Bakteriya wasu halittu ne masu ƙwayar halitta guda ɗaya wadanda ba a iya gani da ido kai tsaye saboda tsananin ƙankantarsu, sai da taimakon na’urar ganin ƙananan abubuwa.
Ana samun bakteriya da yawa a ciki da wajen kowace irin halitta, ciki har da mutane. Ana kuma samun su a saman da kuma a cikin abubuwa kamar ruwa, ƙasa, da abinci, wanda hakan kan mayar da su masu muhimmanci a cikin halittun duniya.
Wasu bakteriya na da illa ga ɗan’adam, suna iya haifar da cututtuka da matsalolin lafiya, amma yawancinsu ba su da lahani. Jikin yana buƙatar wasu nau’ikan bakteriya don aiki yadda ya kamata, kamar waɗanda ke rayuwa a cikin a ɓangaren na’urar narkar abinci (digestive system).
Nau’ikan bakteriya
Libretexts. (2023) akwai nau’ikan bakteriya da yawa, waɗanda ake rarrabe su ta fuskar; marasa lahani, masu taimakawa, ko masu lahani, masu cutarwa. A tsarin kimiyyar Microbiology, bakteriya na iya zama halitta mai ƙwayar halitta (cell) guda ɗaya tal, amma kuma suna iya wanzuwa cikin ayari mai yawa, ko wani na bin wani, ko kuma a nau’i bibiyu.
Akwai nau’ikan bakteriya har guda biyar a zahiri ta fuskar siffarsu:
- Rod (bacilli)
- Corkscrew (spirochaetes)
- Comma (vibrios)
- Spiral (spirilla)
- Spherical (cocci)
Ana kuma siffanta bakteriya da aerobic, anaerobic, ko facultative anaerobes. Waɗannan sharuɗɗan suna bayyana ta yadda suke karɓar iskar oxygen.
Bakteriya nau’in aerobic na buƙatar iskar oxygen don rayuwa, amma bakteriya nau’in anaerobic za su mutu ne idan suka kasance a cikin iskar oxygen. Facultative anaerobes suna aiki mai kyau tare da iskar oxygen, sai ba sa bukatar ta don rayuwa.
Kamannin bakteriya
An rarraba bakteriya ta fuskar siffarsu, suna iya rayuwa a ɗaiɗaikunsu ko kuma a cikin gungu. Misali, ana samun staphylococcus aureus bacteria, a cikin gungu masu zagaye suke rayuwa. Clostridium bacteria kamar sanduna ne kuma guda ɗai-ɗai suke.
A wasu lokutan da ba kasafai ba, bakteriya suna da ƙarfi da rikitarwa. Haka nan za su iya rayuwa a cikin matsanancin yanayi. Sannan kuma suna da wata irin garkuwa mai tauri wanda ke ƙarfafa juriyarsu ga ƙwayar halittar bini (white blood cells) a jikin mutum.
Wasu nau’ikan bakteriyar suna da jela, wadda aka sani da flagellum, a harshen kimiyya. Wannan jela tana taimaka musu wajen motsawa daga waje zuwa waje. Wasu kuma suna da wani abu kamar gashi, wanda ke taimaka musu wajen mannewa da junansu ko kuma saman ƙasa.
Bakteriya masu haifar da cutuka
Yawanci dai bakteriya ba su da ba lahani ko illa, amma duk da haka wasu na iya haifar da cututtuka ga jikin ɗan’adam. A cewar Cherney, K. (2022), akwai wasu cututtukan da bakteriya ke haifar da su;
1. Ciwon kunne
Cututtukan kunne da bakteriya ke haifarwa na iya shafar cikin kunne ko wajensa, cutukan sun fi kama yara fiye da manya, kamar yadda Cibiyar Kula da Cututtuka da Daƙile su (CDC) ta bayyana suna iya haifar da:
- Ciwon kunne da fitar ruwa
- Zazzaɓi
- Wahalar ji
- Yara ƙanana na iya nuni su ja kunnen da abin ya shafa.
2. Sinusitis
Sinusitis yanayi ne da ke tasowa a sakamakon wata cutar da ta riga ta kama mutum, wato ba ciwo ba ne mai zaman kansa ba, yawanci yakan zo bayan kamuwa da mura ko ciwon da ke da alaƙa da sanyi. Alamomin sinusitis sun hada da cushewa da zafi a hanci da goshi da kuma fitar da majina mai kauri koriya. Haka nan ana iya jin takura a kumatu kuma ana samun yoyon hanci, zazzaɓi, da tari.
3. Ciwon makogwaro (Strep throat)
Saɓanin mafi yawan lokuta na ciwon makogwaro da bakteriya ke haifar da su, Strep throat cuta ce da bakteriya nau’in Streptococcus group A ke haddasawa. Bayan matsanancin ciwon makogwaro, wannan cuta mai tsanani da saurin yaɗuwa na iya haifar da alamomi da dama, a cewar CDC. Waɗannan alamomi sun haɗa da:
- Zazzaɓi
- Kumburin tonsils
- Matsalar haɗiya da magana
- Jajayen tabo a saman baki
- Tari mai zafi
4. Bakteriya mai haifar da sankarau
Cutar sankarau cuta ce mai tsanani da saurin yaɗuwa wacce za ta iya haifar da cututtuka na dindindin ko barazanar kisa cikin sauri. Alamominta suna faruwa ba zato ba tsammani kuma suna iya haɗawa da zazzaɓi, taurin wuya, da kuma tashin zuciya.
5. Cutar mafitsara (Urinary Tract Infection – UTI)
Idan ana fuskantar yin fitsari da zafi ko yawan fitsari akai-akai, akwai yiyuwar an kamu cutar mafitsara ko ciwon koda wanda ake kira UTI. Waɗannan suna faruwa ne lokacin da bakteriya suka shiga cikin urethra kuma suna shafar sashin mafitsara ne. Sauran alamun UTI na iya haɗawa da zazzabi, fitsarin jini, ko ciwon baya sama-sama. Kwayoyin riga-kafi na iya magance yawancin UTIs.
6. Bacterial vaginosis (BV)
Wannan wani yanayi ne wanda ke faruwa lokacin da aka samu bakteriya masu cutarwa da yawa a cikin farji idan aka kwatanta da yawan bakteriya masu taimaka wa jiki, hakan na da matsala kuma yana haifar da rashin daidaiton bakteriyar da jiki ke buƙata. Wannan na faruwa sakamakon magungunan antibiotics ko douching. BV na iya haifar da:
- Fitar da wani ruwa mai launin ƙasa-ƙasa ko fari
- Jin zafi a lokacin fitsari
- Ƙaiƙayi
- Wari mai karfi
7. Salmonella
Salmonella wani nau’in bakteriya ne da ke iya haifar da kamuwa da kamuwa da cutar ga mutane. Abinci shi ne mafi yawan wuraren da ake samun bakteriya nau’in Salmonella, kuma ana iya yaɗa su ga mutane daga dabbobi masu siffar ƙadangare. Alamomin rashin lafiya daga irin wannan nau’in ƙwayoyin cuta na iya haɗawa da ciwon ciki, gudawa, da zazzaɓi. Ba kamar sauran nau’ikan cututtukan bakteriya ba, cututtukan da ke haifar da Salmonella galibi ba a bi da su da maganin riga-kafi.
8. Cututtukan fata na kwayoyin cuta
Akwai nau’in bakteriya da ke da ko cutarwa ga fatar jiki, wasu daga cikin ire-iren cututtukan fata da bakteriya ke haifarwa sun haɗa da:
• Cellulitis
Cellulitis cuta ce ta bakteriya gama-gari, wacce ke haifar da yin ja da kumburi da dumi a yankin da abin ya shafa. Haka nan tana iya haifar da fatar jiki ta yi kama da ɓawon lemu.
• Folliculitis
Ta haɗa da bayyanar abu mai kama da ƙuraje, folliculitis cutar fata ce da ke samuwa a ƙofofin gashi. Yana iya aukuwa ta hanyar duk wani abu da aka gogawa fatar jiki da zai iya rikita ta, kamar aske gashin ko sa matsatsun tufafi.
• Impetigo
Wannan ciwon fata ta bakteriya wacce ke janyo fata ta rika yin kaushi har ɓangori-ɓangori da raunuka masu launi. Wannan cuta dai kan faru ta dalilin bakteriya nau’in Staphylococcus ko kuma Streptococcus, kuma tana da saurin yaɗuwa.
9. Bakteriya masu yaɗuwa ta hanyar jima’i
Duk da cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ƙididdige bakteriya guda 30, masu yaɗuwa ta hanyar jima’i, ana iya samun cututtukan guda uku (STIs) wanda za a iya warkarwa da maganin riga-kafi. Waɗannan sun haɗa da:
• Chlamydia
Wadda za ta iya haifar da fitar da maniyyi da ba a saba da shi ba, da kuma yin lahani na dindindin ga mata.
• Gonorrhea
Wadda za ta iya haifar da cututtuka a cikin al’aura, makogwaro, da dubura.
• Syphilis
Wadda ke haifar da raƙuman fata da ƙumburi, kuma zai iya haifar da matsalolin lafiya idan ba a kula da su ba.
Alfanun bakteriya
Masu bincike sun yi kiyasin cewa akwai mafi yawan ƙwayoyin cuta a jikin ɗan’adam fiye da yawan ƙwayoyin halitta (cells). Yawancinsu suna da fa’ida, a cewar Professional, C. C. M. (2024) a shafin Cleveland and Clinic:
1. Yawancin bakteriya masu fa’ida a cikin jikin mutum suna cikin na’urar narkar da abinci (digestive system) ko microbiome na hanji. Wadannan bakteriya suna taimakawa wajen ragargaza abinci da kiyaye lafiya.
2. Wasu mutane suna shan probiotics akai-akai ko lokacin shan maganin riga-kafi don tallafawa lafiyar hanji. Waɗannan ƙarin sun ƙunshi nau’ikan bakteriya masu taimakawa, kamar Bifidobacteria da Lactobacillus.
3. Haka nan ana amfani da bakteriya don samar da nau’ikan abinci, yin yoghurt da sauerkraut da kimchi da kombucha.
4. Tsarin muhalli kuma ya dogara ga bakteriya don yin aiki yadda ya kamata. Misali, bakteriya suna karya matattun halittu a cikin muhalli, kamar matattun ganye, sakin carbon dioxide da abubuwan gina jiki cikin tsari. Idan ba tare da sakin carbon dioxide ba, shuke-shuke ba za su iya girma ba.
Illolin bakteriya
Idan aka ci ko aka haɗu da bakteriya masu cutarwa, za su iya haihuwa a cikin jikin kuma su yaɗa cutuka waɗanda za su iya lalata ƙwayoyin halittar tissues daga ƙarshe kuma su janyo rashin lafiya. Bakteriya masu cutarwa suna haifar da cututtuka kamar:
- Ciwon makogwaro
- Cutukan fata
- Kwalara
- Tarin fuka
- Gurɓata abinci
Bakteriya masu bijirewa magani
A kullum bakteriya masu haifar da cututtuka na ƙara bijirewa magani. Saboda haka shan magani a lokacin da bai cancanta ba na iya haifar da haɗari mafi girma. Bakteriya na iya tasowa kuma su zama masu juriya da bijirewa ga magani.
Idan aka samu bakteriya masu bijire wa magani, hakan na iya rage ingancin maganin riga-kafi lokacin da ake buƙatar su. Shan maganin riga-kafi lokacin da ba a buƙatar su na iya ƙara haɗarin ga bijirewar.
Maganin riga-kafi wani lokacin yana taimakawa wajen ceton rai, amma CDC ta kiyasta cewa fiye da kashi 28 na magungunan da ke da alaƙa dalilan shan su ba su da mahimmanci.
Idan ana buƙatar shan maganin riga-kafi, zai iya taimakawa rage haɗarin bakteriya masu bijirewa ta:
- Shanye dukkan magugunan da aka ba wa mutum koda kuwa an warke
- Kada a sha ko yin amfani da magani wani ba koda irin cutar ce
- Kauce wa tsallake lokacin shan magani
Manazarta
Cherney, K. (2022, April 7). Understanding bacteria: what it is and how it affects you. Healthline.
Professional, C. C. M. (2024, May 1). Bacteria. Cleveland Clinic.
Libretexts. (2023b, August 31). 2.1: Sizes, shapes, and arrangements of bacteria. Biology LibreTexts.