Akwai amfani kala daban daban da dabbobin gona da suke wajen taimaka manoma da makiyaya da kuma al’umma gaba daya a rayuwarmu ta yau da kullum wadannan amfani sun hada da:
Suna samar da abinci masu gina jiki misalansu shi ne
- Madara
- Nama
- Kwai
Suna samar da kudi ga manoma sannan da samar da kudaden shiga ga kasa gaba daya ta hanyar cinikayya.
Suna zama hanyoyin samun albarkatun kasa, misali:
- Jima (fatar manya dabbobi da kanana domin yin takalma da jaka da sauransu a wasu kamfanoni)
- Madara (ana amfani da ita a kamfanoni da suke yin yoghurt da sauransu)
- Nama da kwai (ana amfani da su ta hanyar tsire, kilishi da kuma abinci da sauransu)
Yana rage zaman banza wajen samarwa matasa aikin yi, misali:
- Kiwon kaji
- Kiwon shanu
- Kasuwancin dabbobi
- Sana’ar fawa.
- sana’ar noman ciyawa da saidawa
Yana samar da taki ga manoma sannan ana amfani da shi ta hanyar girki misali
- Kashin dabbobi na zama takin noma ga manoma
- Busashen kashin shanu ana amfani da shi wajen yin girki da kuma maganin borin jini
Suna taimakawa wurin daukar kayan gona zuwa gida da kasuwanni misali dabbobin su ne
- Doki
- Jaki
- Rakumi
Ana amfani da dabbobi wurin aikin karfi a gona kamar misali
- Sa da rakumi ana amfani da su wurin yin hudar gona ko bajiya.
Kadan ke nan daga cikin amfanin dabbobin gona a cikin al’umma. Na gode, sai mun hadu a makala ta gaba.