Skip to content

Ciwon nono

Ciwon nono shi ne alamar rashin jin daɗi a cikin nono ɗaya ko duka biyun ko kuma jin wani yanayi mara gamsarwa saɓanin yadda wurin yake. Ciwon da ya shafi sashe ɗaya kawai na nonon ya fi damuwa, musamman idan ya zamana ya yi tauri ko kuma yana zubar da ruwa.

Ciwon mama kan shafi duka nonuwa biyun.

Wa ke kamuwa da ciwon nono?

Ciwon nono abu ne da mata kan yi fama da shi a wasu lokutan mabambanta. Sannan kuma ciwon bai ware manya ko kuma matasa ba, ma’ana dai yana iya kama kowacce mace matukar dai ta kai munzalin fitar da nonon a kirjinta.

Ire-iren ciwon nono

Akwai ire-iren ciwon nono da dama da mata kan yi fama da shi kamar:

1- Ciwon nono cokacin al’ada

Ciwon nonon yana fara bayyana ne kwanaki kaɗan kafin al’adar, abin da mata da yawa ke fama da shi ke nan. Ciwon nono yana ɗaya daga cikin alamomin da suka fi yawa kuma na ɗabi’a waɗanda ke tare da al’adar mace. Yawancin mata suna jin zafi da laushi a cikin ƙirjin kwanaki kaɗan kafin zuwan hailarsu. Kodayake ciwon nonon na iya zama mai ban haushi kuma yana haifar da rashin jin daɗi, yawanci ba ya haifar da barazana ga lafiya.

Alamomin wannan nau’in ciwon nono sun bambanta daga wata mace zuwa wata. Wasu matan na iya jin zafi a cikin nono ɗaya, yayin da wasu na iya jin zafi daban-daban a cikin nonuwa biyu. Haka nan ana iya jin kumburi da taushi, da wataƙila jin nauyi a cikin ƙirjin.

Ciwon nono lokacin al’ada

Matakan kariya

Domin kawar da ciwon nono kafin haila, mata za su iya bin wasu matakai masu sauƙi. Daga cikin wadannan matakan akwai:

Wanka da ruwa mai ɗumi: Yin wanka da ruwa mai ɗumi yana taimakawa rage zafi da jin a cikin nono.

Tausa mai laushi: Tausasa nono a hankali  na iya taimakawa wajen inganta kwararar jini da rage zafi.

Sa rigar nono mai inganci: Yin amfani da rigar nonon da ke ba da tallafin da ya dace ga nono yana rage zafi.

2- Ciwon nono lokacin samuwar ciki

Nazarin ya nuna cewa akwai dalilai da yawa masu yiwuwa na ciwon nono a farkon ciki. Daga cikin waɗannan dalilai:

Haɓaka samar da hormone: samar da hormones yana ƙaruwa lokacin daukar ciki, irin su estrogen da progesterone, wanda ke taimakawa wajen shirya nono don shayarwa. Wannan ƙaruwa a cikin hormones na iya haifar da haɓakar nono da laushin jijiyoyi a cikin nono.

Canje-canjen da ake yi wajen shirya nono don shayarwa: Canje-canjen ƙirjin a shirye-shiryen shayarwa ya sa nono ya ƙaru kuma hanyoyin jini suna ƙaruwa. Wannan canjin zai iya haifar da laushi da girman nono da zafi.

Canje-canjen nama na adipose: Akwai canji a cikin rarraba mai a cikin jiki yayin daukar ciki, kuma nonuwa suna karuwa. Wannan canjin zai iya haifar da matsala da kumburi a cikin ƙwayar mammary kuma hakan zai haifar da jin zafi da ciwo.

Vasodilatation: Vasodilatation yana faruwa ne saboda karuwar jini a ƙirjin, kuma wannan na iya haifar da karuwar barazanar kamuwa da ciwon nono.

Abubuwan da ke haifar da ciwon nono a farkon ɗaukar ciki na iya bambanta daga mace zuwa wata, don haka yana da kyau mace ta saurari jikinta kuma ta gane duk wani canji na alamun da za ta iya ji. Ana kuma ba da shawarar sanya rigar nono mai nagarta.

Akwai nau’in ciwon nono mai zubar da ruwa

3- Ciwon nono lokacin shayarwa

Ciwo ne da mata kan yi fama da shi a lokacin shayarwa wanda Hausawa kan kira da (Mageduwa). Ciwo ne mai tsanani yana da azaba sosai. Kan nono kan yi ja ya ɗaɗe tare da yankawa ya shata kamar zai cire, wasu lokutan ma na wasu matan idan ciwon ya tsananta kan nono yana iya gutsirewa gabaɗaya. Idan mace tana fama da wannan ciwo wata har suma take yi idan yaro ya kama. Wata kuma idan yaro ya kama yana sha har tana zubar da hawaye saboda azaba. Akasari a irin nau’in wannan ciwo mata ba su cika amfani da magungunan asibiti ba. Sun fi amfani da maganin gargajiya domin sauƙin ciwon.

4- Ciwon nono lokacin yaye

Shi wannan nau’in ciwon nono ne dake faruwa dalilin rashin ba wa yaro abincinsa, domin ya kai lokacin da zai daina sha ko kuma mahaifiyarsa take ganin ya kai lokacin da ba za ta iya jura tana ba shi yana sha ba. Wannan rashin shan da yaro ke yi, kan iya sa nonon ya yi sundundun ya yi tauri domin asalin ruwan nonon yana haɗuwa ne yana dunƙulewa daga ruwa zuwa ƙwaya. A wasu lokutan yakan haifarwa da mata zazzaɓi mai zafin gaske, tare da ɗaɗɗaurewar ƙirji.

Maganin ciwon nono

Lokacin yaye ma nono kan yi ciwo.
  • Maganin Hormone: Magungunan da ke toshe wasu hormones a jiki.
  • Maganin asali: Magungunan da ke kaiwa ga takamaiman sinadarai a cikin ƙwayoyin kansa.
  • Immuno therapy: Magungunan da ke taimakawa tsarin garkuwar jiki don kashe kwayoyin cutar daji.
  • Chemo therapy: Yana magance cutar kansa da cutuka masu ƙarfi.
  • Maganin Radiation: Yana magance ciwon daji da ba da kariya mai ƙarfi.

A lura cewa takamaiman magani da tsarin jiyya zai dogara ne da yanayin ciwon nono.

Manazarta

Admin, L. (2021, August 3). Ciwon nono a lokacin daukar ciki, kumburin mammary gland. Lafiyayyan Abinci Kusa Da Ni.

Contributors to Wikimedia projects. (2024, May 4). Ciwon nono.. Wikipedia.

Mayo Clinic.  (2024, February 10). Breast cancer – Diagnosis and treatment – Mayo Clinic.

Sharkawy, M., & Sharkawy, M. (2023, September 11). Abubuwan da ke haifar da ciwon nono a farkon ciki kuma yaushe ne kumburin nono ya fara lokacin daukar ciki? تفسير الاحلام.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading