Skip to content

Abubuwan da ke karya azumi

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu har zuwa rananr sakamako.

A wata makala da ta gabata mun yi bayani akan falalar azumin watan Ramalana inda muka kawo kadan daga cikinsu. A yau za mu duba wasu daga cikin abubuwan da za su iya batawa mutum azumi. Ga su nan kamar haka:

1. Cin abinci ko shan abin sha da gangan

Allah Ya ce: “Kuma ku ci ku sha har farin igiya ya bayyana a gare ku daga bakin igiya daga alfijir, sa’an nan kuma ku cika azumi zuwa dare”. Suratul Bakara, aya ta 187.

Saboda haka, duk wani abin da aka saka a baki ya wuce makogoro zuwa cikin ciki, to yana karya azumi, haka nan duk abinda ya shiga ta hanci ya wuce makogoro har ya isa ciki, to shi ma yana karya azumi.

Amma duk wanda ya ci ko ya sha bisa mantuwa, to azumin sa bai karye ba. Saboda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yace: “Wanda ya manta yana azumi sai ya ci ko ya sha, to ya cika azuminsa, Allah ne Ya ciyar da shi, Ya kuma shayar da shi”. Buhari da Musulim ne suka rawait Hadisin.

Wannan Hadisi yana nuna idan da gangan mutu ya ci ko ya sha, to azuminsa ya karya, sa’banin in a mantuwa ya ci ko ya sha.

2. Duk abinda ya ke daukan ma’anar ci da sha

Abubuwan da suke daukar ma’anar ci da sha suna karya azumu, misali:

  1. Karin jinni da za’a yiwa mara lafiya yana karya azumi, saboda yana madadin ci ko sha ga mai jinya.
  2. Allura da ake yi wa mara lafiya wanda yake madadin abinci ko abin sha, shima yana karya azumi, haka nan ruwa da ake daura wa mara lafiya.

3. Yin Jima’i

Wannan shine mafi girma cikin abubuwan da suke karya azumi, kuma laifinsa ya fi ko wanne girma. A duk lokacin da mai azumi yayi jima’i, to azuminsa ya karye, azumin farilla ne, ko na nafiya.

Idan jima’in ya auku ne a watan Ramadan da rana ga mai azumi, to dole ya tuba ga Allah Madaukakin sarki akan wannan zunubi mai girma, kuma ya kame bakinsa na wannan ranar da yayi jima’i, tare da biyan azumin wannan ranar, da kuma kaffara mai tsanani akan shi. Kaffarar itace: ‘Yanta baiwa mumina. In kuma bai samu ba, to zai yi azumin kwana sittin a jere. In kuma bai samu wannan ba, to zai ciyar da miskinai sittin.

Dalili a kan wajabcin kaffara shine Hadisin Abu Haraira (Allah Ya yarda da shi), yace: ‘Wata rana mun kasance muna zaune wajen Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) sai wani mutum ya zo masa, yace na halaka! Sai (Annabi) ya ce masa: “Me ya same ka?” Sai (mutumin) ya ce: Na sadu da matata alhalin ina azumi. Sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Shin zaka samu baiwa ka ‘yanta ta?”. Sai ya ce: A a. Sai ya ce: “Shin zaka iya yin azumi watanni biyu a jere?” Sai ya ce: A a. Sai ya ce: “Shin kana da damar ciyar da miskinai sittin?” Sai ya ce” A a. Sai Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya zauna, muna nan cikin wannan hali, sai aka zo wa Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da wani masaki mai dabino a cikinsa. Sai ya ce: “Ina mai wancan tambayar?” Sai ya ce: Ni ne. Sai ya ce: “Karbi wannan, ka yi sadaka da shi”. Sai Mutumin ya ce: Ya Manzon Allah! Shin akwai wanda ya fini talauci? Na rantse da Allah tsakanin duwatsun Madina guda biyu babu wasu iyalai da suka fi iyalaina talauci. Sai Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi dariya har sai da fikokinsa suka bayyana. Sa’an nan ya ce: “Ka je ka ciyar da shi ga iyalanka”. Buhari da Muslim ne suka rawaito shi.

4. Yin abinda zai fitar da maniyyi

Fitar maniyyi ta hanyar rungumar mace ko shafa jikinta, ko sumbatar ta, ko ta hanyar wasa da al’aura, ko ta hanyar kallon mata, duk wannan baya halatta ga mai azumi, saboda suna cikin abubuwan da ya wajaba ga mai azumi ya nisance su. Ya zo a Hadisil kudusi, Manzon Allah ya ce: ‘Allah Madaukakin Sarki Ya ce: “Yana barin abincinsa da abin shansa da sha’awarsa  don ni”’. Buhari da Muslim ne suka rawaito Hadisin.

Duk wanda ya aikata wadannan abubuwa da aka ambata har maniyyi ya zuba masa, to azuminsa ya karye, dole ya tuba ga Allah Madaukakin Sarki, kuma ya kame daga ci da sha a wannan ranar, kuma zai biya azumin wannan ranar, amma babu kaffara akan sa.

Amma duk wanda maniyya ya fito masa ba da son shi ba, kamar ta hanyar mafarki, ko ta hanyar duka da aka masa ko ta wata hanyar ta daban da ba ta hanyar sha’awa ba, to azuminsa bai karye ba.

Idan kuma maziyyi ne ya fitowa mai azumi ta hanyar sumbatar mace ko taba jikinta ko makamancin haka, to malamai sun yi sabani kan karyewar azuminsa. Amma Magana mafi rinjaye itace azuminsa bai karye ba, sai dai ya kamata mai azumi ya kauracewa abinda zai jawo masa fitar maziyyin.

5. Fitar jini ta hanyar yin kaho

An karbo daga Sauban, Allah ya yarda da shi, yace: ‘Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yace: “Wanda ya yi kaho azuminsa ya karye, da kuma wanda aka masa kahon”. Imam Ahamd da Abu Dawud da Tirmizi da Ibn Majah ne saka rawaito shi.

Wannan shine abinda Imam Ahmad da wasu malaman fikihu masu yawa suka tafi a kai. Haka kuma an nakalto maganar daga wasu Sahabbai da Tabi’ai kamar Aliyu Bin Abi Dalib da Abu Huraira da Nana Aisha (Allah Ya yarda da su) da Al-Hassanul Basari da Ibn Sirin da Ada’u da sauransu. Kuma shine zabin Sheikhul Islam Ibn Taimiyya da almajirinsa Ibnul Kayyim da Ibn Baz da Ibn Usaimin.

6. Kwakulo amai dagangan

An karbo daga Abu Hurarira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: ‘Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Wanda amai ya rinjiye shi, to babu ramako akansa, wanda kuma ya janyo amai da ganganci, to ya rama”. Imam Ahmad da Tirmizi da Ibn Majah ne suka rawaito shi.

7. Fitowar jinin haila ko jinin biki

Idan mace ta yi azumi, sai jinin haila ko kuwa jinin biki, wato jinin haihuwa, ya zo mata, to azumin ta ya karye, sai ta ci ta sha. Amma zata rama wannan azumin. An karbo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah Ya yarda da shi), yace: ‘Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yace: “Shin mace ba ta kasance idan tana haila, bata yin sallah, kuma bata azumi ba? To wannan yana daga cikin tawayar addininta”. Buhari ne ya rawaito shi.

Wannan Hadisi ya ambaci jinin haila kadai, amma ana hadawa da jinin haihuwa, saboda hukuncinsu daya ne wajen hana sallah da azumi.

8. Ridda

Yana daga cikin abubuwan dake bata a zumi yin ridda. Idan mai azumi ya yi ridda (wa iyazu billah) to azuminsa ya warware, saboda musulunci na cikin sharudan karban azumi.

Duk wadannan abubuwan masu karya azumi suna karya shi ne idan an samu sharuda guda uku, amma banda fitowar jinin haila da na biki:

  1. Ya zama mai azumi ya san abubuwan suna karya azumi
  2. Ya zama ya aikata su da gangan, ba bisa mantuwa
  3. Ya zama da zabinsa ya aikata, ba tilasta masa aka yi ba.

Wadannan sune abubuwan da suke karya azumi, kuma wajibi ne duk mai azumi ya nisanci aikata su ko kuwa ya kiyaye aukuwansu gareshi. Da fatan Allah Ya karba mana ibadunmu baki daya.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading