• Contrast
    • Font
    • A
  • Sign In
  • Sign Up
    Loading ...
View All Updates Mark All Read
Bakandamiya
  • Home
  • Rubutu
  • Bidiyoyi
  • Sautuka
  • Hotuna
  • Zauruka
  • Profile Type: Personal
  • Profile Views: 6,193 views
  • Followers: 61 followers
  • Last Update: November 25, 2021
  • Last Login: November 25, 2021
  • Joined: December 13, 2018
  • Member Level: Basic
  • Update
  • About
  • Hotuna(2)

Update

The post was not added to the feed. Please check your privacy settings.
  • Yusha'u Alhassan
    Yusha'u Alhassan liked Mustapha musa abu Aisha's post.
    March 13, 2021
    Mustapha musa abu Aisha
    SHIN KANA CIKIN MUTANAN KIRKI???

    An tambayi daya daga cikin magabata wannan tambaya,wani daga cikin Dalibansa ya ce...  more
    Mustapha musa abu Aisha
    SHIN KANA CIKIN MUTANAN KIRKI???

    An tambayi daya daga cikin magabata wannan tambaya,wani daga cikin Dalibansa ya ce dashi"):
    "Shin Malam ina cikin mutanai Salihai mutanan kirki??".

    Sai ya amsa...  moreSHIN KANA CIKIN MUTANAN KIRKI???

    An tambayi daya daga cikin magabata wannan tambaya,wani daga cikin Dalibansa ya ce dashi"):
    "Shin Malam ina cikin mutanai Salihai mutanan kirki??".

    Sai ya amsa da cewa:
    "Idan har kana yawaita yin addu'a ga Mahaifanka to hakika kana cikin Salihan bayi na kwarai,Saboda Hadisin da Annabi s.a.w yake cewa:
    (Idan dan Adam ya mutm dukkan aiyukasa sun yanke"ma'ana ladar aiyukansa ta daina karuwa ko gudana" Sai abubuwa guda ukku:-
    -Sadaka mai gudana
    (Kamar gina masallaci ko rigija ko islam ko hanya).
    -Ko wani ilimi da ka koyar.
    -Ko wani yaro salihi na kwarai da zai riqa yi maka addua).
    @Saheehul Jami'i.

    Sai Annabi s.a.w ya tabbatar mana anan cewa yana cikin babbar alamar salihin mutum ya kasance yana yiwa mahaifansa addua ako wane lokaci.

    Idan kuma bakayi masu addua to kai ba mutumin kirki bane,iya yadda ka manta da yiwa mahaifanka addua iya yadda kake zama mutum banza.

    Dan haka ka yawaita fadar:
    ( رَّبِّ ارْحَمْهُمَا كَمَا رَبَّيَانِي صَغِيرًا )
    "Ya Ubangijina! Ka yi musu rahama, kamar yadda suka yi rẽnõna, ina ƙarami."

    Wannan addu'ar ta kunshi abubuwa guda biyu da akeso mu yawaita yima mahaifan mu.

    1-Nema masu gafara
    2-Da nema masu Rahama da...    less
    • 6 people like this
  • Yusha'u Alhassan
    Yusha'u Alhassan
    Sirrin ƴaƴan kankana da ɓawonta ga ma’aurata


    Kankana na ɗaya daga cikin kayan gona na marmari da ke da matukar amfani ga bil'adama.

    Kankana...  more
    Sirrin ƴaƴan kankana da ɓawonta ga ma’aurata


    Kankana na ɗaya daga cikin kayan gona na marmari da ke da matukar amfani ga bil'adama.

    Kankana wata aba ce mai dauke da ruwa mai zaƙi kuma mai amfani matuka ga jikin bil'adama.

    Masana sun bayyana Kankana da ƴaƴan itaciyar mai matukar amfani ga rayuwar bil'adama, don sindarai da ke cikinta na Vitamins da Minerals da Antioxidants da kuma Calories.

    Kankana na da nau'ika biyar: akwai mai ƴaƴa da mara ƴaƴa, akwai mai kalar ruwan dorawa da dan karami kore da mai kama da lemun zaƙi.

    Sai dai a galibin kasashen Afirka irin Najeriya koriyar kankana mai ƴaƴan itatuwa aka fi sani.

    Kashi 92 cikin 100 na kankana ruwa ne zalla, don haka mai yawaita shanta ba shi da matsalar ƙarancin ruwa a jiki, musamman lokacin zafi, in ji Maijidda Badamasi Burji da ke da ƙwarewa a ilimin abinci mai gina jiki.

    Ga wasu abubuwa 9 da ƙwararru ke cewa kankana na iya a jikin dan Adam:

    Kara ruwa a jiki

    Rashin shan ruwa na illa sosai ga jikin dan adam, hakan yasa ake yawaita jan hankali mutane kan alfannu shan ruwa domin inganta lafiyar jiki.

    Sai dai shan ƴaƴan itatuwa irin kankana wanda kashi 92 cikin 100 ruwa ne zalla zai maye gurbi bukatar da ake da ita na yawaita shan ruwa.

    Sannan kankana baya ga ruwa akwai sinadarin Fiber a jikinta, don haka shan ta tamkar anci abinci ne mai matukar inganci wanda ke kunshe da galibin sinadarin da jiki ke bukata.

    Sinadarin Vitamins da Minerals

    A cikin jeren kayan marmari ko itatuwa, Kankana ita ce wacce ke da karanci sinadarin calories.

    Calories din da ke jikinta bai kai na ƴaƴan itatuwa da ake ganin kwata-kwata basu da zaki ba, danginsu inibi.

    Kofi guda na ruwan kankana na kunshe da sinadaran Vitamin C da A da Potassium da Magnesium da Vitamis B1 da B5 da B6.

    Kariya daga daji ko Cancer


    Shanruwan kankana ma yana da amfani

    Daga cikin sindaran da ake samu a jikin kankana akwai masu bada kariya daga wasu nau'ikan ciwon daji ko cancer.

    Bincike ya nuna cewa masu yawaita shan kankana masu fiye kamuwa da cancer ciki ba.

    Kariya daga ciwon zuciya

    Ƙwararu sun sha cewa ciwon zuciya shi ne kan gaba wajen hallaka mutane a duniya baki ɗaya.

    Sai dai an lura akwai nau'in cimakar da ke taƙaita bugun zuciya da shanyewar barin jiki ta hanyar rage kamuwa da hawan-jini da rage kitse a jiki.

    Sinadarai da dama a jikin kankana na iya samar da waraka da taimaka wajen yaƙi da wadanan cututtuka.

    Garkuwa da kuzari

    Kankana na bai wa jiki garkuwa, sannan yana taimakawa da sinadarin da ke taimawa halittar da suke yaki da cututtuka da kuma samun wakara daga ciwo ko rauni, sannan tana maganin kasala da sa kuzari

    Ƙwarin Ido

    Shan kankana na kara ƙwarin ido da kariya daga kamuwa daga wasu cutuka ido masu lahani ko kai wa ga makanta.

    Mutanen da ke yawaita shan kankana ko ɗiga ruwanta a ido kan tsufa da idanunsu a cewar ƙwararu

    Kumburin gabobi

    Sinadarin citrulline, da ke jikin kankana, na rage kumburin gabobi. Sannan ana amfani da shi a hada magunguna kara ƙwarin gabobi da cutukan da ake samu saboda yawaita zama ko kin motsa jiki.

    Hakazalika yawaita shan kankana da bada kariya daga kamuwa da Basir.

    Gyara fata da gashi

    Vitamins A da C na cikin kankana na da muhimmanci sosai wajen baiwa jiki sinadarin collagen da ke sa fata laushi da kyau da gyara gashi da kwari

    Taimaka wa wajen narkewar abinci

    Kankana da kunshe da ruwa sosai don haka shanta na taimaka wajen narkewar abinci.

    Yawaita shanta na hana cushewar ciki da bai wa jiki dama sarafa abinci da narkewarta cikin dan kankanin lokaci.

    Ko ku san sirrin ƴaƴan kankana?

    Watakil kana/kina cikin mutanen da ke zub da ƴaƴan kankana wajen shanta - ko tsameta kafin ayi amfani ko sarafa kankana.

    To ga wasu bayanai masu muhimmanci da muka tattara da ka iya taimaka mu ku wajen sauya ra'ayi kan ƴaƴan kankana a tattaunawarmu da Maijidda Yahaya.

    Ƴaƴan kankana na da sirika sosai da ba kowa ya san da su ba, suna kunshe da sinadarin Zinc da Magnesium da Potassium da Iron da dai sauransu.

    Ƴaƴan kankana na bai wa jiki garkuwa da matsalar ciwon zuciya da hana ko warkar da ciwon suga da inganta jima'i.

    Ga karin alfannunsa ga jikin dan adam

    1. Yana sa kuzari

    2. Inganta jima'i ko saduwa

    3. Gyara maniyin maza musamman masu matsalar haihuwa

    4. Inganta lafiyar kwakwalwa

    5. Kwarin kashi

    6. Garkuwar jiki

    7. Warkar da Ciwon suga nau'i na biyu ko Diabtes type 2 a Turance

    8. Ƴaƴan kankana na gyara gashi ga mace

    9. Gyara fatar jiki

    10. Lafiyar zuciya

    Yadda ake sarafa ƴaƴan kankana

    Kana iya taunewa hade da kankana, ko a shanyata ta bushe ko a soyata sama sama. Duk yada mutum ya sarafata zai ji dadinta.

    Ɓawon kankana -Boyayyar sirri da akasari ba a san da shi ba

    Na san galibin mutane idan ana shan kankana zub da ɓawonta ake yi ko a shanye jiki a ɓare bayan a zubar.

    To kamar dai ƴar'uwarta gurji, ita ma kankana kyanta a shanye komai har da ɓawonta da galibin lokuta ake ganin an watsar a cikin shara, a cewar ƙwararu.

    Ga wasu dalilai da ka iya sa ki/ka gamsu da waɗanan bayanan

    1.Tana kara gamsuwa wajen kwanciya.

    To amma fa kankana ba maganin karin kuzari ba ce, sai dai wani bincike ya nuna cewa za ta iya taimakawa maza wajen magance matsalar saurin kawowa. Tasirinta wajen kara karfin maza yana zuwa ne daga sinadarin amino da ke jikin ɓawonta.

    Wani binciken ya nuna cewa sinadarin L-citrulline da ke cikin kankana zai iya taimakawa wajen inganta yanayin karfin maza ba tare da wasu illoli da ake samu a magungunan karfin maza ba.

    Hazalika ga mata ɓawan kankana na taimaka musu wajen karin ni'ima musamman idan aka markadata cikin madara, in ji Maijidda Yahaya kwarariya kan abinci masu gina jiki.

    2. Inganta maka kuzari

    Za kuma ta iya inganta maka kuzari bayan kara nishadi a gado, domin sinadarin ruwan citrulline zai iya taimakawa wajen kara kuzari yayin motsa jiki.

    3. Maganin hawan jini

    Idan likita ya ce akwai bukatar jininki ya yi kasa, to gwada cin kankana baki dayanta - har da ɓawonta.

    Binciken masana ya nuna cewa shan kankana na taimakawa manya da tsoffi musamman masu ƙiba yin maganin hawan jini.

    Wata dabarar jin dadin kankana kamar yadda ƙwararru a fanin abinci mai gina jiki ke cewa, shi ne a sanyata a firij don ta yi sanyi a yankata sala-sala a shanye baki daya.

    4. Tana kunshe da Sinadarin Fiber

    Wani alfannun kankana ga jiki shi ne tana ƙunshe da sinadarin Fiber sosai da ke taimakawa matuka wajen kariya daga cututuka, rage kitsen jiki ko suga, da kuma cimma buri ga masu son rage kiba.

    Karin haske

    Wani karin haske da shawarwarin ƙwararru kan shan kankana shi ne mutum na iya bare ɓawonta ya yanka sala-sala sannan ya barbade da yaji, ma'ana a yi kwadonta ga wadanda cin ɓawon zai yi wa wahala.  less
    February 15, 2021
    • 7 people like this
  • Yusha'u Alhassan
    Yusha'u Alhassan
    Tambayar yaushe za ki yi aure tana ƙona min rai'

    12 Fabrairu...  more
    Tambayar yaushe za ki yi aure tana ƙona min rai'

    12 Fabrairu 2021

    

    ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

    Bayanan hoto,

    Kusan kowa ya san yadda ake yawan matsa wa mata da cewa "yaushe za ki aure ne"

    Kusan kowa ya san yadda ake matsa wa mutane su yi aure a yankinsu. Tambayar "yaushe za ki yi aure" na cikin abubuwan da suka fi ɓata wa 'yan mata rai a rayuwarsu.

    "Mutanen da suke matsa wa mutum sun haɗa da danginsa da abokan aiki da waɗanda kuke zuwa wurin ibada tare, wani zubin ma har sai sun ɓata maka rai," a cewar wata lauya mai shekara 27 mai suna Ebunoluwa Tengbe.

    A cikin shirin Sashen Ingilishi na BBC mai suna The Comb, wasu mata matasa biyu sun bayyana abin da ke ci musu tuwo a ƙwarya game da tambayar "wai yaushe za ki aure ne".

    Abokan aikinta a ofis da ke Freetown kan uzura mata cewa tana shafe lokaci mai yawa a wurin aiki, kamata ya yi ta riƙa samun lokacin kula maza a madadin haka.

    a na cikin wata damuwa - ba na jin wata raguwa a jikina har sai lokacin da irin waɗannan tambayoyin suka fara yin yawa, sai kuma ki ji kin fara tantamar halayenki," in ji matashiyar 'yar ƙasar Saliyo.

    Haka ma abin yake a Tanzania, in ji 'yar jarida mai suna Tulanana Bohela.

    Bayan wani taron horarwa, wani mutum ya yi tambayar cewa wai me ya sa Bohela ba ta yi aure ba sannan ya buƙace ta da zama "mai sauƙin kai" da "tawali'u" ko ta samu miji.

    Kazalika, akwai wata ƙanwar mahaifiyarta da ke yi mata addu'a a gaban mutane don ta samu miji a wurin taron danginsu.

    "Ina cikin mata 'yan ƙalilan da har yanzu ban bar gaban iyayena ba zuwa gidan miji," a cewarta.

    Sai dai 'yar shekara 33 ɗin tana zaune ne ita kaɗai, abin da ta ce yana janyo ce-ce-ku-ce a ƙasarsu. Wani lokacin takan faɗa wa mutane cewa tana zaune ne tare da ɗan uwanta don a sauƙaƙa mata.

    Ita ma kanta wadda ta gabatar da shirin na wannan makon, Damilola Odulowu, na fuskantar matsin "wai yaushe za ki aure" a Najeriya.  less
    February 13, 2021
    • 7 people like this
  • Yusha'u Alhassan
    Yusha'u Alhassan liked Abubakar Sulaiman II's photo.
    February 6, 2021
    Kada Wanda Ya Damu Kokuma Ya Karaya Da Wannan Batu Na Haramcin Da CBN Yayi Ai Dama TunTuni CBN Bai Halatta Ba Sannan Dama Cryptocurrency Baya Bukatar Wani Banki Wata Kasa Ya Amince Da Shi Kokuma Akasin Haka. Hasalima Manufar Da Tasa Aka Kirkiro...  moreKada Wanda Ya Damu Kokuma Ya Karaya Da Wannan Batu Na Haramcin Da CBN Yayi Ai Dama TunTuni CBN Bai Halatta Ba Sannan Dama Cryptocurrency Baya Bukatar Wani Banki Wata Kasa Ya Amince Da Shi Kokuma Akasin Haka. Hasalima Manufar Da Tasa Aka Kirkiro Cryptocurrency Shine Samar Da Kudin Da Gwamnati Bata Da Hannu Aciki.
    Don Haka Idan CBN Ta Amice Da Crypto To Crypto Ya Mutu Kenan Kukasance Da Shafin Mu Domin Samun Ingantattaun Bayanain Agameda Bitcoin | Gonar Bitcoin  
    • 4 people like this
  • Yusha'u Alhassan
    Yusha'u Alhassan
    Innalillahi wainnailaihi raju'in.
    Mun yi gagarumin rashin danuwa abokin aiki Ibrahimu Abdulaziz wakilin VOA Hausa a Taraba da Adamawa.
    Allah ya jikansa da rahma.
    February 6, 2021 - edited
    • Abubakar kasimu, Bakandamiya, and Nana Aicha Hamissou like this.
    • Yusha'u Alhassan
      Abubakar kasimu Ameen yarabil alameen
      • February 6, 2021
      • -
      • Report
  • Yusha'u Alhassan
    Yusha'u Alhassan
    Matan aure da 'yan mata miliyon 5.7 suke amfani da dabarar hana daukar ciki a Nijeriya

    Wani Sabon Rahoto ya bayyana cewa matan aure da ‘yan Mata Miliyan 5.7 ne suka yi amfani da dabarar hana daukar ciki a...  more
    Matan aure da 'yan mata miliyon 5.7 suke amfani da dabarar hana daukar ciki a Nijeriya

    Wani Sabon Rahoto ya bayyana cewa matan aure da ‘yan Mata Miliyan 5.7 ne suka yi amfani da dabarar hana daukar ciki a Najeriya.

    Rahoton yace an hado bayanai ne daga shekarar 2012 zuwa yanzu inda hakan ya hana daukar ciki da ba’a shirya ba har guda Miliyan 1.9.

    Rahoton na FP2020 ya bayyana cewa, akwai kuma zubar da ciki 705,000, da kuma mace-mace 13,000 da aka gujewa ta hanyar amfani da mata da suka yi da abubuwan hana haihuwan.  less
    February 4, 2021
    • 7 people like this
    • Yusha'u Alhassan
      Halima K Mashi Abdullahi Allah ya kyauta
      • February 5, 2021
      • -
      • Report
  • Yusha'u Alhassan
    Yusha'u Alhassan
    Maza biyar da matansu suka fi su shahara a duniya


    Kamar yadda maza suka shahara kuma suka mamaye siyasar duniya haka ma...  more
    Maza biyar da matansu suka fi su shahara a duniya


    Kamar yadda maza suka shahara kuma suka mamaye siyasar duniya haka ma mata.

    A wani bincike na Farfesan jami'ar Stanford Alvin Roth kuma wanda aka bai wa lambar yabo ta Nobel ya nuna cewa duk da irin nasarar da ɗaya daga cikin ma'aurata ya samu cikin aure, dukkaninsu za su iya samun farin ciki idan suka fahimci juna.

    Wannan tunanin yana da tasiri musamman ga mazan da suka samu nutsuwa a tare da matansu da suka fi su shahara.

    An ƙarfafa wannan tunanin na Farfesa Rotha wani bincike a 2015 mai taken "Nazari kan yadda mazaje masu ruwa da tsake ke tasiri ga nasarar matansu."

    A binciken an kammala cewa goyon baya da mazaje ke ba matansu yana ƙara ba su damar samun nasara da shugabanci.

    Don haka ga mata biyar bisa goyon baya da suka samu suka fi mazajensu shahara a duniya:

    Douglas Emhoff mijin Kamala Harris

    Kamala Harris ta zama mace ta farko kuma baƙar fata ta farko da ta zama mataimakiyar shugaban Amurka.

    Ta kafa tarihi, duk da cewa mijinta Douglas Emhoff shi ma ya kafa na shi tarihin.

    Gwamnatin Biden ta buɗe masa shafin Twitter a hukumance, inda Mista Emhoff ya zama namiji na biyu mafi girma a matsayinsa na mai gidan mataimakiyar shugaban ƙasa a tarihin Amurka. Kuma Bayahude na farko mijin mataimakiyar shugaban ƙasa.

    An haifi Douglas Emhoff a Brooklyn kuma iyayensa Yahudawa ne, Barbara da Michael Emhoff.

    Ya yi karatu a jami'ar jihar Califonia, Northridge inda ya kammala digirinsa na farko da kuma karatun shari'a.

    Ya yi aiki a kamfanoni da dama na shari'a da kuma kamfaninsa kafin ya zama abokin hulɗar DLA Piper.

    Ya kuma koyar a matsayin Farfesa a ɓangaren shari'a a Jami'ar Georgetown

    Ya kasance wani abin misali cewa maza na iya kasancewa a wani matsayi na ƙarfafawa mata guiwa.

    Joachim Sauer mijin Angela Merkel ta Jamus
    Joachim Sauer Farfesan kimiyya ne a Jami'ar Humboldt da ke Berlin.

    Yana ɗaya daga cikin membobin kwamitin amintattu na gidauniyar Friede Springer, tare da tsohon shugaban kasar Jamus Horst Köhler da sauransu.

    A 1998 ya auri Angela Merkel wacce ita ma masaniyar kimiya ce. Ya taɓa aure da ƴaƴa biyu kafin ya auri Merkel wacce ita ta taɓ aure kafin ta aure shi.

    Lokacin da Angela Merkel ta zama shugabar gwamnatin Jamus a 2005, Sauer ya zama namiji na biyu mafi girma a Jamus bayan shugaban ƙasa.

    An haife shi ne a 1949 a Hosena Jamus, kuma ya zurfafa bincike ne a fannin ilimin sinadarai (Chemistry) a Jami'ar Humboldt da ke Berlin inda ya kammala digirinsa na uku a 1974.

    Sauer ya zama cikakken Farfesa a 1993 a Jami'ar Humboldt a Berlin.

    Matar da ta kwato wa mata Musulmai sojoji 'yancin sanya hijabi a Afirka Ta Kudu

    Saboda shaharar da matarsa ta yi a fagen siyasa, Sauer ya fi samun kulawar kafofin yaɗa labarai fiye da yadda yake samu a bincikensa na kimiyya.

    Lokuta da dama ya ce sha cewa bai damu da nuna kansa ba, kuma ya ki amincewa ya tattauna da kafofin watsa labarai kan fannin siyasa.

    Ikemba Iweala mijin Ngozi Okonjo-Iweala
    Dakta Ikemba Iweala likita ne asalin jihar Abia daga Umuahia. Ya yi karatu a Jami'ar Ibadan, Najeriya.

    Ya samu horo kan fannin tiyata a Birtaniya inda ya yi aiki a asibitoci da dama na Ingila.

    Ya kuma yi aiki a asibitin Jami'ar George Washington a Washington DC.

    Dakta Iweala ya tabbatar da shi mutum ne mai kyautatawa iyali duk da aikinsa na likitanci mai cin lokaci.

    Zai kasance mai farin ciki da auren Ngozi Okonjo-Iweala, da ta riƙe muƙamin ministar kuɗi da kuma ministar harakokin ƙasashen waje.

    Ta kasance mamba a kwamitin gudanarwar kamfanonin ƙasashen waje da suka haɗa har da Twitter da ARC da GAVI da sauransu. Yanzu ita ce mace ta farko kuma ƴar Afirka da ta zama shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya (WTO).

    Sun haifi ƴaƴa huɗu, mace ɗaya maza uku.

    Peter Murrell mijin Shugabar Gwamnatin Scotland, Nicola Sturgeon
    Peter Tierney Murrell shi ne babban jami'in jam'iyyar SNP ta Scotland da matarsa Firaminista Nicola Sturgeon ke jagoranta.

    An haife shi a 1964 a Edinburgh, kuma ya yi karatu a Jami'ar Glasgow a Scotland.

    Murrel ɗn siyasa ne inda tun 1999 yake rike da muƙamin babban jami'in jam'iyyar Scottish National Party, kuma ana ganin jagorancinsa ne ya kai ga nasarar da ta samu a zaɓen 2007.

    A 2010 ya auri Nicola Sturgeon, amma tun a 1988 suka fara haɗuwa a wani taron matasan jam'iyyar SNP da Murrell ya haɗa. Tun 2003 suka yi baiko.

    Clarke Timothy Gayford, mijin Firaminista Jacinda Ardern
    Clarke Gayford, mai shekara 44, ɗan jarida ne kuma mijin Firaiministan Zealand Jacinda Ardern.

    Ya fara karatunsa a makarantar Palmerston North Boys' High. A 1995, ya tafi Jami'ar Otago inda ya kammala karatun digiri.

    Ya kuma tafi makarantar koyon aikin yaɗa labarai ta New Zealand Broadcasting School a Christchurch, New Zealand. Daga can ne ya fara aikin yaɗa labarai a Cow TV (1999) zuwa Channel 9.

    A 2003, ya fara aiki yaɗa labarai gadan-gadan a kafar da ke yaɗa kaɗe-Kaɗe ta C4 channel, inda yake gabatar da shirin matasa.

    Daga nan kuma ya ci gaba da aikin yaɗa labarai a fannoni da dama ciki har da shirin kamun kifi wanda aka nuna a ƙasashe sama da 35.

    Rahotanni da dama sun ce a 2019 Gayford ya nemi auren Ardern. A cewar kafar yaɗa labaran New Zealand, ya sha raka Ardern ƙasashe da dama ciki har da taron shugabannin ƙasashe rainon Ingila a London.  less
    February 3, 2021
    • Lawan Dalha, Hauwa Dalha, and Rahmatu Lawan like this.
  • Yusha'u Alhassan
    Yusha'u Alhassan liked Nafisa Abdullahi Fans Club's post.
    February 3, 2021
    Nafisa Abdullahi Fans Club added new photos.
    Good morning fans 💛 💜
    • 4 people like this
  • Yusha'u Alhassan
    Yusha'u Alhassan has added a new profile photo.
    February 2, 2021
    • 6 people like this
    • Yusha'u Alhassan
      Lawan Dalha Mashaa Allah! Shaihin dan jarida, barka da warhaka.
      • February 2, 2020
      • -
      • Report
    • Yusha'u Alhassan
      Yusha'u Alhassan Barka dai Doctor.
      • February 3, 2020
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
  • Yusha'u Alhassan
    Yusha'u Alhassan liked Rahmatu Lawan's post.
    February 1, 2021
    Rahmatu Lawan shared Lawan Dalha's item.
    • 8 people like this
  • Yusha'u Alhassan
    Yusha'u Alhassan
    Aure: Yadda zamani ya sauya al'adar kukan amare zuwa gidan miji


    Hausawa kamar sauran al'umomi na duniya, mutane da ke da al'adu daban-daban da suka shafi gudanar da...  more
    Aure: Yadda zamani ya sauya al'adar kukan amare zuwa gidan miji


    Hausawa kamar sauran al'umomi na duniya, mutane da ke da al'adu daban-daban da suka shafi gudanar da rayuwarsu.

    Wasu daga cikin al'adu sun shafi yadda ake bikin aure; a ciki har da al'adar da ta shafi yadda amarya take rusa kuka, ta rika guje-guje da zarar za a kai ta gidan nijinta.

    A wasu lokutan ma ko bayan an kai ta gidan mijin ba ta sauya zane, domin za ta rika guduwa ana kamo ta ana dawo da ita, ko kuma ta rika kin walwala da cin abinci, sai dai kuka.

    Duk da yake wannan dadaddiyar al'ada ce sai dai yanzu ana ganin an soma juya mata baya.

    Hausawa wadanda shekarun suka ja sun san yadda wannan a'l'ada ta yi tasiri a zamantakewar aure da ta iyali.

    Ko mene ne yake sanya amarya kuka? Shin al'adar tana gushewa ne? Idan hakan ne, me ya sa?

    Wadannan su ne wasu daga cikin batutuwan da wannan makala ta fito da su.

    Alhaji Mahammadu Umar Mai-Zabura, wani dattijo ne a Maiduguri wanda ya bayyana cewa aure wani muhimmin abu ne a cikin rayuwar kowace al'umma, domin shi ne tubalin gina zuriya a kan kyakkyawar hanya da kuma tushe.

    Ya ce don haka yana da matukar muhimmanci ga ko wace al'umma ta duniya, ya zamanto alakar rayuwarsu ta zamantakewa tsakanin mace da namiji ta kasance ana gina ta a hanyar auratayya don samun karbuwa a al'adance da kuma addini.

    ''Ko wace al'umma tana gudanar da harkokin auratayya bisa manufa da kuma tsarin da ta ga ya dace da ita,'' in ji Mai-Zabura.

    A cewarsa, akwai dumbin dalilai da suka sanya wa amarya take kuka "kuma sun danganta ne ga yanayin yadda aka bi aka aurar da yarinya, da galibi hakan a auren fari ne yakan faru."

    Wadanne dalilai ne ke sa amare kuka?

    Dalilan dai kamar yadda galibin mutane ke fada suna da nasaba da kewar gida da 'yan matan ke tunanin yi da zarar sun bar iyayensu.

    ''Suna jin kunya da fargabar haduwa da wadanda ba iyayensu ba, da dangin da ba nasu ba, suna jin kunyar an hada su da wani namiji , kana suna ganin an raba su da iyayensu, da yan uwansu da kawayensu, zama dandali da suka saba, duk hakan na sa amare yin kuka,'' in ji Mai-Zabura.

    Ya kara da cewa: ''A wasu lokuta ma nisa da gida ko garin da yarinya take shi yake kara sa amarya ta rika kuka, don za ta hadu da wata sabuwar rayuwa da ba ta saba da ita ba kuma a inda take fargabar za ta dade bata ga iyayenta da danginta ba.''

    Hajiya Amina Saulawa da ke jihar Katsina ta shaida wa BBC cewa a baya yakan kasance a wasu lokutan ita yarinyar ba ta ma san wanda za a aura mata ba, don haka babu shakuwa a tare a tsakaninsu, shi ya sa yarinya kan rika kuka idan za a kai ta gidan miji.

    "Amaren kan rika kuka ne saboda galibi wasu a lokacin ba su riga sun mallaki hankalinsu ba, saboda karancin shekaru, ba su fahimci mecec e rayuwar aure ba, sannan ga rabuwa da iyaye,'' in ji Amina.

    Kwana a makabartu da kan bishiya

    Ita kuwa malama Rahinatu Abubakar cewa ta yi gaskiya zamanin da da na yanzu akwai bambanci sosai wajen al'adar kukan da amare ke yi lokacin da za a kai su gidan miji.

    Rahinatu ta ce '' Dalilan da suka sa amarya ke kuka lokacin da za a kaita gidan miji sun hada da tsoron inda za a kai ta, don bata san me zata tarar ba, ga kuma alhinin rabuwa da iyaye''.

    'Shekaruna 12 lokacin da aka yi min aure aka kai ni can garin Bidda jihar Niger, kuma bayan an kai ni na rika guduwa makabarta ina kwana, na ka tada kai da kabari in yi barci na,'' ta ce.

    ''Daga bisani da na ga alamu ana fako na sai na koma hawa kan bishiyar mangwaro ina kwana, don kawai ina gudun gidan miji,'' in ji ta.

    Amma kuma ta ce yanzu lamarin ya sauya, sai dai kuma duk da haka akwai daidaikun wurare da har yanzu ake samun irin wannan al'ada ta kukan aure.

    Hakan na faruwa ne in ji ta saboda a yanzu ana barin yara mata su yi karatu mai zurfi wanda hakan yakan sa su kara mallakar hankalinsu kafin a yi musu aure.

    Ta kuma kara da cewa ''Babban dalilin kukan shi ne saboda ka saba da gidanku, da mahaifanka, da 'yan uwanka, kuma ka san cewa idan ka tafi shikenan sai lokaci mai tsawo, kuma a wasu lokutan akan kai yarinya wani gari ne mai nisa.''

    Ita ma a nata ra'ayin wata dattijuwa Hajiya Fatima Haruna cewa ta yi batun haka yake, yawanci kukan rabuwa da iyaye da dangi ne sassala, duk da cewa akwai sauran dalilai da kan sa kukan.

    ''Shekaruna 13 lokacin da aka yi mini aure, kuma iyayena ne suka zabar min suka ce sai Bafulatani dan uwana,'' in ji ta.

    Ta kuma bayyana cewa a lokacin da aka kai ta gidan miji surukarta ce ta rika kula da ita, sai bayan wata daya sannan ta ga mijin da aka aura mata.

    Sai dai kuma wasu dalilan da suka sa yanzu ba a cika samu irin wannan al'ada da kukan tafiya gidan miji ba shi ne saboda abubuwan sauye-sauye da zamani ya kawo wadanda suka hada da ci gaba a fannin sufuri, baya ga bunkasar hanyoyin sadarwa irin su wayar salula da kuma hanyoyi daban-daban da a ko ina kake a duniya kamar kana tare da mutum.

    Malama Surayya Aminu wata matashiya ce da a shekarun baya aka yi mata aure, kuma ta shaida wa BBC cewa ita ba ta taba sanin ma akwai wata al'adar da ake kuka idan za a tafi gidan miji ba.

    ''Ni kam na sai bayan da na kusa kammala karatun jami'a aka yi min aure, na san babu dadi rabuwa da iyaye da 'yan uwa, amma kuma na san komai dadewa zan bar su, don haka mene ne abin kuka tun da auren soyayya muka yi?,'' in ji ta.

    Ta kuma ce: ''Ai ko a ina ne tun da akwai kafofin sadarwa a koda yaushe ina iya magana da iyayena da 'yan uwana, ko da kuwa hira da bidiyo ne muna ganin juna kamar muna tare, don haka babu wata damuwa''.

    Halima Sani kuwa ta cewa ta yi lokacin da aka yi mata aure na soyayya tana da shekara 21, amma duk da hakan sai da ta yi kukan rabuwa da iyayenta.

    ''Ina son mijin da aka aura min, auren soyayya ne, ina ta murna amma kuma ranar da za a kai ni gidansa sai da hankalina ya tashi, sai wani tunani ya zo min na ga cewa zan fara wata rayuwa da ban sani ba, kuma zan daina ganin iyayena, da 'yanuwana kamar yadda na saba,'' a cewarta.

    Auren dole ko na zabin iyaye?
    Irin wannan aure ne wanda akan nema wa yaro ko yarinya daga cikin dangin uwa ko na uba ba tare da neman shawararsu. Irin wannan aure ana yin sa ne don kara dankon zumunci tsakanin 'yanuwa.

    Ta wani gefen kuma iyayen yarinya kan aurar da ita ga wani saboda matsayinsa, ko kudinsa, ko da kuwa ba ta son shi.

    Duka irin wadannan suna saka amare kuka da guje-guje idan za a kai su gidan miji, kamar yadda Hajiya Amina Saulawa ta ce

    Duk da cewa al'amura sun kara sauyawa game da aurar da 'yaya mata a kasar Hausa, amma kuma har yanzu akwai wasu wuraren da ke bin tsarin da addinin Musulunci ya shardanta cewa auren 'ya mace budurwa, hakkin uba ne ya zaba mata mijin da zata aura, ba tare da saninta ko mahaifiyarta ba.

    Alhaji Mai-Zabura ya ce abin da ya sa hakan yake faruwa saboda yawanci auren fari za ka ga 'yan matan ba su mallaki hankalin da za su iya zabar mijin da ya dace da su ba, don haka iyaye ke zabar musu.

    A wasu lokutan ma akan bayar da yarinya ga wanda ya kai sa'an mahaifinta, ko da kuwa ba ta so, musamman idan iyaye suka ga ta kara shekaru kuma babu wanda ya fito neman aurenta.

    ''Muna ganin idan ba mu yi sauri muka zaba wa 'yayanmu mazajen aure ba, abin ya kan zama da matsala, ko kuma yarinya ta sangarce babu mai aurenta, shi ne abin fargaba,'' in ji Mai-Zabura.

    Hakan ba ya rasa nasaba da kananan shekarun da yarinya ke da shi da za a iya cewa ba ta mallakai hankalinta ba ta yadda za ta iya zabar abin da ya dace da ita, da kan sa auran fari iyaye ne ke da zabi.

    Hajiya Amina ta ce tana da shekara 13 aka yi mata aure, kuma ba su taba ganin juna ita da mijin ba.

    ''Lokacin ina makarantar kwana, kakana ya zo ranar ziyara ya kawo min kayayyaki, daga nan ya saka hannu a aljihunsa ya dauko katin daurin aure yi mika min ya ce 'ga shi nan na riga ya daura miki aure', na kuma amsa na amince haka,'' in ji Amina.

    Amma kuma wasu iyayen sukan bar yarinya ta zabi wanda ta ke so bayan sun fahimci cewa zabinsu na farko bai yi tasiri ba.

    Wasu masu lura da al'amuran zamantakewa na cewa a yanzu saboda zurfin karatu da galibi yaya mata ke yi, sukan kai shekarun da su kan fahimci abubuwan zamantakewar aure da mu'amala da jama'a, kuma yanayin auren na yanzu na soyayya ake yi ba na dole ko na zabin iyaye ba.

    Rawar da wakokin rakiyar amarya ke takawa

    A shekarun baya, ya zama wata al'ada da kuma nishadantarwa a lokacin da za a raka amarya gidan mijinta, 'yan mata kawaye kan rika rera wakoki ga amaryar.

    Galibi irin wadannan wakoki kan sosa ran amarya har ta rika rusa kuka.

    Hajiya Fatima Haruna ta ce tabbas irin wadannan wakoki kan yi tasiri wajen saka amarya kuka a lokacin da za a raka ta gidan miji.

    ''Irin wadannan wakoki sukan tayar da hankalin amaryar da kuma fusata ta saboda kalaman da ke ciki na alhini da sosa rai, ta kan rika tunanin kamar ta rabu da iyayenta da 'yanuwanta ne har abada, sai ta fashe da kuka,'' in ji ta.

    Ta ce '' Wakokin sun hada da kamar su:

    Ayye Mama Ayye Mama

    Mama ye iye

    Ayye mamala bolabo

    Mama ye iye

    Ayye Mama kin tafi kenan

    Mama ye iye

    Da aure yana raka aure

    Mama ye iye

    Da na bi ki mun tafi tare

    Mama ye iye

    Ko tukin tuwo na koya

    Mama ye iye

    Ko damun fura na koya

    Mamaye iye….

    Ta kuma ce akwai waka kamar:

    Ta zama ta zama

    Ta zama…

    Ta zama dauko riga

    Ta zama…

    Ta zama dauko wando

    Ta zama...

    Ta zama dauko hula

    Ta zama…

    Ta zama dama furar nan

    Ta zama…

    Duka irin wadannan wakoki kamar yadda Alhaji Mai-Zabura ya shaida wa BBC, kawayen amarya kan rika rera su ne lokacin da aka dora amarya a kan godiya ko kuma amalanke a wancan lokacin da dangi 'yan rakiya da makada, don su kara tsokana da tsaoratar da amarya.

    Ya ce: ''Hakan ke sa amarya hankalinta ya kara tashi ta fara kuka, tana ganin kamar za a kai ta inda ba za ta sake dawowa ba, kuma cikin wakokin akwai kalaman da ke nuna cewa rayuwar bam ai dadi ba ce, bauta ce da sauransu, shi ya ke sa kukan ai.''

    Sai dai kuma sannu a hankali, duk da ba za a iya cewa an daina wannan al'ada ta kukan zuwa gidan miji ba a wannan zamani, amma kuma bayanai sun nuna cewa lamarin ya yi gagarumar sauyawa ba ma a cikin birane ba har ma da kauyuka.

    Me ya sa al'amura suka sauya yanzu ba kamar zamanin da ba?

    Idan aka kwatanta da yadda lamarin ke faruwa a zamanin yanzu ya sha bamban ba kadan ba a bisa wasu dalilai da ta bayyana na ci gaban da zamani ya zo da shi, kamar yadda Hajiya Amina Saulawa ta yi wa BBC karin bayani.

    ''Yanzu al'amura sun sauya, amma a wasu wuraren har yanzu ana samun ire-iren 'yan matan da ke kuka idan za a kai su gidan miji," in ji ta.

    Amma kuma akwai bambanci tsakanin yadda hakan ke faruwa a wannan zamanin da kuma zamanin da, wato shekaru da dama da suka shude.

    ''Ai a zamanin da, ba a fada wa yarinya ko wane ne mijin da za a aurar mata, galibi auren gida ne ake yi, auren zumunci, yarinya ba za ta san mijinta ba sai ranar da aka kai ta. Tana dakin suruka nan take komai, sai ta kwana talatin ma bata ga mijin ba'', Mai-Zabura ya ce.

    An fi dabbaka al'ada a lamarin aure a zamanin da ko kuma shekaru da dama da suka gabata, inda galibi akan yi wa 'yan matan da basu wuce shekaru goma sha biyu ba ko ma kasa da haka aure.

    Hausawa kan yi wata karin magana da su kan ce ''zamani riga'', saboda yadda wasu abubuwa sukan shude bayan wasu shekaru, a yayin da sabbi suka sha bamban da sukan shigo har su rika cin karo da su a al'adance.

    Malama Fatima Haruna ta shaida wa BBC cewa ai su a lokacin da aka yi musu aure ba su ma san yadda gidan mijin ko kuma mijin yake ba, ba sa saka baki a cikin maganar bikin aure sai dai manya har a yi a gama.

    ''Yanzu babu irin wannan, budurwa ita ke yi wa kanta komai, ita ke zuwa ta duba gidan da za ta zauna, har ma a je a rika jera kayan daki da ita, a kai ta gidan miji, budurwa tana rabon katin aurenta,'' in ji Fatima.

    Yawan shekarun da ake kai wa ba a aurar da yarinya ba shi ma ya taka rawa wajen sauya al'amuran aure, da kuma rashin yin kuka idan za a kai yarinya gidan miji, in ji Mai-Zabura.  less
    February 1, 2021 - edited
    • 5 people like this
    • Yusha'u Alhassan
      Princess Ayshatou Allow me to copy this pls.
      • February 1, 2021
      • -
      • 2 like this
      • -
      • Report
    • Yusha'u Alhassan
      shaatouh Abubakar Nima Dan Allah \nLemme copy this
      • February 2, 2021
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
  • Yusha'u Alhassan
    Yusha'u Alhassan
    A cikin shirin mu na Ilimi abin nema na wannan mako za a tattauna ne kan hakkokin kananan yara akan iyayen su, ciki harda yara almajirai, wani irin nauye-nauye ne da hakkokin yara da Allah ya daura akan iyayensu?
    Akan wannan maudu'i ne muke bukatar...  more
    A cikin shirin mu na Ilimi abin nema na wannan mako za a tattauna ne kan hakkokin kananan yara akan iyayen su, ciki harda yara almajirai, wani irin nauye-nauye ne da hakkokin yara da Allah ya daura akan iyayensu?
    Akan wannan maudu'i ne muke bukatar jin ra'ayinku ta wannan shafi mai albarka.
    sai munji daga gareku.

    A kasance tare da ni mai gabatarwa
    Yushau'u Alhassan.
    Ranar jumma'a da misalin karfe sha daya na safe.
    Ta gidan radio TSBS Jalingo.  
    August 19, 2020
    • Sadik , Bakandamiya, and Lawan Dalha like this.
  • Yusha'u Alhassan
    Yusha'u Alhassan commented on Bakandamiya's photo.
    August 16, 2020
    • 8 people like this
    • Yusha'u Alhassan
      Yusha'u Alhassan Wasan madandini (wasan rufe ido)
      • August 16, 2020
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Yusha'u Alhassan
      Bakandamiya Mashaa Allah! Lallai ka tuna da Aliyu da Fadimatu.
      • August 17, 2020
      • -
      • Report
  • Yusha'u Alhassan
    Yusha'u Alhassan liked Abubakar Sulaiman II's photo.
    August 12, 2020
    Shin kokasan cewar zaka iyayin kowwace iriyar tambaya akan dukkan abinda kake son kasani anan? tambayoyi.com.ng shiga MENU kamika tambayarka
    • Bakandamiya and Yusha'u Alhassan like this.
  • Yusha'u Alhassan
    Yusha'u Alhassan liked Khadija Ahmad 's post.
    August 10, 2020
    Khadija Ahmad
    Assalam alykum barka da dare dan allah video dina yaki hawa bansan me yasa ba a taimakamin dan allah
    • 5 people like this
    • Yusha'u Alhassan
      Bakandamiya Wa'alaikum Assalam Khadijah. Muna dan wani aikin upgrade ne akan video module namu, amma nan da kwana biyu komai zai daidaita, za ki iya ci gaba da posting video in shaa Allah. Mun gode kwarai.
      • August 9, 2020
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Yusha'u Alhassan
      Khadija Ahmad Ok tam nazata daga nice ai allah ya baku ikon gamawa nagode
      • August 9, 2020
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Yusha'u Alhassan
      Bakandamiya Amin madalla.
      • August 9, 2020
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Yusha'u Alhassan
      Bakandamiya Malama Khadija, ki duba dora video ki gani don mun kammala aiki akan shi.
      • August 12, 2020
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Yusha'u Alhassan
      Khadija Ahmad Masha allah ,allah ya kara taimakawa
      • August 13, 2020
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
  • Yusha'u Alhassan
    Yusha'u Alhassan
    Assalamu alaikum 'yauwa maza da mata masu albarka ina yi muku fatan alkhairi da fatan an wayi gari lafiya. Allah ya sadamu da alkhairinsa amin.
    August 10, 2020
    • 5 people like this
    • Yusha'u Alhassan
      Bakandamiya Wa'alaikum Assalam Malam Yusha'u barka da asuba. Amin Ya Rabb, Allah Ya saka da alkhairi.
      • August 10, 2020
      • -
      • 1 likes this
      • -
      • Report
    • Yusha'u Alhassan
      Rahmatu Lawan Wa'alaikum salam. Alhamdulillah mun wayi gari lafiya
      • August 10, 2020
      • -
      • Report
  • Yusha'u Alhassan
    Yusha'u Alhassan liked Lawan Dalha's playlist.
    May 23, 2020
    Karatun Alkur'ani Mai Girma, Surah Ibrahim (014), tare da Limamin Haramin Makkah, Sheikh Maher Bin Hamad Al Muaiqly.
    Quran Surah Ibrahim (014) | Sheikh Maher Al Muaiqly
    Pop-out Player
    • Add to my Playlist
      014. Surah Ibrahim - Sheikh Maher Al Muaiqly (5 plays)
    014. Surah Ibrahim - Sheikh Maher Al Muaiqly
    1 track
    • 8 people like this
  • Yusha'u Alhassan
    Yusha'u Alhassan liked Mahmud Yunusa's photo.
    May 4, 2020
    • 7 people like this
    • Yusha'u Alhassan
      Bakandamiya
      • May 4, 2020
      • -
      • Report
  • Yusha'u Alhassan
    Yusha'u Alhassan liked Lawan Dalha's playlist.
    May 4, 2020
    Tafsirin Alkur'ani mai girma na 08 Ramadan 1441/2020 daga Masallacin An-Noor, Wuse II, Abuja wanda Sheikh (Dr) Isa Ali Ibrahim Pantami tare da Alaramma Abdullahi Abba Zaria ke gabatarwa.
    08 Ramadan Tafsir 1441-2020 | Sheikh (Dr) Isa Ali Pantami
    Pop-out Player
    • Add to my Playlist
      08 Ramadan Tafsir 1441-2020-Sheikh Isa Ali Pantami (19 plays)
    08 Ramadan Tafsir 1441-2020-Sheikh Isa Ali Pantami
    1 track
    • 20 people like this
  • Yusha'u Alhassan
    Yusha'u Alhassan liked Lawan Dalha's playlist.
    May 4, 2020
    Ku saurari tafsirin Alkur'ani mai girma na 10 Ramadan 1441/2020 wanda limamin Babban Masallacin Abuja, Sheikh (Prof.) Ibrahim Ahmad Sa'eed Maqari ya gabatar.
    10 Ramadan Tafsir 1441-2020 | Sheikh (Prof.) Ibrahim Maqari
    Pop-out Player
    • Add to my Playlist
      10 Ramadan Tafsir 1441-2020 - Sheikh (Prof) Ibrahi... (11 plays)
    10 Ramadan Tafsir 1441-2020 - Sheikh (Prof) Ibrahim Maqari
    1 track
    • 14 people like this
View More
Loading ...

About

Personal Information

  • Sunan Farko Yusha'u Alhassan
  • Jinsi Namiji
  • Ranar Haihuwa February 22, 1983
  • Takaitaccen Bayani Marubuci kuma mai sha'awan karance-karance

Contact Address

  • Sunan Gari Jalingo, Taraba
  • Karamar Hukuma Jalingo
  • Sunar Jaha Taraba
  • Sunar Kasa Nigeria

Hotuna

  • Wall Photo­s 8 photos

  • Profile Ph­otos 2 photos

Previous
Next
© 2022 Bakandamiya About Terms Privacy Subscription Earn Money Advertise Contact
  • Facebook
  • Twitter
  • Linkedin
  • Youtube
  • Pinterest
  • Instagram