Skip to content

Amfanin zuma goma sha biyu ga jikin bil’adama

Share |
Amfanin zuma goma sha biyu ga jikin bil'adama

Amfanin zuma yana da yawa bisa fadin masana. Shi dai zuma wani ruwa ne mai zaki, wanda masana a fannin kiwon lafiya suka tantance kuma suka tabbatar da zakinsa bai da wata illa ga jiki ko rayuwar bil’adama. Hasalima dai zuma na samar da kariya ga bil’adama a kan wasu cututtuka daban-daban. Cikin wasu alfanun zuma ga jikin bil’adama, mun yi kokarin zakulo muku wasu kadan daga ciki wadanda suka hada da:

1. Masana sun tabbatar da cewa Zuma na rage barazanar cutar sugar ko diabetes ga jikin bil’adama.

2. Masana sun kuma tabbatar da cewa Zuma na rage radadin cutar mura (respiratory infection or cough).

3. Masana har ila yau sun tabbatar da cewa Zuma na rage barazanar cutar gyambon ciki (Ulcer).

4. Masana sun kuma tabbatar da cewa Zuma na taimaka wa bil’adama wajen buda masa huhu yadda zai yi numfashi ba tare da wahala ba.

5. Masana sun kuma tabbatar da cewa Zuma na rage radadin cutar asma wanda in aka yi dace yakan kawar da cutar gabadaya.

6. Masana sun tabbatar da cewa Zuma na kawar da cutar daji (stroke).

7. Masana sun kuma tabbatar da Zuma na taimaka wa jikin bil’adama wajen narkar da abinci (improve digestion).

8. Masana sun kuma tabbatar da cewa Zuma na kara karfin kashi (active borne).

9. Masana sun kuma tabbatar da cewa Zuma na warkar da rauni ko kunar wuta a jikin bil’adama.

10. Masana sun kuma tabbatar da cewa Zuma na samar da sinadarin glucose ga jikin bil’adama wanda hakan na kara wa garkuwar jikin kuzari (boost immune system).

11. Masana sun kuma tabbatar da cewa Zuma na gyara fatar jikin bil’adama (skin beauty).

12. Masana sun kuma tabbatar da cewa Zuma na dauke da sinadarin amino acids wanda yana rage yawan nauyin jiki ko kiba.

Add to Library

No account yet? Register

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page