitchen aguje shima yabi bayanta yana dariya rufe kofan yayi tayi ta ihun ya budeta amma yaki Ammi kam bata kulasu ba ta mijinta takeyi shi kuma Abbu bai kula ba sai da yazo shiga shine ya bude daya ganta yayi dariya kad'an yana bata hakuri dan yasan Zahra akwai daru. "Hello kana inane kazo yanzu? a dayan bangaren Sulaiman yace "yanzu na ajiye su daddy agida "ok na baka nanda mintina talatin karka kuskura ka wuce hakan kasameni a gidan Anty Raihana" tsaki yaji kasa kasa kafin yace "ok toh angama saina zo" tsaki tayi tace "karma kazo nidai na baka minti talatin. Anty Raihana data tsura mata ido tace "kedai baki rabo da masifa toh Allah kyauta miki" dariya tayi tace "amen Anti ni kinsan bana son bata time" Anty Raihana tace "wai kwata kwata minti nawa kika min daza kice nanda minti talatin" dariya tayi sannan tace "ahaba Anty wallahi na kai awa biyu kuma kinsan yau inason inga yan gida musanman yaya Raihan saboda 3wk kenan ban ganshi ba har gwara Zahra muna ganin juna a school su Yazid kam na manta when last muka had'u shiyasa zan koma da wuri Anty tace "lalle ma yarinyannan wai wato kinfi karfin kije gaida Raihan ne kafim ki fita school ko kuma what d reason behind this you ur stupidity? ta6e baki tayi tace "kai dan Allah Anty ni banda tym ne shiyasa. _*D??I??D??E??E??Y??L??O??V?? T??A??K??U??C??E??*_ l??e co??en? ??are ?????ann? ?ann? ?a?a ?ana z?wa ?a? da? adad'e ?a'aje ?a.?????
  • Hadiza Isyaku KO RUWA NA GAMA BA KI: BABI NA GOMA SHA HUDU Rubutawa: Hadiza Isyaku HAZAKA WRITERS ASSOCIATION ****** "Na amince" Jummai ta faɗa, ba tare da ta yi tunani akan wahalar da ke cikin ciyar da kai ba, ita dai tunda ta samu wurin zama, toh duk abin da kuma zai biyo baya a ganinta ba matsala bane. Ɗakin da tshohuwar ta fito ta nuna mata "Toh ga ɗaki nan ki shigar da kayanki a ciki". Cike da jin daɗi Jummai ta ɗauki jakarta ta nufi ɗakin, kafin ta shiga ɗaya daga cikin matan uku ta miƙe, tare da fara maganar da dole Jummai ta dakata da shiga ɗakin. "Haba Yakumbo! kawai sai ki kama cewa ta shigar da kayanta, ba tare da kin bincika me ke ciki ba, don Allah kada ki zama sanadin shigarmu cikin wani halin, ki barmu mu ji da wanda ya ishe mu". Jummai bata ji haushin maganar matar ba, don ko ita ce sai ta yi fin haka, tunda duniyar a lalace take. Aje jakar kayan ta yi, tare da duƙawa ta zazzage ledar magunguna "Wannan ledar magani ne na ɗana, bai da lafiya", cikin karyayyar murya ta yi maganar bayan ta ɗago. "Toh saura jakar, itama ki buɗe ta a gani", wata kuma a cikin matan ta ce haka. Jiki a mace ta jawo jakar zata buɗe, "Ke rufe jakarki, ki shiga da ita ciki", Yakumbo ta faɗa tana kallon su. Hayayyaƙo ma Yakumbo suka yi ba tare da sun yi la'akari da tsufanta ba, kowa da maganar da take faɗi, sabo da rashin kunyarsu ce ta ce "Ku dai kuka sani, kuma tunda dai ba a kanku zata zauna ba ai shikenan". Duƙawa ta yi ta kwashe ma Jummai maganin, ita kuma ta ɗauki jakar suka shiga ɗakin a tare. Ɗaki ne madaidaici, wanda daga saman rufinsa zaka iya hango sararin samaniya ta wasu ƴan hudoji. Ƙasan simintin kuwa duk ya gurgure. A gefe kuma katifa ce da wasu ƴan ƙullin kaya a kanta, sai kuma tabarma shimfiɗe da kuma randar ruwa. Ajiyar zuciya Jummai ta sauke lokacin da ta gama ƙare ma ɗakin kallo, domin ko da bukkarta take a lalace toh tafi wannan ɗakin daraja. "Lallai da sauran rina a kaba" ta faɗa a ranta. Katse mata tunani Yakumbo ta yi da faɗin "Kin ga ɗakin kamar kango ko?". Murmushi ta ƙaƙaro "A'a" Kai Yakumbon ta ɗan gyaɗa "Toh ga katifa nan ke da yaronki". Jummai ta ce "Toh ku kuma fa", don ta lura katifar ta Yakumbon ce. Yakumbo ta ce "Kada ki ji komai jikata". Godiya Jummai ta yi mata, gefen katifar ta aje kayanta, sannan ta kwanto Ahamad daga goyon, zaunawa ta yi ta fara bashi Mama, ita kuma Yakumbo ta fita wurin sauran matan tana musu nasiha akan ba'a haka, tunda su ma gidannan wani ne ya ji tausayin su ya ce su zauna, bai kamata ba don wani ya zo su riƙa wulaƙanta shi. Cewa suka yi tunda dai ɗakinta ne can ta matse musu. Cikin ɗakin Yakumbo ta dawo, bisa tabarma ta zauna tana fuskantar Jummai da ke ba yaronta Mama. Ɗan shiru ce ta ratsa ɗakin, kowa da abin da yake saƙawa a ransa. Kawar da shirun Yakumbo ta yi, ta hanyar tambayarta sunan ɗanta. "Ahamad" jummai ta ce. "Malam Amadu ne ashe" Yakumbo ta fada tana yar dariya. Ras! Gaban Jummai ya faɗi sakamakon faɗin sunan mahaifinta da Yakumbo ta yi, kai kawai ta iya ɗaga mata, ta cigaba da kukan zuci, addu'ar neman gafarar Allah ta roƙa ma mahaifinta a cikin rai. Fitowar da Yakumbo ta yi daga ɗakin ce taba Jummai damar ɗaga kanta tana kallon rufin ɗakin "Yanzu wannan rufin mai kama da gwagwa idan ruwan sama ya zo ya zamu yi?" tambayar data jefo ma kanta kenan. Kukan da Ahamad ya fara yi ne ya sa ta maido hankalinta gare shi, ɗaga shi ta yi sama tana ƴar dariya "Kukan kuma na miye?" Ƙuri ɗin da ya yi mata ne ya sa ta sumbatar bakinsa sannan ta ce "Sarkin rigima" A cinya ta maida shi tana yi mashi wasa duk don ya yi dariya, sai dai duk yadda ta so ya yi dariyar bai yi ba. Cike da damuwa ta yi magana a ƙasan ranta, "Toh wai ni me ya sa yaron nan bai yi mani dariya, ko dai ya san cewa ta hanyar banza na same shi". Faɗuwa gabanta ya yi, magana ta cigaba da yi da ranta "Toh idan tun yana jariri ya gane kuma yana fushi da ni, toh ina ga kuma idan ya girma" Ido ta lumshe tana jin wani irin ɗaci a ranta, rungume shi ta yi tsam a jikinta ta ce cikin raɗa, "Ka yi haƙuri, ni da Mahaifinka ne muka cutar da kai, ta hanyar samar da kai ba a hanyar da ta dace ba". Wasu ƴan hawaye ne suka gangaro mata a kumatu, ka sa goge su ta yi ta cigaba da kallon Ahamad, ƙasan ranta kuma tana ƙara jin tsanar Habeeb, saboda da bai neme ta ba, da ta hanyar halal zasu haifi ɗansu, tunda har Allah ya hukunta akwai rabo a tsaninsu. Ɗan kukan da ta yi ne ya sa idanunta suka yi nauyi, zamewa ta yi akan katifar tana da ajiyar zuciya, cikin ɗan lokaci kuma bacci ya yi awon gaba da ita. Ta ɗan yi nisa da baccin kenan sai ga yaran gidan sun dawo, wanda hayaniyarsu ce ta falkadda ita, gyara ma Ahamad kwanciyarshi ta yi, sannan ta fito tsakar gidan. Wasu yara ne ta gani waɗanda sadda ta zo gidan babu su, su uku ne, mata biyu sai namiji ɗaya, idan aka haɗa da biyar ɗin ta iske su takwas kenan. Daga cikin Ukun da suka shigo duk hannuwansu ɗauke da roba, biyu da abinci a cikin robarsu, ɗayar kuma babu. Waɗanda suka samo sai murna suke, ɗayar, kuma babbar bata samo ba, fuskarta sai tuƙuburi take kamar zata yi kuka. Tambayarsu aka yi ina suka samo wannan abincin mai ɗan yawa haka. "A wannan gidan ne aka bani" yaron ya ba su amsa yana ta murna, domin wanda ya samo to kasonshi yafi yawa, mafarin wadda bata samo ba take ta fushi. Mamakin yadda yaran suka dabaibaye abincin ne ya kama Jummai, kwata-kwata yaran ma basu lura da ita ba, ta abincin kawai suke. Tambayar kanta ta shiga yi "Me kenan?" Yakumbo ce ta dafa mata kafaɗa, tana son bata amsar tambayar data gani bayyane a fuskarta. A hankali Jummai ta maida idanunta akan Yakumbo da ke faɗin "Toh kin gani, bara ce kaɗai hanyar da muke samun abinci, domin bamu da komai kuma babu wanda yake bamu sai Allah, waɗannan yaran da kika gani rabon su da abinci tun safe, shima sai dalilin wani Alhaji da ke sadakar Fanke da ƙosai suka samu kalacin, ƙila da har yanzu basu ci komai ba". Ƙuri Jummai ta yi ma yaran, ƙasan ranta tana jin wata masifar tausayinsu, musamman da taga yadda suke tsakurar abincin suna ci duk don kada ya ƙare. Ido ta lumshe tare da matse hawayen da suka cika mata ido lokacin da ta ga wani yaro ya tsince shinkarshi biyu da ta faɗi ƙasa ya maida a cikin roba. Tabbas ta yi rayuwar yunwa, kuma da alamun zata koma a cikinta, to amma a wannan karon ba kanta take tausayi ba, ƙananun yaran da basu san babu ba su take tausaya mawa. Cigaba da magana Yakumbo ta yi "Ina tausayinki a kan wannan rayuwar, don haka a ganina ki ɗauki kayanki ki nemi gidan da yafi namu". Kai jummai ta girgiza tare da fashewa da kuka "Ba inda zan je domin nima irin rayuwarku nake, banbancin shine ni azabtar da ni aka yi yunwa, ku kuma Allah ne ya jarabce ku da ita, ina tare da ku har zuwa lokacin da Allah zai kawo mana mafita". Gaba ɗaya matan gidan da yaran kallonta suka riƙa yi, ruƙo ta Yakumbo ta yi "Toh Allah ya kawo mana mafitar". Wasu daga cikin yaran suka ce "Amiin". Abincin da aka ɗan zubo musu a marfi ita da Yakumbo ne aka miƙo musu, wanda dukan shi bai wuce loma ɗaya ba. Godiya Yakumbo ta yi bayan ta karɓa, miƙa ma Jummai ta yi "Karɓi ki ci" kai kawai Jummai ta girgiza don ba zata iya magana ba. Matsa mata Yakumbo ta yi akan ta karɓa, amma ta ƙiya, duk da kuwa yunwar da ke cikinta. Jin motsin Ahamad ne ya sa ta komawa cikin ɗakin, goya shi ta yi sakamakon magarib da ta ƙarato. Fitowa ta yi da nufin yin arwalla, sai dai gidan ba ruwa ko kaɗan. Tambayar ruwa ta yi, Yakumbo ta ce "Bamu da ruwa, amma bari in ɗebo maki a wurin famfo". Tare da Yakumbon suka tafi ɗebo ruwan, a hanyarsu ta dawowa ce suka ga wata Mai Awara. Kada fa ku ce na cika faɗin Awara, Amanar dake tsakanina da ita ce ta sa nake ta haɗa Jummai da ita. Sallah suka dawo suka yi, sannan ta ɗauki Ɗari biyar a cikin ragowar kuɗinta ta siyo musu Awara ta duka. Tasu ita da Yakumbo ta ɗiba, sauran kuma ta miƙa ma matan gidan da yaransu, sai gashi sai washe baki suke suna mata godiya, wanda da farko ba haka ba. Bayan ta dawo ɗaki Yakumbo ta ce mata "Kin ga ki lallaɓa kuɗinki, kowa tashi ce ke fisshe shi a gidan nan". Murmushi kawai Jummai ta yi, don muddin tana da abin badawa, toh ba zata hana yaran can ba. Hira suka shiga yi bayan sun gama cin Awarar, aikuwa Yakumbo ta bata labarin irin ɓarnar da kidnappers suka yi musu a gari. Ta ce "Sun kashe maza, sannan suka kwashi dukiya da mata, yanzu haka a Ƙauyenmu da ƙauyukan da ke kusa da mu duk sun tarwatse, kowa ya kama gabanshi, wasu sun tafi gidajen danginsu, irin mu kuma da bamu da kowa a birni muka yi ta gararanba, har Allah ya sa wani bawan Allah ya ji tausayin mu ya bamu wannan gidan mu zauna". Sosai Jummai ta tausaya musu akan halinda suka samu kansu a ciki, tambayar Yakumbo ta yi alaƙarta da waɗancan matan, Yakumbon ta ce "Gari ɗaya kaɗai ya haɗamu, su iyalan mutum biyu ne, an kashe ɗaya, ɗayan kuma ba'a san inda yake ba". "Ni kuma bani da kowa sai Jikana Namiji, shi kuma Yana Lagos neman kuɗi, bai kuma san inda nake ba, yanzu tunda ba waya". Cike da tausayawa Jummai ta ce "Lallai kuna cikin damuwa, Allah ya kawo muku ɗauki" Yakumbo ta ce "Amiin" "Toh ke kuma matsalar miye ce a garinku?" Yakumbo ta tambayi Jummai. "Mu kuma boko haram ne" Jummai ta faɗa, da yake ta yi musu ƙaryar Maiduguri take. "SubhanaLlahi" Yakumbo ta ce, don tana jin labarin boko haram, wanda ɓarnarsu ma ta fi ta kidnappers Tamboyoyi ta shiga yi mata ina mahaifanta, da mijinta suke. Tunani Jummai ta shiga yi akan ƙaryar da zata yi ma Yakumbo wadda ta yi daidai da damuwarta. Mahaifina ya rasu, mijina kuma ban san inda yake ba, mahaifiyata kuma.." sai ta yi shiru "Me ya samu Mahaifiyar taki", cikin muryar tausayi Yakumbo ta tambaye ta. Kasa bata amsa ta yi, sai ma kuka da ta cigaba da yi, don ba zata yi ƙarya a kan mahaifiyarta ba, sannan ba zata iya faɗin asalin inda take ba. Tausayin ta ne ya kama Yakumbo "Ba zan matsa maki akan sai na ji labarin mahaifiyarki ba, amma ki yi haƙuri, Allah ya jiƙan mahaifinki, mijinki kuma Allah ya bayyanar maki da shi". "Ba Amiin ba" Jummai ta ce a ranta, akan Allah ya bayyana mijinta da Yakumbo ta ce, domin ba ta da buƙatar shi a yanzu. Shirin bacci suka yi, Yakumbo ta kwanta a kan tabarma, Jummai kuma ta kwanta ita da ɗanta a kan katifa. Kasa bacci Jummai ta yi, saboda tunanin mahaifiyarta da kuma ƙannenta, ko wane hali suke ciki yanzu, tunawa da Mahaifyarta ba son ta take ba ya kawar mata da tunanin su. Kukan Yunwa da yaran gidan ke yi ne ya falkar da Jummai, tana buɗe ido ta ga har gari ya fara haske, a gaggauce ta fito da nufin yin alwalla. Sai dai kuma gidan ba ruwa ko kaɗan. Bokiti ta ɗauka ta nufi inda suka ɗebo ruwa a jiya. Abin kallo ta zama a wurin. Bokitinta ta sanya a layi, sannan ta koma gefe ta tsaya. Murya ƙasa-ƙasa ta ji wata budurwa na magana da ta kusa da ita "Ke ƴan gudun hijirar can fa cewa aka yi mayu ne, ɗan gidan Malam Idi da ya rasu tsohuwar gidan ake zargi da lashe shi". Ras! Gaban Jummai ya faɗi, "Yanzu da mayu nake zaune ban sani ba", gazgata maganarsu ta yi ta hanyar tuna yadda Yakumbo ke ta nan-nan da ita, ashe don ta lashe su take yi. "Wallahi ba zan iya rayuwa da mayu ba". Gabanta na wata irin faɗuwa ta ɗauki ruwan ta tafi, a hanya zuciya ta yi ta saƙa mata Yakumbo na can ta lashe Ahamad. Tun a bakin zaure ta aje bokitin tare da nufa ɗakin da sauri. "Kada ki taɓa mani ɗa" ta faɗa a cikin ƙaraji, lokacin da ta ga Yakumbo zata ɗauki Ahamad da ke kuka. Fasa ɗaukar shi Yakumbo ta yi, saboda ta gane abin da take nufi, da sauri Jummai ta ɗauke shi tana dudduba shi. Murmushi Yakumbo ta yi ta ce "Jikata kenan, kema kin gamsu da maganar ƴan waje cewar mu mayu ne ko?". Shiru Jummai ta yi tana ta huci, ganin bata yi magana ba ya sa Yakumbo cigaba da faɗin "Tunda aka fara jifarmu da wannan ƙazafin bamu taɓa kare kanmu ba, don mun san ba kowa ne zai yadda ba, amma kuma mu da mayun ne da talauci bai kama mu ba wallahi". Nazari Jummai ta shiga yi, sai ta gane rashin kyautawarta, kuma ko da Mayun ne ai ba haka ya kamata ta yi mata ba. "Ni fa ba haka nake nufi ba Yakumbo" Jummai ta faɗa idanunta a ƙasa. Kai kawai Yakumbo ta gyaɗa don abin na matuƙar damun ta, "Haba Jikata, ni fa ba yarinya ba ce". Haƙuri Jummai ta yi ta bata, don ta fahimci ƙazafin mutane ne kawai, da yake tana da sauƙin kai ta ce "Shikenan, amma ki riƙa nazari kafin ki yanke hukunci". Labari ta bata akan yadda abin ya samo asali, satinsu uku da zuwa wasu yara suka rasu, sai aka ce sune suka kama su, tun daga nan ƴan unguwar suka fara tsangwamar su, ɗan daka da wankin da suke kawo musu, suka dena kawowa. Yakumbo ta ce "Ƴar nan in yi maita in samu me, wallahi ko yunwa zata kashe ni ba zan iya maita ba, amma kin ji cewa ake ni ce shugabansu", kamar Yakumbo zata yi kuka ta ƙarashe maganar. Magana mai daɗi Jummai ta cigaba da faɗa mata, ƙarshe ta tabbatar mata da sai ta ƙwato mata haƙƙinta, tunda ta riƙe fuskar yarinyar da ta yi maganar. Asabe kuwa na can ta koma kamar zautacciya, duk wanda ya zo yi mata jaje sai ta riƙa faɗa mashi cewar "Wallahi ni ce silar tafiyar ƴata, nina juya mata baya a lokacin da take buƙata ta". Da Alhaji Mainasara ya zo tana faɗin haka ya ce "Ai ba Jummai ce kaɗai kike da silar tafiyarta ba, hatta mijinki Malam Amadu ke kika kashe shi ba kowa ba". Faɗa sosai ya riƙa yi mata duk da ƙanwarta yake aure, amma shekarun da yake dasu suka sa shi rufe ido ya yi ta mata faɗa. ya ce "Ke da Mairo baku da hali ko kaɗan, ku baku san rangwame ba a rayuwarku, duk wanda ya yi ba daidai ba sai kun taka shi iya son ranku, kuma ba'a haka, domin ba wanda baya kuskure a rayuwa". Kuka Sosai ta cigaba da yi, Kabiru dake gefen Alhaji Mainasara ya ce "Ai baki ma fara kuka ba", don yanzu babu mai tausayinta saboda azabtarwar da ta yi ma Jummai, wadda da bakinta ta riƙa faɗi. Haƙuri Alhaji Mainasara ya bata, sannan ya tabbatar mata da zai sa a bincika a garuruwa. Haka aka yi kuwa, kusan duk jihohin Nigeria sai da aka bada cigiyar Jummai, amma ko mai kama da ita ba'a gani ba. Ƙin faɗa ma Asabe aka yi ba'a ganta ba, sai dai aka ce ana ta cigiyar, duk yadda ta kasance za'a faɗa mata. Ƙawar Hajiya Mairo kuwa, tunda ta ƙyalla ido ta ga Habeeb ta shiga kimtsa yadda za'a haɗa shi da ɗiyarta. Da yamma su duka suna zaune a falo hada Hajiya Mairo suna hirar Habeeb. Bayan hirar ta ɗan nisa ta dubi Hajiya Mairo a tsanake "Kin san da gaske nake fa na ba Habeeb Salma". "Ke Hajiya Sa'a" Hajiya Mairo ta faɗa tana dariyar yaƙe, don idan ba ƙaddara ba bata fatan haɗa ɗanta aure da Salma, don a kan idonta motoci ke ɗaukarta suna tafiya. Hajiya Sa'a ta ce "Allah kuwa, in dai Habeeb ɗin ya amince, kin san an dena yi ma yara dole a kan aure". "Hakane abin da ke Alkhairi Allah ya tabbatar da shi" Hajiya Mairo ta faɗa. Hira suka cigaba da yi, a mafarkin ƙaryar Hajiya Sa'a ta ce "Kin ga kuwa idan Allah ya haɗa, sai a ɗaura auren a tura mashi ita can, kin ga karatu ga matarshi". Dariya kawai Hajiya Mairo ta yi, don kallon mahaukaciya take mata, a yadda Habeeb yake cikakken Namiji, ba zata yadda ya aure kwashe-kwashen mata ba. Da daddare bayan Hajiya Mairo ta shige ɗakinta ta kulle, Whatsapp ta shiga suka fara vedio call da Habeeb, don tafi son ta ganshi Live, hankalinta yafi kwanciya. Ganin yadda yake ta ramewa ta ce "Wai lafiyanka kuwa Habeeb, kullum sai ƙara ramewa kake, ko baka da lafiya?" Ido ya lumshe tare da girgiza kai "Lafiya ta Umma, karatu ne kawai", duk da ƙarya yake, ko kusa bai da lafiyar zuciya, saboda kullum cikin kewar Jummai da ɗanshi yake. "Hmm" kawai ta ce don ta san ƙarya yake, "Ka dai je likita ya duba ka, don wannan ramar ba ta lafiya ba ce. "Toh Umma zan je Insha Allah". Hira suka cigaba da yi cikin raha, har take bashi labarin Hajiya Sa'a fa da gaske ta bashi Salma. "Allah ya sauƙe mun in auri wannan yarinyar" ya faɗa ranshi a ɓace. Cikin zaulaya ta ce "Kai kuwa Habeeb, Salma ai bata da matsala". "Haba Umma, ai ba Salma ba, ni yanzu babu wata yarinya da zan iya ɓata lokacina a kanta, bare kuma har in aure ta" "Kenan ba zaka yi aure ba" ta sake tambayar shi. Kai tsaye ya ce "Zan yi mana Umma, aure na da Jummai zan maida" Take kuwa ta haɗe rai "Wace Jummai, bayan wadda ta koma yawon karuwancin ta". "Kamarya ta koma karuwanci, Umma ita fa ba yadda kike zato bace", cikin jin haushin wannan maganar ya yi maganar. Tabbatar mashi ta yi da Jummai ta gudu, don tuni ƴan gulma sun bata labari, kuma har a Tv taga cigiyar ta. Wata irin kiɗima Habeeb ya yi, bai san sadda ya tsinke kiran ba, tare da dafe kai ya shiga salallami, "Me ya sa Fateema zata yi haka, ina ta tafi, kuma wane yanayi ta samu kanta a ciki?" Tambayar da ya yi ta jefo ma kansa, wanda Jumman ce kaɗai zata iya bashi wannan amsa. Ita kuma tana can wurin neman abin da zasu ci ta samu wanke-wanke a wani gidan abinci, ba don ranta yaso ba take aiki a wurin, sai don ta rasa yadda zata yi. Wani mutumi ne ya sa baki aka ɗauke ta aikin, don da farko matar da ke da gidan abincin ƙin ɗaukarta ta yi. Da wannan aikin ne take ciyar da kanta, har ma ta taimaka ma su Yakumbo. Hakan ya sa shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninta da sauran matan gidan, har ma yaransu, tunda duk wani sauran abinci da aka yi a can su take kawo mawa. Wannan mutumi kuwa kullum cikin kyautata mata yake, duk sadda ya zo siyen abinci sai ya ce ita zata kawo mashi. Ta ce "Ai ni aikina wanke-wanke kaɗai", kafe ta ya yi da idanu, daga bisani ya ce "Wannan jikin naki mai kyau ya fi ƙarfin wanke-wanke". Murmushi kawai ta ta yi, ya ce "Je ki ce ma Hajiya na ce ta baki abinci ki kawo mani". "Toh" ta ce tare da juyawa ta tafi, ji ta yi a jikinta kallonta take, waigowa ta yi don tabbatar wa, aikuwa suka haɗa ido, girar da ya ɗaga mata ce tasa ta saurin juyawa. "Wancan mutumin anya ba ɗan iska bane", ta faɗa a ranta lokacin da ta isa wurin Hajiya. Karɓo abincin ta yi ta kawo mashi, idanunsa cikin nata ya ce "Toh zauna mu ci". Da dariya ya ƙarasa maganar. Ido ta ɗan zaro tare da girgiza kai tana dariya. Ɗan shagwaɓewa ya yi tare da faɗin "Toh ki zauna, ina kallon ki ina cin abincin, idan ba hakaba ki ɗauke abincin". Ƙin zama ta yi ta juya tana dariya, dariyar shima yayi, ya bi ta da idanu. shirin komawa gida Jummai ta yi, don ta baro Ahamad wurin Yakumbo, kuma ta san zai buƙaci mama a yanzu. Zagayawa ta yi don bata son mutumin ya ganta, ashe ya ganta har ya bi bayanta ma ya ga gidansu. Da yamma liƙis suna cikin Hira ita da matan gidansu aka aiko yaro da ana kiran Jummai. Tsokanarta matan gidansu suka shiga yi, wai daga fara zuwa aiki har ta yi kasuwa. Dariya tayi, sannan ta fita, ganin wannan mutumi ya sa ta tokarewa a bakin ƙofa. "Kin yi mamaki ko?”, ya faɗa yana dariya. Ƴar dariya ta yi, cikin ranta kuma ta ce "Ko maye ne kai, dole ka shafa ma kurwata lafiya". Gani ta yi ya ƙaraso inda take ya tsaya, cike da kunya ta gaishe. Amsawa ya yi, sannan ya fara janta da hira ta hanyar tsokana, ita dai ba abin da take sai dariya. Ganin ta saki jiki dashi, sai ya bijiro mata da abin da ya kawo shi, cewar yana sonta. Haƙuri ta bashi, tare da tabbatar mashi da tana da aure, don ita bata san da wani sakinta da Habeeb yayi ba, kuma duk shakiyancinta ba zata yi soyayya alhalin da igiyar aure a kanta ba, duk da irin ƙin da take yi ma auren. Bai ji daɗi ba, amma sai ya cije ya ce "Ba komai, ai za'a dai riƙa gaisawa ko". Ta ce "Insha Allah", bankwana suka yi, ya tafi. Cikin gidanta koma tare da ba ƴan gidansu labarin yadda suka yi da mutumin, su sai a ranar suka san tana da aure. Shi kuwa duk da Jummai ta faɗa mashi tana da aure bai dena kyautata mata ba, duk lokacin da ya je gidan abinci ita yake fara nema su gaisa, kuma kusan kullum sai ya yi mata Alkhairi na kuɗi ko wani abu. Da ta nuna ya dena yi mata kyauta hakanan sai ya ce "Ai ba don ina son ki nake miki kyauta ba". "Sai don me?" ta tambaye shi. Amsa ya bata da "Sai don ina tausayinku ke da mutanen gidanku, kuma Alherin da nake maki a zahiri ke kaɗai nake ba, amma a baɗini hada ƴan gidanku, domin ina da yaƙinin kina taimaka musu" Murmushi ta yi tare da gode mashi, domin yana matuƙar taimaka musu, domin rabon da su kwana da yunwa har sun mance, kullum fatan Alkhairi suke yi mashi, domin ya zama ma kamar ɗan gida, lokaci bayan lokaci yana kawo musu ziyara har gida, kuma a zahiri kamar ya aje batun soyayyar da yake ma Jummai a gefe. Ita kuwa Jummai duk yadda kake zaton hankalinta a kwance yake, domin daidai gwargwado ita da ɗanta sun murje sun yi kyau, toh ba haka bane, domin kullum da tunanin gidansu take kwana, tambayar ta kullum take ma kanta "Wane hali ahalina suke ciki?". Wannan damuwa bata ƙaru ba sai ranar da wannan mutumi ya same ta har gidan abinci, tare da bijoro mata da muguwar buƙatarshi a kanta. Bayan sun gaisa kamar yadda suka saba ya ce "Wata magana nake son muyi, fatan zaki bani dama". Ba tare da tunanin komai ba ta ce "Na baka dama". "So nake mu ƙulla alaƙa mai ƙarfi da ke, wadda zaki ƙara samun mafita a cikin rayuwarki". Cikin rashin fahimta ta ce "Alaƙa kuma, wace iri? " "So nake ki bani kanki" Wata irin faɗuwa gaban Jummai ya yi, "Me ka ce" don bata son yanke mashi hukunci sai ta sake ji daga bakinshi. "Cewa na yi Ki bani kanki…." Ku biyo ni a ci gaban labarin in Allah Ya yarda. MAMAN MU'AZZAM
  • Mukhtar Musa Karami Abu Hisham Lokacin taron bada kyautukan gasar muhawarar Bakandamiya ,daga wanne gari zaka zo gurin taron?
  • shafii Yunusa Dr
Previous
Next

Hotuna

  • Wall Photo­s 4 photos

Previous
Next
© 2021 Bakandamiya  -  About Us  -  Terms  -  Privacy  -  Advertise  -  Support  -  Stock Photos  -  Contact Us  -  Mobile Apps
  • Facebook
  • Twitter
  • Linkedin
  • Youtube
  • Pinterest
  • Instagram
Create New Content
  • Kasuwa
Add Link