Skip to content

Cutar laka

Cutar laka cuta ce mai haɗari da ta ƙunshi lalacewar kowane ɓangare na ƙashin tsakiyar baya da jijiya, wanda ake kira da (spinal cord, a turance). Haka nan zai iya haɗawa da lalacewar jijiyoyin ƙarshen ƙashin baya, wanda aka fi sani da (cauda equina). Laka tana aikawa da karɓar saƙonni tsakanin ƙwaƙwalwa da sauran sassan jiki. Cutar laka takan haifar da canje-canje na dindindin a ƙarfin jiki da ji da sauran ayyukan jiki a wurin da rauni ya faru. Mutanen da suka sami matsalar cutar laka na shiga cikin tunani da fuskantar matsalolin zamantakewa.

Cutar laka wacce aka fi sani da spinal cord disorder a turance, ta fi aukuwa sakamakon haɗarin abin hawa.

Masana kimiyya suna da kyakkyawan fatan cewa cigaban bincike watarana zai iya haifar da maganin wannan cuta. Bincike yana gudana a duniya a halin yanzu, ilimin jiyya da wasu dabaru suna ba da dama ga mutane da yawa masu wannan cuta don yin rayuwa mai inganci kuma su zama masu dogaro da kansu.

Alamomin cutar laka

Alamomin wannan cuta ta laka mai haɗari sun kasu gida biyu, wato akwai alamomin farko-farko akwai kuma na daga baya.

Alamomin farko-farko

Alamomin farko-farko na cutar laka bayan aukuwar haɗarin sun haɗa da:

  • Matsanancin ciwon baya ko tsanani a wuya ko kai ko baya
  • Rauni, rashin daidaituwa ko iya sarrafa bangarorin jiki
  • Rashin ji a hannaye ko yatsu ko ƙafafu
  • Ciwon mafitsara ko gaza sarrafa hanji
  • Matsalar rashin daidaituwa yayin tafiya
  • Matsalar numfashi bayan aukuwar raunin
  • Murgudewar wuya ko baya

Alamomin daga baya

Damar sarrafawa da motsa hannaye ko ƙafafu bayan aukuwar wannan cuta ya dogara ne bisa abubuwa guda biyu. Na farko shi ne inda raunin ya faru a kan ƙashin baya. Na biyu kuma shi ne yadda rauni ya munana. A dunƙule dai cutar na iya haifar da alamomi masu zuwa:

  • Rashin motsi
  • Sauyi a yanayin jin zafi, sanyi ko taɓawa
  • Rashin sarrafa hanji ko mafitsara
  • Ƙarfafa ayyukan reflex ko spasms.
  • Sauye-sauye a aikin jima’i, jin daɗin jima’i da haihuwa
  • Raɗaɗi ko wani matsanancin zafi wanda ke haifar da lalacewa ga jijiyoyi a cikin ƙashin baya.
  • Matsalolin numfashi, tari ko ciwon hunhu

Nau’ikan cutar laka

Akwai hanyoyi guda biyu da masana ke bi wajen zayyana nau’ikan cutar laka kamar haka: hanya ta farko ita ce yanayin yadda raunin ya shafi lakar da kuma inda a cikin lakar raunin ya faru. Cutukan laka na iya katse zirga-zirgar saƙonnin jijiya zuwa da komawa daga ko’ina a inda larurar ta faru. Nau’ikan cutar ana bayyana su ta fuskoki kamar haka:

Ta fuskar wajen da abin ya shafa

Wannan ya ƙunshi bangarorin ƙashin baya da laka wanda suka haɗa da:

  • Cervical spine: Wannan sashe ne da yake cikin wuya. Yana farawa daga ƙasan kwanya zuwa kusan matakin daidai da kafaɗu.
  • Thoracic spine: Wannan sashe yana shimfiɗe daga baya na sama zuwa ƙasan cibiya.
  • Lumbar spine: Wannan sashe kuma yana cikin ɓangaren ƙasan baya. Ya kai kusan saman inda mazaunai (ɗuwawu) suka haɗu, amma ƙashin laka ya ƙaru da inci biyu sama da hakan.
  • Sacral spine: Shi ma wannan sashe ne da ke cikin baya. Ya ƙunshi tushen jijiya a ƙasan ƙugu zuwa ƙashin gaba.

Ta fuskar tsananin cutar

Wannan ma ka’ida ce ta zayyana nau’in cutar laka, wato ta fuskar yanayin tsananin ciwon wanda ya haɗa da:

  • Wani sashen lakar: cutar laka wacce ba ta gabaɗaya, ma’ana ba duka lakar ba ce ta lalace, wani sashe ne kawai ya tabu tana kama da rufewar jijiyar kuma tana shafar wasu hanyoyi ne kawai. Wasu sunq kasancewa a buɗe, don haka wasu iyawar da ke ƙasa da rauni sun kasance cikakke.
  • Gabaɗaya lakar: wannan nau’in cutar yana haddasa lalacewar laka gabaɗaya, tana rinjayar dukkan hanyoyi. Babu zirga-zirga da ke shiga. Yawancin lokaci tana nufin matsala ko cuta ta dindindin tare da haifar da shan-inna.

Tsarin yadda laka take

Laka tana da sassa 31, suna jere layi-layi tare da nau’i-nau’i 31 na jijiyoyin lakar. Masana suna amfani da haɗin lambobi da harufa don ayyana su. Harafin yana nuna sashen lakar, yayin da lamba ke nuna ɓangaren. Misali, C8 na nuna ƙashi na takwas.

Cututtukan laka yawanci sun ƙunshi matakai da yawa. Mataki na farko shi ne raunin farko. Amma a cikin sa’o’i da kwanaki masu zuwa, rauni na biyu kuma zai iya tasowa, yana haifar da kumburi da ƙarin lalacewa ga laka.

Alamomin cutar na musamman

Alamomin cututtukan a cewar Cleveland Clinic sun dogara ne a kan jijiyar da abin ya shafa. Akwai nau’ikan jijiyoyin saƙonni guda uku waɗanda cutar ke iya shafar su: sensory, motor da kuma automatic.

• Sensory

Su ne jijiyoyin da ke sarrafa tunani ko hankali, suna ɗaukar bayanai zuwa ƙwaƙwala. Suna sanar wa kwakwalwarka game da duniyar da ke kewaye da mu da abin da ke faruwa da jikinmu.

Laka tana ɗaukar saƙonnin taɓawa (wato taɓawa ta asali). Misalai sun haɗa da zafin jiki ko tsanani ko jijjiga ko rubutu a jiki, da sauransu. Idan aka motsa hannu zuwa fuska a cikin daki mai duhu sosai, za a iya dakatar da hannu kafin ya taɓa hanci, wannan shi ne misali na dakatar da abin da za aka yi niyya. Misalan cututtukan sensory sun haɗa da:

  • Ciwo
  • Lalacewa
  • Tingling

• Alamomin motor

Alamomin motor suna tafiya daga ƙwaƙwalwa zuwa tsokoki. Su ne yadda ƙwaƙwalwa ke motsa sassan jikinka. Alamomin na iya haɗawa da:

  • Rauni wato raguwar ƙarfi
  • Paralysis
  • Spasticity

• Alamomin autonomic

Jijiyoyin saƙonni masu sarrafa kansu suna tafiyar da matakan da ba dole ba ne a yi tunani a kai wato (autonomic sounds) kamar atomatik da jijiyoyin saƙonni masu cin gashin kansu suna ɗaukar matakai na atomatik. Alamomin wannan nau’i na iya haɗawa da:

  • Matsololin bugun zuciya, musamman jinkirin bugawar zuciya (wato bradycardia)
  • Matsalolin hawan jini, musamman ma rage hawan jini (wato hypotension)
  • Matsalolin zafin jiki, musamman ƙarancin zafin jiki (wato hypothermia)
  • Rikicewar tsarin fitsari ko rashin yin bahaya
  • Rashin karfin mazakuta

Dalilan gama gari na cutar laka

Mafi yawan abubuwa ko dalilan da ke haifar da cutar laka kamar yadda Mayo clinic suka zayyana su ne:

• Hadarin ababen hawa

Hadarin mota da babura su ne kan gaba wajen haddasa wannan cuta. Ana kiyasin kusan rabin sababbin cututtukan laka kowace shekara a dalilin haɗarin abin hawa.

• Faɗuwa

Raunin ƙashi da jijiyoyi bayan shekaru 65 yawanci yana haifar da cutar ta hanyar faɗuwa.

• Ayyuka masu tsanani

Kimanin kashi 12% na wannan cuta yana faruwa ne dalilin ayyuka masu tsanani na tashin hankali, yawanci daga raunukan harbin bindiga ko raunin wuka, wanda ya zama ruwan dare.

• Wasanni

Ayyukan motsa jiki, irin su  wasannin linƙaya da nutsewa a cikin ruwa mai zurfi, suna haifar da kusan 10% na wannan cuta.

• Cututtuka

Akwai wasu jerin cutukan kamar ciwon daji da amosanin gaɓɓai da cutar osteoporosis da kumburin ƙashin baya duka suna iya haifar da cutar laka.

Bangarori da dama na laka kan iya samun matsala sakamakon aukuwar cutar laka

Abubuwa masu haɗari

Cutar laka tana da tsananin haɗari da tashin hankali kuma tana iya faruwa ga kowa. Amma akwai wasu dalilai da kan iya ƙara haɗarin aukuwar wannan cuta , za su iya haɗawa da:

  • Jinsin namiji: Cutar laka ta fi shafar jinsin maza. A  zahiri ma dai, mata ba su wuce kashi 20 cikin 100 ba na masu larurar cutar laka.
  • ‘Yan shekaru 16 zuwa 30: Fiye da rabin masu fama da cutar laka na faruwa a cikin mutanen da ke cikin tsakanin waɗannan shekarun.
  • ‘Yan shekaru 65 da haihuwa: Wani kari a cikin rukunin mutane masu fama da cutar laka na faruwa a cikin shekaru 65. Faɗuwa tana haifar da mafi yawan raunuka a cikin tsofaffi.
  • Shan barasa: Amfani da barasa yana haifar da kusan kashi 25% na aukuwar wannan mummunar cuta.

Hanyoyi gwaje-gwaje

Ma’aikatan kiwon lafiya na iya tantance cutar laka ta amfani da hanyoyi da yawa, ciki har da:

• Gwajin jiki

Likita ko ma’aikacin lafiya kan yi wannan gwaji ne don neman alamomi ko kuma shaidar girman raunin.

• Gwajin jijiya

Ma’aikacin lafiya zai yi wannan gwaji ne don tantance yanayin kuzari da tsarin jijiyoyi. Wannan ya haɗa da fahimtar ko za a iya motsa gaɓoɓin ta hanyar auna ƙarfi da duba abin da ake ji da kuma motsin zuciya.

• Ɗaukar hoto

Wannan hanya ce da ta haɗa da yin amfani da na’urorin ƙididdiga (CT) da hanyoyi na maganadisu (MRI). Binciken CT yana da sauri kuma yana nuna cututtuka masu rauni ko matsaloli da ke da alaƙa da ƙashi. Binciken MRI yana ɗaukar tsawon lokaci amma yana ba da cikakkun hotuna na ƙasusuwa, ƙwayar halittar tissues da jijiyoyi da sauransu.

• Gwajin na’ura

Misalan waɗannan gwaje-gwaje sun haɗa da electromyography da  gwaje-gwajen sarrafa jijiya. Suna auna yanayin jijiyoyin da ke kaiwa ga tsokoki, wanda za su iya taimakawa wajen gano lalacewar jijiya ko laka.

Magungunan cutar laka

Magungunan cutukan laka sun bambanta matuƙa. Bambancin farko shi ne ko maganin yana da alaƙa da raunin ko kuma a’a. Wata cutar lakar da ake zargin tana da alaƙa da raunin koyaushe tana buƙatar gaggawar likita. Sauran cutukan laka, sakamakon wasu dalilai su ma suna buƙatar gaggawar likita. Sauran abubuwan da ke buƙatar kulawar gaggawa sun haɗa da:

  • Cututtuka: Waɗannan na iya zama silar mutuwa da sauri idan ba a kula da su ba.
  • Rashin gudanar jini: Kulawa da kwararar jini muhimmin abu ne da ya kamata a bawa fifiko don ceton rai.
  • Yanayin autoimmune: Haka nan waɗannan na iya haifar da rikice-rikice masu tsanani idan ba a yi gaggawar magani ba lokacin da suka haɓaka ba zato ba tsammani, kamar ciwon Guillain-Barr.

Riga-kafin cutar laka

Cutukan laka kusan koyaushe suna faruwa ne haɗarance, wato suna faruwa ne ba tare zato ko tsammani ba. Amma duk da haka akwai abubuwan da za a iya yi don rage haɗarin aukuwar su. Abubuwan sun hada da:

  • Yin amfani da kayan kariya da kamewa a duk lokacin da aka ba da shawara.
  • Yin tuki da hankali da nutsuwa
  • Daƙile faɗuwa lokacin da ta zo ta hanyar riƙe wani ginshikin
  • Yin taka-tsantsan a duk lokacin da ake kusa da bindigogi.
  • Kada a yi nitso ko faɗawa cikin ruwan da ba a iya ganin ƙasansa
  • A guji yin amfani da magunguna barkatai ko magungunan nishaɗi ko barasa.

Kulawar likita

Duk wanda ke da rauni a kai ko wuya yana buƙatar tantancewar likita nan take. Ba ana ɗauka cewa mutumin yana da cutar laka ba ne, a’a har sai an tabbatar da wani abua likitance. Wannan yana da mahimmanci saboda:

  • Wani raunin na laka ba koyaushe yake bayyana nan da nan ba. Idan matsalar ta auku amma ba a sani ba, mummunan rauni zai iya faruwa daga baya.
  • Kumburi ko gurguntaka na iya faruwa da sauri ko kuma zuwa a hankali.
  • Lokaci tsakanin rauni da jiyya karbar kulawar ma’aikatan lafiya na da mahimmanci.
  • Kar a motsa wanda ya ji rauni. Ciwon kai na dindindin da sauran matsaloli masu tsanani na iya aukuwa.
  • A sanya tawul masu nauyi a ɓangarori biyu na wuyansa. Ko a riƙe masa kai da wuya don hana su motsawa har sai likita ya zo da taimakon gaggawa.

Manazarta

Navigating Spinal Injury Symptoms: Types & levels | Shepherd Center. (n.d.).

Spinal cord injury. (2024, August 26). Cleveland Clinic.

Spinal cord injury – Symptoms and causes. (n.d.-b). Mayo Clinic.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×