Skip to content

Amfanin ayaba

Share |

Amfanin ayaba na da matukar yawa ga jikin bil’adama kula da abubuwan da ke dauke a cikinta. Masana sun bayyana ayaba a matsayin ‘ya’yan itace mai taimaka wa jikin bil’adama ta hanyoyi daban-daban, kana ita ayaba ta na magungunan cututtuka daban-daban wa bil’adama. Wasu daga cikin alfanun ayaba ga rayuwar bil’adama su ne:

  • Ayaba na taimaka wa bil’adama ta hanyar samar mi shi da Jini mai inganci a jika.
  • Ayaba na taimaka wa masu dauke da cutar genbon-ciki ko ulcer, kuma ta kan yi riga-kafin cutar saboda da ta na taimaka wa tunbin bil’adama ta hana Acid dake shanye abincin cikin bil’adama shanye abincin kwata-kwata.
  • Ayaba na taimaka wa masu dauke da cutar hawan jini kamar yadda masana suka tabbatar.
  • Ayaba na kuma taimaka wa hanjin bil’adama ta hanyar saukaka yanayin gudun abinci a cikin ta.
  • Ayaba har ila yau an bayyana ta da idan mutun zai ke cin ta akalla sau uku a rana, wato wajen kari, da wajen kalacen rana ko na maraice to potassium din dake cikinta (ayaba) yakan karfafa kwakwalwa, musamman ga daliban ilimi.
  • Har ila yau an bayyana bawon ayaba da yana taimaka wa fatan bil’adama (skin) musamman wadanda sauro ya cije su kuma fatarsu ta tauye. Masana sun tabbatar da in aka goga bawon Ayaba a inda fatar ta tauye hakan na hana fatar kumburi da kuma nuna alaman cizon sauron.

Ayaba dai na dauke da sinadaran da jikin bil’adama ke bukatansu da dama na vitamins.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading