Mawaƙi Dauda Kahutu wanda aka fi sani da Rarara, ya auri abokiyar aikinsa wadda aka fi sani da Aisha Humaira bayan shafe shekaru da dama suna gudanar da sana’ar waƙa tare. An tabbatar da cewa Dauda Kahutu Rarara yana ɗaukar nauyin siyawa duk namijin da matarsa ta haihu a garinsu rago ya yi hakika, kuma yana ɗaukar ragamar siyawa matasa da dama manyan motoci domin zuwa kudu neman abin da za su dogara da shi. Haka yana bayar da tallafin rabon abinci da abubuwan amfani da dama da ake rabawa a gidan mahifiyarsa domin taimaka masu ƙaramin ƙarfi.

Dauda Adamu Kahutu shi ne cikakken sunanansa. mawaƙi ne na Hausa da ya shahara a fagen waƙoƙin siyasa da sauran fannoni a Najeriya, musamman a Arewacin ƙasar. An san shi da salon waƙoƙin yabon shugabanni, kamfen da kuma waƙoƙin faɗakarwa. Rarara na ɗaya daga cikin fitattun wakilan mawaƙa masu tasiri a siyasar Najeriya tun daga shekarun 2015.
Haihuwarsa
An haifeshi a shekarar 1986 cikin jihar Katsina a wani ƙauye da ake kira Kahutu.
Karatunsa
Ya yi karatun Alƙur’ani a makarantar Almajiranci, wata hanyar gargajiya da Hausawa suke amfani da ita wurin koyon ilmin Alƙur’ani wato (ƙolanta). Sai dai bayanai da dama sun tabbata kan cewar bai yi zurfi a fanin karatun boko ba.
Rarara ya ce karatun almajiranci ya koya masa juriya, tawali’u, da ilimin addini, waɗanda suka taimaka masa a harkokin rayuwarsa. Har yanzu yana nuna alfahari da wannan tushe, yana mai cewa “ba ya jin kunyar cewa ya kasance almajiri domin rayuwar almajiranci ita ce rayuwar da ta gina shi”
Ƙabilarsa
Mawaƙin ya fi to cikin tsattson Hausawa kuma ya samu tarbiya daidai gwargwado. Haka kuma ya samu koyarwa addini da kuma al’ada.
Inkiyarsa
Rarara inkiya ce da ake yi masa ita a dalilin waƙa.
Sana’arsa ta waƙa
Rahotanni na nuna cewa ya fara waƙa tun yana matashi, inda ya riƙa gabatar da waƙoƙinsa a lokutan yin bukukuwa a garinsu. Ya kasance sananne ne a fagen waƙa musamman waƙoƙin siyasa.
Waƙoƙinsa
Rarara ya yi waƙoƙi da dama, ga kaɗan daga cikin fitattun waƙoƙunsa;
- Ƙwai Cikin Ƙaya
- Saraki Sai Allah
- Masu Gudu-su-Gudu
- Buhari ya Dawo
- Baba Buhari Doɗar
- Jahata Jahata Ce
- Kwana Darin Dallatu
- Kano ta Ganduje ce
- Ubban Abba Zama Daram!
- Malam Sha’aban Sharaɗa
- Jaagaba Ya Karɓi Ƙasa
- Gawuna Is Coming, da sauransu.
Salon waƙoƙinsa
Rarara na amfani da waƙoƙinsa don yin sharhi kan lamuran yau da kullum, musamman a lokacin zaɓe ko rikice-rikicen siyasa. Daga cikin salonsa na waƙa ya ƙunshi:
- Yabon shugabanni (masu mulki da ‘yan siyasa).
- Sanya waƙoƙi cikin tsarin sarrafa harshen Hausa.
- Amfani da karin magana da harshe mai sauƙi.
- Sarrafa kalmomi masu cike da jan hankali.
- Tattara saƙonni cikin sigar waƙa masu cike da isar da saƙon halin da ƙasa take ciki.
Sana’arsa ta noma
Bayan waƙa kuma yana taɓa kasuwanci da abin da ya shafi noma. Musamman noma, domin ya bayyana hakan a wasu hirarrakin da aka yi da shi a shafukan sada zumunta da kafofin yaɗa labarai. Yana bayyana kasancewarsa manomi cikin alfahari da kuma tsagwaran jarumta.
Noma na ɗaya daga cikin harkokin da yake alfahari da su, kuma yana ƙoƙarin amfani da damar da yake da ita don bunƙasa noma a yankin Arewa, musamman wajen ƙarfafawa matasa gwiwa kan su rungumi noma a matsayin sana’a.
Abubuwan da yake nomawa
Rarara ya shafe shekaru yana gudanar da harkar noma. Yana noma kayan abinci kamar su masara, gero, dawa, shinkafa, da wasu kayan marmari.
Dalilinsa na zaɓar noma
A cewarsa, noma wata hanya ce ta bunƙasa tattalin arziƙin gida da kasa baki ɗaya. Duk da cewa yana da farin jini a fagen waƙa da siyasa, Rarara yana ƙoƙarin zama abar ko yi ga matasa wajen nuna cewa babu abin kunya a harkar noma. Har ma ya taɓa cewa: “Idan duk mawaƙanmu da ’yan siyasa za su riƙa noma, da Najeriya za ta ci gaba sosai.”
Shahararsa
Rarara ya shahara ne adalilin rubutu waƙa da kuma rairata cikin salo da gwaninta da balagar harshe. Sunansa ya soma ƙauri ne a babban zaɓen Najeriya na shekarar 2015, lokacin da yake rera waƙoƙi da dama ga Muhammadu Buhari da kuma shugabancin Goodluck Jonathan a galibin waƙoƙin nasa.
Ya soma ta hanyar gabatar da waƙoƙi masu nishaɗantarwa da tasiri a fannin siyasa. Waƙar da ta fi ba shi suna ita ce wadda ya rera lokacin kamfen na shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2015. Waƙoƙin sa sun kasance wata hanya ta yaɗa manufofin shugabanni da kuma ƙarfafa gwiwar magoya baya. Shahararsa da kuma gogewarsa a waƙa ya sanya har wasu suke kwatantashi da marigari Shata a fagen waƙa saboda ƙwarewarsa.
Baiwarsa
Mawaƙin yana da baiwar abubuwa da yawa waɗanda suka taimaka wurin fito da ƙimar sana’arsa. Akwai kuma dabarar yin bincike kafin ya gudanar da waƙa wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa wurin fito da shi waye. Daga cikinsu akwai:
- Balagar harshe
- Hikima da basira
- Kaifin tunani
Rawar da Rarara ya taka
Rarara ya taka muhimmiyar rawa wajen sadarwa tsakanin shugabanni da talakawa, musamman a lokacin da ake buktatar ƙarfafa goyon bayan jama’a.
Waƙoƙinsa sun zama wani tsani na jawo hankalin dubban al’umma musamman a kafofin yaɗa labarai kamar YouTube, Facebook da kuma Radio.
A cewar masana kimiyyar al’adu, irin waƙoƙin Rarara na ɗaya daga cikin hanyoyin da ke sauƙaƙa fahimtar manufofin gwamnati da kuma jan hankalin jama’a zuwa ga kishin ƙasa.
Iyalansa
Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara yana da matan aure guda huɗu, sai dai kasancewar matansa biyu su ne sanannu sakammakon tu’amali da yanar gizo. Har zuwa yanzu kuma babu wata sanarwa da ta iyakance ‘ya’yansa, amma yana da yara maza da mata daidai gwargwado. Matansa sun haɗar da,
Zainab wadda ta kasance uwargida. Akwai Ummi da Sadiya sai kuma shahararriyar mawaƙiyar nan wadda ta kasance abokiyar aikinsa da ba su jima da yin aure ba wato Aisha Humairah.
Abokansa
Har zuwa yanzu babu mutum ɗaya da akan iya ɗaga a kirashi da abokinsa kai tsaye, sai dai kuma akwai kyakkyawar alaƙa tsakaninsa da wasu mawaƙa, duk da cewa akwai rashin fahimta tsakaninsa da wasu daga cikinsu kamar irin su Naziru Sarkin waƙa. Daga cikin abokan da suke da fahimta tsakaninsu akwai;
- Adam A. Zango
- Babanchinedo
- Ali Jita.
Halayensa
A wata hira da aka yi da mai ɗakinsa Aisha Humaira ta tabbatar da cewa, mawaƙin ya kasance mai ɗabi’ar nan da idan ya sa kansa yin abu to duk yadda kake da shi ba zaka hanashi aikatawa ba. Musamman abin da ya shafi aikin taimako da kyautatawa.
Taimako
Rarara ya shahara wurin taimako baya barin abokansa cikin matsala ko damuwa, musamman waɗanda ke aiki tare da shi ko cikin ƙungiyar mawaƙa. Ana yawan jin labarai na yadda yake ɗaukar nauyin abokai a harkar aure, sana’a ko jinya.
Zumuncinsa
A taruka da bukukuwa, Rarara yakan nuna zumunci da girmamawa ga abokansa. Wannan yana ƙarfafa haɗin kai da amintaka a tsakaninsu. Yana ɗaukar abokansa kamar iyalinsa yana zuwa shagulgulensu, kuma yana gayyatarsu a na shi.
Haɗin kai wurin gudanar da aiki
A cikin harkar waƙa da siyasa, yana da abokai da ya fi ɗauka a matsayin abokan hulɗa ko haɗin gwiwa. Wasu daga cikinsu suna aikin raira waƙoƙinsa, wasu kuma aikinsu fassara da gyaran baituka. Yana daga cikin tagawar mawaƙan nan ‘yan (13-13) kusan ma shi ne jagoran tafiyar.
Aiyyukansa na jin ƙai
- Mutane sun bayyana cewa Rarara ya taimaka musu wajen biyan kuɗin asibiti da jinyar wasu cututtuka masu tsada kamar tiyata da magunguna.
- Rarara ya gina gidaje da masallatai ga al’ummar garinsu.
- Ya kafa gidauniyoyi da ƙungiyoyi domin tallafa wa matasa, musamman waɗanda ke da burin zama mawaƙa ko ‘yan wasan kwaikwayo. Ya yi fice wajen ɗaukar nauyin ɗaukar waƙoƙin su, bidiyo, da tallata su a kafafen sada zumunta.
- A lokutan bukukuwa kamar azumin Ramadan ko Sallah, Rarara yana raba kayan abinci, tufafi, da kuɗaɗe ga marasa ƙarfi a gidansu, wanda yake gudana ta hannun mahaifiyarsa. wasu lokuta, yana ba da tallafin jari ga mata da matasa domin su dogara da kansu.
- Rarara ya taimaka wajen gina masallatai da makarantu a garuruwan da ya fito, wanda hakan ya sauƙaƙawa mutanen garuruwan samun ilimi musamman na addini ga yara da matasa.
Ƙalubalensa
Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ya fuskanci ƙalubale da dama, musamman a harkar siyasa da rera waƙoƙi masu ɗauke da ra’ayoyi na musamman:
- Shekarar 2024, ya fuskanci matsalar rufe shafinsa na dandalin sada zumunta ta (Facebook), bayan ya yiwa shugaban ƙasa mai ci a yanzu waƙa mai taken:
“Tinubu ya ƙara keɓance talauci da rashin tsaro”.
Bisa wannan dalili mutane suka rufar masa, har ta kai shi ga rasa shafinsa na Facebook mai mabiya sama da miliyan ɗaya.
- Wasu na sukar salon waƙarsa da cewa tana haifar da rarrabuwar kai, musamman lokacin da ya fi mayar da hankali kan jam’iyya ɗaya ko mutum ɗaya.
- Ya fuskanci barazana da tashin hankali a lokacin da aka sace mahaifiyarsa, wadda ta yi kwanaki 20 a hannun masu garkuwa da mutane.
Nasararsa
- Mawaƙin ya kasance sananne ne a fagen waƙa musamman waƙoƙin siyasa. Wanda hakan ya ba shi damar taka matakan nasarar rayuwa da yawa, ya kuma samu damammaki wurin gudanar da lamuransa.
- Ya kafa Rarara Multimedia Ltd, kamfani da ke samar da waƙoƙi da shirye-shiryen nishaɗi.
- Ya yi ƙaurin suna a babban zaɓen Najeriya na shekarar 2015, lokacin da yake rera waƙoƙi da dama ga Muhammadu Buhari da kuma adawa da shugabancin Goodluck Jonathan a galibin wakokin nasa.
- A watan satumba na shekarar 2020, Rarara ya nemi gudummuwa daga masoyan Muhammadu Buhari, da a tura masa Naira dubu dai dai (1,000) domin sakin bidiyon minti biyu (2) na yabon Muhammadu Buhari, cikin kasa da awanni arba’in da takwas (48), ya karbi Naira miliyan hamsin da bakwai (57) don sakin wakar da ya yabi Muhammadu Buhari.
- Shugaban ƙasar Najeriya ya yi masa kyaututtukan da dama.
- Wasu daga cikin gwamnonin ƙasar Najeriya sun yi masa kyautuka.
- Ya samu karramawa daban-daban daga kungiyoyin al’adu da na matasa, ciki har da sarauta ta girmamawa a wasu yankuna na Arewacin Najeriya. Haka kuma, an yaba masa da kafa kungiya wadda ke tallafawa matasa wajen raya waka da fasaha.
- Ya rike muƙamin Daraktan Yada Labarai na Kamfen a jam’iyyar APC.
- A ranar 5-7-2025 ya yi auran yaransa guda takwas, waɗanda suka kasance ma’aikata a kamfaninsa na waƙa kuma shi ya ɗauki nauyin komai na bikin.
Manazarta
BBC Hausa. (2020). Dauda Kahutu Rarara ya bayyanawa duniya wasu ayyukansa na taimako. BBC Hausa.
Daily Interest Hausa. (2022, December 15). Tarihin Dauda Kahutu Rarara.YouTube.
Dauda kahutu rarara on Apple Music. (n.d.). Apple Music – Web Player.
Premium Times. (2022). Rarara’s philanthropy beyond politics. Premium Times.
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.