Skip to content

Ba’a

Ba’a wata ɗabi’a ce ta Hausawa da ta ƙunshi yin wasa da wasu rukuni na mutane ta hanyar sa su dariya ko fara’a da zolaya ko tsangwamar su da yi musu ƙage ko muzanta su. Wato wasa ne na faɗa wa mutum wasu kalamai waɗanda akasari ba gaskiya ba amma cikin raha da annashuwa. Ba’a, na ɗaya daga cikin rassan adabin bakan Hausa wacce ke cikin rukunin azancin zance. Ba’a, salo ce ta iya magana da Hausawa kan yi amfani da ita a gurare da dama dan bayar da dariya. tana ɗaya daga cikin salon da wasu daga cikin makaɗan ban-dariya ke amfani da ita wajen bayar da dariya.

Ba’a na daga cikin dabi’un Hausawa da ake nazarin ta a fannin adabi da al’adu.

Abubuwan da ba’a ta ƙunsa

Ba’a aba ce da ke iya zuwa a cikin zance ko mu’amala a tsakanin mutane. Don haka abu ne mawuyaci a ce ga iya abin da ya ƙunsa. To sai dai duk da haka, muna iya ba da misalan wasu ɗaiɗaikun abin da ke wakana a tsakanin mutane waɗanda ake iya kallo a matsayin ba’a.

  • Muzuanta mutum cikin wasa ta hanyar amfani da salon kamance. A irin wannan ba’a, za a kalli mutum a ce wani sashe na jikinsa ko wani aiki da ya yi, ya yi kama da wani abu. Misali:

– DuHbi kanta kamar na mage

– Kalli haƙoranta! Wa ga Kacako? Sunan wani gari.

  • Ba mutane dariya ta hanyar ba da wani labari musamman a lokacin da ake hira. Irin wannan labari zai iya kasancewa gaskiya ne ko kuma shaci-faɗi kawai.
  • Sa mutun yin abin da bai yi niyya ba ta hanyar latsa shi. Misali ka ce mutum tafi wani wuri ana gudanar da wani abu don ya yi kallo. Yana zuwa sai ya tarar ba a komai. Idan ya yi magana sai wanda ya yi ba’ar ya ce latsi, wato ya latsa wanda yake yi da shi.
  • Yi wa mutum alƙawarin da ba na gaskiya ba alhali wanda aka yi wa alƙawarin yana tunanin da gaske ne. Sai lokaci ya yi y ace masa, kai ni fa ba’a nake yi.
  • Tayar da hankalin mutum ko tsorata shi da gangan alhali zolaya ake yi. Idan bayan wani ɗan lokaci idan mutum ya gane ba’a ake yi sai hankalinsa ya kwanta.
  • Nuna kasawar mutum ta hanyar kushe ƙoƙarin da ya yi da gangan amma cikin wasa.

Mutanen da ke yin ba’a

A al’umar Hausawa kowa yana iya yin ba’a. Wato babu babba ba yaro. Ba namiji ba mace. To sai dai akwai bukatar a fahimci cewa, ɗabi’a cewa da ke shiga jinin wasu mutane. Ko’ina suke za a same su suna ba’a. Wasu kuma sukan yi ta ne na taƙaitaccen lokaci kuma da wasu mutane na musamman.

Mutanen da ake yi wa ba’a

Ita ba’a ana iya yi wa kowa. To amma dai kowace ƙwarya da abokiyar ɓurminta. Wato mutum zai yi ba’a ne kawai da wanda suke iya yin wasa da dariya. Sai kuma idan cikin taro ne mutum ya yi ba’a da duk ilahirin mutanen da ke wuri. Misalin abokan yin ba’a a tsanin Hausawa su ne:

  • Tsakanin mata da miji
  • Tsakanin taubasa (ɗan mace da ɗan namiji)
  • Tsakanin Hausawa da wasu ƙabilu da suke wasannin barkwanci, kamar tsakanin Katsinawa da Nufawa ko Kanawa da Zagezagi.
  • Tsakanin abokai ko ƙawaye
  • Tsakani jikoki da kakanni ko dangoginsu
  • Tsakanin abokan wasa na sana’a, kamar mahauta da masunta
  • Tsakanin abokai ko ƙawaye na karatu
  • Tsakani ƙanin miji da matar yaya ko
    mijin yaya da ƙanwar mata
  • Tsakanin mutum da mai sunan kakansa
  • Tsakanin manya da yaran da ba su girma ƙwarai ba. Manya su ke ba’a da yara ta hanyar yi musu wasannin da suka ƙunshi zolaya

Mutanen da ba a yi wa ba’a

Duk da yake an ce kowa na iya yin ba’a a alumar Hausawa, to sai dai ba kowa ne mutun zai iya yin ba’a da shi ba. Akwai wasu rukunai na mutanen da mutum ba zai iya yin ba’a da su ba. Waɗannan mutane kuwa su ne:

  • Iyaye ba a yi musu ba’a musamman idan ’ya’yan sun girma
  • ‘Yan’uwan iyaye su ma ba a musu ba’a
  • Abokan iyaye su ma suna cikin mutanen da ba a yiwa ba’a
  • Malamai magada Annabawa
  • Yayye, idan ƙannai sun girma.
  • Ubangida ko maigidan (misali wanda ya koya wa mutum
    sana’a ko aiki)
  • Suruki da duk mai matsayi irin nasu a dangantaka
  • Sarakuna ko shugabanni ba a yi musu ba’a
  • Alkali musamman a kotu ba a yi masa ba’a

Muhimmancin ba’a

Ba’a tana taka muhimmiyar rawa a al’umar Hausawa. Daga ciki akwai:

  • Samar da raha da annashuwa tsakanin mutane.
  • Ɗinke ɓaraka a tsakanin mutane. Akan yi amfani da ba’a a shashantar da wasu lamurra da suka haddasa saɓani a tsakanin mutane. Galibi masu yin sulhu ko sasantawa idan suka sa dabarar ba’a suna saurin shawo kan lamarin.
  • Ba’a tana ƙara danƙon zumunci a tsakin masu yin ta. A duk lokacin da ake wasa da dariya, sai a ga dankon zumunci yana daɗa samuwa. Misali, ma’auratan da suka saba yin ba’a a tsakanin su, za a ga da wuya a ji su suna faɗa da juna.
  • Ba’a tana zama wata dama da ake samu wajen tarbiyantar da mutane musamman yara. Cikin sigar wasa sai a ja hankalin mutum a kan abin da ake so ya gyara na mu’amala ko zamantakewar rayuwa.
  • Ba’a tana ceto wasu mutane daga shiga cikin tsattsaurar hukunci. Misali, idan yaro ya yi wa ubansa laifi, kuma ya yi alwashin ɗaukar mummunar matakin ladabtarwa, to abokin ba’a na iya shiga cikin lamari ta hanyar wasa da ɗariya da lallashi ya sasanta su kuma uban ya janye matakin da ya ɗauka.

Manazarta

A. I. da Gusau, S. M. (ed) (2010). Al’adu da ɗabi’un Hausawa da Fulani. Kaduna: El–Abbas Printers & Media Concept.

Dr. I. Abdullahi da Pro. A. M. Bunza (2023) Course Guide Hau 114 – Ɗabi’un Hausawa. ISBN: 978-978-058-847-2 National Open University of Nigeria

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×