Lawan Dalha
Mashaa Allah! Wannan maudu'i mai muhimmanci dake bukatar sa hannun mutane da kuma hukumomi daban-daban. Amma hakika, ma'aikatan media ke da babban rawa da za su taka. Allah Ya yi jagora.
"Allahu Akbar, Allahumma Ahillahu Alaina Bil-Amni Wal-Iman, Was-Salamati Wal-Islam, Lima Tuhibbu Rabbuna Wa Tarda, Rabbuna Wa Rabbukallah". 📚 Tirmizi (3/157)
Ma'ana: "Allah ne mafi Girma, Ya Allah! Ka sanya tsayuwarsa a garemu ta zamo kwanciyar hankali ce, da imani, da aminci, da musulunci, da kuma gamokatar da abin da ka ke so Ya Ubangijinmu, kuma ka ke yadda da shi, Ubangijinmu da Ubangijinka (ya kai wannan jinjirin wata!) shi ne Allah". Allah ya sa mu dace
Sahabi Albarra'u ɗan Azib yace: Manzon Allah (S.A.W) ya yi masa wasiyya idan ya zo zai kwanta barci, bayan ya yi alwala kuma ya kwanta ta ɓangaren damansa da yace:
Sahabi Albarra'u ɗan Azib yace: Manzon Allah (S.A.W) ya yi masa wasiyya idan ya zo zai kwanta barci, bayan ya yi alwala kuma ya kwanta ta ɓangaren damansa da yace:
"Allahumma aslamtu nafsi ilaik, wa fawwadtu amri ilaik, wa wajjahtu wajhi ilaik, wa alja’tu zahri ilaik, raghbatan warahbatan ilaik, la maljaa wala manja minka illa ilaik, amantu bikitabikal-lazi anzalta, wabi-Nabiyyikal-lazi arsalta".
Ma'ana: "Ya Allah! Na sallama raina gareka, na maida al’amarina gareka, na fuskantar da nufina gareka, na dogara da kai (a cikin dukkan al’amurana) saboda kwadayin abin da ke gareka, da tsoron ka, babu mafaka, babu matsira daga gareka sai zuwa gareka, nayi imani da littafinka da ka saukar da kuma Annabinka da ka aiko".
A ƙarshen Hadisin sai Manzon Allah {S.A.W} ya ce: ".... Ka sanya waɗannan kalmomi su zama ƙarshen maganarka, idan ka mutu a wannan dare naka, to ka mutu akan Tafarki".
Acikin wata riwayar kuma ya ƙara da cewa: "Idan ka wayi gari zaka wayi gari a cikin alkhairi". Bukhari/Muslim
Darussa:
1- Falalar yin alwala kafin kwanciya barci.
2- Kwanciya ta ɓangaren jiki na dama.
3- Ambaton Allah a lokacin kwanciya barci, domin ka rufe aikinka na ƙarshe a wannan rana da ambaton Allah.
Ma'ana: "Ya Allah! Ina neman tsarinka daga gushewar ni'imarka, da juyawar lafiyar da ka ba ni, da gaggautowar uƙubarka, da dukkanin fushinka". (Muslim: 2739)
Yana daga cikin addu'oi ingantattau da aka ruwaito daga farin jakada Manzon (S.A.W) yana yi a zaman tahiyar ƙarshe na sallah; bayan karatun tahiya da... moreADDU'A TAKOBIN MUMINI 01
Yana daga cikin addu'oi ingantattau da aka ruwaito daga farin jakada Manzon (S.A.W) yana yi a zaman tahiyar ƙarshe na sallah; bayan karatun tahiya da salati:
"اللَّهُمَّ اغفِرْ لي مَا قدَّمْتُ، وَمَا أخَّرْتُ، وَمَا أسْرَرْتُ، وَمَا أعْلَنْتُ، وما أسرفت، وما أنت أعلم به مني ، أَنْتَ المُقَدِّمُ وَأَنْتَ المُؤَخِّرُ لا إِلَهَ إِلاَّ أَنْـتَ" 📚 رواه مسلم ٥٣٤/١
Ma'ana: "Ya Allah! Ka gafarta min abin da ya wuce, da abin da zai zo, da abin da na ɓoye, da abin da na bayyana, da abin da na yawaita na zunubi, da abin da Kai ne ka fini saninsa, Kai mai ne gabatarwa, kuma Kai ne mai jinkirtawa, babu abin bautawa da gaske sai Kai"
Fitsarin kwance da a turance ana kiranshi “Bedwetting” ko kuma “incontinence” sannan a kimiyyance kuma ana kiranshi da “nocturnal enuresis”, matsalace ta yin fitsari... moreFITSARIN KWANCE (BEDWETTING/NOCTURNAL ENURESIS).
Fitsarin kwance da a turance ana kiranshi “Bedwetting” ko kuma “incontinence” sannan a kimiyyance kuma ana kiranshi da “nocturnal enuresis”, matsalace ta yin fitsari yayin da mutum yake bacci ba tare da maiyin fitsarin yasan yayi ba (involuntarily).
Yawanci ana samun fitsarin kwance ne a yara da suke a rukunin shekara daya zuwa bakwai (1-7years), saboda kankantar jakar ajiye fitsarin yara (bladder), ba kasafe take iya rike adadin fitsarin da jiki yake samarwa da daddare ba. Sannan yara basa iya samar da isashshen sinadarin hormone da yake rage adadin fitsarin da jiki ke samarwa da daddare maisuna “antidiuretic hormone” sai hakan ya haddasa rashin iya riqe fitsari ga yara da daddaren.
A bisa al’ada ta girman yaro, a tsakanin shekara daya zuwa shekara bakwai na farkon rayuwa, saboda yanayi da tsari na gudanar da rayuwar yaro, yakanyi fitsari ayayin da yake bacci ba tare da ya sani ba. Hakan kuma ba wata matsalace da za’a tsangwami yara ba, domin suma basu san sunayi ba, ba yin Kansu bane (involuntarily). Wasu yaran sukanyi kullum wasu kuma sukanyi yau gobe basuyi ba, wasu ma idan sukayi sau daya sai bayan kwanaki suke kara yi (jefi-jefi), wasu ma da sun fara sukan daina yi, ya danganata da nutsuwa, tsarin rayuwa, saitin ruhi (mind-set) da na qwaqwalwar (brain set-up) yaro a tsakankanin kwanakin. Bayan shekara bakwai yara sukan daina yin fitsarin kwance, saboda cigaban kwakwalwa suka samu yana canja tsarukan rayuwarsu.
Matsalar fitsarin kwance matsalace da horo da tsangwama basa maganceta sai ma ta kara ta’azzara. Hakuri da dabaru da fahimtar da yara da canja musu tsarin kwanciyar bacci da na rayuwa (change in lifestyle) shine mafita. Iyaye su dunga hakuri, kada su dunga kyarar ‘yayansu, ko subar wani ya kyare su, ko da sunga sunshiga damuwa akan Matsalar su kwantar musu da hankali, domin walwalarsu tana da tasiri wajen daina yin fitsarin kwancensu. Babu dacewa a hukunta yara ko a tsangwamesu akan abinda basu san ma sunayi ba kuma bazasu iya hana kansu yi ba.
Kuskuren da iyaye sukeyi shine, su kanyi horo tare da tsangwamar yara idan suna fitsarin, wanda hakan yake jawowa saboda fargaba da tsoro da damuwa da kunchi da suke shiga, sai Matsalar fitsarin kwancen ta zama cikin tsaruka (pattern) da kuma shirye-shiryen (programs) da ruhin dan adam (mind) yake bawa jiki ya gudanar ba tare da mutum yana sane ba. Duk lokacin da yara sukazo kwanciya fargabar kada suyi fitsari a dakesu ko a tsangwamesu sai ya zama shine abinda yake tunawa jiki cewa idan sun kwanta suyi fitsari, domin shi ruhin dan adam dama yana dauke da shiryayyun tsaruka (programmed patterns) na yin fitsarin kwancen, fargaba da tsoro kuma suna tunatar da ruhi ya zama a shirye domin yin fitsrain. Mafiya yawan lokuta a dalilin hakan sai yara su girma sun wuce shekara bakwai (7years) suna fitsarin kwance.
Daga nan Matsalar ta faro, amma daga lokacin da yara suka girma suna fitsarin kwance, wasu sai aci gaba da tsangwamarsu ana ganin cewa suna sane ma sukeyin fitsarin, tayaya da girmansu za’ace suna fitsarin kwance, ko kuma ayita dugunzuma mai matsalar cewa “duk ga ‘yan uwanka nan basayi saikai”, irin wadannan maganganu sukan haddasa shiga kunci ga mai dauke da Matsalar har takai ya samu wani matsala da ake kira PTDS (Post-Traumatic Stress Disorder), hakan yasa yayita mugayen mafarke-mafarke, ko yayita mafarki gashi a wani bandaki a tsugunne zaiyi fitsari, kuma dagaske sai yayi fitsarin yana cikin mafarkin, ko ya ganshi a bakin kwata ya tube zaiyi fitsari. Daga hakane, wasu sai ace aljani ne ya shiga jikinsu ko ya shafesu, wasu kuma ace Matsalar ma fitsara ce take damunsu da sauransu. Alhaili babu ko daya aciki wanda ya faru, kawai matsalace da ta faru tun daga yarintarsu, saboda tasirin damuwa da kunci da tsangwama da horo sai Matsalar ta dasu a cikin qwaqwalwa da ruhinsu (ya zame musu post-traumatic stress disorder) sai fitsarin kwancen yaci gaba da maimaituwa lokaci-lokaci a cikin rayuwarsu ba tare da suna sane ba ko kuma zasu iya hana afkuwar hakan ba.
GA WANDA YA GIRMA YANA FITSARIN KWANCE, ABINDA YA KAMATA YAYI SHINE;
1) Shan ruwa mai yawa da sassafe, da kuma shan ruwa mai yawa da daddare idan za’a kwanta (wani zaice, a’a! ya za’a sha ruwa da yawa yayin kwanciya bayan so ake kada ayi fitsarin kwance?, babu damuwa acikin yin hakan zuwa wani lokaci).
2) Daina ci ko shan duk wani abinci ko abun sha mai dauke da sinadarin “caffeine” kamar su chocolate , coca cola, coffee, goro, taba, furanto, bonbita, milo, da sauransu, domin sinadarin yana motsa jakar ajiye fitsari “bladder”.
3) A daina yin fitsari lokacin da za’a kwanta
4) A dunga yin fitsari bayan duk awa biyu ko da ba’aji fitsarin ba, amma banda dab da lokacin baccci.
5) Canja lokutan bacci, da tsarin kwanciya bacci (canja salon kwanciya).
6) Kwantarwa da hankali, da kuma yarda za’a daina.
Matukar mai fama da Matsalar zai lizimci wadannan shawarwari zai rabu da Matsalar fitsarin kwance cikin lokaci kankani. Matsalar fitsarin kwance ba matsala ce ta asibiti ba, matsala ce ta abinda ya shafi kwakwalwa da ruhin Dan adam, wanda maganinta kawai shine caccanja tsarukan rayuwa da kuma kwantar da hankali.
Iyaye kuma da suke da ‘yaya masu fama da wannan matsala, su taimaka musu su dunga kwantar musu da hankali, kada a tsangwamesu ko a tsokanesu ko a tsanesu, ko a dunga nuna musu laifinsu ne da sukeyi.
Assalamu alaikum
Wannan zaure an bu?e shi ne domin ya?a karatukan malamai da rubuce-rubucen da suka shafi addini musulunci. Muna fatan Allah ya bamu ikon amfanuwa da juna. Ameen