Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu da kyautata.
Yana daga hikimar Allah Madaukakin Sarki fifita wasu mutane akan wasu, Ya kuma fifita wasu wurare akan wasu, Ya kuma fifita wasu watanni akan wasu, haka nan kuma ya fifita wasu ranaku akan wasu. Daga cikin watannin da Allah Ya fifita akan sauran watanni shine watan Ramadan mai albarka.
Watan Ramadan yana da falala masu yawa wanda ya kebanta da su kan sauran watanni. Ga kadan daga cikin cikinsu:
An saukar da Al-Kur’ani a watan Ramadan
Allah Ya ce: “Watan Ramalãna ne wanda aka saukar da Alƙur’ãni a cikinsa yana shiriya ga mutãne da hujjõji bayyanannu daga shiriya da rarrabawa”. (Suratul Bakara, aya ta: 185).
Azumin watan Ramadan yana kara taƙawa
Allah Ya ce: “Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda su ka gabace ku, tsammãninku, zã ku yi taƙawa”. (Suratul Bakara, aya ta 183)
A watan Ramadan a na bude kofofin Aljannah, a na rufe kofofin wuta, kana a na daure shaidanu
An karbo daga Abu-Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: ‘Yayin da watan Ramadan ya tsaya, sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Hakika Ramadan ya zo muku, wata ne mai albarka, (wanda) Allah Ya wajabta muku azumtar sa. Ana bude kofofin Aljanna a cikinsa, kuma ana rufe kofofin wuta a cikinsa, ana kuma daure shaidanu a cikinsa. A cikinsa akwai wani dare wanda ya fi dare dubu, duk wanda aka haramtawa alkhairinsa, toh hakika ya haramtu”’. Imam Ahmad da Nasa’I ne suka rawaito wannan Hadisi.
Azumin watan Ramadan yana kankare zunubai
Daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: ‘Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Salloli biyar, daga Juma’a zuwa Juma’a, da kuma Ramadana zuwa Ramadana, suna kankare abin da ke tsakaninsu, idan an nisanci manyan zunubai”’. Muslim ne ya ruwaito shi.
A wani Hadisin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Wanda ya yi azumin watan Ramadan, yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Watan Ramadan wata ne da Allah yake ‘yanta bayinsa daga wuta
An karbo daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: ‘Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Idan daren farko na Ramadan ya kasance, akan ɗaure shedanu da aljanu masu taurin kai, kuma akan rufe ƙofofin Wuta, ba a buɗe koda ƙofa ɗaya daga cikinsu, kuma akan buɗe ƙofofin Aljanna, ba a rufe koda guda ɗaya daga cikinsu. Sai mai shela ya yi kira: Ya mai neman alheri ka kusanto. Ya mai neman sharri, ka taƙaita. Kuma Allah yana da waɗanda yake ‘yantawa daga shiga Wuta, wannan kuma a cikin kowane dare”. Imam Ahmad da Tirmizi da Nasa’I da Ibn Majah ne suka rawaito Hadisin.
Aikin Umrah a cikin watan Ramadan ana ninninka masa lada, har ya kai ladan aikin Hajji
Daga Abdullahi Bin Abbas (R.A), Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Umrah a cikin Ramadan tana daidai da aikin Hajji, ko (tana daidai da) Hajji tare da ni”. Buhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Malamai sun yi bayani cewa wannan Hadisin yana nuni kan umrah a Ramadan tana daidai da aikin hajji a lada ne, ba wai umrar tana zama madadin Hajji na farilla ba. Duk wanda bai taba yin aikin Hajji ba, to in ya yi Umrah a cikin watan Rahamada ba za ta dauke masa aikin Hajji ba.
Kebantar watan Ramadan da sallar Tarawihi
Watan Ramadan ya kebanta da sallar tarawihi wadanda suke da falaloli masu yawa (dukkan Malamai sun hadu akan sunnah ne yin su)
Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Wanda ya yi tsayuwar sallah a watan Ramadan, yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito Hadisin.
Imam An-Nawawi yace: “Fadin Manzon Allah S.A.W (Wanda ya yi tsayuwar Ramadan) wannan sigar tana nuna kwadaitarwa da kuma (nuna yin sallolin) mustahabbi ne, ba wajibi ba ne. Kuma Malamai sun hadu akan tsayuwar Ramadan (sallolin tarawihi) ba wajibi ba ne, mustahabbi ne”.
A cikin watan Ramadan akwai daren lailatul ƙadri wanda ya fi dare dubu daraja da falala
Allah Yace: “Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi (Alƙur’ãni) a cikin Lailatul ƙadari (daren daraja). To, me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul Ƙadari? Lailatul Ƙadari mafi alheri ne daga wasu watanni dubu”. (Suratul Kadri, aya ta 1 – 3).
Imam Al-Baghawi yace: “Ma’anar wannan aya itace: Aiki nagari a cikin lailatul Kadiri ya fi alheri kan ayyuka a dare dubu in an cire lailatul Kadiri a cikinsu”.
Ya tabbata a Hadisi Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Wanda ya yi tsayuwar daren lailatul Kadiri, yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito Hadisin.
Watan Ramadan wata ne na ciyarwa da kyauta da sadaka
An karbo daga Abdullahi Ibn Abbas Allah ya yarda da shi, ya ce: “Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance ya fi dukkan mutane kyauta, kuma ya kasance lokacin da yafi kyauta shi ne a cikin Ramadan, lokacin da Mala’ika Jibrilu yake haduwa da shi. Kuma mala’ika Jibrilu ya kan hadu da shi a kowane dare a cikin Ramadan, sai ya yi bitar Al-kur’ani tare da shi. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya fi iska mai kadawa alheri”. Buhari da Musulim ne suka rawaito Hadisin.
Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Duk wanda ya ciyar da mai azumi abin buda baki, to yana da lada kwatankwacin ladan mai azumin, ba tare da an rage wa mai azumin ladan sa ba”. Imam Ahmad da Tirmizi da Ibn Majah ne suka rawaito shi.
Yin itikafi a watan Ramadan
An karbo daga Nana Aisha Allah ya yarda da ita, ta ce: “Annabi (tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi) ya kasance yana itikafi a kwanaki goman karshe na Ramadan har Allah Ya dauki ran shi, sa’an nan sai matansa suka yi itikafi bayan sa”. Buhari da Muslim ne suka rawaito wannan Hadisi.
Wadannan a takaice su ne kadan daga cikin falalar azumin watan Ramadan. Allah Ya karba mana ayyukanmu a cikin watan, Ya sa muna cikin yantattun bayinsa, amin.