Skip to content

Dangantaka cikin Hausawa

Share |

Al’umma kalma ce da take nufin jama’a ko kabila da ke zaune a wuri daya tare da amfani da harshe da al’ada iri daya. Sannan yanayin zama kuma, ya danganci yadda mai gida yake zaune da iyalansa, kuma tsarin iyali shi ne ginshikin da aka gina al’ummar Hausa a kansa. Haka zalika a wani bangaren kuma, dangantaka kuma ta hada iyali daban-daban. Iyali ya kunshi dukkanin mutane da ke karkashin ko kulawar wani mutum. Don haka iyali sun kunshi maigida da matarsa ko matansa da ‘ya’yansa da jikokinsa da danginsa da duk ma wadansu wadanda ke zaune a karkashinsa ko karkashin ikonsa suna da dangantaka ko ba su da ita.

Dangantaka dake tsakanin al’umma

Dangin Bahaushe sun hada da dangin uwa misali kakanni, ‘ya’yan uwa, kannen uwa da sauransu, akwai kuma dangin uba misali yayye da kannen uba. ‘Yan uwan uwa mata da ‘yan uwan uba maza suna da cikakkiyar nasaba da rayuwar mutum tun daga haihuwa zuwa aure da kusan komai na rayuwarsa.

Kasancewar al’ummar Hausawa ba suna zaune ne kara zube ba. Hasali ma tun kafin zuwan addinin musulunci suna da nasu wasu tsararru da ingantattun hanyoyi da al’ada ta yarda da su kuma kowa ke kokarin ganin bin su don isar da zumunta.

Wannan cikakken tsari shi ne kashin bayan zumunta a tsakanin dangin malam Bahaushe. Dubi wadannan karin magana:

  1. Babban wa uba
  2. Dan uwa rabin jiki
  3. Naka sai naka
  4. Hannunka ba ya rubewa ka yanke kayar

Za a ga cewa Bahaushe ya sami kyakkyawar hujja ta dogaro da cewa dangi a wurinsa riga ce ta alfarma ta shiga taro da babu Wata kamarta.

  • “Babban wa Uba” na nuni da muhimmancin ladabi da girmama na gaba daga cikin iyali.
  • “Dan uwa rabin jiki” na nuna karfin zumunci da muhimmancin kyautata wa juna a cikin dangi.
  • “Naka sai naka” na nuna duk abin da zai ta so na taimako naka ne zai iya maka.
  • “Hannunka ba ya rubewa ka yanke kayar” na nuna komin lalacewar dan uwanka har abada dan uwanka ne ba abin da za ka yi ka fid da shi ya zama ba dan uwanka ba.

A tsari na al’ummar Bahaushe kowa da irin gudummawar da yake bayarwa dangane da harkokin rayuwa irin ta yau da kullum. Hakan ya sa dangi a tsarin zaman iyali ke haduwa domin bayar da tallafi ga ‘yan uwansu idan bukatar hakan ta taso. Misali bikin suna, shayi ko lokacin da ya sami kansa a cikin wani hali na kaka-ni-ka-yi.

Muhimmancin dangi ga al’ummar Hausawa bai tsaya kurum a nan ba, ya hada zamowarsa ginshiki kuma abin dogaro a lokutan da ake neman wani abu na alherin rayuwa misali aure, sana’a, muhalli. Kuma dangi babban bango ne don kariya daga dukkan barazana. Misali idan aka dubi aure, al’ummar Hausawa kan yi bincike a kan wanda za a aura wa da wanda za a aura daga garesu. Dalili kuwa Bahaushe na daraja dangi fiye da dukiya wannan ta sa Bahaushe na asali da wuya ya aurar da ‘yar sa ga bako wanda ba a san danginsa ba.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading