Skip to content

Dakin gwaji (Laboratory)

    Aika

    Ɗakin gwaje-gwaje, wanda ake kira “laboratory” a Turance, wuri ne da ake gudanar da bincike, gwaje-gwaje, da nazarin kimiyya domin ganowa, fahimta ko tabbatar da wasu bayanai na ilimi da fasaha. A ɗakin gwaje-gwaje ake gudanar da ayyukan da suka shafi kimiyya a fannoni kamar chemistry, physics, biology, medicine, da kuma wasu fannoni na injiniyanci da fasahar zamani. Ana amfani da ɗakin gwaje-gwaje ne wajen binciken kimiyya (scientific research), tabbatar da ingancin kayayyaki, ko kuma nazarin sinadarai da ƙwayoyin halittu.

    Importance of Labs in School For Students0
    Ɗakin gwaje-gwaje yana da muhimmancin wajen koyo da koyarwa.

    A cikin ɗakin gwaje-gwaje, ana amfani da kayayyakin aiki na musamman da na’urori da aka tsara don gudanar da irin wannan aiki. Binciken da ake yi a nan zai iya kasancewa na ilimi ne kawai, ko kuma a matsayin na ci gaba da ƙirƙirar sabbin hanyoyin da za su amfanar da al’umma.

    Ɗakin gwaje-gwaje yana taka muhimmiyar rawa a fannonin kiwon lafiya, ilimin halittu, ilimin kimiyyar sinadarai, har ma da ayyukan masana’antu. Yana taimakawa wajen gano cututtuka, tabbatar da ingancin magunguna, ƙirƙirar sabbin Kayayyakin amfani, da tabbatar da sahihancin abubuwan da aka kera ko aka shirya.

    Nau’o’in ɗakunan gwaje-gwaje

    Kamar yadda ake da nau’o’i daban-daban na ɗakunan karatu, haka nan akwai nau’o’in ɗakunan gwaje-gwaje bisa ga irin aikinsu da fannin da suke aiki a kai. Wasu daga cikinsu sun haɗa da:

    Biology laboratory

    Wannan ɗakin gwaje-gwaje ana amfani da shi domin duba rayuwar halittu; misali ƙwayoyin cuta, ƙwayoyin halitta (cells), jini, ƙwayoyin halittar gano (genes), da sauransu. Ana amfani da na’urar microscope, petri dishes, slides da pipettes a irin wannan ɗaki.

    Chemistry laboratory

    A wannan ɗakin gwaje-gwaje ake gwajin sinadarai daban-daban. Akwai matakai na haɗa sinadarai, nazari a kan tasirinsu, da kuma gano siffofin sinadarai. Na’urori kamar burette, beaker, test tube, conical flask da bunsen burner suna nan sosai.

    Physics laboratory

    Wannan ɗaki na gwaje-gwaje yana ba da damar nazarin abubuwan da suka shafi makamashi, motsi, lantarki, haske da sauran siffofin kimiyya. Ana amfani da voltmeter, ammeter, galvanometer, multimeter, da prism.

    Medical laboratory

    Wannan ɗaki ne na nazarin jinin mutum, fitsari, ruwa a jiki, ƙwayoyin cuta, da kuma gano cututtuka. Ana amfani da centrifuge, microscope, test kits, da incubator a irin wannan ɗaki.

    Agricultural laboratory

    Shi ma fannin kimiyyar aikin gona yana da nasa ɗakin gwaje-gwajen kamar sauran fannoni na kimiyya. A irin wannan ɗaki ne ake gwajin ƙasa, ruwa, iri, da takin zamani domin ƙara yawan amfanin gona. Ana amfani da pH meter, soil test kits, da spectrophotometer.

    Computer ko ICT laboratory

    Wannan ɗaki ne shi ma da ake amfani da shi wajen koyar da ilimin kwamfuta da gwajin manhajoji (software) ko hardware (na’urorin computer). Ana amfani da kwamfutoci, manhajoji da network systems.

    PAC1200
    Computer ideal room

    Tarihin ɗakin gwaje-gwaje

    Tarihin ɗakin gwaje-gwaje yana da dogon zango, musamman a duniyar ilimi. A zamanin da, malaman kimiyya suna gudanar da bincikensu a gida ko cikin masallatai da coci. Wasu daga cikin shahararrun masana kimiyya kamar Ibn Sina, a addinin Musulunci, da Galileo Galilei a tsarin Renaissance sun gudanar da bincikensu a irin wannan yanayi.

    A ƙarni na 17 zuwa 19, ilimin kimiyya ya fara bunƙasa sosai, inda jami’o’i da cibiyoyin bincike suka fara samar da wuraren da ake gudanar da gwaje-gwaje bisa ƙa’ida. Wannan shi ne asalin samar da ɗakin gwaje-gwaje na zamani.

    A Najeriya, an fara ginawa ko samar da ɗakunan gwaje-gwaje na zamani ne a zamanin mulkin mallaka, musamman a makarantu, asibitoci da cibiyoyin bincike. Wasu daga cikin tsoffin cibiyoyin da aka kafa ɗakunan gwaje-gwaje sun haɗa da Nigerian Institute of Medical Research, da Ahmadu Bello University Zaria. Zuwa yau, ɗakunan gwaje-gwaje na da matuƙar muhimmanci wajen horar da ɗalibai, gano cututtuka da kuma tallafa wa masana’antu.

    Muhimmancin ɗakin gwaje-gwaje

    Ɗakin gwaje-gwaje yana da matuƙar amfani a rayuwa, musamman wajen tabbatar da gaskiya da inganci a fannonin ilimi da aikace-aikacen kimiyya.

    • Babban amfanin ɗakin gwaje-gwaje shi ne tallafa wa koyarwa da karatu. A makarantu da jami’o’i, ɗalibai suna koyo ta hanyar gani da gwadawa, ba kawai karanta littafi ba. Hakan yana taimaka wa fahimtar darusa da kuma cusa dabaru a zukatan ɗalibai.
    • Ɗakin gwaje-gwaje yana da matuƙar amfani wajen binciken kimiyya. A masana’antu da asibitoci, ana amfani da ɗakin gwaje-gwaje wajen gano sinadarai masu haɗari, gano cututtuka da ƙirƙirar magunguna. Bincike na asibiti da likitanci ba zai yiwu ba idan babu ɗakin gwaje-gwaje.
    • Bugu da ƙari, ɗakunan gwaje-gwaje suna taimakawa wajen samar da sabbin fasahohi da hanyoyin da za a inganta rayuwa. Misali, an fi gano maganin cututtuka kamar COVID-19 a ɗakunan gwaje-gwaje. Har ila yau, a fannin gona, ana amfani da ɗakunan gwaje-gwaje wajen kimanta irin ƙasa da takin zamani don ƙara yawan amfanin gona.

    A takaice, ɗakin gwaje-gwaje na haifar da cigaba a rayuwa, tattalin arziki, kiwon lafiya, da ilimi.

    Matsalolin ɗakin gwaje-gwaje a Najeriya

    A Najeriya, ɗakunan gwaje-gwaje suna fama da matsaloli masu yawa waɗanda ke hana su yin aiki yadda ya kamata.

    • Babbar matsala ita ce rashin kuɗi da rashin kayayyakin aiki. Yawancin makarantu da jami’o’i ba su da kayayyakin aiki na zamani. Ana amfani da kayan da suka tsufa, kuma wasu ba su da kayan aiki kwata-kwata.
    • Sauran matsaloli sun haɗa da rashin wutar lantarki da rashin kayan dijital kamar kwamfutoci da na’urorin zamani. Hakan yana haifar da tsaiko wajen gudanar da gwaje-gwaje na kimiyya, musamman na ICT da likitanci.
    • Ƙarancin horarwar ma’aikata da malamai ma wata matsala ce. Wasu ma’aikata da ke aiki a dakunan gwaje-gwaje ba su da cikakken horo, musamman a matakin makarantu na gaba da sakandare. Wannan yana rage ingancin koyarwa da amfanin ɗakin.
    • Lalacewa da haɗari ma na faruwa. Idan babu tsari da kayayyakin kariya, akwai haɗarin fashewar sinadarai, ƙonewa, ko fitar tiririn sinadarai masu cutarwa. Rashin tanadin kayan kariya kamar lab coat, gloves, da safety goggles yana barazana ga lafiyar ɗalibai da ma’aikata.
    • Rashin kulawa da na’urori na daga cikin manyan matsaloli. Wasu ɗakunan suna da na’urori masu tsada amma babu mai kula da su yadda ya kamata, wanda ke jawo su lalace ko su daina aiki.

    Hanyoyin magance matsalolin ɗakin gwaje-gwaje a Najeriya

    Don magance waɗannan matsaloli, akwai buƙatar ɗaukar dukkan matakai, wato na gaggawa da na dogon lokaci.

    • Na farko, ya zama dole gwamnati ta ƙara kashe kuɗi a fannin kayan aiki da gyaran ɗakunan gwaje-gwaje. Ya kamata a samar da sabbin kayan aiki da sabunta na da domin ɗalibai su koyi aiki da sabbin fasahohi.
    • Horar da malamai da ma’aikatan ɗakunan yana da matuƙar muhimmanci. Akwai buƙatar horar da su a kai a kai domin su fahimci sabbin hanyoyin amfani da na’urori da tsare-tsare masu aminci. Haka nan, jami’o’i da kwalejojin ilimi su ƙara ƙarfafa fannin koyar da “Laboratory Science Technology” da horar da sabbin ƙwararru.
    biologylab
    Dakin gwaje-gwaje na kimiyyar Biology.
    • Wutar lantarki da na’urorin lantarki ya kamata a tabbatar suna aiki a kowane ɗaki. Za a iya amfani da solar panel a wuraren da ba su da wuta mai ƙarfi.
    • Samar da tsarin kiyayewa da tsafta a dakin gwaje-gwaje ya zama wajibi. Hakan zai haɗa da tanadin kayan kariya, tsarin share wurare da cire sinadarai masu haɗari cikin tsari.
    • Haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu da ƙungiyoyin ƙasashen waje zai taimaka wajen kawo kayan aiki, horo, da tallafi. Akwai ƙungiyoyi kamar UNICEF, WHO da UNESCO da ke taimakawa ƙasashe masu tasowa wajen haɓaka ilimi da kimiyya.
    • Akwai buƙatar wayar da kai ga makarantu da gwamnati game da muhimmancin ɗakin gwaje-gwaje wajen haɓaka ilimi da fasaha a ƙasa. Idan aka mayar da hankali kan wannan fanni, zai taimaka wajen samar da ƙwararru masu fasaha da za su ciyar da Najeriya gaba.

    Kayayyaki da na’urorin ɗakin gwaje-gwaje

    • Beaker: Wannan roba ce ko gilashi da ake amfani da ita wajen auna ruwa ko sinadarai, haɗa su tare, ko ɗumama su a cikin ɗakin gwaje-gwaje.
    • Bunsen burner: Ana amfani da wannan na’ura domin samar da harshen wuta don ɗumama sinadarai ko ruwa. Ana haɗa ta da bututun gas.
    • Test tube: Wannan ƙaramin gilashi ne mai tsayi, ana amfani da shi wajen gudanar da ƙananan gwaje-gwaje da haɗa sinadarai ƙanana.
    • Filter paper: Takarda ce ta musamman da ake amfani da ita wajen tace sinadarai, domin raba ruwa daga tarkace ko ƙazanta.
    • Conical flask ko erlenmeyer flask: Gilasai ne, ana amfani da su wajen haɗa sinadarai da tafasa su ba tare da su zube ba.
    • Funnel: Ana amfani da funnel wajen sauƙaƙa zuba ruwa ko sinadarai daga babban abu zuwa ƙarami, ko a tace ruwa da filter paper.
    • Thermometer: Ana amfani da ita don auna yanayin zafin ruwa ko wani sinadari.
    • Balance: Na’ura ce da ake amfani da ita domin auna nauyin sinadarai ko wasu kayan gwaji domin daidaitawa.
    • Pipette: Wannan kayan aiki ne da ake amfani da shi don ɗaukar sinadari cikin adadi mai tsauri kuma daidai.
    • Burette: Kayan aiki ne da ake amfani da shi wajen sakin ruwa ko sinadari daidai-daidai a cikin gwajin titration.
    • Mortar & pestle: Ana amfani da su wajen niƙa sinadarai masu ƙarfi su koma gari ko su yi laushi.
    • Measuring cylinder: Gilasai ne masu sigar silinda da ake amfani da su wajen auna ruwan sinadarai daidai gwargwado.
    • Clamp stand: Wannan kayan aiki ne da ake amfani da shi don riƙe wasu kayan gwaji a tsaye, kamar su burette ko flask, domin su tsaya yadda ya kamata.
    • Watch glass: Karamin farantin gilashi ne da ake amfani da shi wajen duba sinadarai, ko barin ruwa ya bushe.
    • Wire gauze: Ana shimfiɗa wannan ƙaramar ragar ƙarfe a kan murhu ko kan harshen wuta domin a dora beaker ko flask, yana taimakawa wajen yaɗa zafi daidai da buƙata.
    • Desiccator: Wannan na’ura ce da ake amfani da ita wajen adana sinadarai masu bukatar a tsare su daga danshi.
    • Crucible & lid: Wannan ƙaramin kwano ne da murfi da ake amfani da su wajen tafasa sinadarai da zafi mai yawa.
    • Test tube rack: Wannan shi ne abin da ake amfani da shi don riƙe test tubes da tsayar da su tsaye, musamman lokacin aiki da su.

    Manazarta

    Josiah, O. F. (2022). Adequacy and effective utilization of laboratory equipment as predictors of secondary school students’ learning outcome in Edo North Senatorial District, Nigeria. International Journal of Social Relevance & Concern, 10(9), 31 – 41.

    Odachi, (2017). Impact of practical activities in chemistry laboratory exercises in schools in Eastern Nigeria. IDOSR Journal of Education and Scientific Research, 23, 59 – 67.

    Ebek, S. O. (2023). Availability and utilization of laboratory facilities and secondary school students’ academic achievement in Biology in Calabar Education Zone, Cross River State. International Journal of Science Education, 15, 13.

    Fasoye, T. E. (2018). Assessment of laboratory facilities, teachers’ and students’ involvement in basic science practical activities in junior secondary schools, Osun State, Nigeria. (Thesis). Obafemi Awolowo University.

    *** Tarihin Wallafa Maƙalar ***

    An kuma sabunta ta 16 August, 2025

    *** Sharuɗɗan Editoci ***

    Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

    Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

    Maƙalar ta amfanar?
    EAa

    You cannot copy content of this page

    ×