Skip to content

Cutar damuwa

Share |

Cutar ‘Depression’ wato damuwa wata nau’i cuta ce da ke addabar ƙwaƙwalwa inda take sa wa mai cutar yawan baƙin ciki, ƙyamar aikata abin da mutum ke so a da, da kuma rashin son shiga mutane ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba.

Akwai tarin bayanai daga masana mabambanta game da bayanin kan wannan cuta ta damuwa. Yayin da cutar kuma ta kasu zuwa fanni-fanni da kuma matakai daban daban.

Cutar damuwa kan hana mutum shiga cikin jama’a.

Haka kuma akwai bayanai da dama game da sababban samuwar cutar daga bakin masana da yawa. Al’adar shiga yanayi na baƙin ciki ko ƙunci na dan wani lokaci wannan ba za a kira shi da cuta ba, saboda hakan ya faru ne ƙila akwai wasu matsaloli da su ka tasowa mutum kamar rasa aiki, mutuwar aure da kuma sauran matsaloli na rayuwa. Sai dai waɗannan lamurra idan suka ta’azza su ne za su jawo cutar damuwa dauwammiya ga mutum.

Sau da yawa, mutane kan shiga cikin halin damuwa da rashin walwala saboda wasu abubuwa na yau da kullum na rayuwa. Amma idan mutum ya ci gaba da kasancewa a wannan hali na damuwa tsawon makonni ko watanni, likitoci kan ce ya gamu da cutar matsananciyar damuwa.

Akan yi wa wannan cuta kallon ƙaramin abu ko wasu ma su ce rashin haƙuri ne ko rashin tawakkalin wanda ya gamu da ita. Sai dai masana sun ce abin da mutane ba su gane ba shi ne cuta ce kamar ko wace irin cuta da kan kama wani ɓangare na jikin mutum. Haka kuma cuta ce da ke shafar ƙwaƙwalwa da tunani wanda mai fama da ita ba shi da iko a kanta.

Ko da Wikkitimes ta samu zantawa da Yahya Auwal, masani a fannin kiwon lafiya ya bayyana cewa cutar da ke da alaƙa da ƙwaƙwalwa ba za a ce kai tsaye ga abin da ke jawo shi ba, sai dai akwai abin da ake kiranshi da ‘predisposting factor’, sai kuma akwai yanayin halittar ƙwaƙwalwa idan tana da ƙarancin jijiyon aika saƙo. Sannan kuma akwai gado shi ma ana iya gadon sa daga iyaye idan akwai wanda yake da wanan lalura. Ko kuma faruwar wani abu mai gigitarwa ga rayuwar ɗan Adam ka hatsari ko rasa wani abu muhimmi na rayuwarsa.

Mai cutar damuwa kan iya rasa barci gabaɗaya.

Za ta iya yi wa rashin lafiya mai tsanani irin ciwon siga ‘Diabetes’, ko matsanancin zazzaɓin cizon sauro wanda ya yi sanadin taba ƙwaƙwalwa.

Shaye-shaye irinsu wiwi, shan barasa da sauran kayan maye su ma duk su na janyo cutar damuwa. Sai kuma mummunar ƙaddara da ta faru a rayuwar mutum musamman mace kamar fyade, rabuwar aure na bazata, Haka kuma cuttukan ƙwaƙwalwa da suka faru da mace lokacin haihuwa wanda ake kiranshi da ‘Puerperal psychosis’.

Alamomin cutar damuwa:

• Keɓewa da ƙin shiga mutane. Dokta Ɗayyibah Shaibu, ƙwararriya a ɓangaren lafiyar ƙwaƙwalwa ta ce alama ta farko da ake gani a masu wannan cuta ita ce keɓe kai.

“Idan a baya an saba ana zama da mutum a yi hira, sai a ga yanzu ya fi son zama a ɗaki shi kaɗai sannan zai rage walwala.

“Ko fita za a yi gaba ɗaya mutanen gidan, mai cutar tsananin damuwa zai ce shi ba za shi ba a tafi a bar shi a gida”,

• Yawan barci ko ƙauracewar barci da tsananin cin abinci ko rashin cin abinci inda har mutum kan ƙara ƙiba ko rage ƙiba na daga cikin manyan alamomin wannan cuta.

Amma ga mai fama da ita, tsananin baƙin ciki na babu gaira babu dalili yake ji a ransa. Haka kuma, likitar ta ce cutar hawa-hawa ce. Akwai wadda ta yi tsananin da sai an daɗe ana shan magani kafin a samu sauƙi sanna akwai wadda ɗebe kewa da bayar da shawarwari kawai ke iya magance ta.

Cutar damuwa na iya haifar da rashin cin abinci.

Suwa cutar take kamawa?

Dokta Ɗayyibah ta ce cutar tsananin damuwa na iya kama ko wane jinsi na mutane sannan ana ganin ta a manya da yara duka.

Sai dai ta ce an fi ganinta a mata da matasa da suke daidai shekarun balaga. Masana lafiyar ƙwaƙwalwa sun ce sau da yawa idan wani iftila’i ya samu mutum ne ya ke shiga halin tsananin damuwa kamar rasa wani makusanci ko kora daga wajen aiki ko haihuwa mai cike da tangar0ɗa da dai sauransu.

Dokta Ɗayyibah ta ce yanayin halittar ɗan Adam na taka muhimmiyar rawa wajen samun wannan matsala.

“Wani Allah ya halicce shi da juriya. Ko da abin tashin hankali ya same shi zai daure kuma ba zai zauna masa a rai ba.

“Wani kuma ba shi da haka. Allah ya halicce shi yana da rauni kuma ba ya iya jure jarrabawa, to irinsu ne suka fi gamuwa da matsalar tsananin damuwa”

Amma likitan ta ce wani lokaci ma haka kawai mutum kan shiga damuwa har ta zamar masa wannan cuta.

Ana warkewa daga cutar tsanain damuwa?

Dokta Dayyibah ta ce ana warkewa tsaf daga wannan cuta idan aka samu taimakon da ya kamata.

“Idan aka lura wani ya fara nuna alamomin wannan cuta, abu na farko shi ne a kai shi asibiti. Akwai magunguna da hanyoyin da ake bi a asibiti ga masu fama da cutar damuwa.

Akwai wurare na musamman da aka keɓe saboda masu lalurar kawai. Sannan akwaiɓmagunguna sannan akwai likitoci na musamman da aikinsu kawai ɗebe wa masu wanann cuta kewa da ba su shawarwari kan yadda za su tafi da rayuwarsu. Sannan ta ce maskusantansa su riƙa jansu a jiki da nuna masa kulawa. Duka waɗannan ne ke samar da kwanciyar hankali a tare da masu cutar har su samu lafiya . Akwai hanyoyi daban-daban da ake bi don ganin an magance wannan lalura kamar su:

1. Zuwa ganin likitan ƙwaƙwalwa don neman shawararin yadda mutum zai kula da kansa har ya daina shiga damuwa.

2. Hulɗa da mutane. Musamman ma bambanta domin samun cuɗanyar tunani da mu’amala.

3. Cin abinci mai kyau da kuma samun hutu da bacci wadatacce.

4. Shan magunguna (Antidepressants) wanda za su taimaka wurin rage ciwon.

5. Ba wa ƙwaƙwalwa hutu: Shi kuma wasu na’ura ne masu amfani da wuta wanda suka aika wa zuwa kwakwalwa irin su ‘electroconvulsive therapy da kuma vagus nerve stimulation’.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading