Azumin watan Ramadan na daga cikin ayyukan da Allah Ya wajabta wa bayinsa, kuma rukuni ne daga cikin rukunan Musulunci guda biyar, kamar yadda ya tabbata a Hadisin da Abdullahi bin Umar (R.A.) ya rawaito, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “An gina Musulunci akan abubuwa guda biyar; Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, da kuma shaidawa Annabi Muhammad Manzon Allah ne, da tsayar da sallah, da bada zakkah, da aikin hajji, da azumin watan Ramadan”. Buhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Lallai yana daga cikin ni’imomin da Allah Ya yi wa bayinsa yadda ya sanya musu lokuta masu falala da daraja don yin ibadoji masu girma, ta yadda bayinsa ke yawaita ayyukan alheri a wadannan lokutan. Kuma Allah yana kankare zunubai, yana ninninka ladan ayyuka, Ya kuma saukar da rahamominsa. Daga cikin wadannan lokuta akwai watan Ramadan wanda Allah Ya saukar da Al-Kur’ani a cikinsa kamar yadda ya fada: “Watan Ramalãna ne wanda aka saukar da Alƙur’ãni a cikinsa yana shiriya ga mutãne da hujjõji bayyanannu daga shiriya da rarrabawa”. (Suratul Bakara, aya ta: 185)
Watan Ramadan wata ne mai albarka da alkhairai masu yawa, watan azumi ne da nafilfilun dare, watan rahama ne da gafara da kuma yantar da bayi daga wuta, watan kyauta da sauran ayyukan alheri.
Yadda za mu amfana da falalar watan Ramadan
Akwai abubuwa da dama da ya dace Musulmi ya yi don fiskantar watan Ramadan. Ga kadan daga cikinsu:
1. Addu’a
Yawan addu’a Allah Ya kai mu wata mai albarka na Ramadan, saboda haka magabata suka kasance suna yi, suna rokon Allah har tsawon wata shida da ya nufe su da kaiwa watan Ramadan, sa’an nan bayan azumi suna yin addu’a na tsawon wata shida kan Allah Ya karba musu ayyukan da suka yi a watan.
Idan watan Ramadan ya tsaya akwai addu’ar da ake yi kamar yadda ya tabbata a hadisi. Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: “Allahumma ahillahu alaina bil amni, wal iman, was salaamati, wal Islam, Rabbi, wa Rabbukal Laah”. Hakim ne ya rawaito wannan hadisi.
Ma’anar Adduar ita ce: Yaa Allah kasa (wannan wata ya kasance) na samun tsaro, da imani, da zaman lafiya, da Musulunci, Mahaliccina, kuma Mahaliccinka Allah.
2. Godiya ga Allah
Yin godiya ga Allah wanda Ya raya mu, Ya kuma nuna mana watan Ramadan, watan da ake yin rige-rigen ayyukan alheri a cikinsa. Mutum nawa ne yayi azumin bara tare da mu, amma bana Allah bai nuna masa na wannan shekarar ba, Allah Ya dauki ran shi, yana cikin kabari, yana neman addu’ar yan uwansa musulmai, yana burin ina ma da Allah zai dawo da shi duniya ya samu wannan daman ta yin ibada a watan Ramadan? Lallai wannan ni’ima ce babba, dole mu gode wa Allah a kan ta.
Imam An-Nawawi a cikin littafinsa “Al-azkar” ya ce: “Ka sani, an so ga wanda wata ni’ima ta zahiri ta jaddadu agare shi, ko kuma aka tunkude masa wani bala’i ko musiba, yayi sujudar godiya ga Allah Madaukakin Sarki, kuma ya gode masa, kuma yayi yabo gare Shi da abinda ya dace da matsayinsa”
3. Farin ciki da zuwan watan Ramadan
Ya tabbata a Hadisi Manzon Allah S.A.W., ya kasance yana yi wa sahabbansa albishir da zuwan watan Ramadan, yana cewa: “Ramadan ya zo muku, wata mai albarka, wanda Allah Ya wajabta muku azumtar shi, ana bude kofofin sama (Aljannah), ana kulle kofofin wuta, ana kuma daure shaidanu. Akwai wani dare a cikin watan wanda ya fi dare dubu. Duk wanda aka haramtawa alherinsa, to hakika ya haramtu”. Imam Ahmad ne ya rawaito wannan hadisi.
Ya dan uwa mai albarka, yaya ka ke ji idan wani bako mai daraja da kake jiran sa tsawon shekara zai zo maka, ya kake ji idan ya zo maka? To ga Ramadan nan ya zo mana. Wani tanadi ka masa? Shin ka shirya tarban sa ta hanyan aikata kyawawan ayyuka a cikinsa?
4. Biyan bashin azumin baya da yake kan ka
Wajibi ne ga duk wanda ake bin shi bashin azumi, ya gaggauta biya kafin watan Ramadan ya riske shi. Hadisi ya tabbata, Nana Aisha (RA) tana cewa: “Ramakon azumin Ramadan yana kasancewa a kaina, bana samun damar biya sai a cikin watan Sha’aban”.
5. Neman sanin hukunce-hukuncen azumin Ramadan kafin zuwan watan
Wajibi ne ga musulmi ya nemi sanin yadda zai bautawa Allah, ciki har da yadda zai yi azumin Ramadan, saboda baya halatta musulmi ya bauta wa Allah cikin jahilci. Daga cikin hanyoyin neman sani; tambayar Malamai. Allah Ya ce: “Ku tambayi ma’abota ilimi in kun kasance baku sani ba”. (Suratul Anbiya, aya ta 7).
Mai littafin Akh-dhari yace: “Baya halatta (ga musulmi) ya aikata wani aiki har sai ya san hukuncin Allah a cikinsa. Kuma Ya tambayi maluma (don neman sani)…”.
6. Tuba ga Allah Madaukakin Sarki kan ayyukan zunubai da ka aikata a baya
Mutum ya tuba ga Allah, sannan kuma ya yi kekkyawan niyya kan ba zaka koma aikata sabon ba, saboda fiskantar watan gafara da rahama.
Allah ma daukakin Sarki Ya yi kira ga bayinsa da su rika tuba zuwa gare shi kamar yadda ya fada: “…. Kuma ku tũba zuwa ga Allah gabã ɗaya, yã ku mũminai! Tsammãninku, ku sãmi babban rabo”. (Suratul Nur, aya ta 31).
Mai Akh-dhari yace: “Sharudan tuba sune: Nadama kana bin ya cude, da kuma niyya kan ba zai koma zuwa aikata zunubai ba cikin abinda ya saura na rayuwar sa, kuma ya bar aikata sabo nan take in ya kasance ya cudanya da shi”.
8. Yin kyakkyawar shiri don ribatan watan Ramadan
Saboda kwanaki yan kadan ne masu saurin karewa, yana da kyau mutum ya yi kyakkyawar shiri don ribatar lokacin. Idan mutum bai yi haka ba, to yayi asara.
Allah Ya ce: “Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda su gabace ku, tsammãninku, zã ku yi taƙawa. Kwanuka ne ƙidãyayyu“. Suratul Bakara, aya ta 183-184
9. Daura kyakkyawar niyya don azumtar watan Ramadan mai daraja, tare da imani da neman lada
Manzon Allah S.A.W yace: “Duk wanda ya azumci Ramadan yana mai imani da neman lada, to Allah zai kankare masa abinda ya gabata na zunaban shi”. Buhari da Muslim ne suka rawaito shi.
10. Kwadaitarwa kan ciyar da masu azumi
Ya zo a Hadisin Manzon Allah S.A.W. ya ce: “Duk wanda ya ciyar da mai azumi abin buda baki, to yana da lada kwatankwacin ladan mai azumin, ba tare da an rage wa mai azumin ladan sa ba”. Imam Ahmad da Tirmizi da Ibn Majah ne suka rawaito shi.
11. Shiri na musamman game da karanta Al-Kur’ani da fahimtar ma’anoninshi
Mala’ika Jibril A.S. ya kasance ya na haduwa da Manzon Allah S.A.W. sau daya a kowane watan Ramadan don su yi darasin Al-Kur’ani. Ya kuma hadu da shi sau biyu a shekarar da ya rasu.
Wasu daga cikin magabata sun kasance suna karanta Al-Kur’ani gaba dayan sa a cikin kwana uku na watan Ramadan, har a kan samu wasu daga cikinsu suna sauke shi a kowani dare a cikin kwanaki goman karshe na watan.
12. Shiri na musamman don kyautata mu’amala da mutane
Musulmi ya yi shirin kyautata mu’amalarsa da mutane, ya kuma kiyaye harshesa da gabobinsa, da kuma kauracewa abinda Allah Ya haramta
Manzon Allah S.A.W. ya ce: “Duk wanda bai bar karya da kuma aiki da shi ba, to Allah baya bukatar ya bar abincinsa da abin shansa”. Buhari ne ya rawaito wannan hadisi.
Wadannan sune kadan daga cikin abubuwan da Musulmi ya kamata ya yi a lokacin shigowar Ramadan mai albarka. Allah ya bamu ikon azumtar sa da kuma yin sauran ayyukan ibada a cikinsa. Allah kuma ya karba mana ayyukanmu, Ya sa muna cikin wadanda za’a yanta su a cikin watan, amin.