Albasa tana daga cikin kayan lambu da ake amfani da su sosai a girke-girke a sassan duniya. Tana da matukar amfani ga jiki saboda tana ɗauke da sinadarai masu gina jiki, magungunan cututtuka, da kuma kare lafiyar jiki gabaɗaya.
Kamar sauran kayan lambu da yawa, albasa na zuwa da siffofi da girma da launuka daban-daban tare da ɗanɗanon na musamman don amfani daban-daban. Laununkan albasa da ake gani a kasuwannin yau da kullum a yayin saye su ne; fara da ja da launin rawaya. Waɗannan su ne ire-iren albasa da aka saba gani a kasuwannin gida Najeriya.
Amfanin sinadiran albasa
Albasa mulmulalliya ce, kayan lambu ce wadda ake shukawa kuma take girma a ƙarƙashin ƙasa bayar ganyen da take saki da ake kira lawashi. A cikin tsarin abinci mai gina jiki, albasa na da wadataccen sinadarin ruwa da carbohydrates, da fiber, tare da furotin da bitamin har ma da maiƙo ko kitse. Tana da muhimmanci ga lafiyar jiki wajen:
Inganta garkuwar jiki
Yawan sinadarin bitamin C da wasu sinadaran kamar quercetin suna sa albasa ta zama mai taimakawa wajen gina garkuwar jiki. Dukkan sinadaran guda biyu suna hana lalacewar tantanin halitta kuma tana ƙara inganta sinadarin ƙarfe, wanda ke taimakawa jiki yaƙar gajiya, juwa, ciwon kai, da matsalar sanyi.
Daƙile cututtuka masu tsanani
Mahimman sinadaran gina jiki a cikin albasa suna rage haɗarin kamuwa da cututtuka na yau da kullun kamar nau’in ciwon sukari nau’i na 2, ciwon daji, da cututtukan da ke da alaƙa da zuciya. Sinadarin quercetin-flavonoid antioxidant a cikin albasa, yana hana kumburi, rage haɗarin hawan jini, da daidaita sukarin jini. Hakazalika, albasa musamman jar albasa, ta ƙunshi sinadarin anthocyanins da yawa, wanda ke yaƙar nau’in ciwon sukari na 2, kuma yana rage haɗarin cututtukan zuciya. Albasa tana ba da kariya daga cututtukan daji masu alaƙa da ciki, hanji, da mahaifa. Sinadarin flavonoids da sauran sinadarai na organo-sulfur suna da daƙile cutar daji. Wannan ya bayyana dalilin da ya sa mutanen da ke cin albasa da yawa ba sa fuskantar barazanar kamuwa da cutar kansar hanji kusan kashi 79% fiye da waɗanda ba sa ci.
Inganta lafiyar hanji
Tsarin ciki ko hanji yana aikin cin abinci da narkewa, zuƙar sinadaran gina jiki, da fitar gurɓatattun abubuwa daga jiki. Lafiyar hanji ta dogara da ƙananan ƙwayoyin bakteriya da fungi a cikin hanjin. Albasa ita ce tushen samuwar sinadarin fiber da prebiotics, masu gina jiki guda biyu waɗanda ke samar da abinci ga ƙwayoyin halitta na cikin don kyakkyawar narkewar abinci da kuma inganta garkuwar jiki.
Nau’ikan albasa a Najeriya
Tsawon lokacin da albasa ke ɗauka a shuke kafin cire yana da tasiri ga ɗanɗano da amfaninta a kayan abinci. Za a iya yin amfani da albasa bayan ƙwallon ya girma sosai, ta kai munzalin balaga, haka nan za a iya amfani da ita ko da ba ta girma ba. Albasar da ba ta nuna ba, wato ba ta girma ba sosai, yawanci tana da ƙarancin ɗanɗano idan aka kwatanta da manya.
1. Jar albasa
Jar albasa za a iya cewa ita ce mafi yawan nau’in albasa a Najeriya. Tana da ƙwari da zafi da ɗanɗano mai yaji, wani lokacin tare da zaƙi. Ɗanɗanon albasar yana raguwa idan an dafa ta.
2. Farar albasa
Ba kamar masu launin ja da rawaya ba, farar albasa na ɗauke da ƙarancin sinadarin sulfur da kuma adadi mai yawa na sukari, wanda hakan yana sa ta yi zaƙin da za q iya cin ta a ɗanya. Wannan dalili ne ya sa ba ta zugi a idanu idan ana yanka ta, saɓanin jar albasa.
3. Albasa launin rawaya ko ruwan ƙasa
Launinta yana bambanta daga rawaya mai haske zuwa launin ruwan zinari. Albasa mai launin rawaya tana da ɗanɗano mai kaifi da matsakaicin zaƙi wanda ke ƙaruwa idan an dafa ta.
Sinadarin ɗanɗanonta na da yaji kuma yana da yawa; don haka, a guji cin ta ɗanya. Madadin haka, a yi amfani da ita wajen suya ko a miya.
4. Koriyar albasa
Albasa da albasar bazara da scallions, nau’in albasa ne da ba su girma ba suna da lawashi da kuma ƙwallon albasar. Ana amfani da albasar nan uku marasa girma a wasu yankuna, a wani bangare saboda yanayin ɗanɗano da kamanninsu iri ɗaya ne. Ba kamar wacce ta girma ba, wannan nau’i tana da ɗanɗano kamar tafarnuwa.
Bambanci tsakanin albasar bazara, koriyar albasa, da scallions.
Albasarar bazara ita ce mafi girma kuma tana da ɗanɗano mafi ƙarfi a cikin ƙananun nau’ikan albasa uku. Duk da cewa wannan nau’i ba ta girma sosai, amma tana da ɗanɗano fiye da manyan albasa.
Tsawon lokacin da albasa take ɗauka a shuke a ƙasa, yana ba da dama ga ƙwallon albasar ya girma sosai. Ita kuwa albasa nau’in scallion tana da ƙarancin lokacin daɗewa a ƙarƙashin ƙasa. A sakamakon haka, tana da fararen jijiyoyi a maimakon ƙwallo. Wannan nau’i na albasa ba ta da girma idan aka kwatanta da koriyar albasa. Sabanin haka, koriyar albasa tana da matsakaicin fari da ƙwallo, yayin da albasar bazara take da babban ƙwallo zagayayye.
Hanyoyin adana albasa
Albasa kayan gwari ne mai saurin lalacewa idan ba a kula da ita ba, saboda haka ga jerin hanyoyi da shawarwarin da ya kamata a bi don adana albasa:
- A ajiye ta a waje mai sanyi da duhu, waje mai kyau da hasken rana bai isa kai tsaye ba ko kuma zafi ba.
- A zuba ta a cikin buhu ko garara mai ƙofofin shigar iska ko kwandon da ke ba da damar shigar iska don hana taruwar danshi.
- A ware ta da sauran nau’ikan kayan lambu, kamar dankali. Albasa, musamman jar albasa, tana fitar da sinadarin ethylene – ƙwayar tsiro ce da ke saurin fitowa.
- A ajiye yankakkiyar albasa a cikin abin da iska ba za ta riƙa shiga ba ko a saka su a cikin firiji.
- Albasar da ba ta da girma tana da ɗan gajeren lokaci fiye da manya albasa.
- Don ajiya na ɗan lokaci, cire duk wani tarkace daga albasa.
- A yanke lawashin kafin idan za a jiye na dogon lokaci.
- Cire duk wani ruwa mai yawa daga jikinta ta hanyar shanya ta na ɗan lokaci.
Matsalolin albasa
Duk da cewa binckie ya tabbatar da albasa tana da matukar amfani ga lafiyar jiki ta fannoni da dama, a hannu guda kuma akwai wasu illoli da za ta iya haifarwa idan aka yi amfani da ita ba daidai ba ko kuma idan jiki bai dace da ita ba, ko kuma ta zarta ƙima. Ga wasu jerin matsaloli da illolin albasa ga jiki:
Warin baki
Ɗanyar albasa tana iya haifar da warin baki. Hakan dai yana faruwa ne sakamakon sinadaran sulfur da ke cikinta wanda ke samar da wari marar daɗi.
Hargitsa ciki
Albasa na iya haifar da ciwon ciki ga wasu mutane da kumburin ciki bayan sun ci albasa. Wannan na faruwa ne sakamakon rashin daidaiton wasu sinadarai da ke cikin albasar.
Jin zafi a ido ko yoyon hanci
Wasu mutane na iya samun matsala da albasa ko tiririnta wanda zai iya haifar da alamomi kamar zubar hawaye ko zubar majina daga hanci ko kuma kumburi a fuska da makogwaro.
Haifar da yin amai
Cin albasa da yawa na iya haifar da yawan amai ko ciwon ciki ga wasu mutane, musamman idan ba sa sha’awar albasar.
Raguwar jini
Albasa na ɗauke da wasu sinadaran da ke iya rage yawan jini, wanda zai iya haifar da matsala ga waɗanda ke amfani da magungunan karin jini ko kuma masu fama da matsalolin jini.
Mafita ga Illolin albasa
- A rage yawan albasa da ake ci sannan a tabbatar da cewa an dafa ta sosai.
- Idan ka ga alamun rashin jituwa da albasa, yana da kyau ka daina amfani da ita sannan ka tuntuɓi likita.
- A rage yawan albasa da ake ci ko kuma a dafa ta sosai kafin amfani da ita.
- A yawaita shan ruwa da kuma tsabtace baki da hakora bayan cin albasa.
- A tuntubi likita kafin yawaita amfani da albasa, musamman ga wadanda ke amfani da magungunan rage jini.
Manazarta
Kadiri, T. “. (2024, March 31). Onion colors: 4 Types of onions in Nigeria and how to cook with them. Pricepally Blog.
Rdn, A. B. M. (2023, February 13). Onions 101: Nutrition Facts and health Effects. Healthline.
Nutritionist, J. W. –. R. (2024, December 7). Top 10 health benefits of onions. Good Food.