Buga maƙala a Bakandamiya Encyclopaedia yana bin matakai da dama kamar haka:
Bincike da rubutun maƙala
Bakandamiya na samun maƙalu ta hanyoyi guda biyu: daga marubuta da editocin Bakandandamiya, sai kuma marubuta na wajen Bakandamiya waɗanda suke aiko mana da maƙalu don ba da gudummawa.
Hanyoyin tantance maƙala
Bayan marubuci ya kammala rubutun maƙala, sai ya ɗora ta a nan. Akwai buƙatar yin rajista kafin a iya ɗorawa. Da zarar an ɗora, abu na farko shi ne, editocinmu masu tantance bayanai da alƙaluma, wato fact checkers, za su duba. Idan maƙalar ta wuce wannan mataki, za a miƙa ta ga editocinmu masu duba tsarin rubutu da nahawu, wato language editors. Matakin karshe shi ne inda masu tsare-tsaren rubutu da saka hotuna za su yi aiki akai don buga maƙalar.
Waɗannan matakai da muka lissafa na buga maƙala suna iya ɗaukan daga sati ɗaya zuwa wata ɗaya kafin a kammala aikin buga maƙala.
Bayan mun buga maƙala, idan kuma har an ga wani kuskure a cikinta, to a tuntuɓe mu. Za mu sake yin bincike akai sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.
Rashin amicewa da maƙala
Idan har maƙala ba ta samu karɓuwa ba, ko kuma ta na buƙatar a sake wani babban aiki a kanta, to editocinmu za su tuntuɓi marubucin ta imel da ya aiko da maƙalar.
Muna maraba da maƙalunku da shawarwarinku da duk wani abu da zai taimaka wajen inganta aikin Bakandamiya Encyclopaedia.
Mun gode.