Skip to content

Aminu Ado Bayero

An haif Alhaji Aminu Ado Bayero ne a shekarar 1961, ya yi makarantar firamare a Kofar Kudu da ke Kano Municipal; daga nan ne ya garzaya Birnin Kudu ta jihar Jigawa, inda ya yi karatunsa na sakandare. Sarkin ya shiga jami’ar Bayero da ke Kano, inda ya sami digiri a fannin koyon aikin jarida da kimiyyar siyasa.

Sarkin Kano na 15, tare da tsohon gwamnan Kano, Umar Ganduje

Aminu Ado Bayero ya kuma je makarantar koyon tukin jirgin sama da ke Aukland a California ta kasar Amurka, ya kuma yi hidimar kasa a gidan talabijin NTA da ke garin Makurdi na jihar Binuwai, daga bisani aka ɗauke shi aiki a kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Kabo Air.

Iyalinsa

Aminu Ado Bayero yana da matan aure guda biyu da yara huɗu, kodayake bai jima da auren ta biyun ba. Ta biyun da ya aura mai suna Hauwa’u Adamu Abdullahi Dikko, a karshen shekarar da ta gabata. Matarsa ta farko har yanzu ba a bayyana sunanta ba saboda kamar ba ta da sha’awar shiga cikin jama’a.

Sarauta/Muƙamai

A shekarar 1990 mahaifinsa Alhaji Ado Bayero (marigayi) ya fara ba shi mukamin sarauta, inda aka naɗa shi Ɗan Majen Kano kuma Hakimin Nassarawa. Daga nan ne kuma aka kara masa girma zuwa Ɗan Majen Kano Hakimin Gwale a dai shekarar ta 1990.

A shekrar 1991 kuma likkafa ta kara gaba inda aka naɗa shi Turakin Kano kuma Hakimin Dala a watan Janairun 1991 zuwa Janairun 2001, ma’ana dai ya shekara 10 a wannan mukami. Alhaji Aminu Ado Bayero ya zama Sarkin Dawakin Tsakar Gida, Hakimin Dala daga watan Janairun 2001 mukamin da ya rike har zuwa 2014.

A watan Oktobar 2014 Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya nada shi a matsayin Wamban Kano kuma ɗan majalisar sarki. Ya riƙe muƙamin har zuwa watan Mayun 2019. A watan Disambar 2019 ne kuma Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa shi Sarkin Bichi na farko bayan kirkirar sabbin masarautu.

Sarkin Kano na 15, Aminu Ado da shugaban ƙasa Tinunbu

A watan Oktoban 2022, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba shi lambar yabo ta kasa ta Najeriya mai taken Kwamandan Tarayya (CFR)

Aminu Ado Bayero shi ne Chancellor na jami’ar Calabar  (University of Calabar).

Ayyukansa

Sarkin Kano na 15 tare da Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf

Alhaji Aminu Ado ya fara aiki a kamfanin jiragen sama na Kabo Air, a matsayin jami’in hulda da jama’a daga 1985 zuwa 1990 inda ya riki matsayin darakta a kamafanin.

A bangaren kungiyoyi kuwa, Sarkin Kano Aminu Ado Bayero shi ne shugaban kungiyar masu wasan kwallon kwando ta jihar Kano, kuma shi ne uban kungiyar ‘yan asalin Ilorin.

Manazarta

BBC News Hausa. (2020, March 10). Aminu Ado Bayero: Tarihin Sarkin Kano na 15 a jerin Sarakunan Fulani. BBC News Hausa

Michael Kuduson. (2020, March 12). Tarihin sabon sarkin Kano Aminu Ado Bayero. Radio France International.

Naijahistory. (2024, May 25). Aminu Ado Bayero Biography, Family, Controversies, Dethronement. OldNaijaHistory.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading