Skip to content

Alamomin so

Alamomin so da maza ke nuna wa mata na kama da juna kawarai. Haka kuma so din wani irin yanayi ne da kan sa mutum ya tsinci kansa a cikin wani hali na daban. Sai dai mi? Abu ne shi mai dadi a kuma gefe guda abu ne mai matukar ban tsoro. Duk da kasancewar sa hakan bai zama abin kyama ga mutane ba. Da yawa kan rungume shi da hannun biyu.

A gefe guda a na samun mata na fadawa cikin tasku saboda makauniyar soyayya wadda daga baya ta kan zamo dana sani. Saboda sun kasa gane da gaske ne ana son su ko kuwa yaudara ce.

“Ina son ki” abu ne mai saukin fadi a baki, sannan kalmomi ne da mutane kan fada a mabambanta lokutta.

Wasu fadin hakan da gaske ne har cikin zuciyarsu wanda wasu kuwa ba haka zancen yake ba, su kan fadi hakan da wata manufa tasu boyayya.

Wasu kuwa komi za a yi ba zasu iya fadar kalmar “Ina son ki” ba, koda kuwa suna son mutum su kan kasa fadar hakan. Jin wadannan kalmomi ba wani sabon abu bane, kuma ba wai alama bace da ke nuna namiji na son mace, alal hakika fadin kalmar ita kadai bata isa shaida na cewa namiji na son ki ba. Don kuwa kowa na iya fadar ta a gaske ko kuma ta sigar yaudara.

 Kalmomi ne, ki bar su a kalmomi. Akwai abubuwa mafi muhimmanci da suka fi kyau mace ta lura da su a tarayyar ta da namiji. Ya su mazan suke, mi suke yi, wadanne irin halaye ne suke nunawa idan suna son mace da gaske?

 Zan kawo wasu daga cikin wadannan alamomi da zasu tabbatar ma da mace cewa namiji na sonta da gaske.

Sai dai bai zama lallai a samu dukkan wadannan alamomi ga mutum guda ba, sai dai mi? A kalla akwai wasu daga ciki dake nuna hakan kasancewar ba lallai ne namiji ya mallaki dukkan ababen da mace ke bukata ba.

1. Namijin da ke girmama ki

Girmamawa wata nau’in dabi’a ce da kowane mutum ke so walau babba ko yaro. Komin kankantar mutum yana bukatar wannan girmamawar. A tarayya ta soyayya wani namijin son ne kawai a baki bai san ta yaya zai girmama masoyiyar sa ba, kuma girmamawa anan ba wai tana nufin ka zama ba ka da abin cewa sai abinda mutum yace ka yi. A’a girmamawa a nan ana nufin masoyi ya zama mutum mai girmama duk wani abu da ya shafe ki.

Ya zama mutum mai girmama ra’ayinki, sannan ba zai takura mi ki ba akan na shi ra’ayin matukar ya san kema a kan gaskiya ki ke. Maimakon ya canza mi ki naki ra’ayin zai tsayu tsayin daka wajen ganin ya taya ki cimma nasara a matakan rayuwar ki. 

Duk namijin da zai tsayu wajen ganin haka, ya zamo mai girmama ra’ayoyin ki tare da dora ki a kan ingantacciyar hanya sai mu ce kin yi dace. Domin hakan ba karamar rawa zai taka ba a rayuwar ki, sannan ba ki da shakkun cewa zai hantare ki ko ya muzguna mi ki.

2. Namijin da ki ka mika ma dukkan yardar ki

Yarda abu ne mai matukar wahala musamman a wannan zamanin da mu ke ciki. Abu ne da dole sai an gina shi, kuma baya faruwa a lokaci daya.

Ba kowane irin mutum bane abun yarda. Duk girma, kyau, asali, mulki da ilimin mutum kuwa ba za ki taba yarda da shi a lokaci daya ba. 

Ba za ki hadu da namiji yau ba ki ce kin yarda da shi.

Samun yarda a tsakanin masoya abu ne mai matukar muhimmanci da kuma wuyar ginawa. Ba tare da yarda ba tarayyarku a kowane lokaci ka iya rugujewa.

Sannan ita yarda ba tana nufin namiji ba zai ci amanar ki ba ko ba zai mi ki karya ba. Abin nufi a nan shine kina da kwarin gwuiwa a kan shi cewa a duk lokacin da kika bukaci taimakonsa zai kasance a tare da ke. Sannan ki kan samu natsuwa a tare da shi wajem bayyana mi shi sirrikan rayuwar ki da fargabar ki ba tare da kin ji wani darr na cewa zai iya mi ki gori a lokacin da fada ya hada ku ba, ko fadawa wani sirrinki ba.

Duk wani abu da ya shafe ki rufaffe ne a wajensa. Ya kan saurare ki ba tare ya gaji da matsalolinki ba. A kowane lokaci yana tare da ke.

3. Namijin da ke son abubuwa da dama dangane da ke

Kowane mutum nada na shi nakasun a rayuwa, yana da inda ya gaza. Wanda ba lallai bane ba mu gane hakan a wasu lokuttan. Wasu nakasun namu ma bamu san da su ba. Amma shi wanda yake son ki ya san da su kuma a hakan yake son na ki. A kullum ya kan kara ganin wasu ababen da suka hadu suka bada ke, sai su kara zama dalilai na kara sonki.

Sai ya zamo ya sanki ma fiye da yanda kika san kanki. Saboda ya ga raunin ki, ya ga karfin ki da iyawarki. Amma hakan ba zai sa yayi amfani da raunin ki ko wani aibu na ki wajen kaskantar da ke ba.

Sai dai ya rungumi duk abinda kika zo da shi da hannu biyu cike da so da kauna ba tare da kyama ba saboda ke din dai yake so ba waninki ba.

4. Namiji dake nuna yana sonki

Fadin kana son mutum ba kamar aikatawa bane ba. Akwai mazan da bayyana irin soyayyar da suke ma mace a baki abu ne mai wahala a wajensu. Amma su kan bi duk wata hanya wajen ganin sun nuna hakan a aikace wanda a zahiri mafi yawan maza sun fi bayyana soyayyar su a aikace. 

A kowane irin hali ko yanayi yana tare da ke, yana ba ki duk wata kulawa da kauna. Duk abinda ya san zai faranta mi ki shi yake yi, a kowane lokaci yana baki muhimmanci sosai.

Ya kan kula da duk irin yanayi da kike ciki ta yanda ko murmushi kika yi ya san ma’anar shi. Yanayin canzawar fuskar ki yana lura da ita.

5. Namijin da ba shi da burin da ya wuce ki zama matarshi ba

A kowane lokaci maganar shi ba ta wuce ta yanda rayuwar aurenku za ta kasance, yana ganin ki a matsayin uwar da za ta tarbiyyantar da yayansa.

Yana mi ki tanadin wata ingantacciyar rayuwa mai cike da buririkka da alkawura.

6. Namijin da ya dauke ki da muhimmanci

Matukar namiji na sonki da gaske, duk yanayin aikinsa sai yayi kokarin sama mi ki lokaci saboda kina da muhimmanci a wajen sa, kuma duk yanda ya kai da kololuwar zama mara lokaci saboda ke din mai muhimmanci ce. A dabi’a ta dan adam komin rashin lokacinsa sai ya sama ma abubuwa mafi muhimmanci a rayuwarsa lokaci. A duk lokacin da rashin samun lokaci da shi ya faru saboda wani babban dalili sai ya tabbatar da cewa hakan ba zai dame ki ba, zai yi iya bakin kokarin shi wajen ganin ya faranta ma ki.

7. Namijin da komin rintsi yana tare dake

Kasancewa tare da namijin da abu kadan zai faru ya ji cewa ba zai iya cigaba da soyayya da ke ba, a lokaci guda ki ga ya na neman hanyar tserewa irin wannan ba mijin sure bane.

Amma duk namijin da a lokacin da wata matsala ta faru a lokacin ne zai ji cewa ba zai iya rabuwa da ke ba, to shine mijin aure. Duk rintsi duk wuya yana tare da ke. Zai kasance a duk lokacin da kika bukatar taimako shi mai mai tallafa mi ki ne.

8. Namijin da ya dauke ki abokiyar rayuwa

Duk da wasu matan na ganin maza na da girman kai ta wani fanni, akan samu namijin da zai dauka ke da shi duk daya ne. Ra’ayin ki da na shi duk daya ne matukar akan turbar gaskiya ne. Hakan ba yana nufin ba zaku samu sabani ba, sai dai sabanin zai zo ne bisa fuskar fahimta saboda ku din mutane guda biyu da suka dauki kawunansu duk daya. Sannan babu wanda zai kalli wani ta fuskar kaskanci.

Sannan ya zamo ba ki da shamaki wajen musayar ra’ayi da shi bisa ga fahimtar juna. Ku kan zauna ku fahimci juna wajen warware matsalolinku.

Matukar kika samu namiji mai yin hakan tabbaci hakika yana matukar ganin muhimmancin ki a matsayin ki ta abokiyar rayuwar shi. Sannan a duk wani abu da ya shafi rayuwar ki ya kan danganta shi a matsayin abu da ya shafe ku ba ki daya ba wai ke kadai ba. Saboda yana ganin ke da shi kun zama daya.

Kadan kenan daga cikin alamomin da mace za ta game cewa namiji da gaske take. Ina fatan wannan makala za ta ba ku haske akan irin mazajen da ku ke tare da su, shin suna dauke da irin wadannan alamomi? Duk da kasancewar kowace irin soyayya na da irin nata kalar kalubalen, sannan bai zama dole sai namiji ya zamo yana dauke da dukkan wadannan alamomi ba. Matukar an samu kaso hamsin sauran a hankali da kuma hakuri da juna za su biyo baya. 

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×