Skip to content

Yadda ake amfani da darsau wajen kayata labari

Share |

A maƙalar da ta gabata ta dabarun rubutun labari, mun tsaya da bayani ne a kan haɗakar salo sama da ɗaya wajen samar da labari. Mun bayyana yadda ake saƙa salo mabambanta su ƙara armashi a cikin labari, mun kuma faɗi muhimmanci ko amfanin yin hakan. Yau insha Allahu za mu tattauna ne a kan Ɗarsau.

Me ɗarsau ke nufi?

Ɗarsau na labari:- Cikakkiyar kalmar ita ce ɗarsawa. A rubutu na Adabi marubuci yana amfani da ita ne wurin yi wa masu nazarin shi saƙa, ko nune ta yadda zai sanya musu irin tunanin da yake so su yi a zukatansu. Idan yana so su yi mamaki sai ya ɗarsa musu wasu kalamai cikin hikima su fara mamaki, idan yana so su yi al’ajabi, ko su ji tsoro, ko su fara wata tantama, ko kuma ya sanya musu tausayi ko farinciki duk akwai hikimar da ake yi ta hanyar amfani da ɗarsau a ɗarsa musu waɗannan tunanin.

Ya ya ake yin ɗarsau?

Hikimomin yin ɗarsau  su za mu tattauna a wannan maƙala insha Allah. Za mu riƙa ɗaukar kowacce gaɓa ta ɗarsau ɗaya bayan ɗaya muna tattauna ta da misalanta. Kamar kullum yau ma zan so na yi amfani da wani tsagi na labari wurin ba da misalan don a fi fahimta. A don haka, zan yi amfani da labarina na Da ma Sun Faɗa Mini don fito mana da misalan tarin ɗarsau ɗin da ke cikinsa.

Ɗarsau na al’ajabi:- Wannan shi ne ɗarsau na farko da aka fara saƙa labarin da shi. A labarin an nuna cewa Zainab ta yi mafarki da ‘yan ƙungiyar asiri sun ce za su shanye jinin jaririn da za ta Haifa. Bayan ta farka daga mafarkin a firgice kuma ga abin da ya biyo baya:

“Mene ne? Me ya faru?” Ya shiga tambayarta a kiɗime kamar yadda ita ma take ba shi amsar a kiɗime tana waige-waige.

“Bi . .. bi . . . biyo ni suka yi za su kashe ni.” Jin haka ya ƙara jawo firgitacciyar matar tashi jikinsa bayan ya fahimci mafarki ta yi. Don haka sai ya fara yi mata addu’o’i yana tofa mata yayin da ita kuma take maƙale da shi kamar za ta shige jikinsa, fuskarta ta haɗa gumi sharkaf kamar sabuwar kuturwa a rana. Bai daina addu’ar yana shafa bayanta ba har sai da ya tabbatar ta samu nutsuwa ta dawo cikin hayyacinta ta nutsu sosai sannan ya tambayeta abin da ya faru.  Nan take ta kwashe labarin mafarkin nata gaba ɗaya na ganin dodonnin mutanen da ta yi da kuma ce mata da suka yi wai sai ta ba su ɗan cikinta sun sha jinin shi.

Jin haka ya yi shiru alamun damuwa suka bayyana ƙarara a kan majigin fuskar shi, tuni ma ya saki matar tashi ya miƙe tsaye ya fara safa da marwa a cikin yalwataccen ɗakin nasu mai dishi-dishin hasken lantarki na bacci.

“Murad.! Me ya faru?” Zainab ta tambaye shi tana mai ƙara yin nazarin shi ganin yadda a cikin ƙanƙanin lokaci yanayinsa ya sauya. “Da ma sun faɗa mini.” Ya ambata hakan daidai lokacin da ya goya hannayensa a baya da alamar ƙololuwar damuwa a tare da shi.

“Dama sun fada maka?” Zainab ta maimaita furucin na shi ƙasa-ƙasa.

“Su waye suka faɗa maka? Kuma me suka faɗa maka?” Ta yi masa tambayar da ta dawo da shi hayyacinsa ya yi firgigit kamar ya tashi daga bacci, sai a sannan ya fahimci ya yi suɓutar baki zancen zuci ya fito fili, kamar yadda ita ma Zainab ɗin sai a lokacin ta gane cewa bai san lokacin da ya ce ‘Da ma sun faɗa mini’ ɗin ba.

Idan muka yi nazarin wannan misalin, daga lokacin da Aliyu ya ce da ma sun faɗa mini, marubucin ya ɗarsa wa masu karatu al’ajabi da tunanin yadda aka yi aka haihu a ragaya. Su waye suka faɗa masa? kuma a ina ya san su da suka faɗa masa? Waɗannan su ne tambayoyin da za su mamaye zuciya cike da al’ajabi gami da son sanin amsoshin su. Da ire-iren wannan hikimar ake so marubuci ya riƙa ɗarsa wa masu nazarin shi al’ajabi ta yadda zai riƙe su su kasa ajiye labarin sai sun ga ƙwal-uwar-daka.

Ɗarsau na zargi:- Bayan mijin nata ya ƙi ya faɗa mata su waye suka faɗa masa, kuma me suka faɗa masa, ga hikimar da marubucin ya yi amfani da ita wajen ɗarsa wa masu karatu zargin shi:

“Ba . . . ba . . . babu komai . . . Ai ban san su ba” Zainab ta tuno a yadda ya ba ta amsar sai ka ce wanda wani ya ce masa ya san su. ‘To amma kuma idan babu rami me ya kawo zancen a kula da rami?’ Zuciyarta ta fara tuhumar shi, lokaci guda kuma Shaiɗan shi ma ya zage da aiki tuƙuru wajen yi mata aringizon hujjoji da za su tabbatar mata da cewa Aliyunta ɗan mafiya ne.

“Kin ga fa Aliyun ki yaro ne matashi da ba zai haura shekaru talatin da biyu zuwa da uku ba, amma idan ana lissafa masu hannu da shuni na unguwarnan idan bai zo na ɗaya ba to ba zai taɓa wuce na biyu ba, ko dama a inda ya samu na shi kuɗin kenan ƙungiyar asiri?” Tuhuma ta farko daga sheɗan.

“Kin ga dama su biyu ne waɗanda duniyarsu ke haskawa a unguwar nan, da shi da wannan maƙocin naku Alhaji Suma’ila dilan manfetur. Kuma kin san batun tsayawa fasalta kyan gidajenku, ko kuma ƙiyasta abin da aka kashe wajen gina su ɓata lokaci ne, abu ɗaya dai da mutum zai saka a ransa shi ne ba ƙananun kuɗaɗe aka narkar wajen gina su ba, to abin tambaya shi ne mece ce sana’ar mijinki da har zai iya gina gida irin wannan?

Shi dama Alhaji Suma’ila dilan man fetur ne wanda yake da gidajen mai, don haka idan ya gina nasa gidan babu mamaki tunda dama da mai kama ake yin ƙota. Duba da yadda aka ce harkar man fetur na garawa. To amma Aliyunki fa wanda ba komai ba ce sana’arsa face sayar da goro? Shin ko shi ma goron ana samun kuɗi da shi ne kamar fetur? To amma babu mamaki saka zaren makaho a allura.

Ba ma wannan ba! Ko kin manta da wannan ɗakin da yake cikin gidan nan naku wanda tunda kike ba ki taɓa shiga ciki ba kamar yadda ba ki taɓa ganin Aliyu shi ma ya shiga ba? To ko dai a cikinsa Aliyunki yake cin mushensa? Kinga fa kusan shekara ɗaya kenan da ɗaura aurenku da Aliyu, amma sau ɗaya kika taɓa leƙa ɗakin, shi ma kuma duhu bai bari kin iya ganin komai a cikin shi ba Aliyu ya fito ya ja hannunki kuka koma falo.”

A daidai wannan gaɓar za ku tarar duk mai nazarin an ɗarsa masa zargin Aliyu, duba da irin abubuwa da suka saɓa da tunani na cikin gaɓar labarin, don haka mai nazari zai fara zuba kadarar mujiyarsa don ganin rashin gaskiyar ta Aliyu a gaba.

Ɗarsau na tantama:- Ita kuma a wannan gaɓar marubucin yana so ya kiɗima masu nazari su kasa gane cewa Aliyu yana da laifi ko ba shi da laifi ne. Don haka sai ya sake yin amfani da ɗarsau wajen ɗarsa musu tantamar wancan zargin nasu na sama.

“Anya kuwa Aliyunki zai aikata abu irin wannan? ko kin manta yadda ya kasance mutum mai matuƙar ibada ko kaɗan salla  ba ta wuce shi a jam’i, kar ki manta fa duk abin da Aliyu yake yi ana kiran salla to kuwa ya haƙura har sai an idar. Sallar nafila kuwa dare da rana cikin yin ta yake, ga shi kuma ba ya rabo da azumin nafila, haka kuma akwai shi da kyakkyawar mu’amala ta yadda babu yadda za a yi ka zauna da Aliyu bai shiga ranka ba.

Aliyu yana da tsananin tausayi da yawan kyauta. To wai anya kuwa a samu ƙuma a jikin kifi?  Anya kuwa mutum mai irin wannan halayyar zai yi abin da ki ke zargin shi?”

“To amma idan ban zarge shi ba ta yaya wanda bai ɗanɗana fura ba zai ce sikari bai ji ba?   Su waye suka faɗa masa kuma me suka faɗa masa?” Duk ta jera wa kanta jerin gwanon waɗannan tambayoyin da amsarsu ba zasu samu ba a gareta.

Da zarar mai nazari ya zo gaɓar nan, zai fara yarda a ransa cewa tabbas bai kamata mutum mai kyawun hali ya zama ɗan mafiya ba, don haka gaba ɗaya za a iya ɗarsa masa tantama ya kasa gane alƙiblar labarin.

Abin lura: Ɗarsau ba shi da wata iyaka, ana iya ɗarsa wa mai nazari duk abin da aka ga dama a cikin ransa don a cimma wata manufa ko a ribaci zuciyarsa. Ana iya ɗarsa masa farin ciki, ko baƙin ciki da duk wani abu mai kama da hakan.

Za mu dakata a nan sai a maƙala ta gaba insha Allah. Kafin sannan kada ku manta ƙofar gyara, sharhi, tsokaci, ƙarin bayani ko shawara a buɗe take.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue Reading