Skip to content

Danmasanin Kano

Gabatarwa

Alhaji Yusuf Maitama Sule, Ɗanmasanin Kano, malamin makaranta ne, ɗan siyasa sannan kuma basarake. Tabbas, Alhaji Yusuf Maimata Sule, Ɗanmasanin Kano, ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ciyar da ɗaiɗaikun mutane gaba har zuwa kan gwamnatin tarayya. Da shi aka yi fafutikar ƙwatar ‘yanci da kuma ganin yunƙurin tabbatar da haɗin kan ƙasa da ɗorewar zamanta a matsayin ƙasa guda.

Haihuwarsa

An haife Yusuf Maitama Sule a birnin Kano unguwar Yola, a shekara ta 1929. Wannan suna ‘Maitama’, ya samo asali ne daga Galadiman Kano Yusuf, wanda a lokacin da yake kan kujerar Galadiman Kano, an yi yaƙin da ya haifar da yawan amfani da makaman da aka sarrafa daga tama. (Wani sidanari ce da ake haɗa ƙarfe da ita). Saboda haka, sai aka riƙa kiran Galadiman da sunan Maitama. Da aka haifi Yusuf, sai ake masa laƙabi da wancan suna, shi ne sunansa ya zama Yusuf Maitama. Mahaifinsa kuma sunansa Sule.

Alhaji Yusuf Maitama Sule, Ɗanmasanin Kano.

Tsowarsa da karatunsa

Tun tasowar Yusuf Maitama Sule, ya fara karatun Alƙur’ani a makarantar Malam Rabi’u.

A shekarar 1937, Madawakin Kano Mahmudu ya saka Yusuf Maitama a makarantar Elimantare ta Shahuci (Shahuci Elementary School). A ƙa’idar karatun, ɗalibi kan shafe tsawon shekaru huɗu kafin ya kammala karatu a wannan mataki na elimantare. Amma ta ɓangaren Yusuf Maitama, ba haka aka yi ba, kasancewar shi ɗalibi mai kaifin basira, shekaru biyu ya yi a makarantar, sai aka ba shi dama ya rubuta jarabawa zuwa mataki na gaba kuma ya samu nasarar shiga makaranta ta gaba wato makarantar midil (middle school).

Ya shiga wannan makaranta a shekarar 1940, kuma cikin ƙanƙanen lokaci ya samu karɓuwa a gurin malamai da ɗalibai saboda ƙwazonsa da kuma son jama’a. Shi ne ɗalibin da ya fi kowa ƙwazo da hazaƙa a darasin Turanci da kuma na addini Musulunci. A wannan mataki na tsakiya; wato midil, ɗalibi zai yi karatu na tsawon shekaru biyar. A wannan matakin ma, kaifin basirar Maitama ta ba shi damar rubuta jarabawar zuwa makaranta ta gaba, bayan zaman shekara uku da ya yi a makarantar.

Maitama, ya shiga Kwalejin Kaduna (Kaduna College) a shekara ta 1943, lokacin yana da shekaru goma sha uku a duniya. Maitama, a zamansa na wannan makaranta ya shiga ƙungiyar wasan kwaikwayo, ƙungiyar da ya riƙe shugabancinta har na tsawon shekaru biyu. Shi ne ladanin makaranta a lokaci guda kuma mataimakin liman. Ya riƙe muƙamin mai unguwa (prefect). Yana daga cikin ɗaliban da aka riƙa ɗiba suna fita zuwa wasu garuruwa domin karantar da jama’a, a ƙarƙashin tsarin nan na yaƙi-da-jahilci.

A shekarar su ta fita, suka rubuta jarabawar kammala sikandire mai suna “Cambridge School Certificate Examination”. Amma cikin rashin sa’a, bai samu nasarar cin wannan jarabawa duka ba, ta yadda har zai samu fita zuwa Ingila don ƙaro karatu, ba wai domin ba shi da ƙoƙari ba. Ganin haka, sai malaminsa na Turanci, ya ba shi shawarar shiga Babbar kwalejin elimantaren horar da malamai da ke Zariya (Higher Elementary Teachers College, Zaria).

Yusuf ya shiga babbar kwalejin elimantaren horar da malamai da ke Zariya (Higher Elementary Teachers College, Zaria), a shekarar 1947. Shigar Maitama wannan makaranta, da yake ya ɗauki darasi daga abubuwan da suka gabata, saboda haka sai ya riƙe wuta har sai da ya fita da kyakkyawan sakamako daga wannan makaranta, wanda kuma hakan ce ta sa aka tura shi garin Kano domin zamowa malami a tsohuwar makarantarsa ta farko.

Gwagwarmaya da aiki

• Daga shekarar 1948 zuwa 1953, ya zama Malamin Makaranta a Makarantar Tsakiya ta Kano (Kano Middle School), wacce yanzu ta zama Kwalejin Rumfa (Rumfa College). Ya bayar da gagarumar gudunmawa da suka haɗa da, koyarwa a aji, kafa ƙungiyar wasan kwaikwayo ta makaranta, da sauransu.

• Shi ne Ɗanmajalisar wakilai ta tarayya, da ke wakiltar yankin Birnin Kano, a zamanin mulkin Turawa 1954.

• Ɗanmajalisar Wakilai ta Tarayya, a shekarar 1959 zuwa 1964, mai wakiltar yankin Dawakin Tofa.

• Ya sake yin a karo na biyu a kan wannan kujera daga shekarar 1964 zuwa 1966, da ƙuri’ar da yawanta ya kai 14,256, adadin da ya babshi damar yi wa abokin takararsa Alhaji Sani Kanta daga jama’iyyar adawa ta NEPU kayen raba gardama. Wanda shi ya samu ƙuri’ar da adadinta ya kai 1,237. Zamanin mulkin Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa.

• Ya riƙe muƙamin Ministan Ma’aikatar Tama, Ƙarafa da kuma Makamashi (Minister of Federal Ministry of Mining and Power), daga 1964 – 1966, a lokacin mulkin Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa.

• Jami’in Hulɗa da Jama’a na taron tsarin mulkin ƙasa na wucin-gadi (Ad-hoc Constitutional Public Relations Coordinator). Zamanin Mulkin Yakubu Gowon, 1966.

• Ya zama Kwamishina a Jahar Kano, a shekarar 1968. Kwamishinan ma’aikatar ƙananan hukumomi (commissioner, ministry for local government, Kano State), daga baya aka mayar da shi ma’aikatar gandun daji da ci gaban karkara (Ministry of forestry and community deevlopment), a ƙarshe kuma ya yi kwamishinan ma’aikatar yaɗa labarai, harkokin matasa, wasanni da kuma al’adu (ministry of information, youth, sport and culture). Zamanin mulkin Gwamnan Kano Audu Baƙo.

• Ya Ƙirƙiro dashen bishiyoyi, wanda aka yi a faɗin jahar Kano,  lunguna da saƙo-saƙo na faɗin tsohuwar jahar Kano, za a iya cin karo da bishiyoyi kamar maina/darbejiya, da kuma maɗaci.

• Ɗanmasani ne ƙirƙiro katafaren gidan namun daji na Kano (Kano Zoo).

• Ya zama shugaban Majalisar Harkokin Al’adu ta Najeriya, a shekarar 1972. Ya bayar da gagarumar gudunmawa kamar assasa taron shekara-shekara na bukukuwa da wasannin gargajiya (Annual National Festival of Art and Culture), wanda aka fara shi a garin Kaduna a cikin shekarar 1972. Sai kuma buƙatar samar da Hukumar Al’adu da Jagoranci ta Ƙasa (Ministry for Culture and National Guidance) da ya miƙa wa gwamnatin Najeriya a shekarar 1973, daga baya, gwamnati ta mayar da wannan majalisa ta zama reshen gwamnati, inda aka canja mata suna ya koma Majalisar Harkokin Al’adu ta Ƙasa (National Council for Art and Culture). A shekarar 1975, zamanin Mulkin Janar Yakubu Gowon.

• Shugaban riƙo (Part Time Chairman) na Majalisar Harkokin Al’adu ta Ƙasa (National Council for Art and Culture) a shekarar 1975. Kuma a lokaci guda, tabbataccen shugaba (full time chairman) na kwamatin shirye-shiryen halartar taron duniya karo na biyu, na bukukuwan wasannin gargajiya da al’adu na baƙaƙen fatar Afirka (Second World Black and African Festivals of Arts and Culture).

• Shi ya zamo Babban Kwamishinan Ma’aikatar Sauraron Ƙorafe-Ƙorafen Jama’a (Chief Commssioner Public Complaint Commssion), daga shekarar 1975 – 1978.

Ɗanmasanin Kano, Yusuf Maitama Sule tare da Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

• Shi ne Wakilin Najeriya na Dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya (Nigeri’s Permanent Representative to the United Nation), 1979 – 1983, a zamanin Mulkin Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari.

• Ya zama Ministan Ma’aikatar Jagoranci ta Ƙasa (Ministry of National Guidance), a shekarar 1983, wacce babbar manufarta ita ce, dasa halayen ɗa’a a zukatan ‘yan Najeriya, yaƙi da rashin ɗa’a, da kuma haɓɓaƙa kyawawan halaye. Duka dai a zamanin Mulkin Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari.

• Shugaban Hukumar Gudanarwar Cibiyar Nazarin Harkokin Siyasa (Chairman Governing Council for Centre for Democratic Studies),1992, a zamanin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

• Ya gudanar da wasan kwaikwayo ta gidan radiyon Kano. Shirin da ya samu karɓuwa sosai a wajen jama’ar jahar Kano har ta kai ga samun kyauta daga mai martaba sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero, a shekarar 1947.

• Ya gabatar da darasin koyar da Turanci ta gidan radio (English by Radio), domin ilimantar da jama’ar Kano, a shekarar 1948.

• Ya yi sanadin buɗe ɓangaren Hausa a jaridar Daily Commet ta Nmandi Azikwe. Ɓangaren da aka yi wa suna da Hantsi Leƙa Gidan Kowa, a shekarar 1948.

• Ya taimaka wajen kafa ƙungiyar malaman makaranta ta Arewa (Northern Teachers Association), 1949.

Muƙamin Ɗanmasanin Kano

A cikin shekarar 1954, bayan zamowar Alhaji Yusuf Maitama Sule, jami’in yaɗa labarai na hukumar gargajiya ta Kano, sarkin Kano Muhammadu Sanusi I, ya nemi Alhaji Yusuf Maitama Sule, da ya zaɓi dukkan sarautar da yake so a naɗa shi, ba tare da ya nema ba.

Bayan samun wannan tayi daga wajen sarki, sai ya nemi shawara daga Malam Ahmad Mettidan, wanda shi kuma a lokacin ma’aikaci ne a gidan radiyon tarayya (Nigerian Broadcasting Corporation). Inda ya ba ba shi shawara cewa, ya zaɓi sarautar Ɗanmasani, ita wannan sarauta asalinta daga Katsina ne. Akwai wani waliyyi daga cikin waliyyan Katsina guda huɗu ana kiran shi Wali Ɗanmasani, aikin sa a fadar Katsina shi ne jagorantar sarki da masarautar Katsina a kan al’amuran addini. Bayan rasuwar wannan waliyi kuma, sai sunan ya zama sarauta, aka naɗa ɗansa a kan wannan kujera, sannan aka ci gaba da kiransa da malam Ɗanmasani.

Tun daga 1984 zuwa 2017, Yusuf Maitama yake riƙe da sarautar, ya samu shekaru 63 yana riƙe da wannan sarauta. Ya yi aki tare da wanda ya naɗa shi, marigayi sarki Muhammadu Sanus I (1953 – 2017).

Gwagwarmayar siyasa da neman ‘yanci

A shekarar 1950, Alhaji Yusuf Maitama Sule, da Malam Bello Ijumu, suka kafa Ƙungiyar Siyasa ta NEPU. Wannan kuma ya biyo bayan tuntuɓarsa da Malam Bello Ijumu ya yi, a gidansu da ke Yola, kan dacewar samar da wata jama’iyyar siyasa a daidai wannan lokacin. Sannan kuma shi malam Bello Ijumu, wanda yake Bayarabe ne a ƙabila, kuma mazaunin Sabon Garin Kano, ya buƙaci Maitama da ya saka wa wannan jama’iyya suna. Shi kuma a nasa ɓangaren, Maitama sai ya ɗauko tsohon sunan rusasshiyar ƙungiyar siyasar tasu shi Malam Bello Ijumu, wato NEPA, ya cire harafin ƙarshe na A, ya maye gurbinsa da U.  Saboda haka sai sunan ya tashi daga NEPA mai ma’ana ta Northern Elements Progressive Association, ya koma NEPU da ma’ana ta Northern Elements Progressive Union. Jama’iyyar da daga baya ta zama cikakkiyar jama’iyyar adawa, wacce ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen kafuwar jamhuriya ta farko da kuma samun ‘yancin Najeriya daga hannun Turawa.

Takarkarun jama’iyyu siyasa

– Ya yi takarar Ɗanmajalisa Wakilai mai Wakiltar mazaɓar Birnin Kano, 1953 zuwa1966, bayan sun kafa jama’iyyar siyasa ta NEPU. Daga baya, aka mayar da shi jama’iyyar NPC, aka kuma ba shi takara cikin sa’a, Allah ya bashi nasara.

– A zaɓe na biyu na wannan jamhuriyya ta farko, ya sake tsayawa takarar Majalisar Wakilai ta tarayya, wannan karon kuma a mazaɓar Dawakin Tofa, nan ma cikin sa’a, ya samu nasara.

– Haka nan a shekarar 1949, ya sake tsayawa zaɓen a karon na uku, nan ma dai a matsayin ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Mazaɓar Dawakin Tofa. A wannan zaɓe ma ya sake samun nasara.

– A lokacin Jamhuriyya ta biyu 1978 zuwa 19853, Alhaji Yusuf Maitama Sule, ya shiga jama’iyyar NPN, jama’iyyar da ya tsaya neman takarar kujerar shugabancin ƙasa. Daga baya ya janye wa Alhaji Shehu Shagari.

– Ya shiga jama’iyyar NRC a shekarar 1992.

Ɗanmasanin Kano, a Tsakiya, Lokacin Ba Shi Digirin Girmamawa a Zamanin Mulkin Shugaba Buhari, a NDA Kaduna.

Siyasarsa ta Duniya

A zamanin shugabancin Firimiya Abubakar Tafawa Ɓalewa, Alhaji Yusuf Maitama, ya samu halartar taron da aka gabatar a garin Konakire (Conkery), ƙasar Gini (Gunea), a matsayin wakilin Firimiya Tafawa Ɓalewa. A wannan taro, ya yi gogayya da shugabanni irin su Kwame Nkruma na Ghana, Leopold Songhor na Senigal, da kuma Modibo Keita na Mali.

Ya kuma halarci taron Inuwar Afrika (All African Forum), wanda aka gabatar a cikin watan Juli (June) na shekarar 1960, a Adis Ababa.

Yana cikin waɗanda suka je Majalisar Ɗinkin Duniya ranar 2 ga watan Oktoba na shekarar 1960. Wato kwana ɗaya ke nan bayan samun ‘yancin kan ƙasa.

A zamanin mulkin Shehu Shagari (1979), Maitama ya wakilci Najeriya a Taron Tsarin Mulkin Ƙasar Zimbabuwe, wanda aka yi a Ɗakin Taro na Lankasta (Lancaster House), a garin Landan.

Kammalawa

Alhaji Yusuf Maitama Sule, Ɗanmasanin Kano. Haifaffen cikin Unguwar Yola ne, wacce ke tsakiyar ƙwaryar Birnin Kano. Mutum ne da Allah ya yi wa baiwa da kaifin basira, haƙuri, juriya, kawaici, gaskiya, riƙon amana, sadaukar da kai, da kuma fasaha da ƙwarewa wajen magana.

Ɗan siyasa ne shi a gida da wajen Najeriya. Ya bayar da gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan al’ummu, garuruwa, ƙasashe a faɗin duniya.

Manazarta

Abubakar A. T.  (2001). Maitama Sule Ɗanmasanin Kano. Ahmadu Bello University Press, Zaria-Nigeria.

Northern Nigerian Publishing Company Ltd. (1979). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Gaskiya Corporation, Zaria.

The NEWS (2015). In Pictures NDA honours Alani Akinrinade, Maitama Sule. An ciro a shekarar 2017, daga shafin: http://thenewsnigeria.com.ng/2015/09/in-pictures-nda-honours-alani-akinrinade-maitama-sule/

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×