Skip to content

Fasahar blockchain

Share |

Mutane da dama suna yawan tambaya dangane da ainihin abin da ake nufi da fasahar blockchain da irin ayyukan da ake iya aiwatar da ita. Masana a wannan fanni suna ta kokarin yin bayani daidai gwargwado, sai dai sarƙaƙiyar da ke cikin ta ya sa da wuya a samu cikakken bayani gama gari dangane da ita. Kusan kowa da irin yadda yake kallon ta da kuma irin abin da yake tsammani ana aiwatarwa da ita.

Mafi yawa sun fi karkata a cewar fasahar Blockchain ita ce ƙashin bayan cinikin kuɗaɗen intanet da ake kira Cryptocurrency. Sai dai fa abin ya wuce nan, domin kuwa ana iya amfani da fasahar a kusan duk wani abu da ya shafi musayar bayanai da sarrafawa da kuma adanawa. An hakikance cewar duk abin da ya shiga cikin rumbun bayanan wannan fasahar, to fa zai zama jidalin gaske kafin a iya sauya wani abu daga ciki. Watau ba kamar sauran rumbunan ajiyar bayanai ba da ake iya canja wani abu da hanzari ba.

A yanzu haka bangarorin lafiya da na ilmi da kimiyya da cinikayya da kuma ayyukan gwamnati na soma karkata zuwa amfani da wannan fasaha ta blockchain. Abin tambaya shin me ake nufi da fasahar blockchain, daga ina ta samo asali?

Ma’anar fasahar blockchain

Kalmomin Ingilishi biyu aka haɗe waje guda. ‘Block’ na nufin ‘Tubali,’ Chain kuma na nufin ‘Sarka’. Idan an haɗe kalmomin, ana iya ambatonsu da ‘Sarƙaƙƙen Tubali’. A bisa ma’ana kuwa, Blockchain gungun wasu masarrafai ne da manhajoji da suke musayar bayanai tsakaninsu a nan take. Idan aka sanya bayanai a cikin na’ura guda, nan da nan kafin ƙiftawa da bismilla bayanin zai karaɗe ilahirin na’urori da rumbunan bayanai ta yadda babu yadda za a iya canja bayanin cikin hanzari.

Kowanne tubali  yana da adadin yawan bayanan da yake dauka. A bisa doron yadda aka tsara Bitcoin, karamin tubali baya wuce nauyin megabayit guda. A cikin kowanne megabayit ana samun bayanai kimanin dubu huɗu. Hakanan duk bayan minti goma ake samar da sabon tubali wanda zai ɗauki wasu bayanan da za a cigaba da rarrabawa da adanawa. A farkon shekara ta 2014, an ƙiyasta cewar akwai tubalan bayanan da suka kai adadin gigabayit 20. 

Hakanan a ranar 20 ga watan Mayu, 2021 shafin Statistia ya bayyana cewar Bitcoin kaɗai yana ɗauke da bayanan da ya kai nauyin gigabayit 338 (Megabayit 1024 ne ke zama gigabayit daya. Adadin bayanan na iya zama 4000 sau 1024 sau 338!). Sannan kullum bayanan ƙara hauhawa suke yi gwargwadon yawan amfani da aka yi da fasahar.

Siffofin blockchain

A bisa nazarin yadda ake gudanar da fasahar blockchain, za mu ga cewar duk da cewar ainihin ababen da suka samar da ita dama can a akwai su, ta sha bamban da sauran hanyoyin ko rumbunan adana bayanan da ake da su. Wasu daga siffofin fasahar da suka fidda ta zakka sun hada da:

1. Immutability – Rashin canjawa

Hanya ce ta sarrafawa da adana bayanai ta yadda babu mai iya gogewa ko canjawa da zarar an shigar da su. Duk abin da ya riga ya shiga ciki, to fa zuwan sojan badakkare ne, babu ranar fita. Sai dai kafin a shigar da bayani cikin fasahar sai an bi wasu matakai na tantancewa da tabbatarwa, idan abin ya zama daidai sai wasu na’urori da ake kira nodes su shiga sarrafawa da musaya tsakaninsu. Cikin ƙiftawar ido miliyoyin nodes sun san abin da ake ciki. Sai a tura bayanin zuwa tubali inda za a yi masa matsuguni na dindindin. A tsarin blockchain, babu wani bayanin da ya fi wani. Kowanne matsayin darajarsa guda, ya danganta da abin da mutum yake son bincikowa kurum.

2. Decentralized – Zaman gashin kai

A tsarin fasahar blockchain, babu tartibiyar gwamnati ko wani mahaluki da yake da ikon juya akalar tafiyar da lamuranta. Ɗauki misalin Bitcoin, wanda yake bisa doron fasahar ta Blockchain, babu ƙasa ko gwamnati da take bayar da umarnin sakinsa ko riƙe shi. Don haka nan ya zama mai zaman gashin kansa. Illa iyaka dai, zaman gashin kan yana da nasa mishkilolin da za mu yi maganar su nan gaba.

Haka nan mutane kowa na da ikon ajiye duk wani abu ba tare da an yi masa bin diddiga ba. A halin yanzu, jama’a da dama suna adana muhimman bayanansu na cinikayya da kadarori da yarjejeniya da uwa uba kuma kudin intanet watau cryptocurrency. Suna boyewa ne ta amfani da wasu ɗalamisai da ake kira ‘Private Access Key’. Koda ana iya ganin gilmawar bayanan amma ba za a iya sanin mamallakinsu ba balle asan inda yake har sai an iya amfani da ɗalamisan nan yadda ya kamata.

3. Distirubuted ledger – Littafin gama-gari

Kamar yadda muka bayyana, duk abin da aka ɗora a cikin wannnan fasahar to ya je kenan babu fita, hakanan kowa na da ikon dubawa ya ga abin da ke wakana ba tare da sanin ainihin mamallakin abin ba. Wannan ya zama kenan duk da fasahar tana bada dama ga kowa ya ga irin ayyukan da ke gudana, amma babu damar a iya sanin diddigi har sai idan mamallakin ne da kansa ya bayyana ko kuwa aka iya samun cikakken sirrin ɗalamisan nan da suke zama tamkar ɗan makulli.

4. Fast settlement – Cika aiki

Fasahar Blockchain tana da matukar sauri ta yadda da zarar komai ya daidaita bayanan za su isa inda ake buƙata ba tare da jinkiri ba. Wannan ta sa harkokin ciniki na intanet da ake yi da cryptocurrency suke da matuƙar sauri fiye da tsarin aikin banki na gargajiya da aka sani. A tsarin Blockchain na Bitcoin, mafi yawan lokacin da za a ɗauka kafin bayanai su yi zaman dirshan shi ne minti goma. Duk da haka wasu kuɗaɗen intanet da suka biyo baya suna ta ƙoƙarin rage wannan lokacin. Misali, Etherium na ɗaukar sakan 15 ne kacal wajen sarrafa bayanai, Dogecoin na ɗaukar minti ɗaya, Litecoin kuma yana ɗaukar minti biyu da rabi. Saɓanin bankunan gargajiya da ke iya ɗaukar awanni ko ma kwanaki kafin bayanan su tabbata.

5. Reward – Ladan kamasho

Idan a gwamnatance ne, babban bankin ƙasa yana da ikon bayar da umarnin fitar da sababbin kuɗade da kuma janye su domin inganta tattalin arziki. Amma a tsarin cryptocurrency da ke tafiya bisa doron fasahar blockchain, ana samar da sababbin kuɗaɗe ne ta hanyar zabari watau ‘mining’, ana kuma janye su ta hanyar babbaka su watau ‘burning’. Ta wannan fuska ne masu dawwamar da lokacinsu cikin wannan fasahar suke samun kamasho. Idan misali ina son tura kuɗin intanet ga adireshin wata ma’ajiyar watau ‘wallet’. Zan faɗi abin da zan tura sannan zan faɗi ladan kamashon da zan biya. Wannan ladan shi ake kira ‘transaction fee’. Yawan ladan da na bayar shi zai sa na’urorin ‘nodes’ su rugo domin su isar min da saƙona akan kari. A wannan kokawar sarrafa bayanan da suke yi, suna aiwatar da wani irin sarƙaƙƙen lissafi da ake kira ‘hash algorithm’. Da zarar sun isar da saƙon, sai su raba kamashon tsakaninsu gwagwadon ɗawainiyar da kowa yayi.

A cikin ƙoƙarinsu na sarrafa wancan lissafi na hash algorithm shi ake kira mining, kuma ta nan ne ake samun sabon kuɗin intanet na cryptocurrency. (Za mu samu lokacin cikakken bayani akan zabarin mining da abin da ya kunsa).

Akwai wasu siffofin na Blockchain da suka haɗa da Peer to Peer, Hash to Hash da kuma Trusted Layer. Wasu masanan suna ɗaukar kowanne a matsayin siffa mai zaman kanta,wasu kuma suna cusa su cikin waɗancan biyar da muka ambata.

Tarihi

Bari mu nutsa cikin duniyar tarihi domin ganin inda wannan fasaha ta samo asali. Daga cikin abin da masu nazari suka wassafa shi ne, tun cikin 1991 wasu manazarta, Stuart Haber da Scott Stornetta suka soma tunanin hanyoyin da za a samar da ƙunshin bayanan da za a iya ajiyewa ta hanyar surkulle watau ‘cyrptography’ sannan idan an samar da bayanan ba za a iya canja lokacin da aka ƙirƙire su watau timestamp. A 1992 kuma wani mai suna Dave Bayer ya shiga cikin tafiyar suka samar da dabarar ƙunsa bayanai a curi guda na tubali sannan a rarraba zuwa wasu wuraren.

Wannan aikin da suka yi, sanadiyyar wasu fasahohin kamar Bittorrent, Bitcomet da kima Bitcoin. Shi Bitcoin, wanda wani (ko wasu) da ba a sani ba mai suna Satoshi Nakamato ya samar a shekarar 2009, na bisa doron fasahar Blockchain ne, kuma a cikin takardar da aka fitar ne watau ‘Whitepaper’ na Bitcoin aka ambace ta. Sai dai a takardar farko kalmomi biyu a rarrabe watau Block Chain, sai daga baya a shekarar 2016 ne aka haɗe kalmomin wuri guda kamar yadda ake rubuta su a halin yanzu. Da haka za mu fahimci cewar, fasahar Blockchain ta daɗe a samuwa kimanin shekaru 18 kafin bayyanar kuɗin internet na cryptocurrency.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading