Skip to content

Da wa ka ke mu’amala a shafukan sada zumunta?

Share |

Abu guda da mutum zai yi a yau wanda zai yi matukar kyautata rayuwarsa shi ne sa ido tare da tantance irin mutane ko shafukan da muke hulda da su a kan shafukan sada zumunta.

Saboda me? Saboda suna matukar tasiri a rayuwarmu ta yadda suke sauya mana tunani ba tare da mun yi la’akari da hakan ba. Kamar ya? Saboda suna daga cikin masu cika tankin ilimi da tunanin da muke da shi su kuma sa mu daukar matakan da suke shafar rayuwarmu ta yau da kullum.

Saboda haka yin nazari kan wadannan shafuka da ra’ayoyin da ake wallafawa a kansu ba abin wasa ba ne.

Annabi (SAW) ya ce misalin aboki na kwarai kamar mai sayar da turare ne, ko bai sam maka ba za ka sha kamshi. Shi kuwa abokin banza kamar makeri ne, in ba ka kone ba, ka kwashi warin hayaki.

A wannan zamanin da muke wuni a kan shafukan sada zumunta, abota ba sai kuna zama a gari guda da mutum ba. Yau kana iya kulla abota da mutane a kowane sassa na duniya kuma su zamo tamkar abokanmu na zahiri ta yadda suke debe mana kewa su ilimantar da mu su kuma nishadantar da mu.

To kamar yadda mutanen da kake zagaye da su a zahiri ke matukar tasiri a rayuwarka, haka ma wadanda ka zagaye kanka da su kan shafukan sada zumunta suke tasiri. Saboda haka ku duba ku gani, masu shirme kuka zagaye kanku da su ko masu nagarta? Don kamar abinci da muke ci ne; idan ka ci mai kyau zai nuna, idan marar kyau ne ma za a gani. Abin da ka shuka shi za ka girba.

Masana dabi’un dan adam sun ce abu mafi sauki da mutum zai yi domin ya sauya rayuwarsa shi ne ya yi tunanin wane irin mutum kake son zama, sannan sai ka shiga zagaye kanka da mutane masu irin wannan halayya ko ilimin da kake bukata. Kana son zama marubuci ne? To ka kasance kana bibiyar marubutan da kake alfaharin zama kamarsu. Kana son zama dan kasuwa ne? Kasance da ‘yan kasuwa. Kana son fahimtar inda duniya ta dosa? Kasance da manazarta masu sa ido a kan wannan harkar.

Sannan ana yawan cewa mutum ya nemi mentors wato mutane wadanda za su haska mana rayuwa ta hanyar sharwarwari domin cimma wani burin da muka sa gaba. To yanzu shafukan sada zumunta sun saukake hanyar samun mentors. Yau idan akwai wani da ya ke burge ka kana iya saka shi a cikin jerin mutanen da kake kira mentors ba tare da ma ya sanka ba. Ta hanyar bibiyar shafukansa na intanet kana dibar ilimin da yake wallafawa akai-akai. Ni kai na ina da tarin mutanen da nake kira “long distance mentors” wadanda nake yawan bibiyar rubutunsu domin na karu. Kuma na karu matuka domin sun ba ni kwarin gwiwar ci gaba da yin rubutu.

Sannan ka hado da mutane masu mabambantan ra’ayoyi ba sai masu ra’ayi iri guda da kai ba domin gudun daukar tsattsauran ra’ayi a game da kowace irin harka.

A wata shawarar da wani attajiri daga jerin masu kudin duniya, Charlie Munger, ya bai wa wasu daliban wata jami’ar Amurka da ake yaye, yake cewa: Idan kuna son ku bunkasa a rayuwarku, to ku guji daukar tsattsauran ra’ayi da kafewa a kan kowane irin batu. Ya ce kafin ku dauki ra’ayi a kan wani abu, to ku tabbata kun fahimci manyan hujjojin da dayan bangaren suka dogara da shi.

Yin hakan zai taimaka wajen samun cikakkiyar fahimta kafin daukar matakan da ka iya sauya rayuwarmu.

A duniyarmu ta yau ilimi ke aiki saboda haka kada ku yi sakaci wajen neman ilimi mai inganci domin gane inda duniyar ta dosa. Idan ba ka taba tantance jama’ar da shafukan da kake mu’amala da su ko kuma ka dan kwana biyu ba ka biyo ta kansu ba, to ka tabbata yau ka fara. Ka raba jaha da mutanen da ba su da abin yi sai gulma, zagi, da duk wani shirme don gudun daukar dabi’ar da ba za ta amfane ka ba.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading