Skip to content

Ciwon mara

Mene Ne Ciwon Mara?

Hukumar Lafiya ta Burtaniya (NHS) ta ce ciwon mara abu ne da ya zama ruwan dare kuma wani ɓangare ne na haila. Kuma ciwon yakan dauki kwana biyu zuwa uku ko fiye ana yi.
Sannan yakan zama matsananci ga wasu mata, yayin da wasu kuma yakan zo musu ne sama-sama, in ji hukumar. Mata na jin ciwon mara ne a cewar NHS idan naman da ke jikin mahaifa ya murɗe. Kodayake, hakan na faruwa a kodayaushe, amma ba kasafai ake ji ba saboda a hankali yake yi.
Sai dai a lokacin jinin al’ada ya fi matsewa sosai domin ya taimaka wajen fitar da jinin.

Hukumar ta kara da cewa lokacin da mahaifar ke matsewa tana matse jijiyoyin jinin da ke jikinta, kuma a dalilin hakan sai jini da iskar Oxygen da ke kaiwa ga mahaifar ya katse. To rashin iskar oxygen a mahaifar yana sa ta fitar da wasu sinadarai wadanda ke kara ciwon mara. Daga shekara tara (9) zuwa sama yawanci ‘yaya mata suke fara fuskantar ciwon.

Ciwon Mara a yayin jinin al’ada

Da yawan ‘ya’ya mata, na fuskantar ƙalubale yayin da suka kai minzali zama cikakkun mata. A duk wata, lokacin al’ada na gabatowa ciwon mara, ciwon ciki, ciwon baya har da ƙafafuwa kan yi dambarwa a jikin ‘ya mace Hakan har ya kan iya kaiwa ga suma, wasu na amai; wasu kuwa sukan gagara motsawa daga inda suke, duk su fice daga hayyacinsu. Idan an nemi maganin an gagara dacewa akan yi kokarin shan kowanne irin magani ba tare da duba ingancinsa ba sai don nema wa kai mafita da salama.

Haƙiƙanin gaskiya a kimiyance wannan lalurar ba ta da wani tsayayye tartibin magani da kai tsaye za a iya cewa magani ne na magance ta. Har ya kan kai ga shan wasu magungunan na kara ingiza radadin ciwon ba tare da an ankare ba. A takaice ma yawan shan maganin asibiti da allurai kan iya janyo wata matsalar ga mahaifar ‘ya mace.

Yana da matukar hatsari kasancewar shan maganin asibiti da allura ga wannan lalurar kai tsaye, wanda in komai ya gagara saituwa a karshe akan ba wa iyaye shawara da su yi gaggawar aurar da ɗiyarsu, bisa tunanin cewa auren zai iya kawo ƙarshen lalurar, amma sai da kuma kash! Hakan ba ya tabbatuwa ga kowacce ‘ya mace, wasu ko da da auren nasu sukan sha fama a duk lokacin da jini zai zo musu. Wanda hakan kan iya janyo matsala ko taɓarɓarewar yanayin mace, maimakon yin aure ya sa ta yi kyau da kumari sai saɓanin hakan ya kasance, ta ƙare a tsaye. Ita ba ta haihu ba, ita ba ta samu cikakkiyar lafiya ba.

Wasu daga cikin mata sun bayyana yadda yanayin yadda suke tsintar kansu a irin wannan hali. Ga abin da wata matashiyar budurwa take cewa:

“Tun kafin al’adar ta zo mini idan wata ya kama ya yi kwana goma zuwa sha biyu, nake fara jin ciwon ciki. Da zarar ya zo kuma sai ciwon mara da bayana da ƙafata, ba na iya takawa ko ina zai kumbura ko tauna, ba na iya cin komai sai ruwan zafi kawai. Ba ya dainawa har sai ana gobe zan yi wanka, ya zama duk lokacin da zan yi sai an yi mini allura. Da yin allurar ya yawaita kuma babu wani ƙwaƙƙwaran sauƙi. Likitan da kansa ya ba wa iyayena shawara a kan a daina yi mini allurar kawai, a yi haƙuri domin ci gaba da hakan zai iya ba ni matsala a gaba, musamman a gidan aurena.”

Wata matar aure kuwa cewa ta yi:

“Gaskiya ina jin jiki kuma ina shan wahala matuƙa gaya, tun kafin na yi aure a duk lokacin da zan yi al’ada, tana farawa nake fita hayyacina in suma har ylta kai ga kullum cikin jinya nake, zazzaɓi kuwa ba ya bari na Mutane da dama sun sha faɗin cewa idan na yi aure zan daina, amma kuma abin mamakin da aurena yanzu har da yara biyu kuma ban fasa wannan gigitaccen ciwon marar ba. Abu ɗaya ne zan iya cewa yanzu ba na suma, sai dai fama da laulayin nan kuwa yana nan har na kan ji cewa wannan ciwon cikin shi ne ƙaddarata tunda tun muna neman magani har mun gaji mun hakura. Su ma asibitin in ka je tun suna ba da maganin har sun koma ba da shawarar a yi haƙuri gudun nemo wa kai wata matsalar.”

Hakan ma wani tabbaci ne da ke bayyanar da barazana tare azabtuwar da mata ke yi a lokacin al’ada. Hakan ya sa ake ci gaba da gudanar da bincike wajen zaƙulo magani da hanyoyin da za a bi wanda kan iya zamtowa katari ga masu fama da wannan lalurar cikin sauƙi.

Dabaru ko sirrikan da kan iya taimakawa wajen taƙaitar ciwon ba tare da an galabaita ba, kuma ba tare da an takulo wata matsalar ba sun haɗa da:

Na Farko: Mace ta yi ƙoƙarin mayar da ruwan ɗumi ruwan tsarkinta a kowanne lokaci ba sai lokacin zuwan jinin ba. Ya zame mata jiki wanda in har ba wai ta rasa ba sai ta yi amfani da ruwan sanyi ba. A shawarce zai fi kyau tana yi dana ɗumin. Kuma shi ma ruwan ɗumin ba ana nufin mai zafi da zai iya ƙona ta ba, ruwa mai ɗan ɗumi daidai gwargwado.

Na Biyu: Gujewa shan zaƙi a kowanne lokaci, kamar sikari, alewa da dai duk wani abu da ya danganci zaƙi. Hatta shayi ma a rangwanta cika sugar.

Na Uku: Yayin da mace ta fara jin sauyi a jikinta ta daina shan ruwan sanyi, in so samu ne ma a daure a daina shan ruwan fridge mai sanyi sosai ko mai ƙanƙara. Kuma sannan ta dinga gasa mararta da ruwan ɗumi a duk lokacin da ta zo yin wanka, inda hali hakan ma ya zame mata jiki.

Na Hudu: Da zaran mace ta ji alamu ko ta ga lokaci ya gabato ta nemi cittarta ɗayan da Cinimon ta dafa a ruwan zafi ya dahu sosai sannan ta dinga ɗiba tana shan ƙaramin kofi.

Na Biyar: In babu Cinimon ta samu ‘Bay leaf’ shi ma ta dafa shi, a tabbatar ya dahu sannan a dinga shan ruwan ƙaramin kofi kamar wancan.

Waɗannan hanyoyi ne ingatattu kuma nagartattu da bin su zai kawo sauƙi. Mata da dama sun jarraba kuma sun samu sauƙin ciwon fiye da ƙwayoyin Bature ko allura da kan haifar da wata matsalar.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×